ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

114K 15.7K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

40

1.7K 386 57
By KhadeejaCandy

“Taya taya?”

“Naje gidanka da zimmar n fadawa mahaifiyarka cewar kana asibiti sai na tararda gidan a hargice kofar kuma a bude, ta nan na ci karo da wannan littafin”

“Ba nawa ba ne”

Ya fada yana kokarin boye mata, bayan ya gama jin abun har cikin jininsa.

“Kai ne sunanka ne da na yarinyar daka kira lokacin dana kadeka”

Zaunawa tai saman kujerar tana kallon tashin hankalin dake cikin idonshi.

“Rayuwarka abar tausayi ce Sadiq kuma tabbas kana ciki hadari...”

Ajiyar zuciya ya sauke ya rasa inda zai saka kansa yaji sanyi, Zinneera ta tona masa asiri ita kuma wannan ta san komai, hakan na nufin mahaifiyarsa da yan'uwansa na kusa da jin komai, indai har hakan ne zai faru ba zai zauna garin ba, tomin ba zai yarda ayi ta yi da shi ba. Can a cikin duniyar tunaninsa ya cinkayo Ummi tana watso masa wasu kalamai da suka soma kwantar masa da hankali.

“Abunda ka aikata abu ne mai kyau Sadiq, domin ceton mahaifiyarka kai yi gashi kuma tana raye, ni kuma na rasa tawa Mahaifiyar duk kuwa da irin tarin dukiyar da muke da ita... Na san daraja uba tun daga lokacin dana rasa tawa sai nake ganin kima ko wace mace mai amsa sunan uwa...
   Zuciyata cike da tausayin abubuwa biyu daka rasa, masoyiyarka wacce ta zabi wani saboda kai, da kuma kwanciyar hankali da natsuwa daka rasa na abunda ka aikata. Haka wani lokacin abubuwa suke zo mana ba yadda muka tsammace su ba, amman tabbas ka cancanci farinciki Sadiq”

Komawa yai ya kwanta ya fada duniyar nazari. Can kuma ya dago ya kalleta.

“Za ki iya min wani abu?”

Ta gyada masa kai.

“Za ki iya aje min wannan sirri a cikinki?”

Dan murmushi tai kadan ta soma wasa da yatsun hannunta.

“Idan har ba zan aje maka wannan sirrin ba, ban da dalilin zubar da hawayena a kanka ba”

“Wane tabbaci nake da na cewar ba za ki fadawa kowa ba”

Tai shiru har na tsawon lokacin sannan ta ce.

“Saboda abunda zan aikata, ba zan kowa ya san sirrina ba mussaman mahaifina”

“Ban fahimta ba”

Tashi tai tsaye tana kallonsa.

“Yanzu dai ya kamata ka huku tukuna, sannan wani abun ya biyo baya...”

Kayan tea data shigo da su ta shiga hada masa, sannan ta shiga toilet din dakin ta dauko wata ruba ta tara masa ya wanke bakinsa sannan ya sha tea, bayan ya gama ya sauko yana takawa daker ya shigo toilet din yai alwala ya fito yai sallah daga zaune, sannan taje ta kira nurse ta duba shi ta bashi magani tare da wasu allurai. Bayan nurse din ta fita ne ya sauko ya dauki wayar daya jefar, abun ka da nokia ba tai komai ba sai dai marfin ne ya tsage battery kuma ya fita, sai da ya maida battery sannan ya kunna wayar. Sakon mtn ne ya fara shigo masa kamin na Zinneera ya biyo baya.

_Wallahi ban Fada ba Sadiq ka yarda da ni, ban fadawa kowa abunda ka aikata ba, kawai na ce bashi ake binka_ 

Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama karanta sakon, yai farinciki Sadam ya saketa amman a yadda sakin ya zo masa ne be yi masa dadi ba, zai tabbatar da gaskiyar maganar cewar bata fadawa kowa ba ne idan har ya ganta face to face. Number ta yai dialing me kamar daman can jiran kiran take nan da nan ta daga.

“Kina ina yanzu”

“Ina gidanmu”

Ta amsa tana ta kokarin danne kukan dake son hanata magana.

“Kin koma karanta?”

“Aa sai next week”

“To idan kin koma ina son na hadu da ke mu yi magana”

“To amman Wallahi ban fada ba, taya zan fada musu asirrinka?”

“To ya akai yasan da maganar?”

“Sakon daka turo min ne, kanwarsa Suraiya ta gani saboda wayar tana hannunta sai ta dauko ko kisa kake nufin mu aikata, kuma na saka masa maganin bachi shine suka dauka da gaske ne”

“Akan me kika saka masa maganin bace? Ko dan kar ya kusance ki ne?”

Ta gyada masa kai kamar yana gabanta.

“Eh”

“Good girl, amman ke wace irin wawuya ce da zaki bar wayarki hannun wani bayan kin san zan iya kiranki ko da yaushe”

Tai yi shiru sai hawaye take.

“Idan kin shiga scul ki kira ni”

“To na gode”

Ta fada kamar wacce ta roki abu aka bata. Shi kuma ya kashe wayar ba tare daya rarrashe akan ta daina kukan da yake jiyo sautinsa ta cikin karamar wayar tasa ba, he just don't know why yanzu yake jin rashin damuwa da kukanta, ba kamar da ba da yake jin hawayenta kamar jinin jikinsa ne yake zuba, and shi be ma jidadin mutuwar aurenba a yanzu indai har tonon asirinsa ne zai saka Sadam ya saketa to babu tantanma yaji sirrinsa, da aika mata sako kawai be isa ya saka shi sakinta ba, taya ma zai saketa ba tare daya ji dalilin kudin da ake binsa ba. And he don't believe Sadam zai saketa hakan ne kawai ko kuma daman can yana neman dalilin sakin tunda ya gama da ita wata kila yasha zumarta shiyasa yaji baya bukatarta a yanzu, anya Zinneera ba boye masa take ba.?
Yai zurfi a duniyar tunani har sai da kalaman Ummi suka dawo da shi.

“Da nine kai ba zan taba kallon yarinyar nan ba, balle har na kira na ji irin makircin da zata shirya min”

“Sai Kum gashi ba ke ce ni ba”

“Shiyasa ai na rigaka gane karyarta”

Ta fada yana jan kujerar dake facing dinsa ta zauna. Da ido ya bita har ta soma dora masa da wasu kalaman.

“Idan har da gaske yarinyar nan taimakonka zatai miyasa ba tai wankakau ba ko kuma tai ga aiki, ko kuma ta kirkiri wata sana'ar ta daban da zata iya taimaka maka ka samu kudi, amman ba wai ta aure wani ba, kuma dan ta raina maka hankali tace saboda kai tai kai kai kuma ka yarda, idan har da gaske ne miyasa ba tai amfani da mutumen ba ta saka ya samo maka babban aiki ko kuma wata hanya da zaka samu kudin ba, ko kuma ita ta samo ta baka?”

Sadiq ya natsu sosai yana nazarin kalamanta.

“A yadda na karanta a littafinka, kace ta aikata hakan ne saboda mutumen yace sai ka bashi kudin nan da shekara daya, taya zata samu miliyan ashirin nan da shekara daya dan kawai ta auri billionaire? Kai tsaye zai dauki kudin ya bata ba tare da wani dalili ba? A kaddara kyautar mota yai mata, ta miliyan ashirin ko sama da hakan, kasan manyan motoci irin wadannan basa boyuwa a garin nan ko? A take za a kama wanda ya sace ta sai a tarar kai ne, ga ta jefaka cikin wani halin kenan, idan kuma ta siyarda motar ko zinari ko gida ta baka kudin shi dole zai san inda kudi suka je, ta nan kaga asirinka ya tonu, a taikace babu wata mafita da yarinyar nan zata sama maka kudi naira miliyan ashiri a shekara daya kai tsaye ta baka. A magana ta gaskiya ta tsakani da Allah abunda na fahimta Yarinyar nan ta guje maka ne kawai ta auri wanda ya fika kudi yadda zata samu ta dama, kuma ta gujewa abunda ka aikata, domin za tai tunanin kamar ko yaushe za a iya zuwa a kashe ka, saboda baka da kudin, ko kuma wani abun ya faru, idan har babu son ranta miyasa iyayenta suka amince? Suma basa son aurenka da ita kenan?”

Ta fada masa gaskiyar abunda analysis dinta ya bata, domin iyakar gaskiyar tunanin da abunda ta fahimta Zinneera ta cuce shi ne kawai tai aure ba wai saboda shi ba.

“Ina fada maka duka wannan ne saboda, bana son ka sake shiga wata damuwar, bana son wani ya sake yin shirinsa kuma yai galaba akanka ya saka cikin damuwa, a yanzu farinciki da kwanciyar hankali ne kawai abunda kake bukata”

Wani dogon numfashi yaja ya sauke ya runtse yana son kin yarda da kalamanta duk kuwa da kasancewar wani bangare na zuciyarsa na raya masa cewar hakan shine gaskiya.

“Amman ke ina ruwanki da rayuwata...?”

Ya fada yana bude idonsa ya kalleta, sai tai murmushi ta kalli Mama wacce ta turo kofar dakin ta shigo...

ZINNEERA POV.

Tana aje wayar ta hade wani abu dake mata yawo a makoshi, hankalinta ya dan kwanta yanzu jin da tai kamar Sadiq ya yarda da ita, domin idan har din ma ya rika ganin laifinta to babu inda zata juya ta ji sanyi, idan har aka ce wanda ta aikata dominsa ya juya mata baya.
    Tasan Sadam be cancanci abunda ta aikata masa ba, sai dai abun ya zo mata ne ta yadda ba tai tsammani ba, a iya abunda ta tsara a rayuwarta zata bi hanyoyin da zata samu kudin ta bawa Sadiq sannan ta bullo da wata hanyar ta dabam da zata saka Sadam ya saketa. Amman yanzu komai ya cha6e mata, ta 6ata ran mutane da dama ta 6ata ran Umma a maimakon ta farinta mata tai kyautata mata, ta 6ata ran Daddy da Mommy, yau kuma duk son da Abbah yake mata ya juya mata baya saboda a abunda ta aikata. Kuma tasan za ayi tai yi da ita ne a unguwa ace auren da aka daura shekaranjiya ya mutu har ta dawo gida. Sai yanzu take ganin rashin kyautawa da tai na auren Sadam tun farko, miyasa ba tai wani bare can ba ko kuma ta nemo wata hanyar amman ba irin wannan data saka ta batawa kowa rai ba.

Tunda Umma ta zari Hijab ta fita Zinneera na cikin daki har tai abunda za tai ta dawo. Bata fito ba sai da akai kiran sallah azabar shima kuma sai da taji Umma ta shige dakinta, tana kunyar hada ido da ita, ga wani uban tsoronta da Allah ya saka mata yanzu, ba tsoro na ta daketa ba, tsoro na yi mata mumman furuci ko fada mata wata kalma marar dadi. Lokacin da tai sallah azahar ne ta shigar da akwatunan cikin dakinta sannan ta koma ciki ta gabatar da sallah, tana zaune a gurin har aka kira sallah la'asar, bayan ta gabatar ta dauki carbin da ke dakin tai ta lazimi, duk shiga da fitar da Aleeya da kanenta ke yi cikin dakin bata yarda ta hada kai da su ba, sam bata dauka abunda ta aikata yana da girma basai yau, kunyar kowa take ji ciki kuwa har da Aliyu da yake karamin kanenta. Haka ta wuni har magariba tana jin lokacin da Umma ta kira Aleeya da Larai da Aliyu ta basu abinci rana ita kam ba a bata ba, sai da aka gama na dare daman shi Nabeel ba dawowa yake gida da rana ba sai jifa jifa.
  Lokacin da Aleeya ta shigo dakin daga tsaye ta miko mata abinci tana tabe baki.

“Wallahi na tabbatar da ace Umma ce ta haifeki da cikinta da ba zaki mata abunda kikai ba, kuma da na san ba dan Allah kika auri Sadam ba, da ban bari ko kamshin rigarsa kin ji ba, ana ganin ki marar wayo ana tausaya miki ashe makira ce,  kin ma wuce makira kin zama yar ta'adda tun da ransa kike nema kuma ki kwashe duniyarsa, ko kunya ba kya ji”

Kasa karbar abincin Zinneera tai tun da ta daga kai tana kallon Aleeya kalamanta ke sukarta zuciyarta kamar ana yanka namam jikinta. A yanzun ma kwalla ne suke ta zubar mata ta kasa cewa komai kamar wacce aka daurewa baki. Dukawa Aleeya tai ta aje mata abincin ta fita, duk irin yunwar da Zinneera take ji sai taji abinci ya fita mata a rai, eyes ball dinta har ciwo suke saboda kukan da sha yau.
  Bata taba jin ta tsani kanta ba kamar yau, kowa ya juya mata baya, komai ya chabe mata...

SADAM POV.

He spend more than one hour a gafen titi sannan ya dauki hanyar gidansu, sai da ya faka motarsa a gidan sai kuma yaji yana son kasancewa shi kadai, sai dai baya son idan ya zauna ya rika tunanin Zinneera ko abunda ya shafeta so yake ya shafeta a tarihim rayuwarsa, wanda yasan ba zai iya yanzu ba, amman idan ya soma gwadawa zai iya.
  Ba taba jin zalumci da cutarwa ba irin yanzu, idan aka bashi biro da takardar aka ce ya rubuta azzalumi a yanzu, sunan Zinneera zai rubuta ba dan komai ba, sai dan aurensa da tai bayan ta san Sadiq take so, da ace ba ta aureshi ba zai iya jurewa ya auri Aleeya ko waninta ya zauna da ita ta koyawa kansa sonta har ya saba. Amman komai ya zo masa ba a yadda yake tsammani ba, yana murnar ya aureta sai kuma ya tarar saboda wani ta aureshi, and the most saddest part maybe bata taba sonsa ba.
   And what he feels right now is like kamar an raba zuciyarsa da gangar jikinsa, zafi yake ji a ko wane bangare na kashinsa kamar an azabbatar da shi, be taba tsamman shiga wannan yanayin ba, duka duka yaushe yai auren nan? Ace yanzu kuma har ya rabu da ita, be taba samman zubar da hawayensa akan wani makamancin wannan ba, kuka yake sosai kamar ance masa Mommy ko Daddy ya rasu, shi kansa ba zai iya tuna rabonsa da irin wannan kukan ba, tun yana karami amman a yau gashi yana zubarda da kwalla muryarsa na amsa amo yana bugun sitari kamar karamin yaro saboda Zinneera.

“Why Suraiya why? Miyasa ba ki barta ta kashe ni ba? Why on earth baki bar ni na san Zinneera wani take so ba ni ba?”

Kokarin dora laifin yake akan yar'uwarsa, har yanzu ya kasa ganin laifin Zinneera sai dai idanuwansa ba zasu daina ganinta azzaluma ba, zuciyarsa kuma ba zata daina kaunarta har ta koma ga mahallincinsa. Pink lips dinsa sun yi ja sosai kamar an shafa masa janbaki saboda taunarsu da yake. Tissue paper dake cikin motar yasa ya share hawayensa ya gyara fuskarsa yadda Mommy ba zata gane ba, sannan ya maida facing cap din ya saka bakin gilashi ya bude motar ya fito zuwa cikin gidan.

A falo ya samu Mommy da Daddy har ma da Suraiya, Siyama ce kawai bata nan kasancewar yau Thursday akwai scul. Lokacin da yai sallama ya shigo all what he try to do is smile ta yadda zai nuna kamar abun be yi effecting nashi ba amman ya kasa, guri ya samu kusa da Suraiya ya zauna yana gaishesu.
Da mugun tausayi Mommy take kallonsa tana amsa masa. Kamin Daddy ya dora da zancen da Sadam ya tarar suna yi.

“Sai zuwa gobe, zan je na samu Commissioner of police, a kira Sadiq da iyeyensa ayi musu gargadi duk abunda ya samu yarona shi zan sa a kama”

Sadam ya cire gilashin idonsa ya dago ya kalli Daddy.

“Daddy ba sai an yi wannan ba, komai ya riga ya wuce, and i don't think Zinneera zata iya aikata kisa ko da kuwa sata akai, auren yake nufin ta kashe kuma na gamsu da hakan, and babu wanda zai iya maka abunda Allah be maka ba, kuma Daddy i already divorce her...”

Daddy ya kara kallonsa da mamaki.

“Ka sake ta? Sadam da dai ka bari an yi bincike, so babu abunda baya isa sakawa, amman Zinneera yarinya mai karamar kwakwalwa ba wani wayo ne da ita ba, duka fa shekarunta goma sha bakwai ne ko sha takwas, zai iya yuwa yaudararta yai, tunda shi zai iya bin ko wace hanya dan ganin ya kashe maka aure, tunda shi ma yana sonta kuma yarinyar nan ance tana da aljanu kasan kuma mai irin wannan lalurar ba cikakken hankali ne da su ba, kuma ta haka za a iya gano wani abun ma da ba a san da shi ba... Sadam ba a saurin saki sai idan abu ya kai ya kawo kuma ya ci tura, yanzu ko da gaske tana da niyar aikata kisan kai, ba zata aikata ba tunda ta san an gano gaskiyarta kunya ma zata ji”

Sadam yai kasa da kansa. Sai Mommy ta ce

“Ni na saka ya saketa domin barazana ce a rayuwarsa, ban ga amfanin zama da mai son kashe ka ba...”

“What...! Ke kika saka ya saketa? A matsayinki na wa? Dam kina mahaifiyarsa sai ki saka shi ya tsaba ma Allah? Kin fi kowa sanin yadda danki yake son yarinyar nan yanzu kuma da kika saka ya saketa ba kisan wani abu zai iya biyowa baya ba? Be kamata kima shiga rayuwar aurensa ba, ki barshi a karon kansa idan ya gaji da ita ko kuma ya gano gaskiyarta sai ya zabi zama da ita ko rabuwa...”

“Amman Alhaji wannan yarinyar baraza ce ga rayuwarsa...”

Daddy ya tari numfashinta.

“Sadam ya fi tazama barazana ga rayuwarta, domin za a iya garkuwa da ita saboda ke ko mu tunda ansan muma da kudi, waya sani ma ko cilasta mata yai akan sai ta aikata ko kuma ya kasheta? Wai meya saka baki tsayawa ki yi tunanin kamin ki aikata abu? Mtscheeeeeee”

Ya karasa yana jan tsaki cike da bacin rai.

“Saki nawa kai mata?”

“Uku”

Mommy ta riga shi amsawa, a dole ta saka Sadam yai shiru be ce komai ba.

“Daddy ban ga amfanin zama da yarinyar nan ba, shi hankalinsa ba zai kwanta ba muma na mu ba zai kwanta ba”

Suraiya ta fada tana kokarin fahimtar da Daddy dan kar ya dora laifin akan mahaifiyarta. A take Sadam ya katsa mata tsawa har sai da ta razana.

“Will you shut up?”

Ba Mommy kadai ba har Daddy kallonsa yake yadda yai maganar ya nuna cewar ransa a bace yake. Sallamar Umma ce ta dago da duka hankalinsu Daddy ya amsa mata ita kuma ta karasa kusa da su tana bata fuska kamar ta fasa kuka.
Kasa ta zauna ta dafe kanta nan da nan sai hawaye, tana ganinsu ta san magabar ce suke tattaunawa.

“Wallahi Wallahi da nasan abunda yarinyar nan take shiryama kenan ba ban amince da auren nan ba, kuma Wallahi ko da baka saki Zinneera ba sai na run ke ka akan ka saketa domin bata dace ta zama sukukar Yaya ba, ba ka min komai ba sai alheri baka taba cutar da ni ba, shiyasa ba zan taba yarda wani abun ya same ka ba.. Amman yarinyar nan ta bata komai kuma ta ci amanata”

“Aa kar hakan ya dame ki ai yara ne, hakan ba zai taba zumuncinmu ba ko kadan, daman ai ba da saninki zata aikata ba kuma ba za tai shawara da ke ba”

Cewar Daddy yana aje mumfashi. Mommy ma ta dora da

“Wallahi mu ba mu ga laifinki ba ko kadan, ai nasan ba da hadin kanki za ayi wannan abun ba”

“Wallahi ban sani ba, kuma ba komai ba ne sai bakin gado, halin uwarta ne ta dauko, kuma ban taba tsammanin cewar yarinyar nan bata dauke ni kishiyar uwa ba sai yau, daman ance tsintacciyar mage bata mage, dan Wallahi da ni na haifeta da ba zata min haka ba”

“Aa karma ki dauki wannan, kawai shirme ne irin na yaran zamani”

Daddy ya fada yana kokarin mikewa tsaye dan baya son maganar. Umma ta dago fuskarta da hawayeta kalli Daddy ta ce.

“Alfarma nake nema a gurinka, indai har da gaske zumuncin da kake magana be lalace ba, ina son ka amince Sadam ya auri Aleeya ....”

Da sauri Sadam ya kalleta with shock, Suraiya da Mommy ma kallonta suke har Daddy dake tsaye....

________________________

Wattpad ghost readers ina ganinku fa, ba comment ba vote. 🙄🤦 ku nake fara yi ma update kamin nai ma yan whatsapp amman sun fiku comment, amman yanzu za ayi canji next update sa na fara musu kamin nai muku indai ba ku gyara ba 🤷😎
   Whatsapp readers ina godiya comments dinku na burgeni kuma yana sani nishadi 😍❤ 

Continue Reading

You'll Also Like

113K 4.5K 49
(DISCONTINUED) Tommy is an immortal that has live for a long time, but he still retain the attitude and appearance of a 17 year old boy but he never...
4K 316 22
Mutane kala uku ne a duniya. Na farko masu rauni Na biyu masu karfi Na uku masu bada umarni A ko ina ma duniya suna raye. Suna kasuwancin su ne akan...
Alina By ihidethisapp

General Fiction

1.6M 40.4K 80
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...
730K 14.3K 46
We have seen over protective brothers, there are maybe 6 , 7 or 8 brothers but what if a girl has 18 brothers, with her over protective parents and c...