ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

116K 15.9K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

38

1.2K 221 80
By KhadeejaCandy

“Ki amsa mana ko ba magana ake miki ba? Baki da wani abu da zaki wanke kanki ko? Baki da wani abun cewa shiyasa kikai shiru kina mana kukan munafurci”

Mommy ta fada a fusace. Zinneera kam babu abunda take sai aikin hawaye, bata jin nauyin wani abu kamar yadda take jin nauyin Sadam da mahaifansa da kuma Umma a yau ba, sun cika mata ido ta ko'ina da har bata iya daga kai ta kallesu, ji take kamar ce komai a mafarki ne na gaske ba, ina ma kasa zata bude ta nutse a ciki...

“Zinneera ki ce wani abu mana...”

Sadam ya kira sunanta kamar mai koyon magana gaba daya jikinsa yai sanyi.

“Babu wata kalma da zan fada ta wanke ni a gurinka ko a gurin iyayenka Sadam, dukan abunda zai fito daga bakina ba zai yi ma kowa dadi ba, iyakar abunda zan iya fada shine ba kai yake nufin na kashe ba, aurena yake nufin na kashe”

Ta fada muryarta na gargada still kanta na kasa. Mommy ta tabe baki.

“Karya kike Allah dai ne ya tona asirinku, kuma Wallahi dana yafi karfin ku, sannan bari kiji na fada maki duk abunda ya samu dana sai na hukunta ki”

Sai a lokacin Zinneera ta dago idonta da suka kumbura sukai ja ta kalli Mommy.

“Kuna da damar ku yi duk abunda kuke so, saboda abunda na aikata nasan be kamata na aikata hakan ga danku ba, amman bana da wata mafita ne sai wannan”

“Me kike kokarin fada?”

Umma ta tari numfashinta tana zare mata ido alamar karta fada. Amman sai ta risina kasam guiyoginta tana kallon Sadam.

“Ka yafe min Sadam, ban aure kan dana kashe ba, Sadiq be turo min sako dan na kashe ba. Amman a yau ina son ka san gaskiya, ban aureka dan ina sonka ba, sai dan nemanwa Sadiq mafita... Naira miliyan ashirin ake binsa, kuma bashi da inda zai same su shiyasa na yake shawarar aurenka wata kila ta hakan na samu hanyar da zai biya kudin ba da amincewarsa na.... ”

Zinneera bata karasa ba, Mommy ta dora hannu aka tana salati Daddy kuma kai ma Zinneera kuri da ido. Sadam kan murmushi yai idonsa suka cika da kwalla, sai ya sauka daga kan gadon ya nufi kofar fita, da sauri Suraiya da Mommy suka rufa masa baya. Daddy ya kalli Umma wacce ta dora hannu a ka tana kuka ya ce.

“Kar abunda tai ya dame ki, na san ba za a hada kai da ke a cutar da Sadam ba, ba kuma zata nemi shawararki lokacin data aikata ba, Yayan zamani ne wadanda soyayya take canja musu tarbiyar iyaye zuwa nata, muje na sauke ku gida”

Kasa cewa komai Umma tai dukan kokarinta na taga ta tsagaita kukanka ne, tana gaba Zinneera na biya kowa sai kallonta yake yadda take zubarda hawaye kamar an mata mutuwa, ta kasa daga kanta har suka isa gurin motar Daddy, gidan baya Zinneera ta shiga baya. Umma tai tunanin ko gida zai wuce ya aje su tare amman sai taga Daddy ya fara isa gidan da aka kai Zinneera ya tsaya ta gate ya juyo ya kalleta.

“Fita ki shiga gidanki”

“Gidanta kuma? Ai kamata yai mu wuce gida tare da ita kawai”

Umma ta fada still tana hawaye.

“Shi zai yanke hukunci idan zata zauna a gidansa ko aa, Sadam ba karamin yaro ba ne, at least ya san cewa ita din barazana ce ga a rayuwarsa...”

Wani irin abu Zinneera taji ya ratsa mata zuciya marar dadi har sai ta lumshe ido ta bude, sannan ta fita daga motar ta tsaya bakin gate din tana kallon motar Daddy har ta daina hango shi. Samun kanta tai ta kasa shiga cikin gidan, tana jin kunyar kallon gate din gidan ma balle kuma ta shiga ciki ta zauna. A saman wani dan suminta ta zauna wanda aka zagaye fulawon kofar gidan da su, sai ta kasa kanta cikin guiyoyinta tai ta ranka kuka. After like one hour wata bakuwar mota ta doso gate din, Zinneera bata dago ba har motar tai horn aka bude mata ta wuce ciki, sai kuma ta ji an sake bude karamar kofar gate din. Kallonta bayanta kawai Sadam ke yi, zuciyarsa na sosuwa da kalamanta na dazun, wanda sanarwar mutuwa sunfi masa dadi sau dubu akan abunda ya ji, ina ma Suraiya bata binciki wayarsa ba, da duk wannan be faru ba, domin kazantar da baka gani ba tsabta ce, ko kadan hakan be taba soyayyarta a zuciyarsa ba, sai dai ya bude wani sabom shafin bakinciki da nadamar aurenta a rayuwarsa...
  Bata waigo ba, har sai da taji an rufe gate din sannan ta mike tsaye ta kama hanya ta soma tafiya ba tare da ta sa inda zata je ba, domin a yanzu tana halin rana zafi inuwa kuna, sai dai komai fushin da Umma zatai da iya bata da kamar gidan mahaifinta.
Da hawaye shakaf ta tare mai Napep a gafen titi tana rokonsa.

“Dan Allah ka taimaka min ka kaini Abdullahi fodio road”

Ganin hawayen idonsa yasa ya tausaya mata yace ta shigo. Tun da suka kama hanyar gida sai fargaba da kunya suka kara kamata, har kofar gida ya aje sannan tai masa godiya ya juya ya wuce ita kuma ta dafa kofar gidan ta taka zuwa cikin gidan. Lokacin data shiga jikin kofar ta tsaya kamar wata marainiya.

“Wallahi kin bani kunya Zinneera ban taba nadamar rainon ki ba sai a yau, daman ance tsintacciyar mage bata mage, yau kin tabbatar min da haka”

Umma dake zaune tare da Aleeya ta fada mata tana watsa mata wani kallon mamaki da bakinciki daga inda take. Zinneera ji tai kamar ta juya ta fita daga cikin gidan, sai dai idan ta fita ina zata je? Aleeya ta girgiza kai

“Kin bamu kunya Zinneera kin lalata zumunci da amince dake tsakanin Umma da Daddy, miyasa ba ki yi tunani ba kamin ki aikata?”

Bata ce komai ba sai aikin hawaye take kamar zata karar da su gaba daya.

“Shiga ga daki can ki zauna ko ba zama kika zo yi ba? Daman ai dawowa kikai ki muna min ni matar ubanki ce ko? To shiga ki zauna”

Umma ta fada tana nuna musu dakinsu lokacin da take nan ita da Aleeya. Uffan dai Zinneera bace ba tana rabe a gurin har aka kira sallah magariba, alwalar ma ba tai ba sai da taga Aleeya da Umma sun shiga dakin, sannan tai saurin daukar buta tai alwala daga inda take ta shimfida dankwalinta already tana da hijab a jikinta ta kabbatart sallah. A gurin tai isha'i daga Umma har Aleeya babu wanda ya kula ta balle har yace mata ga abinci, duk da kasancewar Umma ta girka ne kawai ba dan ta ci ba, domin bacin ran dake cikin ranta ya kuranye mata yunwa tun da rana har dare duk kuwa da hadarin daya hade garin kamar za a sako da ruwa.
              Sai misalin sha biyu saura kwata Abbah ya dawo tare da Nabeel kamar yadda Abbah yake zuwa da shi wani lokacin idan Nabeel bashi da aiki domin ya koya masa yadda sana'ar tasa ta tukin take ko dan wata rana. Suna shigo Zinneera tai saurin mikewa tsaye kanta a kasa, akwai hasken wutar lantarki amman hakan be saka su ganeta ba, domin ba su tsammaci ganin a gidan ba a kuma wannan lokacin.

“Wacece wannan”

Abbah ya fada yana haska fuskarta da fitilar touch light dake hannunsa.

“Zinneera ce”

Umma ta amsa masa daga can da take tsaye jikin kofar dakinta tana gyara daurin zanenta.

“Wace Zinneera”

Abbah ya sake tambaya domin tantancewa.

“Zinneera dai yarka wacce ka aurar shekaranjiya”

“Miya kawo ta nan?”

Wannan karon Nabeel ne yake tambayar cike da mamaki.

“Auren ta kashe ta dawo”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”

Shine abunda Abbah yake ta maimaitawa.

“Miya faru?”

A nan Umma ta gutsura masa wani bangare na abunda ya faru, a take Abbah ya kifa mata mari kuma ya saka kafafunsa ya halbeta har sai da ta fadi ta buge bakinta da kujerar karfe dake kusa da ita. Shurinta Abbah ya hau yi kamar an aiko shi.

“Ni za ki kunyata? A daura miki aure shekaranjiya ki dawo min yau, kija min tsegumi a unguwa, ki auri mutum dan ki kashe shi? Duk uban alherin da iyayen yaron nan suka miki baki gani ba, halin uwarki ne zaki nuna min a cikin gida”

Tun Zinneera na kuka har ta koma hada shi da Allah tana bashi hakuri daga baya kuma ta koma kiran Umma wacce ke tsaye tana kallon Abbah na jibgarta.

“Wayyo Allah dan Allah Abbah kai hakuri ma shiga uku, mutuwa zan yi Umma ki taimaka min”

Abbah be saurara mata ba har sai da Nabeel ya rikeshi.

“Fita ki bar min gida ba zaki kwana a nan ba”

Nabeel ya kalleshi da sauri.

“Abbah ina zata je dare ne fa yanzu”

“Duk inda zata je sai dai taje amman ba zata kwana min a cikin gida ba, tashi ki fita”

Ya karasa a fusace yana katsa mata tsawa. Tashi Zinneera tai tana karkarwa kamar zata fadi ta nufi kofar fita.

“Abbah duk abunda zaka mata kai mata amman karka tura ta waje a yanzu, garin akwai hadari kuma dare ne yanzu fa, ina zata je ta kwana”

“Duk abunda zai sameta sai dai ya sameta amman ba zata kwanar min a cikin gida ba”

“Umma ki saka baki, macece fa dan Allah kar kai mata haka”

Umma ta girgiza kai a Nabeel kai.

“Ni babu ruwana a ciki, Zinneera ni da ita a yanzu sai dai ido”

Nabeel zai sake magana Abbah ya nuna shi da yatsa.

“Idan ka sake cewa wani abu kai ma kora ka zan yi kaje ka sama mata gurin kwana”

Dole yai shiru ba dan ya so ba, dan baya ganin wannan hukunci na Abbah a daidai. Karasa Abbah yai ya rufe kofar gidan ya juyo cikin gidan yana ta huci. A bakin kofar gidan ta zauna ta saka dayan hannunta ta tare gefen fuskarta inda jini ke mata zuba, sai ga guntun haurenta a hannunta, faduwar hauren baya rasa nasaba da buguwar da gefen bakinta yai da kujerar karfe. A gurin ta kwanta ta takore, duk wani tsoro da fargaba da take ji idan tana ira kadai yau babu shi a tattare da ita. Ruwan sama ne mai karfi ya soma saukowa nan take nepa ta dauke tashi Nabeel yai daga dakinsa da yake kwance ya dauki abun lullubinsa da tabarma ya lallabo a hankali ya bude kofar gidan ya fito, yadda ya tararda Zinneera kwance bakin kofar ruwan sama na dokanta sai da yaji kamar ya zubar mata da kwalla. Hannu yasa ya taba ta sai ta dago ashe ba bachi take ba, tabarma ya shimfida mata a barandar dake kofar gidan ya mika mata abun rufa. Karba tai ta koma a gurin ta kwanta ta lullube tana kallon yadda ya zauna kusa da ita.

“Abbah zai iya fushi da kai”

Ta fadar cikin yanayin dake nuna tana jin zafin magana saboda gefen bakinta daya fara kumbura.

“Komai zai yi sai dai yai Zinneera, ba zan barki ki kwana a nan ke kadai ba...”

Kwantar da kanta tai kasa tana hawaye.

Continue Reading

You'll Also Like

5.5K 723 38
Wallahi ko zaka mutu bazan taba auren kaba yaya Abba na tsaneka na tsani duk mai sonka, "ni sa'ad nakeso kuma shi zan aura" ta karasa fada tana fashe...
323K 25.3K 70
'Mijin yar'uwata nake so, farin cikin da yake baiwa matarsa nake son samu fiye da hakan, so nake na rabashi da matar sa da ya'yan sa ya zamto ba kowa...
815 116 44
AL'ADARMU No description, Just get your self ready, seat properly and enjoy reading this amazing heart touching story AL'ADARMU
1.1M 37.7K 61
WATTYS WINNER When her fiancΓ© ends up in a coma and his secret mistress, Halley, shows up, Mary feels like her world is falling apart. What she does...