MAKAUNIYA CE

By Jiddasmapi

17.9K 991 101

Ta mak'ance ta dalilinshi Amma baisan dahakan ba, ya wulak'anta ta, anci mutuncinta a gidansu.. More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
page 35
page 36
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
Completed✔

page 20

407 24 6
By Jiddasmapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 20...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

"Yana fad'in haka yajuya yabar gidan gaba d'aya, zuciyarshi a cunkushe yarasa me zaiyi yanzu, Asibiti ya nufa wajen Minal"

Daddy da duk haushi yake ji yasa ya tashi a tsawace yace "haba Hajiya meyasa zaku baiwa wannan dak'ik'iyar matar guba tasawa Minal a abinci, yanzu baga irinta ba, nasan halin Bilal idan yace zaiyi Abu to babu Wanda ya isa ya sashi, gashi kun jawo yafasa Auren Afrah, wannan ai bala'i ne"

Hajiya babbace tace "dakata Umar, karka sake kace zaka d'aura mana dukkan laifi, kai me ze hana ka zuba mata, sai mune zaka baiwa, kuma yanzu kana mana tsawa, ai idan yasan wata to besan wata ba, Dan yaga nayi shiru? To wallahi be isa ba saiya Auri Afrah koda boka koda Malam"
Tana gama fad'an haka taja hannun Afrah fuuuuu wacce take ta kuka sai d'aki.

Sun bar Daddy tsaye baki bud'e yarasa me yake ciki, sallamar 'yan sanda ne ya katseshi daga tunani, DPO ne yace "Alh munzo muyi bincike akan kisan kan da akayi"

Azuciye Daddy yajuya yace "get out from my Room!!!"

DPO ne yace "kamar yaya? Akan me zamu Fita? Ai sai munyi binciken da aka turamu"

Daddy ne yace "to bata mutu ba, kuyi abinda zakuyi, idan kunga dama Ku bincika har cikin kwalban drinks"
Yana fad'in haka yabar musu wajen, cikin jin haushin su Hajiya Babba sun b'ata mishi plan"

"Bilal yana zuwa Asibiti, yawuce d'akin da aka kwantar da Minal, yana shiga yaga ansa mata uniform na patients, blue, kanta babu d'ankwali, hakan yasa gashinta ya bazu, akan gadon, fuskarta tayi fayau, idanunta a rufe, karasawa yayi kan gadon da take, d'ankwalinta ya d'auko ya d'ago kanta a hankali, yad'aura mata, a hankali yakara maidata, kura mata ido yayi, yanajin tausayinta a kasan zuciyarshi, doctor ne ya turo kofar yashigo"

Doctor yace "Bilal ka samo ruwan sanyi da towel ka goge mata jikinta"

Bilal yayi shiru daga baya yace "doctor babu mata ne wad'an da zasuyi mata hakan?"

Doctor yace "malam Bilal ita fa matarka ce, me zai hanaka yimata hakan?"

Bilal ne yace "okay doctor zanyi mata"

"Fita doctor yayi"

"Bilal ne yamik'e tareda d'ibo ruwan sanyi acikin wata 'yar roba da farin towel, zuwa inda take yayi, ya zauna, ya rasa ta ina ma zai fara, saida yad'an ja lokaci kafin ya d'agata ya fara cire mata uniform d'in, bayan yacire mata ne yasa towel d'in a ruwa ya fara goge mata jikinta a hankali, yana gamawa ya shafa mata wani lotion me dad'in kamshi, ya mayar mata da kayanta ya kara kwantar da ita, tareda rufeta da bargo"

"Mayar da robar yayi da towel d'in, yazo ya zauna kusa da ita yariko hannunta yana murzawa a hankali, tausayinta yakeji har cikin zuciyarshi, cire bargon yayi tareda hawa gadon shima ya kwanta a gefenta, yaja bargon ya rufa musu, a haka har bacci ya d'auke shi"

"Doctor ne yashigo d'akin da niyan yimata wasu Allurori, ganin Bilal yayi kwance a kan gadon, dariya yayi, a fili yafurta " Allah ya shiryeka Bilal"

"Daddy yau yana cikin bak'in ciki, wayarshi ma ya kashe, Dan bayason damuwa, Yarasa wani shawara zai bawa kanshi, tunawa yayi da Alhaji Nura, da sauri ya d'auko wayarshi ya kunna tareda neman numbar Alhaji Nura"

Yace "Hello Alhaji Nura kana inane?"

Ta d'ayan b'angaren akace "ina Company ne Alhaji lafiya?"

Daddy yace "okay ina son ganinka yanzu a Farm house, katse wayar yayi ya nufi parking space, driver ne yaganshi yace " Alhaji tafiya ne? "

Daddy ne yaja tsaki yace "Aa ba tafiya bane gudu ne"

"Shiga motar yayi yafice da mugun speed".

"Yana zuwa farm house, yad'an zauna yana jiran Alhaji Nura, ranshi ne yafara b'aci sosai, wayanshi ya d'auko tareda lalub'o numbar Alhaji Nura cikin fad'a, yace "zakazo ne ko bazakazo ba?"

Alhaji Nura yace "gani dab da k'ofa ranka shi dad'e"

Motarshi ne yadanno kai, cikin farm house, da sauri ya karasa inda Daddy yake yanata kai kawo.

"Lafiya Alhaji?"

Daddy yace "ina kaga lafiya, Asirinmu ya Tonu awajen Bilal, ji nake kamar in kashe Hajiya babba, wallahi yau da ace Hajiya ba ita ta haifeni ba da saina kasheta da hannun"

Alhaji Nura yace "me ya faru Alhaji kamin bayani yanda zan game"

Daddy yace "ina gubar danace maka yau zan baiwa Hajiya babba tasawa Minal a abinci?, shinefa taje takaiwa wata dak'ik'iyar mata, gashi matar ta tona mana Asiri, kuma Bilal ya sallameta da mak'udan kud'ad'e"

Alhaji Nura yace "shine kake tada hankalinka? Inda kayi kuskure shine, daka nuna gaskiyar Hajiya a idonshi, yanzu abinda zakayi  Asibiti zakaje ka samu Bilal, ka nuna mishi cewar Hajiya babba da Afrah sunyi kuskure, kaga daganan saika rab'e dashi ka kwashi dukiya nima a d'anmin nawa rabon"

Daddy ne yace "Shiyasa nake son inyi shawara dakai, sabida kanada basira d
Sosai, yana fad'in haka yashige mota sai Asibiti"

Alhaji Nura ne yayi dariya yace "ita rake dama bata zubar da ruwa Dan kanta, sai an matseta tukun, zakasan kana Neman shawara a wajen Alhaji Nura"

"Daddy yana zuwa Asibiti yaga Bilal kwance a gado d'aya da wannan Makauniyar, abin ya matukar b'ata mishi rai, da sauri ya karasa inda suke kwance, lek'awa yayi yaga duk suna bacci, a hankali cikin sand'a yaje wajen ruwan da aka d'aura mata, tareda kara gudun ruwan sosai tsabar mugunta, sand'a yake yanason yabar d'akin, daidai bakin kofa ya tsinto muryar Bilal yana cewa.

"Daddy me kazoyi a nan?"

Jikin Daddy ne yafara Rawa cikin in ina yace "Am...am dama nazo naduba jikkn nata ne kuma naga duk nuna bacci shine nace bari in d'an....Bilal ne ya katseshi dacewa "ai jikin natama da sauk'i, saura kawai ta farfad'o"

Daddy yace "to..to Allah yakara mana sauki gaba d'aya"

Bilal yace "Ameen"

Daddy ne yafita a d'akin.

Bilal yajuya yana kallon Minal, shafa fuskarta yayi a hankali yafurta "sleeping Beauty"
Sauka yayi akan gadon tareda rufa mata bargon"

_washe gari_

"Umma ce da Madina sukazo Asibitin, idanun Umma duk sun kumbura tsabar kuka, sakamakon Fad'a musu da akayi cewar Bilal ne yayiwa Minal duka har Asibiti"

Suna shiga Bilal yaga Umma, kallo d'aya yayi mata yagano akwai alak'a tsakaninta da Minal, Dan akwai kama sosai, d'an duk'awa yayi yace "sannu da zuwa Umma"

Umma ce tace "dakata!!! da gani nasan Kaine Bilal, meyasa zakayiwa 'yata wannan dukar? Kaika haifeta ne? Baka ganin rauni datake d'auke dashi? Minal fa Makauniya ce, bakada tausayi ne? Allah ya isa tsakanina dakai tunda kake cutar da 'yata, ai an fad'amin komai, an fad'amin duk abinda kakeyi mata"

"Duk'ar dakai Bilal yayi yana bata hakuri"

Ko sauraronshi Umma batayi ba, Ranta ya b'aci sosai, sai matsifa take.

Zama tayi a gefen Minal tana kuka sosai.
Madina ce take lallab'ata.

"Bilal fita yayi a d'akin, yaje cikin Asibiti, yazauna, tagumi yayi yana tunanin yanda rayuwarshi take tafiya, kwata kwata babu jin d'adi babu kwanciyar hankali, ita Minal da a 'yan kwanakin nan idan yaga fuskarta yana samun nutsuwa da farin ciki ga mahaifiyarta tazo dawata maganar"

Hajiya babba ce da Afrah a d'aki Afrah tana ta kuka wai Bilal ya fasa Aurenta, Hajiya babba ce taketa lallab'ata Amma taki tayi shiru, ran Hajiya babba ne ya b'aci.

Tace "Zakiyi shirune ko saina koreki a d'akin nan? Haba Afrah ya zaki kaskantar da kanji awajen namiji kiyita rusa uban kuka? Koda shike bazan hanaki kuka ba, wata kilama idan kina kukan zaki d'an rame, ko kyayi fasali  kila ya yadda ya Aureki, Amma kin aje jiki kamar drom, wazai yadda ya Aureki?"

Afrah ce tace "haba Hajiya babba, ya zakice haka? Kina ganin yanda yake nuna yafison wancan blind girl d'in a kaina"

Hajiya tace "Afrah basai kin zageni da turanci zansan ranki ya b'aci ba, kifad'a da Hausa ma yanda zanji me kikace da sauk'i"

Afrah tace "Hajiya Blind girl fa nace, kuma yana nufin Makauniya"

"To ai saiki fad'a da Hausa yanda zan gane, yanzu ki kwantar da hankalinki, ni Salamatu nace saikin Auri Bilal"

"Bilal duban agogo yayi yaga lokaci yaja sosai, tashi yayi zuwa d'akin, yana zuwa yaga drip na Minal ya kare, a zuciyarshi yace.
Yaushe akasa mata ruwan gashi harya kare"

"Yana kashe drip d'in yayi tunanin Minal ta gaji da kwanciyar, zuwa yayi wajenta yana kokarin 'dagata"

Da sauri Umma ta ajiye butar data fito dashi a band'aki, tace "idan ka tab'a jikin 'yata Allah ya isa ban yafeba"

"Bilal ne ya tsaya cak ko motsi be kara ba".

_✔ote & Comment_

Jiddah S Mapi

Continue Reading

You'll Also Like

158K 12.6K 21
"Why the fuck you let him touch you!!!"he growled while punching the wall behind me 'I am so scared right now what if he hit me like my father did to...
187K 37.8K 56
Becca Belfort i Haze Connors, choć przez swoich znajomych zmuszani do spędzania razem czasu całą paczką, od dawna się nie znoszą. Dogryzają sobie prz...
400K 38.3K 32
She is shy He is outspoken She is clumsy He is graceful She is innocent He is cunning She is broken He is perfect or is he? . . . . . . . . JI...
1.8M 140K 63
"ရှင်သန်ခြင်းနဲ့သေဆုံးခြင်းကြား အလွှာပါးပါးလေးကိုဖြတ်ကျော်ခါနီးမှာမှ ငါမောင့်ကိုစွန့်လွှတ်တတ်ဖို့ သင်ယူနိုင်ခဲ့တယ်၊ လူတွေက သံသရာမှာ ရေစက်ရယ်၊ဝဋ်ကြွေး...