ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

114K 15.7K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
44
45
46
47
48
49
50 End

43

1.5K 316 158
By KhadeejaCandy

Daure da tawul Suraiya ta fito daga bandaki da alama wanka tai. Sai ta samu Mommy zaune saman gadonta tana jiran fitowarta.

"Suraiya kin tabbatar ba ki fadawa kowa ba?"

Shine abunda Mommy ta fara tambayarta.

"Ban fadawa kowa ba, amman miyasa kike tsoron a aji?"

"To ai ba abun dadi ba ne Suraiya, yarinyar da tai kokarin kashe shi sai kuma yanzu ace zata haihu da shi? Haba wannan ai ba abun murna ba ne"

"Amman Mommy maybe cikin na shi ne fa"

"Na ji na san na shi ne ai, amman gaskiya ba zai zauna da ita ba, dan nasan yana sonta har yanzu zai yin kokarin maidata"

"Ba kin ce saki uku ba ne"

"Uku na ce yai shi kuma yai daya, Suraiya bana son yarinyar nan a yanzu, mu yi mata hallaci iya hallaci mun nuna mata so iya so, amman ta zabi saka mana da kashe Sadam? Gaskiya ba zan iya yarda ta haihu da shi ba"

"To yanzu me za ki yi?"

"Zubar da cikin za'ayi"

Suraiya tayi saurin kai hannu ta rike bakinta tana zaro ido.

"Kisan kai fa kenan Mommy? Aa gaskiya nima ba sonta na ke ba, amman be kamata laifin wani ya shafi wani ba, idan ta haihu da shi ba wani abu bane kuma nasan Sadam sai so abunda zata haifa"

"Yarinya ce ke karama Suraiya ba zaki gane abunda na ke nufi ba, bana son ki fadawa kowa maganar nan, kar Sadam yaji maganar nan balle Alhaji, kuma ina son ki yi mata allurar zubar da ciki tun kamin maganar samun cikin ta kawo gidan nan, nasan za su iya tunanin fadawa Alhaji ko Sadam dan haka ki yi mata allura kawai cikin ya zube ki yi duk abunda za ki iya a yau din nan ba sai gobe ba domin za su iya zuwa fadar cewar tana ciki...."

"Mommy Wallahi ba zan iya kashe rai ba"

"Cikin wata nawa ne?"

"Ban sani ba sai ta kai fitsarin an auna, Mommy dan Allah kar ki cilasta ni Wallahi ba zan iya ba, ko da na wani ne balle na Sadam, kuma Wallahi kin san duk yaji ba zai yafe min ba"

"Au fada masa za kiyi? Ni ban isa nai sirri da ke ba?"

"Ba zan fada ba. Amman gaskiya ni ba zan iya aikatawa ba"

"To ki jira ni zan yi da kaina tunda haka kike so"

Mommy ta fada a fusace sannan ta tashi ta fice daga dakin cikin bacin rai.

"Da na san haka abun nan zai zama Wallahi da ban fada ba..."

Cewar Suraiya cikin kukan da bata san da zamansa ba sai yanzu.

ZINNEERA POV.

Tana shigewa dakin, Umm ta nufi dakinta rike da baki tana ta salati kamar wacce ta ji wani mugun abu.

"Umma lafiya?"

Aleeya dake aikin gyaran dakin ta tambaya.

"Ina lafiya Ciki ne da ita...?"

Aleeya ta rufe baki da sauri.

"Ciki?"

"Eh daman ni naga alamar hakan"

"Yanzu ya za ayi kenan?"

"Zubarwa mana, idan aka bar cikin har ta haihu ke kina ganin Sadam din zai aureki ne? Kuma ai Yaya zai iya cewa ta a gyara auren tunda saki daya ne, ni ko wallahi ba zan bari haka ta faru ba, tunda ta zabi cimin mutunci ba kuma zan yarda ta je tai riba biyu ba, ai ba dan ke bana son ki samu jindadin ba na hanaki na goya mata baya, amman yanzu tunda na gano manufarta wargatsa zumuncina da Yaya wallahi ba zan bari ya lalace ba, kuma wannan jindadi sai dai wata ta same ko kuma ke amman ba ita ba"

"Amman Umma idan Sadam yaji an zubar da cikin zai iya dora mana laifi shi da Daddy da Abbah"

"Eh ai shiyasa na fada miki, dan bana son kowa ya ji, ai banga ta zama ba dole ayi abunda za ayi a zubar da cikin tun kamin ya girma ko aji, ai shi kina ganin Sadam din kamar be yarda ba zai iya kokarin mayarda aurensa"

"Amman Umma idan ni baya so na fa?"

"Yana son ki ai, ba ke ya fara so ba kamin ta zo ta wargazar da lamarin, sai yanzu na gane ma hassada ce tsagwanronta Wallahi, daman idan baka haifi dan ba dan kishiya ba zai taba son ka ba"

Ya karasa fada tana tana janyo hijabinta. Aleeya da ke binta da kallo tana nazarin maganganunta ta tambaye ta.

"Ina zaki je?"

"Ai ban ga ta zama ba, dole na je na samu yan abubuwan na fara tun yanzu"

A hanzarce ta fice daga dakin har ta kai kowa sai kuma ta dawo ta shiga dakin da Zinneera take kwance tana aikin kuka.

"Ke lafiya"

Jin muryar Umma yasa ta dan dago tana share hawayenta.

"Cikin kike yi ma kuka? Ki kwantar da hankalinki za a samu yadda za ayi a zubar kin ji?"

Ta fada cikin sigar rarrashi.

"Umma ba kyau zubar da ciki, kuma zubarwar ba zai amfana mana komai ba"

Cike da mamaki Umma take kallon jin irin furucin daya fito daga bakinta. Zaunawa tai kusa da ita tana kokarin fahimtar da ita.

"Zai amfana mana, ke za ki samu damar auren Sadiq din, kin ga idan har ya san kin haihuwa zai iya fasawa, kuma daga karshe Sadam din ya wulakanta ki da abunda za ki haifa"

Dagowa tai ta kalli Umma da jajayen idanuwanta.

"Ba zan iya sake aikata wani kuskuren ba Umma ko da hkan na nufi ba ni da hankali, ba zan iya kashe rai ba, ran ma kuma wanda yake a jikina, nasan Sadam ba zai so cikin nan ba, amman ni zan rumgume shi a matsayin kadddarata...."

"Amman ban taba tabbatar baki da wayo da hankali ba sai yau Zinneera..."

"Ban taba yin komai daidai ba, komai nai shirme ne, nawa tunanin dabam yake dana kowa, amman wannan karon Umma ko me za ki kira ba zan zubar da cikin nan ba"

"Ke baki da wayo, a cikin ba a busa masa rai ba, dan tayi ne, sun fada miki ko wata nawa ne?"

"Aa sai gobe idan sun dibi jinina"

"To kin gani, gobe sai kije a auna a gani idan be kai wata hudu ba, salun alun za a cireshi, kuma kin ga idan kika bar cikin nan Sadam ma zai iya cewa ba nashi ba ne, kuma mutane za su tai miki zargi...."

Zinneera ta fashe da kuka.. Har ga Allah bata son zubar da cikin nan, ko da kuwa Sadiq ne ya cilasta mata balle kuma Umma, tasan gaskiya ne abunda ta fada, ta ci amanar Sadam akan me zai so abunda zai fito daga jikinta. Amman ita ta shirya zama da cikin ko da kuwa hakan zai zama wani kuskuren. Umma ta tashi har zata fita sai kuma ta dawo ta karbi wayar Zinneera ta fita ta ita, hankalinta zai fi kwanciya da aje wayar a hannunta gudun kar Zinneera ta kira Daddy ko Sadam ta fada musu kamar yadda tai lokacin da zata fada musu cewar tana son Sadam.
Wunin ranar Zinneera kuka tai ta yi, kukan daya zame mata kala biyu, kukan butulcin da Sadiq yai mata, da kuma kukan cin amanar Sadam da tai, sai a yanzu take gane cewar abunda ta aikata babban kuskure ne, ga cikin da take da shi bata san makomarta ba.
Sai bayan sallah isha'i Umma ta shigo dakin dauke da kwanon ruwa mai wani garin magani a ciki, kusa da Zinneera ta zauna fuskarta gwanin tausayi ta ce.

"Zinneera ya jikin"

"Da sauki"

"Ungo wannan ki sha"

Ta fada tana mika mata. Kallon maganin kawai Zinneera tai bata karba ba ta soma magana cikin kasalalliyar murya ta masu jin yunwa domin tun da suka dawo daga asibitin bata saka komai a bakinta ba.

"Umma minene?"

"Maganine ki sha, zai taimaka miki"

"Umma dan Allah ki yi hakuri naji ana cewa har mutuwa ake gurin zubar da ciki"

Ta fada cikin kuka.

"Ke babu abunda zai same ki ai wannan cikin dan tayi ne, be kai irin wacan ba, kuma zubar da cikin nan shine kawai mafita a garemu"

Tun Umma na lallabata har ta soma yi mata da fada.

"To bari kiji na fada miki, matukar baki yarda an zubar da cikin nan ba, babu ruwana da ke, kuma wallahi abunda za ki ci sai ya gagareki a gidan nan dan kina ji kina gani zan dafa abu na hana ki, kuma Sadam ba son abunda za ki haifa zai yi ba, balle kuma iyayensa, ki koma wahala da shi kina daukar dawainiyarsa ke kadai, wata kila ma ki rasa wanda zai aureki da yaron ko yarinyar"

Umma na fadar hakan ta tashi ta fice ta bar mata dakin tana watsa mata harara. Hannu Zinneera ta dora saman kai ta fashe da kuka.

"Na shiga uku.... Ni dai bana da sa'ar komai a rayuwata...."

A gurin ta kwanta ta cigaba da kukanta, tana jin cewar ba zata iya shan komai dan zubar da cikin ba ko da kuwa abunda Umma ta zayyana mata hakan ne zai faru.....
Haka ta kwana da yunwa ga ciwon zuciya dake taso mata kamar zata fasa kirjinta ta fito. Washe gari bayan ta yi sallah asuba ta zauna saman sallayar tana ta tunani kala kala. Sai da ta tabbatar Abbah ya fita Aleeya kuma ta tafi makaranta sannan ta tashi ta jiki ba gwari ta fito waje. Dakin Nabeel ta nufa sai ta same shi ciki yana shirin fita, yana kallonta sai duk ta bashi tausayi gaba daya ta canja ta fita daga kamaninta kamar ba ita ba idanuwanta sai lumshi suke alamar yunwa da rashin karfi na tattare da ita.

"Zinneera..."

Ya kira sunanata sai ta amsa daga jikin kofar dakinsa da take tsaye.

"Ya Nabeel dan Allah ka taimaka min ka siyo min Indomie na ci yunwa na ke ji"

Ta fada idonta cike da kwalla.

"Ba ki ci Abinci ba?"

Bata son fada nasa cewar Umma ta hanata abinci tun jiya. Dan haka tai wata karyar.

"Bana komai sai indomie"

"Zinneera ko baki da lafiya ne? Ita kadai kike so?"

"Eh da kwai, kuma jiya naje asibiti amman basu dauki jinina ba sun ce sai yau dan Allah Ya Nabeel idan kana da kudi ka bani na hau Napep naje na kai musu fitsarin da jini"

Ta fada hawaye na sauko mata. Ajiyar zuciya ya sauke duk sai yaji wani iri tausayin yar'uwarsa ya kama shi.

"Zinneera ba ki yi ma kanki adalci ba, da yanzu kina can gidan mijinki cikin gata amman dubi yadda kika dawo duk duk lalace ga shi kowa yana fushi da ke"

Sakin labulen dakinsa tai ta juyo ta dawo dakinsu tana kukan nadama da bakinciki. Kwance tai dan bata jin karfin zama tana da kukan daya zame mata kamar dole, ta yi minti arba'in a haka sannan Nabeel ya shigo dakin rike da kula dayan hannunsa da bakar leda. Gabanta ya aje mata kular da ledar.

"Ga indomie nan an dafo miki, wannan ki hau napep din ki je idan aka baki takardar magani ki fada min"

Ya karasa yana mika mata dari biyar daya ciro daga aljihunsa. Da sauri ta tashi zaune ta karbi dari biyar din tana masa godiya.

"Na gode"

Bata damu da wanke hannu ba saboda ciwon da take ji, sai kawai ta bude kular ta saka hannu a ciki ta fara cin indomie, tsaya yai yana kallonta yadda take cin abinci har mamaki ta bashi.

"Idan aka dafa abunda ba ki so ki rika min magana na siyo miki wani abu ki ci, ba wai ki yi ta zama da yunwa ba, duk abunda kika aikata kin riga kin aikata idan kika sakawa kanki tunani da kin cin abinci zaki jawa kanki wata matsalar ne kawai"

"To"

Ta amsa tana auna indomie a bakinta. Sannan ya juya ya fice, ita kuma ta rika aika abincin a cikinta kamar ba gobe. Sai da ta ci ta koshi har ta raga sannan ta bude bakar ledar ta dauko gorar wow drink ta bude ta sha, a take cikinta ya daure har sai da ta kwanta na wani dan lokaci sannan ta tashi. Lekawa tai ta hango Umma na aje kwano gurin wanke wanke sai ta koma ta zauna ta dauki kular ta boye da a cikin dakin gudun kar ta gani tai mata fada. Tana zaunawa Umma na shigowa dakin ta mika mata wani dan mulmulen abu dake hannunta.

"Ungo wannan ki tauna"

Karba tai ta rike ba tare da ta tauna din ba kamar yadda Umma ta umarce ta.

"Cewa nai ki tauna ba ki rike ba"

Nan ma shiru bata ce kuma ba kuma bata tauna din ba. Hakan yasa Umma ta mika hannu ta karbu abun.

"Ba ni idan ba zaki ci ba ke kika sani, fito ki yi wanke wanke"

Sai a lokacin ta amsa da to. Umma har zata wuce sai kuma ta dawo ta tambayeta.

"Kina son fura na dama miki?"

Zinneera ta gyada mata kai alamar eh tana sha.

"To bari na dama miki yanzu nan"

Ta fada tana barin dakin ta nufi dakinta da zimmar idan ta dama mata furar sai ta saka mata abun a ciki. Tana shiga dakin ta ji an chafki kafafunta an ja su ta baya ba shiri ta fadi kasa sai jiri ya fara dibanta..

Zinneera na ganin Umma ta shige daki tai saurin daukar Hijab dinta ta saka ta dauki dari biyar din da Nabeel ya bata ta fito da sauri ta saka takalminta ta fice daga gidan da lababe gudun kar Umma ta ji motsin fitarta. Tana fita ta soke kanta kasa, domin har gobe tana jin kunyar gulmar da ake mata da kuma kallon kurilla da ake mata na gulma. Sai da ta kai titi ta tari napep ta hau ta kwatanta masa inda zai kaita.

Gidan Hajiya Karima ta nufo gidan data zauna lokacin da take a nan sokoto, gidan da ta taba zuwa da ita lokacin da Sadiq ya bukaci tai mata hakan. Gate din gidan ta buga sai mai gadin ya fito.

"Ina kwana"

"Lafiya kalau"

"Dan Allah Hajiya Karima na ke tambaya"

"Bata nan tana Kaduna"

"Eh na sani, amman Dan Allah Kaduna a wane unguwa take?"

"Baiwar Allah wace ce?"

Tayi shiru dan bata san me zata ce masa ba.

"Gaskiya ba zan iya fada miki ba, saboda matsalar tsaro"

"To na gode"

Ta fadawa Mai gadin sannan ta koma cikin Napep din.

"Nawa zaka kai ni tasha?"

"Wace tasha?"

"Tashar da ake shiga motar tafiya kaduna"

"Eh to kin san tasha ai ba daya ba ce"

"Wacce zan yi aurin samun mota"

"Bari na kaiki tashar babba ta nan gurin Hajiya Halima ki bada dari biyu"

Bata ko tsaya tayawa ba tace masa.

"To muje"

Suna tafiya tana saka Hijab tana kare fuskarta dan ganin take wani wanda ta sani zai iya hangota a Napep din. Bata bari ya shiga da ita ciki ba, daman suma masu Napep din ba son shiga ciki suke ba saboda biyan haraji, tun kan ya karasa cikin ta mika masa kudinsa ta fita ta doshi cikin tashar sai waige waige take. Tana shiga suka soma tambayarta ina zata je, sai ta ce musu.

"Kaduna zanje amman dan Allah taimako na ke nema"

"Na me?"

"Wallahi bana da kudin mota, kudina suka fadi dan Girman Allah ku taimaka min"

"Babbar magana ana wannan zafi"

Dayan daga cikinsu ya fada sannan ya doshi gurin mayansu ya shaida musu. Abun ka da hakin sakkwatawa a take a cikin yan union din suka hada mata kudin motar kaduna har da canjin dari biyu suka bata, bayan sun yi mata tambayoyi sai ta nuna musu bata da kowa a nan, gabanta sai faduwa yake tsoronta daya kartaga wanda ta sani ko ya santa. Gashi mahaifinta direba ne sai dai shi ta rawon mai ruwa yake dauka nasa passengers.

Cikin motar ta shiga ta zauna bayan an biya mata, tana jiran shigowar sauran passengers, zuciyarta nata raya mata karta ta tafi, gudun kar a sake cewa tai wani laifin, waya sani ko wani halin zata sake fadawa? Tabbas tasan idan har tai tafiyar Abbah da kowa zai kara fushi da ita ne, ta wani bangaren tana ganin kamar bata da wata mafita sai wannan duk da kasancewar Hajiya Karima bata sonta a yadda take gani. Tana cikin motar tana ta aikin hawaye tana sharewa har idonta suka kumbura suka jurma fatar idon tai ja.

'Komai ya bace, wata kila ma idan naje kaduna ba zan tararda ita ba, waya sani ma ko ba zata karbe ni, a ina ma zanje na ganta ban san inda take ba a Kaduna idan naje ina zan sauka?'

Cikin ranta take ta sake saken tana jin kamar ta fasa zuwan, sai dai kuma bata san me zata fadawa mutanen da suka hada mata kudin motar ba. A dole ta hakura har aka hada sauran mutane direban yaja motar suka kama hanya...
Babu komai a zuciyart sai tsoro tana ta tunanin inda zata sauka idan taje, ina zata fara nemanta idan taje, data tuna wannan sai ta fashe da kuka. Zuwa can bachi ta dauke ta bata farko ba sai da suka kusa isa Kaduna. Jin tai hannunta dake cikin Hijabi kamar a saman waya. Hakan tasa tai hanzarin bude idonta tana kallon mutanen dake cikin motar sai ta wasu n bachi wasu kuma na kallon titi. Sake lalubawa tai taji alamar wayar, shigar da kanta tai ta cikin hijabin tana dubawa. Wayarta ce sak, shafa screen din tai ta saka password sai wayar ta bude. Wani irin mugun faduwa gabanta yai har numfashinta sai ya soma gargada.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u"

Ta furta kadankadan yadda babu wanda ji, sai tai saurin kashe wayar gudun kar a kirata. Har suka shiga Kaduna babu abunda Zinneera take sai mamaki har ta manta da wani tunani can sai mamakin wanda ya kawo mata wayar take.

"Ko de ba tawa ba ce?"

Ta tambayi kanta.

"Amman miyasa ta bude idan har ba ita bace"

Sake kunna wayar tai ta shiga gallery tana dubawa taga komai nata a ciki kamar yadda wacan wayar take gashi har da hotunanta. Cikin hanzanri ta sake kashewa. Misalin biyar da mintuna suka isa cikin garin Kaduna, a tasha aka sauke kowa sai ta fito tai tsaye tana kallon mutane hannunta dake cikin Hijab na rike da waya dayan kuma rike da yan canji. Ji tai kamar ace tana da number Hajiya Karima ta kira ta fada mata cewar tana tasha amman babu wannan damar tunda bata da number ta. Gashi bata san wani inkiya da ake mata ba, balle ta fada ko an santa kuma bata san unguwar da take ba. Tafiya ta fara yi ta kofar da take hango mutane suna fita daga cikin tashar tana tafiya tana tunanin inda zata har ta fita cikin tashar gaba daya.
Sai da tai nisa da tashar sannan ta tari napep ta hau ba dan tasan inda zata je ba garin ya gwaraye da hadari.

"Malama ina zan kaiki?"

Tai shiru sai matsar yatsun hannunta take.

"Malama ina za muje?"

"Wata mata nake nema kuma ban san inda zan same taba"

"Wace unguwa take?"

"Ban san unguwar da take ba"

Juyowa yai ya kalleta dan a zatonsa gamo yai, sai yaga idonta da kwalla har suna zubar mata.

"Dan Allah yi hakuri ki sauka kinji"

Ya fada daidai lokacin da yake kokarin tsayawa gefen titi. Babu musu ta share hawayenta ta fita, shiga tafiya da kafa tana sharar kwalla, tana haka har aka soma ruwa. Masu gudu suna fakewa wani gurin suna yi ita kan sai tafiya take tana ta kuka sai da ruwan yai karfi sosai sannan ta nufi wani tsohon shagon kwano ta fake a gurin dake cike da shara ta fashe da kuka...
A gurin ta tsaya har sai da aka gama ruwan sannan ta fito ta cigaba da tafiyarta tana jin ana kiran sallah ga wata azabbabiyar yunwa da take cinta. Tunanin komawa tashar ta fara yi ta sake neman taimako ta koma sokoto tunda nan bata san kowa ba, sai kuma tai tsoron kar direban daya kawo ta ya sake ganinta ta yi the same karyar.
Tafiya take ta yi ba dan tasan inda zata je ba, har ta bullo ta wata unguwa mai manyan benaye. Bata san ta jefar kudin dake hannunta ba, har sai da ta hango wani shago na provision, sannan ta duba hannunta da zimmar ta siya ko biredi ta ci sai taga hannun nata wayan babu kudi sai waya, daman wayar da kudin a hannu daya ta jimke su.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u"

Ta fada tana mai tausayin kanta. Ga cikinta sai kugi yake kamar bata taba saka masa komai ba...
Matsawa tai baya can kofar wani kato gida mai simitin zama a waje ta zauna tana ta sauraren yunwar dake cikin cikinta tana mata yawo sosai. Wani tunanin ne ya zo mata sai ta doshi shagon provision din tana da addu'ar Allah yasa ya amince da alfarmar da zata nema. Baya ta tsaya har sai da ya sallami kowa sannan ta karasa ciki tai masa sallama, sai da ya amsa sai kuma ta kasa yi masa maganar abun ka da wanda be saba ba, sai kawai ta juya tai tafiyarta. A atsakanin jiya da yau tana cikin wani hali marar misaltu wanda ta tabbatar da za a auna jininta a yanzu za a tarar ya hau fiye da kima, shiyasa ciwon zuciya ya hanata sak tsakanin shi da yunwar da take ji bata san wa yafi wani zafi da rashin hakuri ba. Zuwa tai ta tsallaka titi sai taji an danno mata horn da mugu karfi kamar za a cire mata kunne, ba shiri ta saka hannayenta ta rufe kanta ta tsaya a gurin cak duk yadda mai motar yai kokarin taka burki sai da ya dan bankadeta har ta fadi sannan motar ta tsaya. Da sauri ya bude motar ya fito domin tuni Zinneera ta kai mike tsaye tana kokarin karasa tsallakawar...

"Malama ba kiji ciwo ba?"

Juyowa tai ta kalleshi tana masawa da a'a. Kallonta ya rika yi ita ma tana masa kallon sani. Nuna ta yai da yatsansa.

"Zinneera right?"

Sai ta gyada masa kai.

"Ke ce? Miya kawo ki nan"

"Gurin Hajiya Karima zanje"

Ta amsa masa da sauri.

"Kin gane ni?"

Tayi shiru tana da kallonsa tabbas taga fuskar sani amman ba zata iya tuna sunansa ba, da kuma a inda ta sanshi ba.

"Suhail Muhammad Dattijo"

Da sauri ta gyada masa kai.

"Eh na gane na gane"

Dan murmushi yai kamin ya aika mata da wata tambayar.

"Ke da wa kike zo nan?"

"Ni kadai"

"Ke kadai?"

"Eh gidan Hajiya Karima nake nema"

Kallonta yai ya sake kallonta ya sake kallonta sau uku da mugun mamaki. Wannan wace irin wauta ce ko dai ba ita din bace Zinneera mai kama da ita ce.

"Kin san inda take?"

"Aa"

Wayarsa ya ciro ya kira Hajiya Karima ringing uku ta daga.

"Hajiya ga wata yarinya na gani mai kama da Zinneera kuma tace ita din Zinneera ce gidanki take nema"

Daga dayan bangaren Hajiya Karima ta amsa.

"A ina ka ganta?"

"Ina hanyar gida na hadu da ita"

"Bata wayar"

Sai ya mikawa Zinneera iPhone din dake hannunsa, ita kuma tasa hannu biyu ta karba ta kara a kunne.

"Hello"

"Zinneera...."

Hajiya Karima ta kira sunanta a hankali sai ta amsa.

"Na'am.... "

"Bashi wayar ba shi wayar"

Ta fada da sauri, sai Zinneera ta mika masa, ya karba.

"Fada min inda kuka na zo na same ku"

"Bari na kawo miki ita Hajiya, ai tace gidanki take nema"

Yana kashe wayar ya budewa Zinneera motarsa ta shiga, sannan shima ya shiga ya daman a key take ribas kawai yai ya dauki wata hanyar. Yana driving yana satar kallon Zinneera har suka isa wani kasaitacce gidan zamani. Horn daya yai aka bude masa gate din gidan, tun kamin yai parking Hajiya Karima ta fito da gudu daga main house din ta nufo inda suke tana kallon Zinneera wacce ta fito daga cikin motar jini na bin kafafunta....

4k words 😲
Sai wani satin 🚶

Continue Reading

You'll Also Like

1.7M 141K 65
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...
8K 415 10
Authentic Dua's from the Qur'an and sunnah for all occasions to be implement on our daily routine.
190K 5.6K 25
/You Story. Y/N stumbles upon a girl in a bar that she falls in love with after sharing a kiss that night leaving her to deal with the aftermath that...
728K 14.2K 46
We have seen over protective brothers, there are maybe 6 , 7 or 8 brothers but what if a girl has 18 brothers, with her over protective parents and c...