ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

116K 15.9K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

Don't Rush Things

1.8K 319 128
By KhadeejaCandy

ALEEYA POV.

A hankali ta kai hannu ta rufe bakinta gudun kar tai numfashi mai karfi Umma taji motsinta daga zauren da take boye, kunnuwanta su jiyo mata komai cewar Zinneera na son Sadam da kuma zancen Umma na cewa karta fadawa kowa ita ta san yadda zata bullowa lamarin. Kwalla ne suka cika idonta suka sauko mata tasan Zinneera ce zata samun Sadam baya ita kuma an sakata ta saka sonshi a ranta. Juyawa tai ta jingina da ginin zauren hawaye na mata zuba, da tasan abunda zata ji kenan da bata dawo daga islamiya daukar Fiqhu dinta ba, miya ma tun farko ta tsaya ta saurara? Miyasa lokacin data shigo zauren ta ji Umma na ambatar Sadam kike so, ta tsaya saurare? Wata kila da yanzu duk bata ji wannan ba.

Takawa ta fara yi a hankali har ta fita daga zauren gida tana hawayen da bata san suna zubo mata ba, sai a yanzu take kara jin kaunar Sadam a zuciyarta, idanuwanta sai yawo suke mata da fuskarsa, kashim turarensa yadda yake drees kalamansa da duk wani abu daya danganceshi.

‘Ba lallai ne ya so Zinneera tunda ni ya gani ya fara so’

Wani bangare na zuciyarta ya fada mata.

‘Aa zai so ta, Zinneera ta fini komai, Zinneera ta fini komai kyaun jiki, kyaun fuska, haske da komai ma, zai so ta’

Ita kadai take ta sakesakenta kamin taji an dafata.

“Aleeya”

Tai saurin juyowa ta kalli kawarta Nafisa.

“Lafiya kike kuka?”

“Kuka na ke yi?”

Ta kai hannu ta taba fuskarta sai ta jita a jike da ruwan hawaye. Saurin gogewa tai.

“Ban ma san sun zubo ba”

“Me ke damunki?”

“Ba komai”

Tai saurin yin gaba ta bar Nafisar a tsaye gudun karta sake yi mata wata tambayar. Kamar wacce ta rikice haka ta koma islamiya, karatun ma sai ta kasa yi har aka tashi, sannan ta kamo hanyar gida ita da Larai da Aliyu bata taba jinta cikin irin yanayin da taji yau ba, bata miye so ba sai yanzu da take jin Zinneera na son wanda take so. So silent haka ta isa gida, sallamarta ma can kasa kasa tai duk yadda tai kokarin ta boye damuwarta sai ta kasa sakamakon cika da idonta ke yi da kwalla. A gindin ice ta samu Umma tana gyaran shimkafa yar hausa, Larai da Aliyu suka nufi gurin da Umma take ita kuma ta nufi dakinsu, sai ta samu Zinneera kwance ta dunkule fuskarta da alama bachi take ko kuka, sai kawai ta aje jakar makarantar a gurin data saba ajewa ta juyo ta fito ta nufi dakin Umma, saman gadonta ta zauna ta bawa kofar dakin baya tana kuka. Umma na ganin yanayin data fito tai saurin tashi tabi bayanta.

A lokacin da taji motsin shigowar Umma sai tai kokarin boye kukanta, sai dai ta makara domin Umma taha hawayen nata.

“Lafiya me akai miki?”

“Kaina ke ciwo”

Ta bata amsa kai tsaye. Sai Umma ta zauna kusa da ita.

“Ko dai kinji Zinneera na son Sadam ne?”

Umma ta fada with lower voice tana kallonta. Kokarin yai tai kamar bata ji ba.

“Me tana son Sadam? Sadiq din fa?”

Tambayar take amman kwalla zuba suke kamar dazun. Umma tai shiru sai kallonta take sai tausayin yarta ya kamata.

“To idan ma naji me zai sa nai kuka ni kaina ne yake min mugun ciwo”

Ta fada tana kokarin tashi daga gurin, sai Umma ta riko hannunta.

“Saboda kina son shi... Bana bukatar ki fada min ko karki fada min wannan zubar hawayen na ki ya karantar da ni komai”

“Umma sake ni ina son shiga bandaki”

Ta fada still tana hawaye, sai Umma ta saketa ita ta fita daga dakin da sauri, hakan yasa Umma jin babu dadi, be kamata ta batawa Aeeya saboda Zinneera ba, kamar yadda be kamata ta ki sharewa Zinneera hawaye saboda Aleeya ba. Soke kai Umma tai da hannunta tana sauke ajiyar zuciya.

Bandakin ta shiga ba tare da buta ba, kuma ba dan tana jin yin wani abun ba, sai dan ta samu damar yin kukanta son ranta, duniyarta ta zagaye da tunani tana neman dalilin da zai sa Zinneera tace bata son Sadiq Sadam take son duk kuwa da irin kaunar da take yi wa Sadiq, ba zata ce dan kudin gidansu ba ne, domin kamin Sadiq da kuma lokacin da Sadiq yake nemanta masu kudin da yayan masu kudin sun nemata amman tace sai Sadiq, to ko dai ya yaudareta ne? Ko kuma wani abun ta gani a tattare da shi? Da gaske jiya gidan Hajiya Karima ta kwana ko boyewa tai? Ko dai wani abun Sadiq yai mata shiyasa tace Sadam take so? Zinneera ta fini bukatar farinciki a yanzu, kuma yar'uwata ce ko raina tace tana so zan iya bata balle saurayinda ko baiko ba a mana ba, Wallahi ko miji nake aure Zinneera tace tana son shi zan rabu da shi ita ta aura balle saurayi, be kamata nai mata hakan ba, ban san iya damuwar da take ciki ba, idan ban fidda ta ba, be kamata na kara sakata ba.

Amman kuma ta rasa wanda zata so Sadam? Miyasa sai Sadam?

Wani bangare na zuciyarta yana kokarin hanata alherin da take son yi ma yar'uwarta. Daga lokacin data kudiri aniyar sharewa Zinneera hawaye sai taji nata kukan ya tsaya duk wani jin da take kamar ba zata iya bar mata Sadam ba, sai ya yaye mata zuciyarta ta cika da kauna da kuma tausayin yar'uwarta, waya sani ma ko tana son ta aurenshi saboda ta ji cewar Umma ba mahaifiyarta ba ce, wata kila tana son hada jini da wani nata ne. Goge fuskarta tai ta fito daga bandakin. Umma bata tsakar gida, sai kawai ta wuce dakinsu nan ma bata samu Zinneera a ciki ba, sai kawai ta kwanta rairan tana kallon ceiling.

ZINNEERA POV.

Bayan fitar Aleeya daga dakin sai tai saurin tashi ta cire tufafin jikinta ta dauki doguwar riga ta saka ta yafa mayafin ta saka ta dauki canjin data dawo da shi ta saka takalma ta nufi kofar fita. Data fito sai kuma ta rasa inda zata je, a bakin kofar gidan ta zauna kafafunta a aje ta rafka uban tagumi tana kallon yaran unguwa dake wasa a kofar gidan dake fuskantar nasu.
Sai a yanzu take jin kamar be kamata tai ma Aleeya haka ba, wata kila tana son Sadam, kuma idan taji abunda tai ba zata jidadi ba, ita kanta tasan be kamata tai hakan ba. Sai bata da wata mafita a yanzu bayan wannan, idan har tace zata bata da Sadiq a yanzu ta jira zuwan wani aiki ne babba, saboda ta kori kowa kuma duk wanda ya zo neman aurenta yan unguwar cewa suke an mata miji, Sadam ne kawai hope dinta a yanzu, ita dai shi kadai tunaninta ya bata bata san wata mafita ba bayan wannan. Hawayen fuskarta ta share ta mike tsaye ta dauki bakin gawayin dake kasa tai rubutu jikin ginin gidan sannan ta jingina tana sauke ajiyar zuciya. Kamin ta dago ta nufi gidansu Zainab kawarta.
Sallama tai kananen Zainab din suka amsa mata, sannan Zainab din ta fito daga falo.

“Oo yau Zinneera a garinmu”

“Ke zuwa gidanmu kike ne, da rainin wayo, ni wayarki na zo ki ara min ba zama na zo ba”

“Wayarki ta lalace hala?”

“Eh tun satin can”

Komawa Zainab din tai ta dauko mata wayar kirar shakidinka bakauye, ta mika mata.

“Yauwa sai na kawo miki, ina Mama hala”

“Taje gaisuwa”

Tana fitowa gidan ta saka number Sadiq ta kira shi. Sai da tai ta ringing sannan ya daga.

“Hello”

“Hello Sadiq ni ce, ka same ni a a bayan gidan Alhaji Sulaiman Chanji yanzu ina gurin ina jiranka”

Shiru yai be ce komai ba, jin hakan sai ta kashe wayar ta koma cikin gida ta bawa Zainab wayarta sannan ta fito ta nufi gurin data kwatanta masa, ya san gurin saboda ita, wani lokacin a can suke zance kasancewar gurin babu mutane sosai, bayan gidan wani baban dan siyasa ne da ake kira da Alhaji Sulaiman Chanji, kato gida ne mai fadin gaske, sai wata makarantar boko wace ta bawa gurin baya, sai ya zama a tsakanin gidan bayan gidan da bayan makarantar wata madaidaciyar hanyace da mutane ba su cika bi ta gurin ba, ko masu motoci da babu sai idan za su yanke hanya suke biyowa ta nan. 

Mikewa tai tsaye tana tafiya da dai daya hannayenta a zube tana kallon kasa, sai da ta kai karshen hanyar duk kuwa da tsayinta ta kara dawowa, ta tsaya jikin wani dutse tana ta kallon inda take zaton Sadiq zai bullo amman be bullo ba, sai da tai kusan minti arba'in a gurin sannan ta hango motarsa ta doso inda take slowly.
Tasan hakan baya rasa nasaba da abunda ya faru, wata kila har yanzu fushi yake da ita.

Tana kallonsa har yai parking kusa da ita sannan ha bude motar ya fito yana kallonta, irin kallon nan na ni fushi nake da ke.

“Ya akai?”

“Rufe motar ka karaso nan maganar da zan yi mai muhimmanci ce”

Rufewa yai ya zuba hannayensa aljihu ya karaso inda take tsaye ya tsana yana kallonta. Ita kuma ta kasa magana kuma ta kasa daga kai ta sake kallonsa.

“Ina jinki”

Har yanzu shiru bata ce komai ba.

“Aiki na ke fa kika kirani”

Sai a yanzu ta dago kai ta kalleshi fuskarta shar da hawaye.

“Sadiq zaka iya min wani abu?”

“Eh minene?”

Ya tambaya da sauri yana kara fuskartata, ganin hawaye a fuskarta ya tashi hankalishi duk kuwa da yasan ba ba lallai sai abu na da muhimmanci Zinneera take zubar masa da kwalla ba.

“Fada min minene?”

Ya sake tambaya yana mika mata dukan hankalinsa.

“Za ka min alkawarin cewa ba zaka auri wata mace ba sai ni?”

Tsayawa yai kallonta for some seconds kamin ya daga kansa sama ya busar da iskar bakinsa, he just don't know why Zinneera take behaving kamar wacce bata cikin hankalinta wani lokacin.

“Daman wa yace wata zan aura ba ke ba? Wannan wace irin magana ce Fisabilillahi? Haba Babyna”

“Ni dai kai min alkawari yanzu dan Allah”

“Na miki alkawari ba zan auri wata mace ba sai ke”

“Ka min alkawari ko yaushe ne zaka jira ni zaka aureni”

“Na miki alkawari zan jira ki ko zuwa yaushe ne zan aureki, shikenan?”

Ta gyada kai.

“Amman Sadiq kasan muhimmanci alkawari ai, ba zaka saba ba”

“Ba zan saba ba, daman bana da niyar auren wata nace sai ke”

“Kuma Sadiq zan roki wata alfarma zaka min?”

“Zan miki fada min ko minene a duniyar zan miki matukar ina da iko”

Sai da ta kalleshi ido cikin ido sannan ta ce

“So nake kaje gidanmu ka ce ka fasa aurena....!”

Haka yaji maganar kamar saukar aradu, sai ya nuna kansa ya waiga ya kalli ko'ina yaga su kadai ne ya sake kallonta.

“To ko dai ba ke bace? Wannan wace irin magana ce Zinneera? Taya zanje gidanku na ce na fasa aurenki akan wani dalili? Saboda me?”

“Saboda mu samu mafita”

“Ta ina samu mafita idan na fasa aurenki? Duk wani kokari da nake a yanzu Zinneera na samun damar aurenki ne, idan fadan da nai miki dazun ne ki yi hakuri kinji ba zan sake ba i promise”

“Ba saboda shi ba ne”

“Saboda kina ganin kamar ba zan iya auren nan kusa ba? Idan nan da wata biyu ko daya kike son na aureki zan iya aurenki shikenan?”

“To kudin fa?”

“Zan biya daga baya”

“Taya?”

“Koma ta yaya ne zan biya, maganar kudin nan ta daina damunki, idan aure kike so nan kusa zamu yi nan da wata biyu kinji”

“Zaka iya biyan kudin nan da shekara daya?”

“Koma yaushe ne zan biya Zinneera”

“Idan baka biya nan da shekara daya ba, rayuwarka tana cikin hadari Sadiq, ba zai kyale ka ba”

“Zan biya nan da shekara daya shikenan?”

“Taya zaka samu miliyan ashiri nan da shekara daya?”

Kansa ya daga sama sai kuma ya sauke yaje gurin motarsa ya jingina da motar kamin ya juyo ya kalleta.

“Akwai wani gida da Baba ya bar mana zai yi miliyan ashirin da biyu shi zan saida sai n biya kudin”

Kai ta girgiza tana hawaye.

“Baka da wata mafita Sadiq, idan baka biya kudin nan da shekara daya ba komai zai iya biyowa baya”

“Babu abunda zai biyo baya ki kwantar da hankalinki dan Allah”

“Ba zai kyale ka ba, yace idan baka biya nan da shekara daya ba, duk abunda yai maka kai ka ja”

“Be ce ba...”

“Yace ya turo maka sako a wayarka ni na goge”

A nan ta labarta masa sakon data goge ranar.

“Maybe ma baki gani daidai ba, maybe ba haka yace ba, kuma wannan duk barazana ce kawai”

“Ba barazana bace da gaske yake”

“Naji da gaske yake, amman fasa aurenki ai ba shi ne mafita ba”

“Shine kadai mafitarmu a yanzu Sadiq”

“Taya? Zinneera don't rush things”

Shiru tai ta hade yawun bakinta kamin ta bude bakin.

“Idan ka fasa aurena, zan auri Sadam hakan zai bani samun kudin da zaka biyashi”

Matsowa yai kusa da ita ya kai hannayensa tmya rike kanta ya matse sosai har sai da ta rumtse ido sannan ya saki kawai shi be yarda yau Zinneera tana cikin hayyacinta ba.

“Nasan abunda na ke yi Sadiq, idan baka biya kudin nan da shekara daya ba komai zai iya biyowa baya, kuma kana da bukatar rayuwa ko dan ni, da mahaifiyarka da kuma yan uwanka duk da kai suka dogara”

“Amman kuma mu rasa wata mafita sai wannan Zinneera?”

Ya fada murya kasa kasa jikinsa yai sanyi.

“Bayan ita bamu da wata mafita Sadiq, babu inda zamu samu miliyan ashiri cikin sauki sai ta wannan hanyar ko mutuncina zan siyar ba zamu samu miliyan ashirin ba, kuma bana son ka aikata wani mummunnan abu, amman idan na auri Sadam zan samu sama da haka”

Idonsa ne suka cika da kwalla.

“Kawai ki ce baki son na yanzu Zinneera, ko kuma ki fada cewar Sadam yai nasara a zuciyarki”

“Wallahi har gobe ina son ka Sadiq, kuma ba zan taba son wani namiji bayan kai ba”

Gefen hannunsa ya kai ya share hawayensa ya duka har kasa ya daga kansa yana kallonta.

“Dan Allah karki wannan abun Zinneera, ki kawar da wannan tunanin a ranki dan Allah ina son Wallahi”

Baya baya tai tana hawaye.

“Saboda kai zan yi Sadiq, saboda rayuwarka da tawa data mahaifiyarka”

Mikewa yai tsaye wasu hawayen na zubo masa.

“Ba zan bari ki aikata ba Zinneera ba zan baki damar da wani namjin zai rabi jikinki ya ji kanshin jikinki ba, zan iya hade zuciya idan kika kwanta katifa daya da wani namijin da ba ni ba, ba zan iya ba”

Ta sanda kanta kasa tana kuka, sai kuma ta dago ta kalleshi.

“Ko da na maka alkawarin cewa babu abunda zai shiga tsakanina da shi?”

“Sadam ba zai aureki ya kyaleki ba, ya nema tun a waje balle ma cikin gidansa ko ba Sadam ba, babu namijin da zai aureki yai ta kallonki kamar hoto, i just can't....”

Ya nufi motarsa yana share hawaye.

“Indai har kana so! indai har kana kaunata! Indai har da gaske zaka iya komai a kaina to kaje gidanmu ka ce ka fasa aurena...!”

Ta fada tana hawaye kamar ba gob. Tsaya yai cak kamin ya juyo ya kalleta idonsa cike da kwalla...

__________________________

Anya Sadiq zai yarda kuwa?
A tunaninku ba ganganci ne Zinneera take kokarin aikatawa ba?

Team Aleeya
Team Sadam
Team Sadiq
Team Zinneera
Team Zabin Rai

Tafiyar fa yanzu aka fara ina fatar kun shirya?
  Duk wanda ya shirya ganin page din gobe yai comment, in ba haka ba sai jibi ko Friday 😉

Share pls.

Continue Reading

You'll Also Like

11.7K 314 41
Irina thought she was the luckiest woman when she got accepted into YG Entertainment company as Media Marketing staff. But the next lucky thing came...
3K 220 26
Is a story about a soldier and love which is completely a fictional character.
Ice Cold By m

General Fiction

2.7M 98.4K 54
COMPLETED [boyxboy] Wren Ridley is always two steps ahead of everyone, or so he thinks. His life seems out of his control when he starts having feeli...
120K 6.9K 44
When she wants to go to her dad's house as she was missing them!! Her husband who was searching online how to "stop your wife from going away from yo...