ZABIN RAI

Bởi KhadeejaCandy

113K 15.7K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... Xem Thêm

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
46
47
48
49
50 End

45

1.6K 342 224
Bởi KhadeejaCandy

SADIQ POV.

Rayuwar farincikin da Ummi a yanzu, ta mantar da shi duk wani farincikin rai da damuwa da yake ciki ciki kuwa har da wacce Zinneera ta saka mishi, Mama ba laifi tana son Ummi domin ta yaba da hankalinta da yadda take nuna musu kulawa ga alheri abun hannunta be taba tsone mata ido ba.
  Wani lokacin yana tasowa daga aiki zata shirya masa abincin tun daga gidan mahaifinta ta aiko masa, ko ta aikowa Mama. Idan yaje fira kuma har cikin falon mahaifinta yake zama suyi firar ta gabatar da gurin mahaifinta suna gaisawa yafi a kirga.

Yau ma sauri yake ta yi saboda Ummi ta fada masa cewar yau akwai surprise, he don't know what it's that's why yake jin kamar ma ya bar gurin aikin ya koma gida, domin ta fada masa a gida surprise din yake, daga baya ya fara tunanin ko abinci ne ta aje masa ko kuma wani abun na kawa ko na ci. Biyu saura kwata ya tashi office sai ya bi ta gidan mai dan karawa motarsa man da yake tunanin ba zai kaishi gida ba. Ya tararda layi kasancewar NNPC ne farshinsu ya dauka kadan dana sauran gidajen mai shiyasa ake musu taro sosai.
Yana cikin motar ya hango abokinsa Husaini yana dago masa hannu, sai ya ciro wayarsa ya kira shi.

“Husaini ya?”

“Daidai ya aikin?”

“Alhamdulillah”

“Ya Zinneerar mu”

“Kai ba wannan maganar”

“Kamar ya?”

“Kai dai bari kawai”

“Ban gane ba? Taya zaka ce ba maganar ka yafe ta ne?”

“Ai dole na yafe, kai da bari na sha ma zamu yi maganar”

Daga haka ta kashe wayar, Husaini na gabanshi a dayan layin dan haka ya rigashi shan mai sannan aka kawo kansa shima aka zuba masa na kudinsa ya wuce. Be lura da Husainin gefen titin fake da motarsa ba har sai da yai masa horn, sai ya faka tasa motar gaban ta Husaini ta fito ya nufo Husaini yana murmushi.

“Kar dai ka ce min Sadam ya fi karfinka”

Husaini ya fada yana bude motarsa ya fito, sai Sadiq ya mika masa hannu suka tabe yana kyalkyal dariya.

“Ba karfina ya fi ba, shima ai ya rasa ta kuma saboda ni”

“Ban gane ba”

A nan Sadiq ya labarta masa abunda ya faru da kuma kudinsa na aurenta indai gar Sadam be kai ga jikinta, da kuma dalilin fasawarsa saboda cikin da take dauke da shi, ciki har da labarin Ummi wacce yake so yanzu, da can Husaini yana ganinta a gurinsa lokacin da yake kwance asibiti idan yaje ganinsa, sai dai a zatonsa yar'uwarsa ce musamman yadda yaga tana da hidima da shi.

“Amman gaskiya Sadiq ka bani kunya, ga yarinya ka samu a bagas, aurenta ya mutu sai kuma ka ce wai ba zaka aureta dan tana da ciki ba? To ai shi Sadam din zai iya maida aurensa kuma kaga ita zatai maka kallon mayaudari”

“Husaini ciki fa nace maka tana da shi”

“To miye dan tana da ciki? Ba sai a zubar ba, kai da ba ka cika burinka na aurenta ba, kuma Sadam zai ji bakinciki idan ka aureta musamman ka zubar da cikin nan”

“No Husaini ni ba zan iya auren mace da wani namijin ya rigani kusantarta ba, ba zan iya auren matar wani ba matukar ya kai ga jikinta”

“Oh kai duk son da kake ma Zinneera na jikinta ne? Daman can ba saboda Allah kake son ta ba? Ai da nasan haka ne da ban baka shawarar ka ashe mata aure ba, nayi zaton son Allah ne shiyasa na ji haushi lokacin da Sadam ya aureta ya barka bayan kai ka shekara hudu tare da ita, kayi wa kanka adalci Sadiq be kamata yarinyar nan ta kashe aurenta saboda kai ba kuma ka gujeta, indai dan ta cikine ka same ta ku sasanta kanku sai a zubar kamin yai kwari”

“Husaini ina da kishi sosai bana son na kusanci mace da wani namijin ya kusance ta, musamman Zinneera”

“Amman ko dan ka bawa Sadam haushi ya kamata ka aureta, kuma ita wannan yarinyar ba budurwa ba ce? Sai ka hada su biyu ka aura, g budurwa ga Zinneera wannan kishin da kake ji duk zai yaye, amman gaskiya be kamata ka juyawa yarinyar nan ba ya ba”

Sadiq ya busar da iskar bakinsa.

“Gaskiya ba zan iya ba Husaini, wani ya riga ya fasa ta, wanin kuma Sadam kazamin mazinaci be kamata mu yi hako rijiya daya ba no way”

“To shikenan Allah ya kyauta, ni zan wuce a gaishe da Ummin”

Husaini ya bude motarsa ya shiga, sai da ya bar gurin sannan Sadiq ya nufi tashi motar ya shiga ya dauki hanyar gidansa cike da tunanin maganganun abokin nasa. Be tuna da surprise din da Ummi tace ta aje masa ba har sai da ya isa gidan, yana ta sake saken abunda zai tarar da zarar ya shiga falon, sai ya samu babu komai a falon ya duba ko'ina a dakin be samu komai ba. Sai a lokacin ya tuna da ya ma za ayi ya samu wani abu a dakin bayan bata da keys dinsa ko abincin da take kawa masa ai a bakin kofar dakinsa take ajewa ko kuma ta aiko masa idan yana cikin gidan. Wayarsa ya ciro da zimmar kiranta sai yaji ana knocked kofar falon be fasa kiran ba sai ya kirata ya kara wayar a kunne ya nufi kofar falon ya bude. Wani matashi ya gani a tsaye rike da wani karamin akwati baki ya mika masa.

“Wai gashi inji Ummi tace ka kirata”

Hannu ya kai ya karba yana fadin.

“Gani nan ina kiranta”

Sai matashin ya juya shi kuma ya maida kofar ya rufe yana ta mamakin abunda ke cikin akwatin. Zaunawa a saman cushion dinsa yana amsa maganar da take masa.

“4486 shine numbers din bude akwatin”

Ya saka kamar yadda ta fada masa sai ya danna akwatin ya bude. Dollars ne a ciki adadin da ba zai iya kiyasinsu a take ba.

“Ummi kudi na gani”

Ya fada bakinsa a sake hankalinsa a tashe.

“Eh ai nasan kudi zaka gani, naira miliyan ashirin ne, so nake ka biya mutumen mai binka kudi ta yadda zamuyi rayuwarmu cikin aminci”

“Ummi ina kika samo wannan kudin haka? Wa kika roka?”

“Ban roki kowa ba, kuma babu wanda yasan na baka wadannan kudin, yanzu dai ka fara jirashin yanzun nan ya fada maka inda zaka kai kudin, idan ka biya zamu yi magana daga baya”

“Baby i love you, amman wannan zai iya zama sirri a tsakaninmu?”

“Da ba zai zama sirrin ba, da babu dalilin da zai saka na baka har naira miliyan ashiri”

“Thank you”

Ya fada yana lumshe ido cike da tear of joy. Ita kuma ta kashe wayar tana dariya, sai a yanzu yake jin Allah ya masa sakamako da hakurin da yai da kuma musanya masa Ummi amadadin Zinneera, jin sonta yake ko'ina a jikinsa. Cikin sauri ya saka number mutumen ya kira shi, sai da tai ringing ta katse ya sake kira sannan ya daga.

“Ina za a kai maka kudin da bindigoginka?”

Sadiq ya fada kai tsaye. Mutumen yai shiru kamin yai dariya.

“Good boy ashe kana tsoron abunda zai biyo baya kamin nan da shekara daya ko? Sakona ya saka ka maida hankali har ka samo kudin ko? ”

Shiru Sadiq yai yana kokarin gasgata maganar da Zinneera ta fada masa cewar saboda sakon yasa ta auri Sadam ta samo masa kudi kamin nan da shekara daya, be taba yarda ba sai a yanzu ashe da gaske ya turo masa sakon kuma takaranta sai ta goge saboda kar ya gani hankalinsa ya tashi.
Can cikin tunaninsa ya tsinkayo muryar mutumen yana fadin.

“Ka aje kudin a gida zan aiko a karba, guns kuma ka aje a gurinka za su yi maka amfani, amman ka fada min mutum nawa yasan sirrinka kamin ka hada kudi? Hudu? biyu? Goma ko ashirin? Karka bar duk wanda ya san sirrinka a raye, domin wata rana zasu butulci maka su tona maka asiri kamar yadda ka butulce min, ka bar gidan a bude za a zo a dauka”

Yana fadar hakan ya kashe wayar. Sai hankalin Sadiq ya tashi tabbas yasan idan har shi be iya rike sirrinsa ba to wa zai iya iya rike masa? Number Ummi ya sake kira ringing daya tai picking.

“Kina ina Ummi ina bukatar ganinki”

“Ka kai masa kudin?”

“Na kirashi yace na bar gidan a bude zai aiko a dauka, kina ina?”

“Ina gida”

“Gani nan zuwa”

Ya kashe wayar sai ya rufe kudin ya shiga bedroom dinsa ya dora akwatin a saman gadonsa ya juyo ya fito ba tare daya rufe gidan ba. Motarsa ya shiga ya dauki hanyar gidansu Ummi, he arrived in time be kuma sha wahala gurin shiga gidan ba, kuwa da irin tarin sojojin da suke gadin gidan, domin ya saba zuwa har sun saba da shi.

“Ina waje”

Ya fada mata a waya bayan ya faka motarsa a harabar gidan.

“Ka zauna a mota, dan bana son cctv ta dauki maganarmu”

“Okay,”

Ya fada cike da jin amince a tare da ita. Bata dauki lokaci ba sai gata ta fito sanye da riga da zane na shadda mai kyau sai dan karamin farin veil data rufe kanta da shi kallonta yake har ta karaso ta bude front seat ta shiga ta zauna, sai ta kalleshi tana murmushi.

“Kamar hankalinka baya jikinka?”

“Hankalina baya jikina Ummi har sai kin fada min inda kike samo kudin nan”

“Ban je nema a wani gurin ba, kudin dana baka a cikin dukiyata na diba”

“Amman kina da kudi mai yawa haka account dinki? Ko dai wani abu naki kika siyar?”

“Ban siyar da komai ba, kamar yadda ka sani mahaifiya mai kudi ne sosai, mijina ma ya mutu ya bar min gadon da baka taba tsammanin ina da dukiya mai yawa kamar ta ba”

A zarane ya kalleta.

“Mijinki? Kin taba aure?”

“Yes na taba aure har da yara biyu”

Ta fada idonta na kokarin cika da kwalla, wani lankwafar da kai Sadiq yai yana kallonta sai yaji maganarta tana ta maimaita kanta a cikin kunnensa....

ZINNEERA POV.

Suhail ya bata dukan kulawar data kamata a cikin daren nan sannan yai mata allurar bachi ta yadda zata samu ta hutu, sai dai abunda ya daure masa kai a lokacin daya aunata ya samu tana daukw da juna biyu shi kuma a iya saninsa da kuma yadda Hajiya Karima take fada masa Zinneera budurwa ce ba tai aure ba, be san yadda Hajiya Karima zata ji idan ya fada mata cewar Zinneera na da ciki tunda bashi da tabbacin cikin na sunna ne ko shege, sai dai zuciyarsa tafi raya masa cewar ba da aure ta samu cikin ba wata kila hakan ne yasa ta gudu ta zo gurin Hajiya Karima.
So he decided not to tell Hajiya Karima har sai yaji daga bakin Zinneera. Bayan a kaita wani dakin kebantaccen na dabam ya fadawa Hajiya Karima ta shiga ta zauna tana ta kallon yarta cike da tausayinta.

“Ta ji ciwo ne?”

“Eh a can cikin mararta ne, amman komai ya tsaya a yanzu”

“Ka tabbatar ba wata matsala? Ko ta bugu sosai ne?”

“No lafiya kalau ne da safe zan sake dubata, and na aiko hoton da aka dauka na mararta amman sai gobe zai fito sai mu duba idan ma da wata matsalar zan gani”

Sai ta dauke idonta daga duban Suhail ta maida gurin Zinneera hawaye na bin idonta. Shi kuma ya juya ya fita yasan abu ne mai wahala ya fada nata cewar ta koma gida ta kwana while Zinneera tana kwance a asibiti, dan haka ya koma gida ya dauko mata carpet da sauran abubuwan bukata ya kawo mata asibitin. Misalin shadaya saura na dare Alhaji Muhammad Dattijo ya zo asibiti tare da Nooriyyah duba Zinneera kamar yadda Hajiya Karima ta fada masa a waya cewar tana asibiti gurin yarta a lokacin daya dawo gida be same ta ba.
    Kiran sallah asuba ne ya tashi Zinneera daga bachin da take, tashi tai zaune sai ga Hajiya Karima zaune a saman karamin carpet sanye da Hijab tana jan carbi.

“Sannu”

Hajiya Karima ta fada tana kallonta cike da tausayawa. Sai Zinneera tai kasa da kanta ba tare da amsa ba, zuwa tai zata sauka sai Hajiya Karima ta mike tsaye ta sauri ta rikata.

“Zan iya tafiya, bandaki zan shiga”

“Bakya jin komai?”

“Bana ji lafiyata kalau”

Bata yarda ta saketa ba har sai suka ka cikin bandakin sannan ta saketa ta juyo ta dawo. Ta soma gabatar da sallah asuba ko da ta sallame Zinneera na gefenta zaune tana jiran ta gama sannan ita kuma ta gabatar da tata sallah. Hajiya Karima na kokarin tashi ta bawa Zinneera carpet din Suhail ya shigo dakin sanye da Jallabiya da alama daga masallaci ya nufo nan.

“Suhail tun da asuba haka?”

“Hajiya ina kwana? Ya mai jiki”

“Lafiya kalau Alhamdulillah”

“Hajiya ya kamata ki tafi gida tunda na zo, kin san Abbah zai bukaci breakfast muma nan zamu bukata idan kin gama sai ki dawo”

“Haka ne, mi kike bukatar a dafa miki?”

Ta karasa tana kallon Zinneera.

“Bana bukatar komai”

Ta fada kamar bata son magana.

“Ko dai baki ji sauki ba ne?”

Hajiya Karima ta sake tambaya.

“Hada mata normal breakfast kawai Hajiya ki kawo zata ci”

“Okay”

Ta dauki wayarta ta wayar Zinneera ta wasu abubuwan ta fice.

“Ki yi sallah bari naje na sauke Hajiya gida na dawo”

Ya fada saboda ruwan alwalar daya ganin a fuskarta, sannan ya juya ya fice ita kuma ta shiga batarda sallah. Bayan ta kare har ta dora da salati sannan ya shigo dakin bakinsa kumshe da sallama hannunsa kuma rike da wasu takardu da hoton mahaifarta da aka dauka jiya. Saman gadon ya zauna a yayinda ita take zaune kasan carpet.

“Ya jikin?”

“Naji sauki”

“Jinin ya sake miki zuba?”

“Aa be sake ba”

Ta amsa mishi kanta a kasa shi ko idonsa suna kanta. Yai shiru na dan lokaci sannan ya ce.

“Ba zan tambaye ki miyasa kika zo gurin Hajiya ba domin mahaifiyarki ce, amman zan tambaye ko kin san kina da wani ciwo ko wata lalurar da zata iya sakawa jini yai ta miki zuba haka?”

Sai a lokacin ta dago ta kalleshi.

“Ina ciki! Ya zube ne?”

“No cikin yana nan, amman yai zubar da zaki kara wata daya akan wata tara ko goma na haihuwarki”

Sai ta maida kanta kasa.

“Ban fadawa Hajiya cewar kina da ciki ba, saboda ban san yadda zata kalli abun ba, kuma ban san hallacinsa ba, Zinneera kina da aure?”

Shiru tai na wani lokaci kamin ta amsa masa.

“Bani da aure a yanzu”

Cike da mamaki ya aika mata da wata tambayar.

“Kin taba aure kenan?”

Bata amsa mishi ba har ya gaji da jiran amsarta.

“Okay daman ina fargabar fadawa Hajiya ne a zatona ko ba dan Sunna ba ne, amman yanzu zan fada mata ko dan lafiyarki”

Ta dago ta sake kallonta da idonta mai ruwan hawaye, sai ta tambayeshi da muryar marasa kuzari.

“Ban gane ba”

“Kina bukatar a zubar da cikin nan kamin ya girma Zinneera”

“Saboda me?”

Ya mika mata hoton mahaifarta dake hannunsa.

“Bakin mahaifarki a tsuke yake, ba zaki iya haihuwa da kanki ba har sai ki sha magani kin ya bude”

Rufe bakinta tai ta fashe da kuka.

“Za ki iya samun wani, zaki iya haihuwa amman har sai idan bakin mahaifarki ya bude”

Dagowa tai ta kalleshi tana kuka.

“Za a iya min tiyata a cire idan ba zan iya haihuwa da kaina ba?”

Ya kalleta da kyau kamin ya amsa mata.

“Yes za a iya, amman akwai yiyuwar ki iya rasa ranki, saboda hawan jini zai iya samunki kuma kin ga ba yi ma mace mai ciki theater idan jininta ya hau, saboda komai zai iya faruwa”

“Amman za a iya cire abunda na haifa da rai kuma a cikin koshin lafiya?”

“Yes that's for sure, inda ba wani abun Allah ya kawo ba”

“To ka bar min cikina, zan haife shi ko ni zan rasa rayuwata”

“Miyasa kike son cikin nan da yawa ne? Be kai matsayin da zai baki illa ba idan har aka cireshi a yanzu”

“Saboda kar a cire cikin nan yasa na gudo daga sokoto na zo nan, ina son na haifi abun cikina ko da ni zan mutu, Ina son nai wani abun da wanda ko abunda zan haifa ya kirani uwa mai hankali kuma mai kaunarsa, na batawa kowa rai kowa fushi yake da ni, mutuwa zata fi min rayuwata na sani, amman ina son kamin ma mutu nai Sadaukarwa wata kila hakan zai saka su yarda ina da hankali da tunani irin na mutane, wata kila su yafe min har su raini abunda zan haifa kuma su yi min addu'a bayan bana raye”

Hawayen dake sauka a fuskarta ne yasa jikinsa yai sanyi.

“Amman Zinneera rayuwarki tana da muhimmanci sama da ta abunda yake cikinki”

“Aa tawa bata da muhimmanci a yanzu, dan Allah ka rike min wannan sirrin kar Hajiya taji kuma kar wani yaji cewar akwai ciwo a mahaifata”

“Na miki alkawari ba zan fadawa kowa ba, matukar zaki fadawa min dalilin daya saka baki son zubar da cikin”

Bata boye masa komai ba, cikin kuwa har da tunanin da take na cewar Sadam ma ba zai so abunda zata haifa ba. Suhail samun kansa yai da mugun tausayinta sai yake tuna lokacin da kai Hajiya Karima gidansu har yake canja mata rubutun da tai cewar suna cewa bana tunani irin na mutane komai ba a daidai na ke yinsa ba, shi kuma ya maida mata cewar akwai wanda yake ganin komai naki a daidai yake.

“Ba zan fada mata matsalar ba, amman zan fada mata gaskiyar cewar kina da ciki”

Ta gyada masa kai tana wani irin kuka mai ban tausayi. Baya iya kallon hawayenta kamar yadda sauraren kukanta yake sashi jin babu dadi, sai ya tashi ya fice daga dakin yana kira Hajiya Karima a waya.

HAJIYA KARIMA POV.

Tana cikin kitchen tana shirya breakfast Aslamiya ta shigo sanye da uniform ta mikawa Hajiya Karima wayarta.

“Brother ya kira”

Da sauri Hajiya Karima ta karba ta kara akunne already Aslamiya tai picking call din.

“Hello”

“Hajiya ina son na Fada miki wani abu ban san yadda za ki dauke shi ba, amman ya kamata ki sani Zinneera tayi aure kuma mijin ya saketa and she's pregnant”

“What”

Tayi saurin aje wukar dake hannunta.

“Idan kin zo bana son ki nuna mata damuwarki, ita tana cikin wata damuwar, na mutuwar aurenta da kuma gudunta da kowa yai”

“Okay”

Ta amsa tana kuka, sai ya sauke wayar ta risina a gurin tana ta kuka. Taya za ace yarinya karama kamar Zinneera an aureta kuma har auren ya mutu? Me tai kowa ya gujeta taya za a aurar da yarta bata sani ba? Wace irin uwa ce ta? Kasa karasa aikin tai ta baro kitchen din ta nufo dakinta tana kuka ta zauna bakin gado ta kai hannu ta dauki wayar Zinneera tana kallonta kamin ta kunna. Hoton Zinneera dake gaban waya take ta kallo tana ta tausayin rayuwar yarta, wace irin rayuwa tai a bayan tafiyata ga wa aka aurar da ita? Tana sonsa ko bata sonsa? Miyasa auren ya mutu? Zinneera tayi karancin da za a ce aurenta ya mutu a yanzu, ta yi karanci a kirata bazarawa a yanzu.

Wayar Zinneera ce tai ringing number Nabeel ta bayyana sai Hajiya Karima ta daga tana kuka ta kara a kunne.

“Zinneera kina ina?”

“Tana nan Kaduna tare da ni”

“Hajiya ke ce?”

“Ni ce Nabeel, Zinneera tana nan tare da ni”

“Ke kika tafi da ita kenan?”

Sai ta fashe da kuka shi kuma ya kashe wayar. Kiransa na tsinkewa na Sadam ya shigo kamar yadda sunansa ya nuna a screen din wayar. Amsa masa tai ta fada masa duk abunda ya tambayeta sannan ta kashe wayar sai kuma ta danna ta kasheta gaba daya, tana ta kuka sosai kamar wani daga cikin yayanta ya mutu. Daker ta karasa girkin ta shirya ta koma asibiti, yadda ta samu Zinneera tana kuka sai yasa ita ta fashe da kukan tana ta rarrashin yarta. Bayan kuka ya tsagaita ne Zinneera ta fada mata dalilin guduwar da tai ta taho gurin ta saboda neman mafaka. Hannu ta kai ta kwanto da Zinneera saman cinyarta.

“Kin aikata kuskure Zinneera be kamata ki auri wani saboda wani ba, kuma be kamata ki kashe aurenki saboda wani ba, duk wanda ke son ki tsakani da Allah ba zai ce ki kashe aurenki saboda ki aureshi ba, sai dai yaji hukuncin Allah idan da rabon auren sai ki aureshi, duk wanda kika kashe aurenki saboda shi kika aure shi ba zai taba ganin kimarki ba, kuma ba zai miki kallon mai mutunci da daraja ba, be kamata ki ki maganar kowa saboda mutum daya ba, kin bi Zabin Rai kuma ya kaiki ga halaka, kamar yadda ni ma Zabin Rai yasa na rasa kima ta da daraja ta uwa a gurinku, amman ni dole ce ta saka saboda matsalar mahaifinku”

Zinneera bata ce komai ba bayan hawayen da take tana jin ranta yana sosuwa da abunda ta aikata, sai rashin adalcin da tai ma Sadam ya tsaya mata a rai har ta kasa hade yawu. Tasan dole Sadam ya kita bata ma cancanci ya so ta ba, a yanzu tana jin duk wata rayuwa da tai a baya kamar mafarki ne sai a yanzu ne ta farka.
Sai da aka kira azahar sannan Hajiya Karima ta baro asibitin ta dawo gida dan shirya abincin rana.

SADAM POV.

Misali hudu na yamma ya isa garin Kaduna, sallah kawai ya tsaya yai ya dauki hanyar gidan Hajiya Karima, da yai horn mai gadin be bude masa ba sai ta ya tambayi waye shi ya fada masa yaje ya fadawa Hajiya Karima sannan ya bude masa ya shigo. Mai gadin ne yai masa iso har cikin falon Hajiya Karima, Sadam be yi zaman minti biyar ba ta fito sanye da doguwar rigar atamfa da mayafinta fuskarta babu walwala, zaunawa tai a kujerar dake fuskarta ta Sadam yana ta kallonsa kamin ta ce.

“Kai ne Sadam?”

Ya gyada mata kai ba tare daya amsa da baki ba.

“Ina Zinneera take?”

“Tana asibiti”

“Wace Asibitin?”

“Kangiwa Special Hospital, Female Ward Room 004”

Jin yai shiru be ce komai ba yasa ta ce

“Yata tayi laifi, ta aikata abunda be kamata ta aikata ba, ta fada min komai a zaton kowa kasheka take kokarin yi bayan kuma ba haka bane?”

“Zinneera bata aikata laifi ba, komai Zinneera tai daidai a duniyata da duniyarta da duniyar duk wani mai tunani”

Ya fada mata kai tsaye yana kallon cikin idonta.

“Da baki tafi kin barta ba, da bata aikata abunda ta aikata ba, da kin yi hakuri irin hakurin da ko wace uwa take yi a gidan mijinta dan ta rike yayanta da kinci moriyar yarki, babu wanda kallon Zinneera a matsayin mai hankali, duk abunda ta aikata mahaukaciya ake kiranta babu wanda zai nuna illar abunda zata aikata da kuma alfanunsa, Zinneera bata da abokin fira balle shawara, Zinneera bata iya tunani kamar ni kamar ke kamar kowa, kin san saboda me?”

Kasa amsa masa tai sai hawaye take.

“Saboda babu uwarta a kusa da ita, da kina kusa da ita ba zaki yarda wani yai ma yarki kallon marar tunani ba balle har ya kirata mahaukaciya, ko da kuwa mahaukaciyace da gaske, zaki yi kokarin ganin kin gyara kin saitata ta zama ya kamar kowa, amman su duka can kallo marar hankali da tunani ake mata kuma babu wanda zai nuna mata abunda take na rashin hankali a natse sai dai ayi mata fada, wanda hakan ka kara ingizata, the more ake kiran mutum wawa ko mahaukaci the more wautarsa da haukarsa ke kara binsa, idan kuma mai hankali kuma ake kiransa mai hankali kullum hankali karuwa yake, to miye laifin Zinneera dan ta aikata abunda take ganin daidai a duniyarta? Mahaifiya Zinneera ta rasa mahaifiyar data kasa hakuri ta rike yayanta, da yanzu Zinneera ta tashi a karuwa ko wata kalar mace ya za ki yi? Duk yadda wata uwar zata so ta ba zata so ta kamar ke ba, amman sai kika 6ace a duniyarta kika shafe labarinki a duniyarta kika zabi rayuwa mai kyau ta jindadi kika kyale yayanki su yi rayuwa marar kyau kika bar su a talauci kika auri mai arziki.....”

“Ya ishe ka haka Sadam....!”

Ta daka matsa tsawa tana mikewa tsaye hawaye na sauko mata kamar ba gobe.

“Ko a kwana daya na dauki cikin Zinneera dole na so ta balle a wata tara, ban fito gidan mahaifin Zinneera dan na auri mai kudi ba, na fito gidan mahaifin Zinneera saboda na nemi na kaina, saboda na inganta rayuwata na nuna masa zan iya rayuwa ko babu shi a duniya, miyasa baka tambayi kanka dalilin samun wadata haka da nai yi ba? Kuma nake cikin jindadi? Sakayyace Allah yai Min, ban tana rokon Allah ya bani miji mai kudi ba, amman na roki Allah ya bani arziki da wadatar da zan iya rike kaina, sai kuma Allah ya bani mijin da ban taba mafarkin aure ba, saboda ban zalince mahaifin Zinneera ba, amman a haka na kasa samu kwanciyar hankali saboda babu Zinneera da Nabeel a kusa da ni, karka yanke hukunci abunda baka sani ba, karka jahilce ni akan abunda Mahaifinta ya fada maka....”

Sadam ya mike tsaye ba tare da yace da ita komai ba ya nufi kofar fita daga falon.

“Kuma karka je kusa da yata ka fada mata wata maganar marar dadi, dan Wallahi ba zan dauka ba, babu wanda zai sake kiran mahaukaciya babu wanda zai sake cewa tayi ba daidai, ba zan yarda rayuwarta ta sake shiga cikin matsala ba, itama tana da gata kamar kai....”

Juyowa Sadam yai ya kalleta, ta nuna shi da yatsa jikinta har rawa yake yadda take hawaye kawai ya isa ya isarda sakon cewa kalamin cdake fitowa daga bakinta har a zuciyarta yake, murmushi yai ya ce

“A yanzu na soma hango zuciyar uwa a tare da ke”

Yana fadar hakan ya juya ya ficewarsa zuciyarsa cike da zumundin son isa gurin masoyiyarsa.

ZINNEERA POV.

Tana zaune saman gadon rumgume da kafafunta ta dora kanta sama tana ta hawaye. Jin an turo kofar dakin ya shigo yasa tai saurin share hawayenta sannan ta juyo dan ganin ko wanene sai ta hango Sadam a tsaye yana kallonta, kallonsa take ciki da mamaki ba ta zaci zai nemi ta ba balle har ya zo kusa da ita, shi ma kallonta yake kallon tausayi da farinciki ji yake kamar yaje ya rumgume ta yai kissing dinta ya fada mata yana kaunarta da abunda ke ciki, kallonta yake babu ko kyaftawa ita kallonsa take idonta da kwalla kamar daman can an hallitosu ne saboda kawai kallon juna. Murmushi ya sakar mata sai tai kasa da kanta tana kwalla shi kuma ya karaso cikin dakin turarensa ya isar mata da sakon karasowarsa a gareta.
Kujeara yaja ya zauna yana kallonta ita kuma ta gagara dago kai ta sake kallonsa.

“Ba za ki ce komai ba?”

Ya tambaya yana ta lekon fuskarta kamar ya cinyeta.

“Na cancanci ka zo?”

“Ba saboda ke na zo ba, ba zan sokoto na zo Kaduna saboda ke ba, ban zo nan dan ke ba, amman zan iya barin sokoto na je ko ina ne a duniyar nan saboda abunda ya ke cikin ki, saboda jinina na zo saboda da na ko yata na zo....”

Hannu ta kai ta ta6a cikinta, bata tsammaci jin wata magana mai dadi kamar haka daga gareshi ba, Umma was wrong da ta ce Sadam ba zai so abunda zata haifa ba, ashe Sadam zai iya binta a duk inda take saboda cikinta?

“Miyasa kika gudu da cikina? Kina tunanin idan wani ya samu cikin zan yafe miki ne?”

Ta dago ta kalleshi

“Umma ta fada min ba zaka so abunda zan haifa ba, kuma ta ce na zubar da cikin saboda haka, ta cilasta ni zubar da cikin, Sadiq ma ya ki ni saboda ciki, ban san wani gurin da zanje ba shiyasa na gudu daga gidan kamin Umma tai min wani da zai zubar da cikin, ban san inda zan je ba, Mommy da Daddy fushi suke da ni shiyasa na zo nan, ban sani ba ko na yi daidai”

Wani lausayinta ne ya lullube zuciyarsa da ruhinsa. Hawayen dake mata zuba yana saukarsu har cikin ransa.

“Kin yi daidai Zinneera, amman Daddy baya fushi ni kuma bana fushi da ke, da kin zo gurina kina tunanin zan ki jinina ne?”

“Umma ta fada ba zaka so cikin ba, saboda abunda nai maka, kuma nima nasan ban cancanci na so abunda yake cikina ba, na cutar da kai da yawa, na yi maka abunda be dace ba....”

“Ke kika min ba abunda yake cikinki yai min ba, and Umma was wrong taya zan ki cikinki? And why on earth zata ce a zubar da cikin?”

“Nima ban sani ba”

Ta furta tana watsa da yatsun hannunta. Kallon hannun yai yana jin kamar ya kai hannu ya rika yatsun.

“Saboda kina da ciki Sadiq ya fasa aurenki? Ko wani abun ne dabam”

“Saboda ka kusance ni, yace indai wani namijin ya kwanta da ni ba zai iya aurena ba”

Ta fada da muryar kuka, Sadam yai murmushi.

“Zan iya tambayarki wani abu?”

Ta gyada kai

“Za ki fada min tsakani da Allah?”

Ta sake gyada masa kai.

“Kin yi alkawari?”

Ta gyada masa kai.

“Wa yake bin Sadiq naira miliyan ashiri?”

Ta hade yawun bakinta.

“Nima ban sani ba”

“Kin yi alkawarin za ki fada min gaskiya, ba zan iya samu ko da wannan a gareki ba?”

“Na masa alkawarin ba zan fada ba, wannan sirrinsa ne?”

Sadam ya ji babu dadi, sai zuciyarsa ta raya masa kamar har yanzu Zinneera na son Sadiq. Sai dai yana jin wani gurin kamar Zinneera bata san abunda take ke so ba, bata san inda ya dace tai son ba shiyasa son yake wahalar da ita.

“I know i shouldn't, fada min ya jikin na ki yake?”

“Wani ya kashe shine aka ce sai ya biya kudin fansa ko a akashe shi nan da shekara daya, shiyasa saka na aureka saboda na sama masa kudin”

“Zinneera kin san ya aijata kisan kan kuma kike son aurenshi?”

“Ban san ya aikata kisan kai ba, sai daga baya kuma dan na Sani be kamata na butulce masa ba”

“Haka ne, shima be kamata ya butulce miki ba, and idan zai gujeki saboda kin samu ciki ba, in har zai iya yi miki haka we can't keep this secret for him”

“Me kake nufi?”

Be amsa mata ba ya juya yana kallon Hajiya Karima wacce ta shigo cikin dakin dauke da kulolin abincin Suhail na rike da wasu sanye da rigarsa ta likitoci matarsa na dauke da wasu kulolin itama....

____________________

To fa Sadiq ya guji Zinneera ya hadu da mai yaya biyu 😑😲 har ya bani tausayi😪

5k words na yau yafi na ko wane page yawa. 😃 bari naje na huta 🚶🚶🚶

Đọc tiếp

Bạn Cũng Sẽ Thích

146K 9.9K 110
Fate of the innocent,,, A very heart touching story
Ice Cold Bởi m

Tiểu Thuyết Chung

2.3M 86.3K 50
[boyxboy] Wren Ridley is always two steps ahead of everyone, or so he thinks. His life seems out of his control when he starts having feelings for so...
22K 828 35
Kim Hana was a dense girl that hasn't learned the meaning of "love" until one day, a young girl would change her mind forever. Little did they know...
296K 21.6K 26
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...