ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

113K 15.7K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

At Hospital

1.5K 225 17
By KhadeejaCandy

Doc Tahir Na daf da fice daga falom ya laluba aljihunsa ya juya da sauri yana fadin.

“Tsaya keys din motar na kan dorowarka”

Dakin ya koma da zimmar daukar keys dinsa.

“Sadiq,... A a hadari? Aa kar ya mutu... Sadiq ba yanzu ba.... Innalillahi...”

Abunda Zinneera ke fada kenan tana kwalla, ganin Doc Tahir ya shigo yasa tai saurin rufe bakinta tana kallonsa kamar daman can ta manta da inda take sai a yanzu ne ta tuna. Kallonta kawai yai sam be yarda ya nuna mata wata alama da zata gane cewar yaji maganarta ba, sai ya karasa gurin bedside drawer din ya dauki keys din ya juyo ya sake kallonta a karo na biyu sannan ya fice.

Yana fita tai saurin dukawa ta dauki wayar ta ta kasheta gaba daya ta zauna bakin gadon har lokacin tana kwalla. Ji tai kamar tai tsalle taje taga halin da yake ciki amman babu dama, waya kade shi? Garin ya aka kade shi? Yana da rai ko ya karya ko kuma ya mutu... Tayi zurfi gurin wannan tunanin da har bata iya jin shigowar Sadam ba sai da ya dafata, sai ta kalleshi a razane tana wani irin daukar numfashi. Shi dan kallon mamaki yai mata ganin yadda ta dawo cikin hayyacinta kamar wacce aka jefowa nunfashi daga sama, babbar rigarsa ya cire ya zauna kusa da ita yana murmushi tare da kai hannu ya rika hannunta.

“Sorry na razana ki... Na razana ki a lokacin da be kamata kiji tsoro ba a rana irin wannan mai muhimmanci da daraja a garemu...”

Sam hankalinta baya gurinsa babu kalaminsa ɗaya daya shiga kunnenta, har sai da ya kai yatsansa ya shafi gefen fuskarta a hankali yaja shi har zuwa gurin wuyanta, lumshe ido tai ta sauke numfashi a hankali hawaye na cigaba da mata zuba, zuciya kuma tana azalzalarta da halin da Sadiq yake ciki. Hannayensa biyu yasa ya juyo da fuskarta saitin tasa har suna iya shakar numfashin juna, ya kai bakinsa saitin cheek dinta inda hawayen suke mata zuba ya sumbace ta sannan ya hade front head dinsu guri hancinta na gugar nasa yana ta kallon fatar idonta yayinda nata idanuwan suke a lumshe.... Sun fi minti biyar a haka sannan yaja ta zuwa kirjinsa ya rumgumeta tsantsan. 
Fashe tai da kuka sosai ta kankame shi sosai tana jin kamar Sadiq yake rungume da ita. Mayafin kanta ya janye ya soma shafa bayanta a hankali alamar rarrashi.

“Ranar yau tafi ko wace rana a gurina daraja da martaba a gurina, na dade ina jiran zuwan wannan ranar, ranar da zan yi raya sunnar manzo na, na taba halalina, sai kuma ta zo min a yanayin da yafi ko wane saka ni farinciki wato aurenki Zinneera...ban san sau nawa zan fada miki ba, ban san yadda zan kwatanta miki ba ki gamsu ba, iyakar abunda zan iya zan nuna miki kauna kyautatawa soyayya gata da zaki tabbatar da cewar lallai kin yi dacen mijin aure... Ina kaunarki sosai Zinneera ban taba jin so wata mace a zuciyata kamar yadda nake jinki ba, ban taba son wata ya mace ba sai ke...”

Kamar wacce ta tuna wani abu sai tai hanzarin dagowa ta raba jikinta da nashi tana share hawayenta. Murmushi yai yana kallonta kamar zai hadeyeta.

“Bachi nake ji”

Ta fada ba tare data kalleshi ba sai kokarin haurawa kan gadon take. Hannu ya kai ya riko farar kafarta wacce tasha kumshi ya shafota ya daga kafar yai kissing din feet dinta.

“Alwala ya kamata mu yi a yanzu mu godewa Allah sannan ki ci abinci kamin mu kwanta”

Wani jarrr taji sai tai saurin janye kafar.

“Bana sallah kuma ban jin yunwa”

Kallonta yai da idonsa da suka soma canja kala murya can kasa kasa kamar mai rarrashi ya ce.

“Kin tabbata? Ba wani abu zan miki ba, sallah kawai zamu yi sai mu kwanta”

“Ina da alwala ta tun a gida”

“Okay amman sauko kici abinci kuma ki canja kayan jikinki lace din jikinki yana da nauyi ba zai bari kiyi bachi da dadi ba, ni kuma ba zan bar abunda zai hana ki jindadi ba, ki saka kayan bachi suna can a wardrobe ni bari nai alwala sai mu gode ubangiji”

Sauka ya fara yi ya shiga bathroom, sai ita tai saurin sauka ta nufi wardrobe din ta bude ta dauki jakarta ta cire maganin ciki ta saka a cikin janen lace din dake cikinta, sannan ta janyo Hijab ta saka ta dawo bakin gadon ta zauna gabanta sai faduwa yake jikinta na karma. Ko da ya fito yana kokarin warware nadin hannun rigarsa shaddarsa fuskarsa cike da ruwan alwalar da yai da kansa ya dauko carpet biyu ya shimfida mata daya ya shimfidawa kansa daya sannan yai gaba ita kuma tana daga bayansa ya kabbatar sallah. Bayan sun gama yai addu'a sannan ya juyo ya kama kanta ya karanta mata addu'o'in da Annabi ya koyar da mu, bayan ya gama ya gangaro da hannunsa ya kada mata yatsansa cikin bakinta yana wasa da halshenta.

“Ya kamata ki ci wani abu.. Bari na dauko mana cups da plate”

Ya fada yana kallon eye ball dake ta jujjuyawa akan fuskarsa. Wani kwarjini taji ya mata da sauri ta sanda kanta kasa ta kawarda bakinta sai ya zare yatsan yana murmushi ya tashi ya fita. Be dauki dogon lokaci ba ya dawo dakin dauke da plate da cup daya. A gabanta ya dire cup din ya janyo manyan ledodin dake gefensu ya bude ya zuba kazar a plate ya bude yogurt  din ya zuba mata a kofi sannan ya dauki cinyar kazar zai ki mata a baki sai ta kawarda fuska.

“Bana jin yunwa”

“Ni ina jin yunwa you must eat”

Ya sake unkurin kai mata a baki sai ta mika hannu zata karba.

“zan iya ci da kaina ni kadai?”

“Kina da yancin hakan indai kin tabbatar min da zaki ci, daman na ki ne ai ke kadai”

“A falo zan ci”

“Kunyata kike ji?”

Ya tambaya yana murmushi.

“Ba zan iya ci a gabanka ba, amman zan iya ci idan na kebe ni kadai”

“Idan kina ke kadai ai ba zaki ci ba, zan jiya rumtse idan kunyata kike ji”

“Wallahi ba zan iya ci a gabanka, amman idan na kebe ni kadai zan iya ci sai kuma n canja kayana”

Jin ta rantse da kuma yadda take masa maganar kamar tai kuka yasa shi kai hannu ya lakaci hancinta.

“Bari ni na koma falon sai ki canja tufafin kuma ki ci abinci amman ten minutes kawai zan baki kin yarda?”

Ta gyada kai sai ya tashi ya fice daga dakin yana murmushi, yasan ba komai take ma hakan ba face tsoron daren farko daren da abokan amarya suke bata tsoro da shi, and yes tana da gaskiya dan be ji zai kyaleta a yau da take halalinsa...
  Tashi tai taje gurin kofar ta tura kofar dakin da sauri, ta dawo ta fiddo maganin dake jikinta ta balla ko wanne hudu hudu ta saka a Hijab dinta ta tauna har sai da ya zama gari sannan ta zube cikin cup din dake cike da yogurt, ta dauki sauran maganin ta nufi wardrobe ta bude jakarta ta saka ciki ta juyo da sauri ta dauki cup din ta saka yatsanta cikin yana garwayawa dan kar a gane domin kalar yogurt din ta soma canjawa kadan, tasan idan kuma maganin ya jika a ciki kalar zata canja gaba daya. Tana haka ya turo kofar dakin ya shigo

“Ba zan iya jira na tsawon lokaci ba, tunda baki canja tufafin ba sai ki canja a gabana daman na fi bukatar haka”

Daga jikinta har cup din da gake rike da shi rawa yake, tsoro ne ya kamata tana ta kallonsa yatsanta a cikin yogurt din har ya iso kusa da ita.

“Miyasa kike gaurayawa ya miki sanyi ne?”

Ya tambaya kana ya kai hannunsa ya dago hannunta ya saka yatsanta a baki ya lashe yogurt din, sannan ya sumbashi saman hannun nata, ya shiga kokarin zaunar da ita. Tana zaunawa sai tai saurin cire Hijabinta gudun kar ya gani ko yaji warin maganin, hakan ya bashi damar kai bakinsa saitin kunnenta ya rada mata.

“Kin ci abinci ko na ciyarda ke yanxu?”

Dayan hannunsa ya kai yana wasa da kashin wuyanta, sai kuma ya dan ciji kunnenta kadan, saurin juyowa tai ta mika masa cup din.

“Ka sanye wannan yogurt din ni kuma sao na ci”

“Taki ce ba tawa ba dan haka ke kadai zaki ci ki sha”

Ya fada kadankadan ta yadda ita kadai zata ji.

“Idan baka sha ba, ba zan bari ka ciyar da ni ba”

“Simple”

Hannu ya kai ya karba cup din ya bude bakinsa ya sanye duka, yadda yake dauki be barshi ya fahimci dandanon yogurt din ya sauya ba. Yana sanye sai tai saurin daukar cinyar kazar ta kai bakinta ta soma ci tana kallonsa. Matsawa yai kusa da ita ya zagaye ta da hannayensa ya saka hannayensa cikin rigarsa tana wasa da cikinta... After like five minutes idonsa suka fara nauyi har wani duhu yake gani, cire hannayensa yai daga jikinta ya jingina da gadon sai bachi. Ajiyar zuciya ta sauke ta tashi da sauri ta dauki cup din karar bude kofar dakin da tai ne yasa shi bude idonsa daker sai dai be iya gane abunda yake faruwa daga haka ya tuntsire a kasan carpet wani bachin gaske ya lula wata duniyar mai nisa da shi. Bude buden dakuna ta shiga yi har ta bude Kitchen, sai ta shiga ta kunna tab din ta wanke cup din ta aje ta ciro maganin dake jikinta ta bude kitchen cabinets tana duba abubuwan dake ciki, wani kofi ta dauko ta zuba maganin ciki sannan ta dauki cup din ta shiga store ta boye shi ta fito da sauri ta dawo dakin. Ganin ya gyara kwanciyarsa yasa gabanta faduwa tunda dazu a jingine da gadon ta barshi, da sannnu ta dauki Hijab din ta shiga bathroom ta wanke inda ta tauna maganin ta fito da shi ta aje, sannan ya fiddo wayarta ta kunna ta fita falo ta shiga dayan dakin mai kice da kayan alatu ta shiga kiran number Sadiq, daman tuntuni hankalinta yana gurinsa tana son taji halin da yake ciki tana yi tana kallon kofa dan gani take kamar Sadam zai iya tashi ya biyo bayanta. Wayarsa a kashe amman after every thirty minutes sai ta sake bugawa. Kamin garin Allah ya waye duk ta matsu akan idonta akai sallah asuba, sai da tai kamar ta tashi Sadam sai kuma wata zuciyar ta hana ta. Misalin bakwai da rabi ta saka Hijab dinta ta bude jakarta ta dauki dubu daya ta fito harabar gidan tana da sauri kamar an biyota, gurin gate din taje yana budewa gurin zarge sakatar ta zarge har da hannunta a take jini ya samu hanyar fita. Mai gadin ne ya fito daga cikin dakin da sauri ya nufo inda take.

“Hajiya lafiya?”

Rasa tai me zata ce masa, bata dauka har da mai gadi Sadam ya aje a sabon gidan ba.

“Bude min wani abu da zan karbo”

“Fada min sai na karbo miki”

“Aa ni zan karbo da kaina bude kawai”

Umrnin data bashi ne yasa ya bude mata gate da yana da mamaki, bayan ta fita ya rufe, ita ta soma sheka gudu kamar an biyota sai da ta kawo gurin round about sannan ta samu achaba ta tara.

“Malam Uduth zaka kai ni”

“Dari uku”

“Muje”

Tsalle daya tai ta haye achaba tana fada masa yai gudu ya kaita. Tasan asibitin uduth tunda ba yau ta fara zuwanta ba, mai achaban na sauketa ta nufi emergency gurin yan hadari, Nurses din data samu a gurin ta fara tambaya tana fada musu daidai lokacin da abun ya faru da kuma sunansa. Kamin ta soma bin dakunan tana duba har ta kai ga wanda Sadiq yake ciki. Sai da ta dudduba taga babu wanda ya ganta sannan ya ta shiga dakin idonta cike da kwalla zuciyarta kuma cike da tausayinsa.
  Saman kujerar dake gefen gadon ta zauna tana kwalla, a kansa aka daura nasa bandeji sai kuma a kafarsa da gefen hannunsa... Jin an turo kofar dakin yasa Zinneera saurin mikewa tsaye ba tare da shiri ba, sai dai ganin bakuwar fuska yasa hankalinsa kwanciya duk kuwa da kasancewar bata san ko wacece ba kuma bata san alakarsa da ita ba. Ummi ta nufota tana fadin

“Ke yar'uwarsa ce ko matarsa...?”

Zinneera bata ce komai ba, ta nufi kofar fita da sauri, ta kai hannu zata bude kofar Doctor Tahir ya turo kofar ya shigo. Mutuwar tsaye tai tana kallonsa ga idonta duk hawaye shabe shabe, kallonta yai daga sama har kasa fuskarta shimfide da mamaki. Saurin ratsawa tai gefe ta fice da sauri. Ya dade tsaye a gurin yana mamaki kamin ya karaso gurin Sadiq ya duba shi, kokarin gano alakarsu yake yar'uwarsa ce ko kuma me?

“Be farka ba?”

“Eh be farka ba”

“Idan mahaifinshi ko mahaifiyarsa ko wani jigonsa ya zo ki sanar da ni”

“Okay Doctor amman idan wata matsalar ce a fada min tunda ni na kade shi”

“Na san da ke ai, wani jigonsa na ce”

“Doctor Akwai wata Matsala ne?”

“Eh akwai”

Yan fadar hakan ya fice daga dakin, ita kuma ta zauna a kujerar jikinta sanyaye tana kallonsa.....
  

.
________________

Ni kadai na ke ganin Zinneera a shashasha?
  Ya zatai idan ta tarar Sadam ya farka?
Me doctor yake nufi da akwai matsala?
Anya Doctor Ba zai Fadawa Sadam ba kuwa?

Dan Allah na rokeku ku taimaka kuje YouTube kui searching Channel dina Taskar Khadeeja Candy kui min subscribe kuma ku danna bell din, haba jama sai rokonku nake kamar na roki kudi 😪😫 subscribe kawai nake so ku faranta min rai mana ta hanyar subscribe dan girman Allah 🙏😭😭😭

Continue Reading

You'll Also Like

447K 17.7K 48
Vikram, a senior officer, prioritizes his duty above all else, much like his father, ACP Rajendra. He has three siblings: one is an officer, and the...
190K 5.6K 25
/You Story. Y/N stumbles upon a girl in a bar that she falls in love with after sharing a kiss that night leaving her to deal with the aftermath that...
1.7M 141K 65
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...
146K 9.9K 110
Fate of the innocent,,, A very heart touching story