ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

114K 15.7K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
47
48
49
50 End

46

1.7K 318 43
By KhadeejaCandy

Ganin Hajiya Karima yasa Sadam mikewa tsaye ya bata kujerar ta zauna, sai dai ba ta zauna a kujerar ba ta zauna kusa da yarta tana taba jikinta.

"Ya jikinki?"

"Alhamdulillah"

Suhail ya mikawa Sadam hannu suka gaisai.

"Sannu"

"Yauwa sannu"

"Zinneera ya jikin na ki?"

Suhail ya tambaya sai ta amsa masa tana murmushi.

"Na ji sauki"

"Allah kara lafiya"

Yasmin ta fada tana murmushi.

"Na yi miki sakwara da miyar agusi an sani ba ko kina ra'ayi"

Hajiya Karima ta fada tana kallon yanayinta idonta yai ja sosai ra rame kamar wacce ta shekara ba ta da lafiya.

"Yasmin ma ta dafa min veggitable kuma ta miki pepper soup"

Suhail ya fada mata jin ta yi shiru bata ce komai ba.

"Ina sha'awar shawarma"

Ta fada tana murza yatsun hannunta.

"Sauko muje na siyo miki"

Sadam ya tari numfashin Hajiya Karima wacce ta bude baki za tai magana. Kallonsa Zinneera tai sai kuma ta kalli Hajiya Karima ta kalli Suhail ta maida kanta kasa. Sadam ya bude ba ki zai yi magana wayarsa tai ringing sai ya firo ta daga aljihu ganin number Daddy ya sashi saurin picking.

"Hello Daddy"

Sai Daddy ya amsa daga dayan bangaren.

"Sadam ya hanya ka isa lafiya?"

"Sorry Daddy mantawa nai na kira ku, na isa lafiya kalau"

"Zinneera fa?"

"Tana lafiya Daddy"

"Ba ta wayar"

Sadam ya mikawa Zinneera wayar.

"Daddy yana son magana da ke"

Zinneera ta dade tana kallon screen din wayar kamar mai kirga seconds din dake tafiya na kiran sannan ta mika hannu ta karba zuciyarta cike da tsoro da kuma fargaba, Hajiya Karima har za tai magana sai kuma wata zuciyar ta hana ta. Lokacin data kara wayar a kunne kin cewa komai tai har sai da Daddy ya fahimcin ta karbi wayar ta hanyar numfashin da yake jin yana fita da karfi ya ce.

"Ya ta kina lafiya?"

Sai idonta ya cika da kwalla har ta kasa amsawa.

"Kin gudu kin saka duk hankalinmu ya tashi, da gurina kika zo ai kin san zan baki mafaka ko?"

"Daddy....."

Sai kuma ta fashe da kuka ta kasa magana.

"Wani abun ne? Fada min idan wata matsalar ce"

"Na gode na gode sa kai magana da ni, na gode da ka tambayi lafiyata, na gode da ka kirani yarka na gode da komai Daddy"

Daddy yai murmushi kamar tana a gabansa.

"Ba komai Zinneera Allah yai miki albarka"

"Amin na gode"

Ta fada hawaye na mata zuba sannan ta mikewa Sadam wayar sukai sallama. Hajiya Karima ya kwanto da kan Zinneera jikinta, tana share mata hawayenta.

"Ta so muje na siya miki"

Sadam ya fada bayan ya saka wayar a aljihunsa.

"Yasmin zata fi ka sanin garin nan, zai fi kyau su je tare"

"Why?"

"Ina son na gwada jininka ne na ga ko zai yi, sai mu kara mata, Yasmin muje P-point ki siya nata shawarma atm dina yana nan mota"

Ya karasa yana mikawa Yasmin din keys din motarsa.

"Amman ka tabbatar ta iya mota sosai? Ko kuma a fara gwada jin in yaso daga baya sai muje"

"Yasmin ta biya mota dan ni na fi son tukinta ma da nashi ya fi yi a hankali"

"Zinneera ku je, takawan yana da amfani za ki kara jin karfin jikinki"

Sadam ya gyara mata takalminta ta saka sannan Hajiya Karima ta rika hannunta.

"Bari na raka su"

"No Hajiya Yasmin zata wadatar wata kila zata fi sakewa da ita fiye da ke"

Da dan mamaki Hajiya Karima ta kalleshi. Kamin ta maida dubanta gurin Yasmin wace ke rike da hannun Zinneera za su fice.

"Allah ya tsare"

Sai da suka fice sannan Suhail ya kalli Hajiya Karima ya ce.

"Daman ina neman damar da zan sanar da ku you as her ex-husband and Hajiya Karima as her Mother you need to know this Zinneera ba zata iya haihu da kanta ba"

A zarane duka suka kalleshi amman Hajiya Karima ce ta samu damar tambayar.

"Kamar ya?"

A take ya jero musu bayani tare da nufar file dinta ya dauko hoton mahaifarta ya nuna musu.

"So idan ba a cire cikin a yanzu ba, za a iya theater a cire cikin amman akwai yiyiwar ta kamu da wannan fisge fisgen bayan haihuwa and kun san ba kowa ke fita lafiya ba"

Hajiya Karima kwalla ya cika idonta.

"Idan har za ku iya tankwata ta yarda a zubar da cikin za ta iya neman lafiya idan mahaifar ya bude sai ta dauki wani cikin ta haihu lafiya kalau kamar kowa, amman na mata magana ta ki ta yarda har alkawari ta ce na yi mata dan kar na fadawa Hajiya"

Murmushi Sadam yai.

"Ku ma cikin kuke son zubarwa? Haka kawai kasa wata mace ta dauki Zinneera su fita and you are here tell me this da wani fake hoton mahaifar wata macen?"

Suhail ya kalleshi cike da mamaki ganin yadda yake kokarin kin yarda da maganarsa.

"A tunanin ka zubar da cikin zan yi? Miye hadina da cikin da zan zubar?"

"Ban sani ba, Zinneera ta yi tunanin idan ta zo nan ta tsira shiyasa saka data gudu ta zo nan, ni ma na yi tunanin tsira tai ashe duk kanwar ja ce, kuma cikin kuke son zubarwa"

"Suhail ba zai maka karya ba, ba shi da alaka da ita ko da kai da har zata saka ya zubar da cikinta, na yarda da shi na san ba zai yi haka dan kawai ya cutar da ita ba"

Yadda hawaye ke zuba a fuskar Hajiya Karima yasa Sadam dan tsayawa ya saurareta har ya kai hannu ya karbi hoton yana dubawa.

"Ban yarda da ku ba kira matarka ka ce ta dawo da Zinneera yanzu nan"

"Sadam Yasmin ba cutar da ita zata yi ba"

Suhail ya fada.

"Ba ni da wannan tabbacin ka kirata ka fada mata ka dawo min da matata"

Sadam ya fada cikin daga murya murya fuska na nuna alamun babu wasa a maganarsa.

"Za ka iya da ita wata asibitin ka bincika lafiyarta idan kana so"

Sadam ya nuna shi da yatsa da idonsa da suka soma sauya kala.

"Na fada maka ka ce ta dawo min da matata yanzu!"

Suhail ya ciro wayarsa ya kira matarsa Yasmin, tana yin picking ya ce.

"Kuna ina?"

"Mun kusa P-point"

"ku juyo yanzu nan"

"Lafiya?"

"Lafiya kalau ku juyo kawai"

Ya kashe wayar ba tare da jira ta sake cewa komai ba. Sadam ya cire hular kansa ya nufi windows cikin yanayin da ba zai iya fassarashi ba, kamin Zinneera ta dawo har jin yai kamar yai tsuntsuwa ya je ya daukota zuciyarsa nata raya masa cutar da ita Suhail zai yi. Sai da ta shigo sannan hankalinsa ya kwanta ya har ya samu damar sauke ajiyar zuciya. Tana kallon yanayinsu ta san ba lafiya ba, ga Hajiya Karima na kuka hankalin Sadam a tashe ga shi kuma ance su dawo daga inda za su je.

"Lafiya?"

"Lafiya kalau"

Suhail ya fada, sai Sadam ya ce

"Miyasa ba zaka fada mata gaskiya? I think itama tana da hakkin ta sani tunda cikin a jikinta yake?"

"Ya fada muku cewar ba zan iya haihuwa da kaina ba?"

Zinneera ta fada da kanta tana kallon Sadam. Sai duk suka yi shiru har Sadam da ke zaton ba san da maganar ba. Juyowa tai ta kalli Suhail.

"Na yi da kai ba zaka fadawa kowa ba, miyasa ka karya alkawari?"

"Saboda suna hakkin su sani kamin abun yai nisa"

"Ba fa musu ba zai canja komai ba, domin ni ba zan zubar da ciki ba"

Hajiya Karima ta kalleta da sauri.

"Aa Zinneera rayuwarki ta fi rayuwar abunda ya ke cikinki, da rayuwarki za ki iya samun wani cikin kuma ki haihu lafiya"

"Ba zan gudu daga gurin Umma saboda cikin nan na zo nan na zubar da shi ba, na yi abubuwa da yawa da yasa saka ake kirana mahaukaciya mutane na amfanin da rashin tunanina suna cutarda ni, haka Sadiq yai min ba zan sake aikata wani kuskuren ba idan kuma cilasta min zubar da cikin za ku yi sai na tafi na barku, ko a titi ne zan iya rayuwa ba tare da kowa ba"

Ta fada cikin kuka sai Hajiya Karima ta tashi tsaye da sauri ta rumgume ta.

"Ba wanda zai zubar da wannan cikin ba a son ranki ba, ko cikin shege ne ba za a zubar ba matukar kina so, yi shiru kin ji..."

Sadam kallon Zinneera kawai ya ke yana ta son karyarta Suhail a zuciyarsa.

"Zinneera za mu je gida a binciki lafiyarki"

"Ba zan iya bina na koma a yanzu ba, Abbah yana fushi da ni Umma da Mommy ma haka, ba zan iya komawa cikin wannan yanayin ba"

"Ban zo nan dan na koma ni kadai ba, na zo nan ne dan na maida aurena na koma a tare da ke, ba zan iya kyaleki ki raini cikin nan ke dai ba"

"Sadam kai hakuri, ba zan iya komawa gidanka ba kuma ba zan iya komawa sokoto a yanzu ba"

Ta fada tana share hawayenta.

"What do you mean?"

Ya tambaya cikin rashin fahimtar maganarta.

"Sadam Zinneera tana bukatar hutu a yanzu..."

Suhail ya fada sai Sadam ya daka masa tsawa.

"Don't tell me what my wife need, wannan tsakanin ni da ita ne"

Yama fadar hakan ya fice daga dakin a fusace. Hajiya Karima ta kama hannu Zinneera ta zaunar da ita ba kin gado.

"In-Sha-Allah za ki haihu lafiya, zan kula da ke zan miki duk abunda kike so, kuma kowa zai so ki, za ki dawo mutum kamar kowa"

"Hajiya za ki iya wucewa da ita gida kin tashi, domin jikinta ya yi kyau"

Suhail ya fada sannan yai ma matarsa alama da ta fice suje...

SADIQ POV.

Ya fi karfin minti biyar yana kallonta sam ya kasa yarda cewar kunnuwansa sun ji masa cewar tana da yaya biyu wata kila dai be ji daidai ba, waya sani ko wasa take masa, amman kwalla da ke idonta na karantar da shi cewar abunda ta fada masa tsantsan gaskiya babu wasa a ciki.

"Amman ai ba ki yi kama da mai yaya biyu ba kama da budurwa kike yi"

"Abun daga kama ba ne Sadiq daga kyau jiki ne, suma yaran nan kanana ne ba wasu manya ba"

Ta kunna wayarta ta nuna masa hotonsu, ga su nan kama da ita sak mace da namiji. Wani gumi ya ji yana keto masa tun daga saman kansa har cikin rigarsa. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u yake ta maimaitawa a zuciyarsa dan be isa ya furta a fili ba.

"Na yarda da kai dari bisa dari shiyasa na ke son na aureka, ina da tabbacin yayana da ni kaina za mu jidadin zama tare da kai"

"Wai idan kin yi aure da yayan za ki zauna suna ina yanzu?"

"Suna can gurin yan'uwan babansu, amman kasan ba za su rasa kawo min ziyara ba"

Ya sake kallonta kamar ya fasa kuka.

"Amman Ummi kin san cewa ni saurayi ne kuwa?"

"Na sani, akwai wata matsalar ne?"

"A a babu komai kawai dai na dauka wai ko ba ki sani ba ne, kin san wasu matan wadanda suka taba aure ba sa son auren saurayi irina"

Ya fada yana murmushin karfin hali kamar ba komai.

"Na yarda da kai 100% wannan dalilin yasa na yarda zan aureka"

"Amman iyayenki za su yarda? Ai da kin fada musu gaskiya ki ce ni saurayi ne"

"Ban boyewa kowa ba, mahaifina ya san da maganar ka, kuma ya san kai saurayi ne, mahaifina yana son abunda na ke so, ni kadai mahaifina ya haifa kuma tun ina da shekara takwas a duniya na rasa mahaifiyata, wannan yasa na taso cikin gata da kaunar mahaifina, yayi ta aure bayan rasuwar mahaifiyata amman Allah be bashi haihuwa ba, a haka har ya hakura ya zauna da Hajiya Hauwa wacce ita ce adadin mahaifiyata a yanzu, amman sam bana jindadinta saboda tana ganin kamar son da mahaifina yake min ya yi yawa, gidan ubana ne nan amman ba ni walwala da sakewa kamar agolar yarta wacce ta zo da ita, bana son na nunawa mahaifina ne gudun abunda zai iya zuwa ya dawo, idan har ya san bana jindadin zama da ita zai iya rabuwa da ita ya kawo wata, domin komai a kaina yake yinsa baya son yaga bacin raina balle kuma kukana, wannan dalilin yasa ban taba nuna masa cewar bana jindadinta ba, amman ina da burin na auri mijin da zai so ni tsakani da Allah na bar mata gidan...."

"Haka ne Allah ya tabbatar mana da alheri"

"Amin ya rabb"

Ya fada tana share hawayen fuskarta.

"Ya kamata na ta fi daman zuwa nai na ji gaskiyar maganar kudin"

Sai tai murmushi

"Na ji ko yanzu hankalinka ya kwanta"

Ya gyada mata kai yana ta faman murmushi kamar gaske. Bude motar tai ta fita shi kuma yai ribas ya danna horn sojojin suka bude masa gate ya fito. Tun da ya kamo hanyar gida yake ta dukan sitarin motar har ya iso, ya dade zaune yana tunanin mafita idan har ya ce ba zai auri Ummi ba me zai biyo baya? Zata tona masa asiri kuma ta karbe kudinta ba ma karbe kudin ne damuwarsa ba kamar tona masa asiri da zatai kuma zata iya sakawa a kama shi, idan kuma ya aureta a haka ya ci baya yana saurayinsa ua auri mai yaya har biyu ai kara ma Zinneera sex kawai akai da ita, amman wannan har ta fi Zinneera yin expired, Sadiq irin mazan nan ne da suke ganin idan wani namijin ya rigasu kai wa ga jikin mace to su babu wani abun amfani da zasu samu a jikinta.
Bude motar yai ya fito yana jin zazzabi na sauko masa, jiki ba kwari ya shiga cikin gidan, yanayin yadda ya tararda falonsa kada ya isa ya karantar da shi cewar masu karbar sakon kudi sun zo sun karbi abunsu. Dan kara tabbatarwa yasa ya nufi dakin ya duba inda ya aje kudi sai ya samu babu komai a gurin, zaunawa yai bakin gadon idonsa cike da kwalla yana nadamar ranar daya fara haduwa da Ummi a rayuwarsa, kamin ya fara tunanin Zinneera yadda ya ke sonta amman Sadam yai masa shigar sauri.

"Sadam duk laifin ka ne, da bata ganka ba da duk wannan dabarar bata zo mata ba, and yanzu ka yi mata ciki"

Ya fada cikin wani irin jin haushi da bakin ciki, domin a yanzu ne yake gane Sadam ne mai laifi ba Zinneera ba. Sadam ne babban makiyinsa kuma Zinneera bata ci amanarsa ba tun da har gashi mutumen ya fada masa cewar ya turo sakon. Ya daga kafarsa ya buga kasa da karfi yana jin kamar ya hadiye zuciya ya mutu komai ya zo masa ba a yadda yake tunani ba.

ZINNEERA POV.

After like 2 hours da fitar Suhail Hajiya Karima ta kwashe sauran kayan da a suke asibitin ta saka a motarsa, sannan ta dawo ta rika hannun Zinneera suka fita daga dakin rike take da hannunta har gaban mota ba dan bata iya tafiya ba sai dan ita Hajiya Karima tana kamar idan bata rikata ba zata iya faduwa saboda ramar da tai. Da kanta ta bude mata gidan gaba ta zauna sannan ita kuma ta shiga mazaunin direba ta zauna sannan tai ma motar keys suka dauki hanyar gida.
Ko da suka isa yamma ta yi sosai Nooriyyah da kanwarta sun dawo daga islamiya suna sanye da uniform, jin Motar Hajiya Karima yasa suka fito da sauri, suna ganin Zinneera suka hau murna suna mata ya jiki kamar daman can sun saba da ita. Hajiya Karima ta rikata har cikin falon ta zauna da ita saman kujera tana murmushi.

"Ga sister ku jiki yai kyau amman sai rama"

"Ai gashi nan a fuskarta kamar waccw ta shekara bata da lafiya"

Nooriyyah ta fada tana kallonta. Hajiya Karima ya mikawa Nooriyyah makullin motarta.

"Je ki dauki kudi a daki ki siwo mata shawarma"

Hannu biyu Nooriyyah tasa ta karba cike da ladabi sannan ta nufi upstairs A
Jawahir na binta a baya tana rokon ko zata tafi da ita.

"Idan kin huta sai mu shiga ciki ki yi wanka kinji?"

Ta gyadawa Hajiya Karima kai kawai amman hankalinta yana can gurin Sadam, ya fita rai a bace ko a ina yaje? Ji take kamar a ace yana kusa da ita for the first time yau tana jin kamar ace a kusa da shi zata rayu.

"Zinneera..."

Hajiya Karima ta kira sunanta ganin kamar hankalinta baya jikinta. Sai ta dago ta kalleta idonta cike da kwalla.

"Damuwa dai kuma? Wani abun ne?"

"Ina tunanin yadda zan gyara wadansu abubuwan ne"

"Kamar mi?"

"Kamar sakawa Sadam ya auri Aleeya, maybe Umma zata yafe min, and if abunda Suhail yake fada ta kasance zata kula da abunda zan haifa ko, kuma mahaifiyarsa zata fahimta ra yafe min"

Hajiya Karima ta yi murmushi cike da rashin jindadin maganar Zinneera amman bata nuna mata ba.

"Be kamata ki fara tunani yanzu ba, kina bukatar hutu ta so muje ki yi wanka sai ki kwanta"

Hajiya Karima ta fada tana rika hannunta. Zinneera bata tashi ba daga zaune da take ta kalli Hajiya Karima ta ce

"Bana son abunda zan haifa ya taso cikin wani hali kamar ni, bana son mutane su tsargu da shi kamar yadda ni ma ake tsarguwa da ni, ina son na gyara tsakani na da kowa"

Hajiya Karima ta dawo ta zauna tare da kai hannu ta rika fuskar yarta.

"Zinneera idan mace tana da cikin fari bata irin wadannan maganganun, cewar za ki gyara tsakaninki da kowa yana da kyau sosai, kuma za ki iya matukar za ki zama jajirtaciya mai yawan neman shawara da kuma Zabin Allah a al'amurarranki, dukan ni abunda yake faruwa da wani ko da ke darasi ne a gareki, karki yarda zuciyarki ta sake yaudararki ta kaiki ta baro, karki hana zuciyarki abunda take so saboda wasu, haka kika yi har kika bata tsakanin Sadam da Sadiq, fada min kina son Sadam?"

"Ban sani ba..."

"Amman shi yana son ki, kuma na tabbatar da babu kauna a tsakaninku babu yadda za ayi ya biyo ki nan hankalinsa a tashe, ke ma kuma da ba za ki tambayeshi ba, ba a saka namijin yin abunda be tashi ba, da ace yana da ra'ayin auren Aleeya da ta aureta ko dan ya rama abunda kika masa, amman be yi kin san saboda?"

"Saboda yana so na?"

Hajiya Karima ta gyada mata kai.

"Wannan dalilin yasa yake ganin kamar ni din ma zubar da cikin zan yi, na zo nan ya fada min magana marar dadi saboda ke, kuma gaskiya ya fada duk abunda kike yi saboda babu ni a kusa da ke ne, kar tunanin abunda kikai wa Umma da Mommy da duk wani ya dame ki, idan har ma cuta ce Sadam ya fi kowa cutuwa a lamarin nan kuma ya yafe miki tun gabanin ki nemi yafiyarsa, ya kamata ki fara tunanin kyautata masa"

"Taya?"

"Ta hanyar komawa ki zauna tare da shi, yana da gaskiya Zinneera kina da bukatarsa a kusa da ke, dan mahaifiyarsa bata son ki ba damuwarki ba ce tunda yana son ki kuma dole ta so abunda kike so"

Zinneera ta yi shiru tana nazarin maganar Hajiya Karima.

"Kin san abunda ya cutar da ke tun farko? Umma bata koya miki saka Allah a al'amurarranki ba, kuma bata nuna miki neman shawara ba, bata koya miki fira da ita ba irin an uwa da 'ya balle har ki karanta mata damuwarki"

"Miyasa ke kika kasa tsayawa ki yi min? Har gobe Umma uwace a gare ni ta raini a lokacin da kika tafi kika bar ni ni da Nabeel, ko da Umma bata min komai ba ai ta shayar da ni nononta na rayu, bana son wani yana fadar aibunta kusa da ni"

Zinneera ta Fada murya a sanyaye hawaye na sauko mata. Sannan ta tashi tsaye ta nufi inda ta hango Nooriyyah ta bi sai Hajiya Karima ta tashi ta bi bayanta.

"Ga dakin nan"

Hajiya Karima ta fada tana tura kofar dakinta, sai a lokacin Nooriyyah ta fito a dayan dakin rike da wayarta Jawahir na riko mata veil.

"Hajiya ki ce ta tafi da ni"

"Dan Allah ki tafi da ita Nooriyyah"

Hajiya Karima ta fada cikin muryar da ke nuna alamar tana daf da fashewa da kuka. Hakan yasa Nooriyyah jin babu dadi ko bata fada mata ba tasan matsalar bata wuce Zinneera. A tare suka shiga dakin da Hajiya Karima ita ta nuna mata bandakin ta dauko mata tawul da sabin tufafin Nooriyyah da zata saka idan ta fito wanka.
Zinneera bata fito daga wankan ba sai da aka soma kiran sallah magariba, hakan nan kawai ruwn zafin suke mata dadi, ta kwanta a cikin tub din ta lumshe ido kamar babu a bandakin.
Sai da tai alwala sannan ta fito ta daure da tawul, a saman gado ta samu tufafin sai ta dauka ta saka bata damu ta shafa mai balle hoto dan turaren data da ganina kan mirror kawai ta fesa ta saka Hijab dinta ta gabatar da sallah, bayan ta gama Jawahir ta shigo dauke da farantin shawarma da gasasshiyar kaza ta aje mata, sannan ta koma ta dauko mata lemu da kofi ta aje mata.

"Hajiya ta ce ki ci da yawa"

Jawahir ta fada tana kokarin juyawa sai Zinneera ta rikota.

"Zauna mu ci tare"

Ba musu Jawahir ta zauna Zinneera ta saka hannu suka soma ci tare, kadan ta ci ta ji bata bukatar Shawarma sai soyayyen kwai da madara, cire hannunta tai shiga bathroom ta wanke hannunta ko da ta fito Hajiya Karima na tsaye ta yi ma Jawahir fadan cin abincin Zinneera da tai.

"Ni na ce ta ci"

"Amman ba ki ci komai ba ai, ko wani abun kike so a dafa miki?"

Ta girgiza kai sannan ta zauna bakin gado.

"Bana bukatar komai, ina wayata"

Hajiya Karima ta bude bedside drawer dinta ta dauko mata wayarta ta mika mata sannan ta dauki farantin suka fice tare da Jawahir. Har ta danna number Sadam sai kuma ta kashe tana ta fargabar kiransa da tunanin abunda zata fada masa idan ta kira shi. Sai ga kiran Sadiq ya shigo wayarta babu suna a number amman ta san numbersa ce saboda ta haddace ta kamar ba zata daga ba sai kuma ta daga ta kara ta a kunnenta.

"Zinneera"

Sai da taja wani ajiyar zuciya ta sauke sannan ta amsa.

"Na'am"

"Kina ina?"

"Lafiya?"

"Magana na ke son yi da ke"

"Ina Kaduna gurin Hajiya Karima"

"Kaduna kuma? Miya kai ki can?"

Ya tambaya cike da mamaki

"Ba komai"

"Ina son magana dake"

"Face to face na ke nufi, za ki iya turo min addireshinki? Zan zo na same ki"

"Zan tambaya sai na turo maka"

"Okay"

Daga haka ya kashe wayar ita kuma ta kurawa wayar ido cike da mamakin kiransa a yanzu da kuma son ganinta da yake. Shigowar Hajiya Karima ce tasa ta dago kai tana kallonta.

"Kina da bukatar wani abu?"

"Ina bukatar na san dalilin daya saka kika tafi kika barni, mi nai miki? Ni da Nabeel? Ko kuma mu ba yayanki ba ne? Mu ba mu cancanci zama a kusa da ke ba? Ko saboda na mu uban yana talaka yasa muka rasa gatanki?"

Zinneera ta tambaya tana hawaye, sai Hajiya Karima ta zauna kusa da ita ta kama hannunta.

"Ban tafi na barku saboda mahaifinku yana talaka ba, ban ki ku saboda talauci ba, na san ban yi tunani mai kyau na tafi na barku ba, amman babu yadda zan yi ne a wacan lokacin, ban san ta fuskar da za ki kalli labarin da zan baki ba, amman ni da tabbacin ba za ki ga laifina ni kadai ba, tafiyar da nai mahaifinki ne sila kuma bana son na baki labarin abunda zai iya zame miki tunani a yanzu"

"Fada min zan iya saurare ko minene"

Zinneera ta fada cike da son jin dalilin tafiyar mahaifiyarsu ta barsu.

SADAM POV.

lokacin daya fice daga asibitin kai tsaye motarsa ya shiga ya dauki hanyar komawa gida, a gusau yai sallah isha'i misalin sha daya saura na dare ya isa sokoto. A gidansa ya sauka a nan ya kwana sai da safe ya shirya ya nufi gidansu, ko da ya shiga gidan Mommy ce kawai ta farka daga bachi ita ma saboda shiryawa Siyama abincin makaranta. A kitchen ya same ta tana kunna gas, tsaye yai bakin kofar kitchen din cikin yanayin damuwa yana kallon Mommy, wacce bata san da shi ba har sai da ta juyo.

"Mommy ina kwana?"

Sai da tai kamar ba zata amsa ba sai kuma ta amsa.

"Lafiya kalau"

Zuwa yai gabanta ya risina ya daga kansa yana kallonta.

"Kowa zai iya fushi da ni duniyar kuma na gama lafiya amman ban da ke, da babu ke a rayuwata da ban zama yadda na ke a yanzu ba, da ba ki raini ni kin tarbiyantar da ni ba, da yanzu na tashi cikin wata kalar rayuwa marar misaltuwa, duk wanda zan so a duniyar bayanki ya ke Mommy, kuma duk abunda kike ki ba zan iya son sa ba ina son ki mommy duk wanda zai so ni ba zai so ni kamar ke ba, na gode Allah daya ba ni ke a matsayin uwa"

Magana Sadam yake hawaye na sauko masa har cikin zuciyarsa yake nufin Mommy da dukan kalamansa. Ita kanta sai da ta ji tsoro ganin yadda danta yake durkushe a gabanta yana hawaye, mutumen daya tafi kaduna jiya jiya yau ya shigo gidanta da safen nan.

"Miya faru Favorite?"

"Ji yadda kika kirani Mommy Favorite, Zinneera bata taba samun wani suna mai dadi daga mahaifiyarta ba, irin gatan da kike nuna mana ita bata saba samun ko daya ba, shiyasa bata iya tsayarda tunaninta tai abu mai kyau, Mommy Zinneera tana cikin wani hali, su ma can son zubar da cikin suke yi, ke ma a nan baki son ta haihu da ni, Umma ma son zubar da jinina take, a lokacin da nai tunani sai gano Zinneera ba tai dacen uwa kamar ke ba, mai son abunda yayanta suke so, kuma ta fi su kin abunda zai cutar da su, Mommy ba zan iya zabar Zinneera na barki ba, na san idan na fadawa Daddy saki daya na yi ma Zinneera zai zama na karyata ki a gurinsa, kuma zai iya sa na maida ita alhalin ke kuma ba ki son zamana da ita, bana son soyayyar Zinneera ta dasa kiyayyata a zuciyarki, a gurinki nake zuwa na nemi taimakon da shawara akan komai nawa? Duk wacce zata gan ni na so ta a yanzu sai da kika raine ni ta gan ni, dan kin ce na rabu da Zinneera sai kuma na kasa? No zan rabu da ita Mommy kamar yadda kike so, ba zan iya bin son wata na kyale n mahaifiyata ba, Mommy I'm sorry please forgive me"

Gaba daya jikin Mommy ya gama sanyi, ita ma hawayen take ganin danta na hawayen.

"Wannan hawayen duk saboda ni ne?"

"Saboda ke ne Mommy dan Allah ki ce kin yafe min"

"Ba ka min komai ba Sadam, ni na san be kamata na zubar da cikin ba, amman ina tsoron kar Zinneera ta sake cutar da kai ne"

Sadam ya mike tsaye.

"Zinneera ba zata iya cutar da ni ba Mommy, abunda ta aikata a yanzu ma kanta ta cutar, ta saka kanta cikin matsala, babu komai a bakinta sai ke da Daddy da Umma da Abbah, tana ta damun kanta da abunda ta aikata muku, ta gudu ta bar nan saboda kar a zubar da cikin taje gurin mahaifiyarta ashe itama bata son jinina, Zinneera bata yi dacen uwa kamar ba a rayuwarta, na tabbatar da ke a matsayin mahaifiyarta ba za ki iya tafiya ki barta ba ta tashi hannun wata macen mai kiranta mahaukaciya, har ta fada hannun wani mutum wanda yai ta juya zuciyarta daga karshe ta dawo tana nadama, Zinneera bata iya banbance fari da baki Mommy saboda rashin mahaifiya, ke ko duk abunda kike ni kike kokarin karewa so kike ki tare ni kar wani abun ta same ni, Na gode Allah daya ba ni uwa kamar ki Mommy love you so much"

Ya fada yana sumbantar hannunta hawaye na sauko masa, da dukan gaskiyarsa yake karantawa Mommy abunda ke ransa bawai dan kawai ta tausaya masa ba, har ga Allah yana jim shi kan tashi uwar ba zata iya tafi ta barshi ba ko da kuwa yanka naman jikinta ake ana soyawa kullum. Cikin ruwan hawaye Mommy tai murmushi tana kallon danta cike da kaunarsa kamar kullum.

_________________________

Me zai kai Sadiq gurin Zinneera? Anya zai auri Ummi kuwa? Anya Zinneera zata yarda a zubar da cikin kuwa.?
Zinneera ta fara ba ni tausayi rashin uwa ciwo ne. Allah ka karawa iyayenmu lafiya da imani. Wadanda suka rasa ta su mahaifiyar kuma Allah ya jikansu. 😟

Wadanda ba su min subscribe ba ku je YouTube kui searching Taskar Khadeeja Candy ku dannan min subscribe. Thank you so much ga wadanda suka yi min subscribe kun nuna kuna tare da ni 100%😍🌹

Continue Reading

You'll Also Like

562K 11.3K 26
Maddy, daughter of Maleficent, was furious when her sister and friends went to Auradon. Left to defend herself, she was offered a place in Uma's crew...
4.2K 475 41
A teenager who was married to sm1 unconscious, when she regains her memory everything got ruined
72K 3.6K 46
Camila Davis is a semi-famous hockey player for the California Cobras. She recently divorced her lying cheating husband and moved her and her kids ac...
113K 2.9K 79
Everyone makes mistake, right? Everyone deserved to be forgiven, right? But, what if, that mistake was unforgivable? What if having affair with a mar...