YARINYAR CE TAYI MIN FYADE

By miss_untichlobanty

156K 10K 1.8K

WANNAN LABARI NE DA WASU BANGARE YA FARU A GASKE. BAN CANJA SHEKARUN YARINYAR BA KO ALAKA BA,AMMA NA CANJA S... More

CHAPTER 1
CHAPTER 2
CHAPTER 3
CHAPTER 4
CHAPTER 5
CHAPTER 6
CHAPTER 7
CHAPTER 8
CHAPTER 9
CHAPTER 10
CHAPTER 11
CHAPTER 12
CHAPTER 13
CHAPTER 14
CHAPTER 15
CHAPTER 16
CHAPTER 17
CHAPTER 18
CHAPTER 19
CHAPTER 20
CHAPTER 21
CHAPTER 22
CHAPTER 23
CHAPTER 24
CHAPTER 25
CHAPTER 26
CHAPTER 27
CHAPTER 28
CHAPTER 29
CHAPTER 30
CHAPTER 31
CHAPTER 32
CHAPTER 33
CHAPTER 34
CHAPTER 35
CHAPTER 36
CHAPTER 37
(FINAL)CHAPTER 38
AKWAI KURA

QUESTIONS AND ANSWERS

2.6K 154 48
By miss_untichlobanty

CHAPTER 29 LOADING......

WANNAN SHAFIN TAMBAYA CE ZAMUYI TA GA MUTANEN DA KE CIKIN LITTAFIN YARINYAR CE TAYI MIN FYADE WATO:

LUBA
ALIYU
LADIDI
SAMIR
AUNTY MARYAM
UMMI

TAMBAYACE NI DA KU ZAMU MUSU KUMA SU BAMU ANSWER WATO DAI ZAMUJI RA'AYOYINSU NE. FATAN ZAI NISHADANTAR DAKU... WADDA SUKA KARANTA LITTAFINA NA WATO (KURUCIYAR MINAL) NASAN SUN FAHIMCI MEKE SHIRIN FARUWA. YANZU DAI MU TATTARA RUNDUNAR MU MUJE DOMIN YIN TAMBAYOYIN. WANI HANZARI BA GUDU BA DUK ABINDA KE CIKIN BAKAN GIZO TOH WANNAN BA MAGANAR SU BACE AIKIN DA SUKA AIKATA NE.

*LUBA*

1. ME ZAKI IYA CEWA GAME DA ZAMANKI DA ALIYU?

Ans: me ko zance? AI kuma kun gani kuma kun sani yana min dadi kamar nayi kuka dukda cewa da fari nayi taurin kai amma AI kunsan mu Mata da jan aji.. koma de menene na bada kai bori ya hau.. ko kunada matsala da hakan? (hambuda dambu a baki)

2. TOH GA WATA TIRKA TIRKA TA DANNO KAI LADIDI TA JEFI CIKIN KI WANDA AKE ZATON AKWAI SHIGAR DA.

Ans: (goge kwalla tare da ajiye kwanon dambun) wallahi Allah in ciki ne dani ta barar mini saina shuka Mata rashin mutunci... azzaluma kawai AI mijin ba naki ke daya bane.

Ladidi : ke fitsararriyar nan dani kike?zan bige miki baki fa.

Luba:(kallon bakida wayo) kina tabani sai nayi miki bugun shinkafar year shafi'u

Untichlobanty: Luba kada kuyi fada mana mu fa tambaya ce ta kawo. ...

Aliyu:(ya daga min hannu tare da tsarewa)

Ladidi:(kwafa)

Luba:(tabe baki)

Fans: hmmm anayi munajin dadi..

3. SHIN KINA GANIN ZAKI CIGABA DA ZAMA DA LADIDI.

Luba: untichlobanty kisan abin yi Dan wallahi bani zama da ita ehe.

Untichlobanty: (daga gira daya) idan kuma naki sai ayi yaya?

Luba: haba yar kawalliye ta AI nasan bazaki min haka ba ko?

Untichlobanty: kanki akeji.

Luba:(hade rai) toh me na yarfa ni?

Fans: haba untichlobanty ya da cin fuska

Untichlobanty: a kara magana yasin sai in kashe luban in aurawa aliyu nana😎

Luba: don Allah kuyi shiru ni ban shirya gamo da mala'ika ba.(kunkuni)

Untichlobanty: najiki wallahi.

*ALIYU*

1. ME ZAKA IYA CEWA GAME DA ZAMANKU DA LUBA

Ans: (cikin huci) ku wato abinda ke gabanku kenan sanin zama na da luba bayan kun karanta? Bayan Dana rai a hannun Allah? Toh zama da ita wasai tana min duk abinda nakeso.

Me tambaya: a ah aliyos ya haka? Daga tambaya ka wani hayaiyako ni? Toh Allah ya bada hakuri.

Aliyu: da fari de luba ce kadai zata kirani da aliyos sannan kuma hakuri AI dole nayishi tunda untichlobanty ta hadani da wata irin kaddara

Untichlobanty : kai aliyos ya kake haka ne bayan kasan da badan fans dinnan ba da kaida luban babu inda zaku.

Maidambu: yauwa ta wajena fada masa de.

Aliyu: fans ayi min afuwa da daukan zafi baki daya bana haiyaci na ne wallahi inason Dana na gama tuzuranci nayi aure sai mutuwa suke kuma Dan ma sai na rasa. Ace sure an fara da mutuwa haihuwa da bari? (Zubar hawaye)

Luba:(shafa bayansa) kati hakuri na sani abin da ciwo, untichlobanty Dan Allah ayi wa mijina sassauci mana.

Umaima L abba: ah ah gaskiya mu babu wani sassauci AI in aka dena cakwakiya labarin zai kare kenan.

Maman jawad: kai sister Adai daga masa kafa.

Sis sumayya: gaskiya nide ina tare da umaima.

Sis mammy: nina haka Dan dama ni aliyu haushi yake bani.

Hauwa baba: aliyun namu ne yake baki haushi?

Mrs mai iyali: yanzu de abinda za'ayi muje wajen adda ramla mai_dambu ta raba fadan nan.

Aka waiga ko ina babu alamun adda ramla....

Sarah : toh muje wajen aunty asmeenat mana.

AsmeenatZeeyan: (ta tsime a kujera) kai ni banason shiririta ku barni typing din bakin dare nake.

SURAYYAHMS: la aunty mu gani ko yau ya za'a kaya?

Asmeenat: ki jira in nayi posting zaki gani😉

Untichlobanty: kaina ciwo yake ko zamu iya ci gaba?

Fans: sosai ma kuwa.

2. YANZU WANI HUKUNCI ZAKA YIWA LADIDI INDAI DAGASKE NE TASA JININKA YABI KORORO?

Aliyu:(dariyar mugunta) ai in na fada babu kanta kenan (hararar ladidi)

Ladidi: (murkuda baki) aikin banza yo me akayi da kwarto mazinaci wallahi sai ka sakeni.

AishaIsmail625: ni wai me muke jira ne bamu jibgi jaka ba?

aysherahmaddanlami: yo AI bata lokaci da asarar karfi ne dukanta... yo me akayi da najasa irinta Wanda ko yan wuta baza su so yin makwabtaka da mai irin halinta ba? Mtsww

*LADIDI*

1. TOH KE AI BA'A MA SAN WATA TAMBAYA TA ARZIKI DA ZA'AYI MIKI BA.

LADIDI: kan bala'I! Wato na lura kaf littafin babu Wanda aka Rena kamar ni sai kace ni na tsara labarin.

Untichlobanty: (kallon bakida wayo) au dani kike ko? Laifi nane da ban kasheki kamar sauran ba yo na kashe matar arziki irin nafeesa ma sai banza ke?

Ladidi:(mikewa tare jijjiga ) toh wallahi kamin ki kasheni ni zan kashe ki yo ni da nake da.... kodan de hmm

Untichlobanty;(murmushi) ai ni inada alkalami ko?

imanahmad__100: wallahi kuwa sister ki kwankwashi kanta alkalaminki

Ladidi: wallahi kuma ba fans kuke ba ko fanka ce ku kara minti 1 cikin gidannan saina shuka muku....

Sis mammy: (dauketa da mari)

Aysha noor: uhm yayi daidai aunty na.

Azieta.com : (ta dannata kasa)yayinda mmn kaza da kaza duka suka nufi kitchen me tabarya ne, me ludayi me bulugari akayo kanta da gudu. Nan aka soma jibgarta.

AYYUSH: kunga mu barta kada mu kasheta kunga hukuncin da aliyu yaso yi Mata bazamu gani ba...

Faltex: kuma fa hakane.

Meenal namecy: kuma fa hakane besty... ke ladidi tafi ki kawo wa mutane  ruwa.

Ladidi: Allah ya isa.

Faeexation: zanbige miki baki.....

*SAMIR*

1. ALHAJI SAMIE KAI KUMA SAI MUKA JIKA SHIRU TUN FARKON LABARI.

1. Ayya ai ba laifina bane untichlobanty za'a tambaya ko? Ni dai Abu daya ne har yanzu ban gane ba.... shekarata 35 fa amma ko rike hannun mace ban taba  tabawa ba.

Fans:😳😧

Samir: eh kun jini daidai har yanzu bata min aure ba fa😔

HadizaAbdou: Ayya wallahi har ka bamu tausayi untichlobanty a duba masa Dan Allah

Untichlobanty: wani hanin ga Allah baiwa ne.

maman-hanna: eh kuma kam gsky kike fadi.

*UMMI*

1.TOH UMMI MUN DADE BAMU HADU BA.  KO AKWAI ABINDA ZAKI IYA FADAWA MATA MASU HALINKI NA DA?

Ummi: wannan haka yake an Dade ba'a gamu ba kam... gaskiya a yanda na lura yanzu Mata baki daya musamman da ake wannan yanayi na lockdown, yawancin Mata sunfi maida hankalinsu ga yadda zasu kula da mai gida fiye da tarbiyyar yayan su. Wasu sai kaji suna ayi ayi ma a bude makaranta sun gaji da zaman yaran a gida. Toh kema kin gaji da yarki da danki balle wani? Kuma abin takaicin ma yanzu yan FYADE da luwadu da madigo sunanan ta ko ina kamar iska. Aide itace babu inda za'aje a fadin duniya ba'a sameshi ba.

Untichlobanty: dadin abin ma ba malamai za'a tambaya akan tarbiyyar yara ba uwa za'a tuhuma.

Ummi: toh de wasu kuma shaf Mandela suke da ba komai za'ayi a gaban yaran ba sai suyita yin abubuwa da basu dace ba toh nide har yau ina nadamar abinda sakaci na ya janyo min dukda cewa Allah ya dubeni ya saisaita rayuwar luba bata baci ba wallahi ki sani ba dole kema sai hakan ya faru da taki ba Dan haka ki kula ki kara da addu'a ba shirmen duniya ba. In kika gama samun abinda kike neman kika kwanta bacci kika tashi kika ganki a kasan kasa fa? Mutuwa fa bata yin alert bare ta baki notice... ana bada notice a gidan haya ne saboda kina biyan kudi amma Allah nawa kike biyansa da kike zaune a duniyar sa?😭😭

Untichlobanty: wasu zasuce ai suna yi masa bauta suna iya kokarin su wajen ganin basu Saba masa ba toh amma  kinsan cewa sallar ki bazata biya numfashin da kika sha ba...yanzu in Allah yace ko wani numfashi daya da raka'a daya zaki biyasa toh kwana nawa zakiyi a duniya? Tayaya zaki biyasa rai da ya baki, yayi ki a mutum, yayi ki me hankali... cikin addinai sama da dubu 200 yayiki musulma... ta yaya zaku biyashi ruwan da mukasha, ruwan saman da tsirai sula fito kai nace ta yaya zaku biya shi kanshi tsoran da kuke shukawa?

Ba wayonka bane zaisa in kunyi shuka ta fito, ko ta fito ma sai taki albarka... nawa ne suka shuka bata tsiro ba. Ku har kuma ganin kun wani sha wahala a shukar toh abar batun aiki da inji ma ko da hannu kayi aikinka kawai ka tone ka bule da kasa ne kaje ka rashe a gindin bishiya. Toh wai karfin da ya bakan ma da yace sai ka biya fa? Daya Baku arzikin gona nawa kuka biyashi? Ya Baku Mata wasu har suka mutu basusan mace toh ku gode Allah ma kunada sha'awa wasu al'auran ma babu... a haka ne wasu yan iska saboda rashin godiya Allah suke lalata yaran mutane. Wata ga farin jinin amma da an aureta za'a sakota ta dinga kwabo kenan kamar tamaula saga hannun dogo zuwa hannun gajere.

Wallahi ko Allah ya halicce ka maraya, abincin da zakayi ma bakada shi kafi Wanda daga cikin uwarsa ma babu rai ya fito tunda kai ka shaki iska. Ko musulunci da Allah ya bamu dan yana son mu ne yana kaunar mu. Da yayi niya sai ya halicce mu ya barmu kamar dabbobi kuma mu mutu ya kamamu ya Kona kuma hakan ma yayi mana rahama ne. Rahamar Allah ne yasa ya haramtawa kansa wasu abubuwan.

Ya haramta ma kansa zalinci amma mu da shi ya haccemu dubi yadda muke zaluntar yan uwan mu bayan ya haramta mana muma amma shi ko ranar alkiyama rashin zalincinsa ne zaisa zai nuna maka laifukanka tas sannan ya tambaye ka ko ba kai bane ya baka dama ka kare kanka. Yo Allah na tuba yanzu ko nan nan gwamnati jihanku kukeson gani ai sai kun cika form. Amma a lamarin Allah babu wannan tausayinsa ne fa yasa zai bamu aljanna bayan rashin mutuncin da kuke shukawa a duniya.

Sau nawa kukeyin laifi kuce astaghfirul lah kuma ya yafe kenan ko zancenta ba'ayi ba? Bayan kun gama sheke AYA kuma sai ya Baku aljanna.
Da sai ya bari kun taho niki niki da ladan ku sai ya tare ku yace duk rahama da yama sai ka biyashi. Kun isa? Wane mutum inji mutuwa.

Dan nace miki je ki nemi kudi ga yadda zakiyi ba yana nufin ni zanci riba bane ke zakici riba ni ko bazai karenina da komai ba kuma bazai rageni ba tunda inada komai toh haka Allah yake duk aikin addinin nan da kuke kanku kukeyi ma Dan haka in kunyi Rowan kunki yin sadaka kunyi wa kanku ruwa kun cuci kanku babu ruwan Allah..

Toh ku saurara kuji.... nasan kuna mamaki... wasu na nazari yanzu toh duk rahama nan da  Allah yayi mana shi baya bukatan wani Abu daga garemu ne ? Tunda ko addini da mukeyi kanmu mukeyi wa... ki nutsu kiji me zaki bawa Allah haka kaima Dan uwa saurari abinda mahaliccinka ke bukata...KU KADAITA SHI SHI KADAI.

Idan kukayi masa wannan shikenan kun fanshi kanku toh amma kadaita Allahn a baki? Ah ah a ZUCIYA NE..amma kuma idan har kayi imani dashi toh ko ba'a ce ba zaka bi umarninsa. Anan ne wasu suka Sami matsala.. zasu sabawa Allah iya son ransu da anyi magana suce tsoran Allah a zuciya take suna kafa hujja da hadisin da manzon Allah SAW yace "attakuwa ha huna" yana ishara zuwa zuciyar sa. Tabbas riya(yin ibada badan Allah ) rubutune akan ruwa bashida wani anfani a wajen Allah toh amma dole kabi umarnin Allah babu gudu ba ja da baya.

Idan ko akace Allah yace kuyi kaza ko kubar kaza ko manzonsa ya fa da amma kuka Saba bakuyi kunsan a maganance me kuke cewa?

ALLAH NI NA YARDA AKWAI KA AMMA BAZANYI KAZA BA KO BAZAN BAR KAZA BA. MANZON ALLAH NAYI IMANI DAKAI INA SONKA AMMA BAZAN YI KAZA BA KO BAZAN BAR KAZA BA.

KAI KU SAURARA WALLAHI A AJIYE BATUN BAUTA GEFE IDAN TSAKANI DA ALLAH KUNASON MUTUM IN YACE KUYI KAZA KO DAN FARIN CIKINSA ZAKUYI... MATA NAWA NE ZA'ACE MANZON ALLAH YACE ... SUCE MIJINA YACE.. MIJINKI MIJIN BANZA HAR ZAKI HADASA DA ANNANBI?  WAI MAZAN MA SAI KAJI SUNA MAMA TA TACE... EH MUNJI MAMARKA TANADA DARAJA KUMA DOLE ATI MATA BIYAIYA TOH AMMA WA YACE AYI MATA BIYAIYAR?

Oh Allah ne ko? Toh wai ku ban gane ba🤔 ince da hakkin mijin da hakkin matar Dana iyayen da koma wayen Allah ne da manzon sa suka ce ku bayar toh wai  toshewar kwakwalwa ta Dan Adam ne kesa kubi Wanda suma Allahn zasubi.

Yanzu idan shugaban kasa yace yi kaza kana fitowa sai jikanshi toh abar batun jika ma sai dansa yace karkayi bazakuyi ba ko? Toh imagine matsayin Allah da mutum kunsan Allah kuwa da girman zatin sa? 🥺😔😢

Fans: 😭😭😭 untichlobanty ya isa haka Dan Allah kuka kike samu (yeeeeyeee😭😭😭😭)

Untichlobanty:🤧😔

Ummi:😭😭🤧wallahi wannan magana taki tasa na kara jin sabuwar nadama a zuciyata Dan Allah Mata kada kuyi kuskuren da nayi dukda na tuba bansan da wani idon zan kalli Allah ba😭😢

Fans: ummi kiyi hakuri 😔

*AUNTY MARYAM*

1. Toh aunty maryam mu fa bamu gane inda kika dosa ba har yau munji shiru bakiyi wa luba bayani ba kuma munga sai canja zance kuke.

Ans: toh AI nima ban gane me kuke cewa ba wani bayani ne akeso nayi wa luba ko na samun admission wai?

SHIRU BABU WANDA YAYI MAGANA... JIJJIGANI AKA FARA YI GANIN NA KWANTA. UNTICHLOBANTY KI RUBUTA MANA... INA GANIN BIBBIYU KAMIN NA RUFE IDO NACE KAI ABAR NI DAN ALLAH MAGANIN MURA NASHA BACCI NAKE JI. DAGA NAN NA ARCE TARE DA FARA NINSHARI KAMAR RAGON LAYYAR DA DUSA TA MAKALEWA😂😂😂

FAN: 😂😂 Wallahi untichlobanty bakida dama yanzu kin gama sa mutane kuka kuma zaki samu dariya sai kace tababbu.

NIDE SOSHE SOSHE NA FARA TAS TAS KAKEJI INA KASHE SAURO..

FANS:😂😂😂

ALIYU: babyn aliyos ki fesa maganin sauro kinsan untichlobanty dinmu ajebo ce yanzu sai jikinta yayi ja saboda ciwon sauro.

Mmn ilham: kuma bamason malaria ta kamata

Nana: kaikai bakisan immune dinta ba ko? Banda mura kamin kiga malaria ta riketa sai an irga yawan shinkafa buhu 10😂😂

Mama: aini bansan dalili ba untichlobanty tana burgeni.

Untichlobanty:(cikin gigin bacci ) very soon zan Baku update

Fans:😂😂 cikin bacci ma mafarkin yin update take.

Y2k: wannan ai maiyar bacci ce

Untichlobanty: dadin abin bana yawun bacci.

Fans:🙆🏻‍♀️😂😂

Y2k: kut dama ba bacci kike ba? Ku kamota.

Untichlobanty: kafa me naci ban baki ba?

Saknerh: ku barta Dan Allah kar ta kasa mana update gobe

KAI BAN TABA YIN RUBUTU ME YAWAN WANNAN BA. FATAN AN NISHADANTU,FADAKARTU DA KUMA ILMANTUWA.

FATA NA GARI MASOYA NA A TSIMAYI CHAPTER 29 GOBE DA IZININ ALLAH!

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

5th July,2020.

Continue Reading

You'll Also Like

1.8M 114K 200
**Story is gonna be slow paced. Read only if you have patience. 🔥** Isha Sharma married a driver whom she had just met. She was taking a huge risk...
FURUCI NA NE By Hauwa A Usman

Mystery / Thriller

43K 3.6K 37
"Baba meyasa kazama boka bokanci fa haramun ne kuma k'arya ne shirka ne Allah baya yafewa mushirki..... "ke Izza ki kiyayeni idan kika nemi d'agamin...
5.2K 465 111
Labarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zat...
1.1M 28K 45
When young Diovanna is framed for something she didn't do and is sent off to a "boarding school" she feels abandoned and betrayed. But one thing was...