ZABIN RAI

Від KhadeejaCandy

113K 15.7K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... Більше

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
43
44
45
46
47
48
49
50 End

42

1.3K 245 128
Від KhadeejaCandy

Wata kalar kunya ce ta baibaiye Zinneera lokacin da ta shiga dakin likita, duk wani bayani sai ta kasa yi idonta ma sai ta kasa dagawa ta kalli Suraiya wacce ke sanye da yellow lace ta dora rigar likitoci sama idonta sanye da farin gilashi, hannunta na dama kuma rike da pen tana kallon Zinneera. 
Sun dauki minti talatin a haka Zinneera ta gagara ko da dago kanta ta kalleta balle har tai mata magana sai matsar yatsun hannunta take.

“Me ke damunki?”

Suraiya ta tambaya kamar da fada.

“Ba komai”

Sai tai saurin mikewa tsaye zata fita.

“Look ni likita ce a nan, babu ruwana da damuwarki idan zaki fadi ciwonki ki fada idan kuma ba ki fada ba ke ta shafa”

Komawa tai ta zauna idonta cike da kwalla.

“Kaina yake yawan ciwo, kuma ina yawan bachi, da kasala, wani lokacin i a jin kamar zan yi amai kuma ba zan yi ba, ga yawan bachi”

Suraiya ta dan tabe baki tana kallonta.

“Yaushe rabon da ki ga al'adarki?”

“Yanzu ina cikin wata na uku”

Dan rubutu tai a takardar guda biyu ta ta mika mata sannan ta dago ta kalleta.

“Kije laboratory a baki wata yar karamar roba ki yi fitsari ki kawo min. Wannan kuma za ki basu jininki ne da fitsarinki sui miki text”

Hannu Zinneera tasa ta karba kamar wacce akaiwa kyautar kudi.

“Na gode”

Ta fada a sanyaye.

“Kar ma ki gode”

Suraiya cewar Suraiya tana watsa mata harara. A sanyaye Zinneera ta fice daga office din rike da takardun dayan hannunta kuma na rike da nikab din data cire lokacin da zata shiga office din ta nufi gurin da Aleeya take zaune tana jiranta kusa da ita ta zauna.

“Tace na kai wannan lab wannan kuma nai fitsari na kawo mata”

“To kije ki kai mana”

“ban san gurin ba”

“Tambaya za ki yi mana, ni ba zan iya tashi rakaki ba kuma mu dawo nan dan wahala”

Mikewa tai ta nufi hanyar fita daga ward din tana kallon wata mai tallar dafaffen kwai, har ta wuce ta sai kuma ta kira domin ranta ya biya sosai.

“Nawa kwai?”

“Naira hansin”

Ragowar naira talatin din siyan kati dake hannunta ta kalla.

“Za ki bar min talatin? Wallahi su kadai suka rage min”

“Aa ba a ce na saida haka ba”

Yarinyar na fadar hakan tai gaba, Zinneera kuma ta hade yawu ta cigaba da tafiyarta. Da tambaya da tambayar har ta isa gurin ta mika musu takardar sai suka ce sai taje ta siyo sirinjin da za a dibi jininta da shu, suka mika mata roba biyu wacce zatai fitsarin a ciki ta kawo musu daya, sannan suka nuna mata inda zata je ya siya dari uku na awon jini da fitsari.

“Zan iya bari har gobe saboda ban zo da kudin awon ba yanzu”

“Ba matsala duk lokacin da kika shirya sai ki kawo, daman ai sai gobe za a dauki jinin saboda ba a son ki karya kuma fitsarin na farkon safe zaki kawo mana”

“To na gode, dan Allah ina zan yi fitsarin?”

Macece ta kwatanta mata inda zata bi ta isa bandakin cikin asibitin. Kwatancen tabi har ta isa bandakin tai fitsari tai sarki sannan ta nufo hanyar dawowa. Wayarta ce tai ringing ganin number Sadiq yasa tai saurin dagawa.

“Hello”

Ya danyi jimmm sannan ya ce.

“Kin tashi lafiya”

“Lafiya kalau, ina asibiti”

“Miya same ki waye ba lafiya?”

“Bana jindadi ne shine Umma tace na je asibiti”

“Ba kya jin dadi?”

Ya tambaya da sauri.

“Me ke damunki?”

A take ta lisafa masa kamar yadda tai ma Dr Suraiya kanwar Sadam.

“Zinneera ina son ganinki idan kin fito asibitin nan”

“Amman tare da Aleeya na zo”

“Ki yi duk yadda za ki iya mu hadu, and ki fada duk abunda likitar ta fada miki kinji”

“To.. ”

Daga haka ya kashe wayar, ita kuma ta nutsa kai cikin ward din, zauna kusa da Aleeya tana jiran sai kowa ya gama fita sannan ta shiga ta kai mata fitsarin,  bata san ta nemi alfarma ta shiga ba.

“Ni na gaji da jira gaskiya gidan zanje, idan an gama sai ki dawo tunda dai ai kin san hanya”

Ban da binta da ido babu abunda Zinneera tai, wani abun daya tsaya mata a makoshi ta hadiye idonta ya cika da kwalla. Sam bata jindadin yadda Umma da Aleeya suke mata a yanzu, Abbah ma kansa ya canja mata bata taba sanin abunda zata aikata zai juyo mata kamar haka ba. A gurin ta zauna sai da kowa ya gama shiga sannan ta mike ta shiga dakin da sallama nikab dinta a hannu kamar dazu. Ko da ta shiga ta tarar Suraiya na hada kayanta da alama ta gama aikinta  sai ta gama komai sannan ta dago ta kalli Zinneera.

“Ya akai?”

“Ga fitsari”

“Je ki aje can”

Ta nuna mata wani guri mai kama da inda ake wanke hannu. Safar hannu ta saka sannan ta nufi gurin ta dauki wani dan abu mai tsawo ta bude fitsarin ta saka ciki, for few seconds ta cire ta zubar da fitsarin a gurin ta zuba wasu sinadaran kashe kwayoyin cuta ta gurin sannan ta zuba ruwa. Sai da ta gama sannan ta dawo gurin abun ta duba shi ganin layi biyu yasa ta juyo da mugun mamaki ta kalli Zinneera, sai ta sake duba abun ta sake kallon Zinneera again. A kwadon shara ta saka abun sannan ta dawo ta zauna still idonta na kan Zinneera baki bude take kallonta. Sannan ta dauki wata farar takarda ta rubuta mata magani ta mika mata.

“Kinje gurin text din?”

“Eh amman ban yi ba saboda ba kudi, kuma sunce da safe zan zo kamin na karya”

“Yes, wannan maganinki ne kije ki siya, and kina da ciki sai dai ba za a iya gane ko wata nawa ba ne sai anyi wacan gwajin fitsarin babba...”

Cikin rudewa Zinneera ta dafe kirjinta.

“Na shiga uku wane irin ciki?”

“Ciki na haihuwa mana”

Suraiya ta fada mata rai a hade. Da sauri Zinneera ta tashi ta fita daga dakin tana hawaye kamar ba gobe... Da sauri Suraiya ta tashi ta cire safar hannunta tana murmushi.

“Oh my God at long last Familyn Kazaure zasu samu first grandchild, am so excited”

Ji tai kamar ba zata iya jira har ta isa gida ta fada ba, dan haka ta dauko wayarta ta kira Mommy.

“Mommy Albishirinki”

“Goro”

“Wane irin goro za ki bani? Albishirin babba ne to all family”

“Lemmi guess, na samu suriki ne?”

“No no no Mommy Zinneera is pregnant....”

She thought Mommy would be happy amman abunda taji ya fito daga bakin Mommy yasa jikinta yayi sanyi.

“What? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u how when i mean a ina kika ji?”

“Nina auna fitsarinta yanzu nan, ta kawo kanta asibiti ne”

“Ba abun farinciki ba ne, kin fadawa Sadam?”

“Aa ban fadawa kowa ba sai ke”

“Karki fadawa kowa, idan kin gama aikin ki dawo gida da wuri”

“Okay ga ni nan zuwa na tashi aikin ma”

Ta aje wayar da jikinta a sanyaye.

ZINNEERA POV.

Bata san ta isa gate din asibitin ba har sai da wayarta tai ringing. Da sauri ta saka hannu ta share hawayen da sai a yanzu ta san da zamansu a fuskarta. Kowa kallonta yake a tunaninsu ta rasa wani jigo ne a rayuwarta, uba ko uwa ko kuma wani wanda ya zame mata bango majingina shiyasa saka take tafiya hawaye na mata zuba. Ta kara wayar a kunnenta tana sauke wani kalar ajiyar zuciya.

“Zinneera kin gama”

Jin muryar Sadiq yasa ta gane shi ya kirata. Sai kawai ta fashe da kuka.

“Lafiya kina ina?”

Daker ta iya daidaita numfashinta har ta bashi amsa.

“Na fito daga asibitin”

“Kina tare da Aleeya?”

“Aa ta tafi tun dazu”

“Okay ki hau Napep ki ce akawo ki Abuja Road zan zo na same ki a gurin”

“Okay”

Yana aje wayar ta cira kafa har ta karasa isa titi, ta tari napep din ta shiga ta fada masa inda zai kaita. Zuciyarta nata raya mata karta fada masa gaskiya, taya ma zata kalli idonsa ta fada masa cewar tana da ciki bayan ta fada masa Sadam be yi komai da ita ba, idan kuma ya ji a wani gurin fa? Ai kara ma ta fada masa da kanta komai daren dadewa zai sani amman idan ta fada masa wata kila abun zai iya zuwa mata da sauki. Har ta isa gurin bata samu matsaya daya a zuciyarta ba, na fadin ko akasin hakan.
  A cikin itatun da suke gurin ta tsaya ita da mai Napep ta kirashi tace sun iso, sai ya shaida nata cewar gashi nan ya kusa karasowa gurin. Ba a dade ba ya iso da motarsa ya fito ya bawa mai Napep din kudinsa sannan suka karasa gurin wata kujerar gini suka zauna.

“Me suka ce miki asibitin?”

Shine abunda ya fara tambayarta lokacin da suka zauna. Sai ta dago kanta ta kalleshi da jajayen idanuwanta sai kuma ta kasa cewa komai.

“Tell me wani ciwon ne?”

“Sun ce ina da ciki ne”

Ta fada masa kai tsaye ganin kamar boyen ba zai haifar mata da d'a mai ido ba. Yar dariya yai ya juya kansa kamin ya juyo ya kalleta, yasan ba wasa take ba, hawayen idonta kadai sun isa su tabbatar masa da gaskiyar furucinta.

“Ciki na tuwo ko na haihuwa?”

Ta yi shiru kwalla sai zubar mata suke.

“Taya to? Ba kin ce Sadam be kai ga jikinki ba? Ba kin ce be yi Sex da ke ba? A ruwa kika sha ko taka shi kikai?”

“Sau daya ne Wallahi kuma ban dauka....”

Ya tari numfashinta tun gabanin ta karasa fadar abunda ke bakinta.

“Ba ki dauka me ba? Miyasa kika boye min?”

“Na boye maka ne saboda....”

“Saboda me....!”

Ya daka mata tsawar data haddasa mata kyarma tana kallonsa a razane. Ya mike tsaye yana kallonta gumi na keto masa ta ko'ina.

“Saboda kin maida wawa ko? Akan me za ki min karya? So kika da ciki be shiga ba sai na aureki na tarar wani ya rigani ko? Wani ma kazami kamar Sadam..!”

“Miyasa ba zaka aureni dan Sadam ya sadu da ni ba Sadiq? Idan ma na haihu zan bashi yarsa ne sai na aureka”

“Oh Really? Nooo ba zan auri ragowar wani ba, ba zan yi kiwonki shekara da shekaru ba yanzu kuma ki fito na aureki ban mori komai ba”

“Kana tunanin wani abu ya ragu daga jikina ne Sadiq?”

“Ya rago mana! Ke kamar da ce? Yanzu Mama za a fara kiranki kin haifawa wani d'a wani wanda ba ni ba, kuma wani ya kai ga jikinta ya mori komai ni kuma kin dawo min da ragowar, ai yanzu kin tashi daga budurwa zuwa wata dabam, dacan kin san ya kai ga jikinki akan me za ki kashe aurenki? Allah ya tsare ban riga na aureki ba da bakinciki da bakin kishin wani ya kashe ni, ke wai wace irin mahaukaciya ce Zinneera... ”

Ta hade yawu da karfi tana kallonsa.

“Ba mahaukaciya ba ce ni Sadiq, na gane sai yanzu jikina kake so ba ni ba, ba son tsakani da Allah kake min ba, saboda ka amfani da jikina kake so ka aureni”

“Ba ni da wata manufa dabam akanki Zinneera tsakani da Allah nake son ki, amman ba zan iya kallonki a matsayin matar wani ba kamin ni, tun farko ke kika ci amanata Zinneera sai da na ce karki yi auren nan amman kika biyewa Zabin ranki kika aureshi yanzu kuma kin dawo ki yaushe ni saboda wawuyace ke”

Kai ta girgiza tana wasu kalar hawaye masu ban tausayi.

“Ban taba yin komai daidai ba a duniyar ka kai da Umma, komai nai sai ku ce min wawuya mahaukaciya, saboda kai nai auren nan Sadiq shin baka gani ne? Na bata da kowa saboda abunda na aikata kuma duk saboda kai ne, mafita nake son nema maka saboda ka rayu ko dan mahaifiyarki da yan'uwanka, saboda na ceci ranka na auri Sadam dan sama maka kudi, amman duk baka gani ba, sai kyamata kake yi? Na rabu da mai so na tsakani da Allah saboda kai Sadiq sakamakon da zaka min kenan?”

“Au duk wannan abun da kika min ma ke kika da bakin magana? Ni zaki fadawa kin rabu da Sadam? To sai ki koma yanzu ai ga dalilinan kin samu”

Yana fadar hakan ya wuce fuuuu ya nufi motarsa cikin wani irin bacin rai marar misaltuwa. Hannu ta kai ta dafa kirjinta motsin zuciyarta take son ta ji so take ta tabbatar a raye take ko a mace, da gaske Sadiq ne yai mata haka? Mutumen data salwantarda farincikin kowa saboda shi, lallai yau ta tabbatar rayuwarta bata da amfani... Faduwa tai kasan guiwoyinta tana ta son tai kuka amman ta kasa, idonta kawai ke zubarda da kwalla bakinta ya ki fitarda amon kukanta, ciyayen dake gurin ta soma lalaba kamar mai neman wani abu, sai kuma ta shiga tsinka ciyayin tana jefarwa, kamin ta koma gefe daya ta rumgume hannayenta. Ta fi minti talatin a haka sannan ta tashi da sauri ta nufi inda ta watsar da takardar maganin da katin asibitin da chanjinta naira talatin ta nufi titi nikaq din ma a nan ta barshi.

Napep ta tara ta hau ta fada masa inda zai kaita, babu kokarin da ba tai ba ta samu tai kuka amman kuka ya ki zo mata har ta isa gida. Fita tai tace da mai Napep din ya jira ta kawo masa kudi, gidansu Zainab ta shiga ta karbo naira dari ta mika masa sannan ta nufi gidansu.
   Da sallama ta shiga sai dai sallamar bata fita sosai saboda muryarta a dakile take, Umma dake rike da tsinsiya ta amsa tana kallon yanayinta.

“Wa'alaikissalam kin dawo”

“Eh”

Ta amsa kasa kasa.

“Me suka ce?”

Ta yi shiru bata ce komai ba.

“Ko ciki ne?”

Umma ta tambaya. Sai ta gyada mata kai alamar eh. Ba shiri Umma ta daki kirji ta saki tsintsiyar ta nufota tana fadin.

“Ke ciki? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, kar ma ki bari kowa ya ji wannan maganar, ko Abbah ki balle Nabeel, wannan ai sai zubarwa”

Zinneera ta kalleta da sauri.

“Zubarwa Umma? Wallahi ba cikin shege ba ne, na rantse da Allah wannan cikin na Sadam ne Allah shine shaidata ban taba kusantar wani namijin ba idan ba Sadam ba”

Ta fada tana wani irin narkewa tana rike hannayen Umma kamar zata shige cikin jikinta.

“Na sani ai, amman Zinneera kina tunanin Sadam zai so wannan cikin na ki ne? Bayan duk abunda kika masa? Ai daga shi har yan'uwansa ba za so ki ba balle su so abunda kika haifa, kuma Sadiq ba zai aureki ba duk kika haihuwa kin ga kin yi two zero, dan haka kara ma a zubar a huta tun kowa be jiba...”

Fashewa Zinneera tai ta wani irin kuka mai tsuma zuciya ta saki hannayen Umma ta nufi dakinsu da gudu...

________________________

Ina yi mana Barka da shiga shekarar musulunci. Allah yasa muna cikin wadanda aka gafartawa wacan shekarar, kuma Allah yasa muna cikin wadanda za a gafartawa a wannan shekarar. Allah yasa mu cika da kyau da imani Allah ya shiryarda mu ya dora mu akan tafarkin tsira, ya kara mana son Annabi Muhammadu Rasulullahi Sallalahu Alaihi Wassalam.

Ameeeen.

Продовжити читання

Вам також сподобається

3.9K 316 22
Mutane kala uku ne a duniya. Na farko masu rauni Na biyu masu karfi Na uku masu bada umarni A ko ina ma duniya suna raye. Suna kasuwancin su ne akan...
446K 17.7K 48
Vikram, a senior officer, prioritizes his duty above all else, much like his father, ACP Rajendra. He has three siblings: one is an officer, and the...
She's their life Від imaginerkives

Підліткова література

727K 14.2K 46
We have seen over protective brothers, there are maybe 6 , 7 or 8 brothers but what if a girl has 18 brothers, with her over protective parents and c...
146K 9.9K 110
Fate of the innocent,,, A very heart touching story