ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

113K 15.7K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

36

1.5K 270 32
By KhadeejaCandy

Zinneera na karanta sakon ta dago da sauri ta kalli Suraiya hankalinta a tashe, so take ta tantace idan Suraiya taga sakon ko kuma akasin haka, sai dai yadda Suraiya ta sakar mata ido tana mata kallon tuhuma ya tabbatar mata da cewar takaranta sakon. Da sauri Zinneera ta juya rike da wayar ta nufi kitchen, sai kuma ta juyo da sauri ta nufi dakinta kamar wacce ta rikice.

_Zinneera inda har da gaske saboda yana ni kikai auren nan, to ya kamata ki kashe shi yanzu, karki tsaya neman hanyar kudi zan..._

Haka Suraiya tai ta maimaita sakon a ranta tana kokarin gano abunda Zinneera take boye, tashi tai ta nufi dakin da Zinneera ta shiga.
Safa da marwa ta samu Zinneera na yi a cikin dakin sai dai ganinta ya saka Zinneera kokarin daidaita natsuwarta. Kallon mamaki da tuhuma Suraiya take mata.

“Waya turo miki sakon nan Zinneera”

Ta tambaya kamin ta karasa kusa da ita. Sai Zinneera ta dauke kai kamar bata ji ba.

“Wa zaki kashe dan'uwana?”

Da sauri Zinneera ta kalleta fuskarta na bayyana tashin hankalin dake cikin zuciyarta, bakinta har rawa yake gurin amsa wa Suraiya.

“A'a Wallahi ba wanda za a kashe, wrong number ne”

“Babu wani wrong number ba, ai ya rubuto da sunanki, Sadam yake nufin ki kashe ko wanene”

A take idon Zinneera suka cika da kwalla, a yadda take tunanin Suraiya ta dauki abu ashe har ya wuce nan, a tunanin Suraiya zata fahimce cewar tana waya da wani namijin ne da aurenta, ashe ita wata daukar dabam take ba wacan ba.

“Na rantse da Allah ba Sadam yake nufin na kashe ba Wallahi ba Sadam yake nufi ba”

“To wa yake nufi? Waya turo miki sakon? Kamar ya akanshi kikai?”

Tuni hawaye ya wankewa Zinneera fuska kuzari da sauran karfin jikinta da take da shi yana kokarin guduwa ya barta, jin zargin da Zinneera take jifanta da shi.

“Wanene...!”

Suraiya ta daka mata tsawa har sai da ta firgita.

“Wani ya gada kai ki kashe dan'uwana ku kwashe dukiyarsa ko?”

“Aa Wallahi ba Sadam yake nufi ba, aurena yake nufin na kashe, ni ba zan iya kashe kowa ba, wai ke ba zaki gane ba ne?”

Zinneera ta fada tana kara fashewa da kuka.

“Taya za ayi na fahimta bayan abunda idanuwa suka gani? Kin bani mamaki Zinneera har wani zai hada kai da ke yace a kashe Sadam? Wane makiyinsa ne wannan? Me Sadam yai masa?”

“Sadiq ne! Amman Wallahi na rantse miki da Allah ba Sadam yake nufin mu kashe ba, aurena yake nufin na kashe”

“Sadiq...”

Suraiya ta maimaita sunan a bakinta tana kallon Zinneera wacce ke aikin kuka cike da tuhuma, kamin ta juya da sauri ta fita daga dakin ta nufo falon inda kawayenta biyu suke zaune.

“Sisters ku tashe muje Mommy ta kirani tace na dawo gida yanzu nan...”

“Lafiya...?”

Daya daga cikinsu ta tambaya.

“Ban sani ba, amman dai tace ko minti biyar karna yarda na kara na dawo gida yanzu, ko na barku a nan naje ns dawo”

Da sauri suka mike tsaye dayar tana rataya jakarta. Sai ga Zinneera ta fito da sauri tana kuka ta nufo gurin da Suraiya take tsaye tana jiran kawayen nata.

“Wallahi Suraiya ba abunda kike tunani ba ne, na ran... ”

“Karki fada min komai, babu kalmar bakinki da zan saurara, kui sauri muje”

Ta Karas tana kallon kawayen nata, ita kan dama tai gaba abun ta. Zaunawa Zinneera tai a gurin ta fara rera kukan abunda zai biyo baya tun yanzu. Suraiya take driving sai da ta fara sauke kawayen nata sannan ta wuce family house dinsu, a gaggauce tai fakin dan ta matsu ta shiga ciki ta fadawa Mommy abunda ta gani, tana rufe motar ta ciro wayar ta kira Sadam wayarta ta dade tana ringing sannan yai picking.

“Kazaure ka zo gida yanzu yanzu tana nemanka”

“Wani abun ne ya faru? ”

“Wani abun babba ma akan Zinneera”

Tana kawai nan ya kashe wayar, ita kuma ta nufi kofar shiga falonsu. A falo ta samu Mommy tare da mutane cikin falon kasancewar har yanzu akwai sauran yan bikin da basu koma ba.

“Mommy ta so ki ji yi sauri”

Ta fada tana nufar upstairs. Yadda Mommy ta ganta da kuma yadda taji furucin ya tabbatar mata da cewar abunda Suraiya take son fada ko yi mai muhimmanci ne, domin ba kasafai suke katse mata fira idan tana cikin mutane ba, sai idan wani abun ne mai muhimmanci. Tashi Mommy tai ta soma taka stairs din cikin takunta na manyan mata ta doshi dakinta inda Suraiya ta shiga.

“Har kun dawo”

Shine abunda Mommy ta tambaya daga shigarta dakin. Hannayenta Suraiya ta kama ta zauna da ita bakin gadon ita ta zauna, sai kuma ta fara tunanin yadda zata fadawa Mommy tasan abun ba zai mata dadi ba, amman babu wata mafita bayan fadin domin ita a ganinta rayuwar dan'uwanta ake nema.

“Mommy yanzu da muka je gidan Sadam, sai muka zauna falo sai Zinneera ta fito tace mana bari ta kawo mana abun tabawa, akan center table ta bar wayarta, ana ta kira bata kusa na dauka zan mika mata kenan sai kiran ya katse sako ya shigo....”

Haka ta zayyana wa Mommy abunda ya faru ciki har da kukan da Zinneera tai da kuma maganar da tai mata na cewar ba Sadam ake nufin ta kashe ba. A take hankalin Mommy ya tashi jikinta yai sanyi daman can idan abu ya shafi yayanta bata wasa da shi balle kuma akan Sadam dan lallenta.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, amman Zinneera tana cikin hayyacinta kuwa?”

Kaminn Suraiya tace wani abu Sadam ya turo kofar dakin ya shigo sanye da manyan kaya wando da riga na farar shadda mai kyau da tsada. Tsaya yai karantar abunda ke fuskarsu bayan ya rufe kofar.

“Zauna”

Mommy ta nuna mishi kujerar gadonsa. Kujerar ya nufa ya zauna yana cigaba da kallonsu zuciyarsa cike da fargabar abunda zasu fada masa, a tunaninsa wani abun ne ya samu Zinneera. Yadda Suraiya ta fadawa Mommy haka Mommy ta fadawa Sadam fuskarta na nuna tsantsar damuwa da firgice.
Murmushi Sadam ya fara yi kamin murmushin ya zame masa dariya, dariya irin sosai din nan har sai ka dauka ko ya tabu. Mommy da Suraiya suka shiga kallon kallo.

“Sadam ka fahimci hakan abunda Mommy ta fada maka kuwa?”

Suraiya ta tambaya tana kallonsa da mamaki.

“Na fahimta mana, amman ku duk kun dauka da gaske? Taya Zinneera zata iya kasheni?”

“Zata iya Favorite idan har wani ya saka ta, kasan Zinneera mata da hankali Sadiq kuma makiyinka ne zai iya aikata komai”

“Na yarda amman ban da kisa Mommy Zinneera tana da tsoro ba zata iya aikata kisa ba”

“Yes Zinneera tana da tsoro da wani zai iya saka ta yi mata cilas kuma dole ta aikata”

“Ballantana ma ba cilas akai mata ba, domin yace ta bar maganar kudin zai samo”

Cewar Suraiya.

“Haba dai maybe ma ba daidai kike karanta sakon ba”

Sadam ya fada yana kokarin mikewa tsaye fuskarsa shimfide da bacin ran dake nuna be jidadin maganar ba.

“Daidai na karanta Sadam babu kuskure a ciki, rayuwarka ake nema, kuma idan har yarinyar nan bata da wata manufa akan me zata rika mu'amala da wani namijin a waje bayan tai aure, indai har da gaske zaman auren ta zo yi? Wani kuma tsohon saurayinta makiyinka Sadiq? Wanda tafi sonsa da kowa? Ya kamata tun farkon daya dawo tace kai take so kai bincike, wata kila shi ya turo ta tunda yana da matsala da kai ta yadda zai iya daukar fansa akashe ka kuma a kwashe maka dukiya”

Sadam ya juyo yana kallon Suraiya da kyau.

“Wata kila saboda ki gani ne ya turo mata sakon, ta hanyar da zai kashe min aure”

“Idan saboda ni kadai ya turo sakon miyasa ita ta san da zaman sakon? Miyasa tace ba kai yake nufin ta kashe ba aurenta? Kuma ya akai yasan ni na zo gidan har na dauki wayarta? Sadam karka makance akan yarinyar dake neman dukiyarka da rayuwarka”

“Ba wani makancewa, ni ina son matata kuma babu wanda ya isa ya rabani da ita, miyasa kika daukar mata wayar tun farko? Ko baki san cewa wayarta sirrinta ba ce? Ina ruwanki da abunda kik gani sai ki kama bakinki ba sai kin fada ba, ko kuma ki kirani ki fada min kadai, wannan zuwan naki be min rana ba, ban jidadin wannan zuwan naki a gidan ba, baki kyauta min ba kuma ban gode abunda kika min ba”

Yadda yake maganar sai ka rantse da Allah ba Sadam ba ne, duk maganar data fito bakinsa ita yake fadawa yar'uwarsa, shi sam lamarim be masa dadi ba domin baya shiri da duk wanda zai bata masa Zinneera. Ba Suraiya kadai ba Mommy ma kanta kallon mamaki take masa.

“Sadam...! Ka fahimci abunda Suraiya take nufi kuwa? Rayuwarka ce a hadari fa, yanzu da bata gani ba sai su kasheka a banza su kwashe duniyar, idan ma ba gaskiya bane ai ya kamata a abincinketa a ji dalilin daya saka take mu'amala da wani namijin da aurenka”

“Ni zan binciki matata Mommy komai zai wuce”

“Ba zai wuce ba, dole ne sai iyayenta da mahaifinka sun shiga cikin wannan maganar, wannan ba abun kyalewa ba ne, ba zan yarda wata can ta kashe min da ba, babu zumuntar uwar ba da uba, ba zaka zauna da ita ba Sadam babu wacce zata saka ni kukan rashin dana”

“Mommy kar kiyo saurin yanke hukunci baki sani ba shirin Sadiq ne. Kin ga abunda kike ja wo ko? Ko kasheni za tai inda baki bincika ba da ban gani ba fa yanzu kuwa be sani ba”

Yana kaiwa nan ya fice daga dakin cikin bacin rai. Suraiya ta nuna kofar bayan ya wuce yana kallon Mommy.

“Anya Sadam yana cikin hankalinsa kuwa?”

“Son ta yake, son da bashi da rana dan Wallahi ba zai zauna da ita ba ko zai mutu”

Mommy ta fada a fusace.

Daga gidansu kai tsaye gidan Amaryarsa ya nufa, ko kadan zuciyarsa bata yarda da abunda Suraiya ta fada ba, balle har ta raya masa wani abu, yafi yarda da cewar Sadiq ne ya shirya hakan ko kuma wani dabam, wata kila ma Suraiya ta samu matsalar ido ko kuma wani za a turawa sakon ya fado a wayar Zinneera. Be taba jin tsanar Suraiya kamar yau ba, idan da gaske ne miyasa bata same shi kadai ta fada masa sai su warware komai a tsakaninsu, amman tasan idan har Mommy ta sani dole maganar zata iya zama babba. Ya dade cikin motar sannan ya fito ya doshi kofar shiga cikin falon wanda shi zai sadaka da cikin gidan gaba daya. Abakin kofar ya tsaya ya huce fushinsa dan baya so ta fahimci cewar yaji maganar. Sannan ya danna karaurawar dake jikin kofar, da sauri ta bude kofar kamar daman can jira kawai take ta danna ta bude masa. Sai na nitsa kai a cikin falon yana kallonta da murmushi, ita ta gagara daga kai ta kalleshi fatarta idonta da fuskarka sun kumbura sosai kamar an daketa, da alama kuka tai har ta koshi.

“Ba zaki tarbe ni ba”

Ya fada try to make her calm ganin ta juya zata koma. Kamar Umarninsa take jira sai ta juyo da sauri ta rumgume shi tsantsan ta fashe da kuka. Hannayensa dake zube cikin aljihu ya cire ya ciro ya rumgume ta yana shafa bayanta. Har cikin ransa yake jin kukanta, zuciyarsa cike da tausayinta.

“Ina sonki sosai Zinneera, i love you so much”

Ya rada mata a kunne yana kara kankame ta a kirjinsa kamar ance masa wani zai kwaceta. Sai da tai kuka ta gaji ya tabbatar ta samu natsuwa sannan ya fan dagota sai ya koma ta kara rumgume shi, ji take ba zata iya hada ido da shi ba, and she feel much comfortable lokacin da take kuka a kirjinsa kamar ace mata duka damuwarta ta yaye. Haka ya jata ya zauna rumgume da ita a kujera, sai kuma ta dago ta dan matsa nesa da shi tana watsa fa yatsun hannunta idonta a kumbure...

“Suraiya ta zo nan...”

“Kawo min wani abun na sha”

Tana fara maganar ya tari numfashinta da sauri har sai da ta dago ta kalleshi, shi kuma ya kai hannu ya dauki remote ya canja channel, ba dan komai yai mata haka ba sai dan baya son tai masa maganar. Tashi tai ta nufi kitchen lokacin data shiga tsaye tai  ta rasa abun yi, tsoro take ji ta fada masa abunda Suraiya ta gani domin ta san zai tambaye gaskiyar lamarin, amman duk da haka ta daure zata fada masa da kanta sai ya tare ta hakan na nufin baya son jin maganarta kenan? Ko kuma dai Suraiya bata fada masa ba? Idan har ta fada masa babu yadda za ayi ya rumgumeta a dazu kuma har ya fada yana kaunarta. Freezer ta nufa ta bude ta dauko five alive.
Amman idan har ba a fada masa ba, da sai ya tambaya dalilin kukanta, ko dai baya son nuna mata ya sani ne, idan har ya tambaye ta yanzu me zata fada masa? Gaskiya zata fada masa dalilin aurenta da kuma burin da take da shi? Aa no ba zata iya ba.

Haka zuciyarta tai ta raya mata abubuwa mabanbanta, tsoro da firgici suka cika mata zuciya na yadda zata Kalli idon Sadam ta fada masa gaskiya, idan ma ya saketa a yanzu me zata fadawa Abbah da Umma? Da wane ido zata kalli Mommy da Daddy? Auren da aka daura shekaranjiya ace har ta fara samun matsala yanzu ko kuma an saketa? Bayan kuma ta hana kanwarta aurenshi sannan duniya ta san ba dan Allah ta aure shi ba.
Da sauro ta nufi store can bayan buhuhuwan data aje kofin nan da ta saka maganin bachi ta dauko ta sake ballawa wanda yafi wacan yawa ta zuba a dankwalinta ta fito ta leko falo, sai ta hangosa tsaye ya bawa kitchen din baya yana waya, koma tai ta sauri ta tauna maganin da dukan karfinta sannan ta juye masa shi a cup sai ta bulbula lemun akai, so take idan ya sha yai bachi wata kila kamin ya farka ta samu wata dabarar da zata tai da kuma abunda zata fada masa. A kitchen din ta bar dankwalin ta fito a firgice kana kallonta kasan bata da gaskiya domin bata da natsuwar dake nuna a kintse take.
  Tsayawa tai a bayansa, yana gama wayar ta mika masa sai ta dan ja baya tana kallonsa, murmushi ya sakar mata yana kallon yadda aka jera mata kananun kitso a kai irin na Amare ga gashin kanta yai baki sosai kamar an shafa mata wani abu. Hannunsa ya mika mata alamar ta matsa kusa da shi, sai ta tsaya kallon hannun kamin ta mika masa nata sai ya janyota jikinsa yai mata side hug kai kissing din saman kanta sannan ya soma kurba lemun.

“Akwai abunda kike son fada min?”

Sai tai saurin barin jikinsa.

“Eh amman ka shanye lemun tukuna”

Samun kansa yai da son kallonta ya sakar mata idonsa yana kallonta kallon da shi kansa be san na minene ba, har ya zauna saman cushion be dauke idonsa daga gareta ba, ji yake kamar ya dafa ya cinye ta zauna cikin cikinsa, lokaci daya ya daga kofin ya shanye lemun sannan ya sake mika mata sannunsa.

“Zo nan Pearl fada min me ke damunki ji kin kumbura fuskarki da kuka”

Bata zo ba, bata kuma mika masa hannunta ba kamar yadda shi ya miko mata nashi hannun ba, sai kawai ta tsaya a gurin tana tunanin ta inda zata fara. Unkurawa yai ya riko hannunta ta matsa kusa da shi sai ya kwanta saman kujera sakamakon bachin mai nauyi daya fara ji, ya kwanto da ita jikinsa ya rumgume ya lumshe ido, sai kuma ya bude idon ya dago kanta ya hade bakinsu, a hankali yake aika mata da sirrin da yawunsa suke da shi a bakinta, kamin ya cire bakinsa ya sake maidata kirjinsa, ya lumshe ido yana tandar baki kamar wanda ya sha minti. Be yi minti uku da rufe idon ba Zinneera taji karar bude gate da fakawar mota a harabar gidan, da sauri ta daga daga jikinsa taje ta leka windows, hango Mommy da Suraiya yasa hankalinta tashi, da sauri ta dawo ta shiga jijjiga Sadam

“Tashi ga Mommy nan ga Mommy nan zuwa”

Daker ya bude idonsa ya kalleta sai kuma ya sake rufewa alamar bachin na son cin karfinsa, da gudu ta shiga kitchen ta kunna tab ta debo ruwa a hannunta ta rugo a guje ta zo ta zuba nasa a jiki sai yai firgigit ya bude sleep eyes dinsa.

“Tashi ga Mommy nan”

Tana fada ana yin knocked din kofar, cikin tashin hankali ta jijjigashi tasa duka karfinta ta dago shi ya tashi zaune amman sai ta kasa, hannunta ta saka tana shafa gefen fuskarsa da karfi har da kwallanta.

“Sadam dan Allah ka tashi zaune”

Daker ya bude idon ya kalleta, can ciki yake jin maganarta kamar wanda yake wata duniyar, tashi yai zaune amman ba zama irin normal zama ba, irin zaman nan na an cilasta ni kuma ina jin bachi. Tana ganin ya zauna ta nufi kofa da sauri ta budewa Mommy.
Bata cewa Mommy komai ba, Mommy ma bata ce mata ba, bayan ina Sadam

“Ga shi can kan kujera bachi yake ji”

Ta fada kamar zata fasa kuka. Mommy da Suraiya suka nufi gurin kujerar, yadda Mommy ta tararda shi yasa hankalinta tashi, ruwa a jikinsa gashi kuma ya zauna a karkace sai sharar bachi yake kamar wanda baya cikin hayyacinsa. Hannu ta kai ta girgiza shi

“Sadam Sadam.....”

Daker ya bude idon kadan ya kalleta sai ya sake rufewa ya bude baki kamar wanda numfashin baya isarsa.

“Me kika masa?”

Mommy ta tambaya da karfi tana kara girgiza shi. Tsaye Zinneera tai a gurin kamar an dasata hawaye nata aikinsu a fuskarta...


SADIQ POV.

  Tare da Mama da kanwarsa Naja'atu suka fito daga asibitin, yadda yake tafiya ma ba zaka ce ya samu rauni a kafarsa ba, a bakin gate din Uduth suka tari Napep suka shiga gidan Baya shi da Mama da kuma kanwarsa wacce ke rike da sauran kayan da suka kwaso a asibitin. Napep dinsu na dagawa mota biyu ta sojoji na shiga cikin asibitin kowa sai kallonsu yake domin kana ganinsu kasan akwai abunda ya kawo su. Kamin su karasa Aliyu Quarters suka hango motar sojojin ta faka gefen titi sojojin kuma akan titi suna binciken motoci.

“Ina ganin garin nan ba lafiya ba, kin ga dazu mun wuce wasu hanyar asibiti yanzu kuma ga wasu a nan”

Sadiq ya fada ba tare da sanin cewar sune suka rigashi isowa nan ba, domin sun je cikin asibitin aka ce an sallame shi yanzu ya fita, sai suka dawo ta gurin hanyar Aliyu Quarters suka tare domin Raliya ta fada musu unguwar da yake, kamar yadda Ummi ta fada mata unguwar data kade shi lokacin da ita Raliya take tambayar inda ta sanshi.

“Wata kila wani abun akai kasan kasar ba a zaune kalau”

Cewar Mama tana kallon Sojojin, Mai Napep din ma yace

“Lallai ba lafiya ba”

Sadiq be gane Raliya ba har sai da suka karasa gurin sojojin ana bincikar Napep dinsu yaji tace gashi nan shi ne. A lokacin ya kalleta da kyau sai ya gane ita yarinyar da tazo dazun tare da Ummi. Daga jin tace gashi nan shi ne, sojojin suka fiddo mai Napep din suka wulga gefen titi a take ya fashe da kuka daman zuciyarsa cike take da tsoro.

“Ba shi ba wacan”

“Ni....!”

Sadiq ya nuna kansa. Sojan dake tsaye kusa da shi ya kifa masa wani wawan mari har sai da yaga wata wuta, jinsa kuma yai nisan zango. Dayan yasa kafarsa ya bugu kafafuwan Sadiq sai gashi ya fadi kasa yana hakki, Mama da Naja'atu suka dora hannu aka suka fashe da kuka mutane kuma suka shiga bawa idanuwansu abinci. Tun a gurin Wani soja ya cire bel dinta ya fara dukan Sadiq kamar zai kashe shi, dayan kuma ya saka kafarsa yana murzar masa kafafuwa. Sannan suka dauke shi suka saka a motarsu sai marinsa suke nan take fuskarsa ta soma kumbura bakinsa na zubar da jini.

Kai tsaye gida suka nufo da shi, sojojin dake gadin gate din suna hango su tafe suka bude musu gate din kamar yadda suka saba. Suna isa suka fito da Sadiq cikin motar suka jefar da shi kasa dayan sojan ya saka kafarsa ya taka masa ciki har sai da yai ihu. Raliya ta nufi main house din da sauri, kamar dazun yanzu ma babu kowa a katon falon sai ta nufi inda ta tararda Daddy dazu, wannan karon sai ta same shi tare da Ummi tana nuna masa abu a laptop shi kuma yana rike da cup idonsa sanye da farin gilashi.

“Daddy gashi can an dauko tun a can ma an fara dokansa”

“Wa?”

Ummi ta bukata.

“Wanda ya mareki a asibiti”

Da sauri ta kalli mahaifinta baki sake.

“What? Ya akai Daddy ya sani”

“Ni na fada masa, shi kuma yace naje na nuna musu inda yake azo da shi”

Da sauri ta tashi tsaye tana lallon mahaifinta.

“No Daddy, laifinane wlh ni na dame shi shiyasa har ya mareni dan Allah karka masa komai Wallahi bashi da lafiya shine fa wanda muka kade”

“Ko wanene shi be kamata ya daga hannu ya mareki ba, wani be isa ya nuna miki yatsa ba Mamana balle har ya kai ga jikinki, ba zan lamunta ba”

“I know Dad amman wannan laifina ne, Daddy be dace ka cutar da shi ba ba san damuwarsa ba, oh my God....”

Ta nufi kofar fita da gudu idonta cike da kwalla......

_________________

Fatar makarantan Zabin Rai sun yi sallah lafiya, Allah ya maimaita mana ina jiran goron sallah na ☺

Continue Reading

You'll Also Like

71.9K 3.6K 46
Camila Davis is a semi-famous hockey player for the California Cobras. She recently divorced her lying cheating husband and moved her and her kids ac...
Alina By ihidethisapp

General Fiction

1.5M 39.9K 80
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...
8K 415 10
Authentic Dua's from the Qur'an and sunnah for all occasions to be implement on our daily routine.
28.9K 2.8K 36
her life is ending becouse of her biogical brother,he rapping her the frist tym that he see her in his life