ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

116K 15.9K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

Phone Call

2.2K 282 19
By KhadeejaCandy

Karasowa Aleeya tai kusa da su hawaye na zuba a idonta. Sai Sadam yai saurin mikewa tsaye ya nufi dinning ya aje kofi sannan ya juyo yana kallon yadda suka rumgume juna suna kuka, be san miyasa yake jin rashin kyautawa a kular da yake bawa Zinneera ba, musamman ma ganin da Aleeya tai musu a yanzu yasa shi.

‘Ba dan wani abun kai ba, sai dan tana bukatar wani kusa da ita, babu wanda zai zargi komai a ciki, kuma me ye abun zargi a ciki?’

Zuciyarsa nata kokarin wanke sa sai dai baya jin natsuwa da hakan, a dayab bangaren kuma yana jin kamar ba zai iya jurewa da hawayen da zinneera take zubarwa ba, yana jin digar ko wane hawaye daya fito daga idonta kamar saukar ruwan zafi a zuciyarsa. Sosai Zinneera ta rike Aleeya tana ta kuka kamar daman can an fada mata a kafadarta zata yi kukan. Sun dauki lokaci a haka sannan Aleeya ta shiga rarrashin Zinneera ba dan ita ma ta gama kukan ba, sai dan tausayin yar'uwata daya cika mata zuciya. Sai da suka zauna a saman sannan Mommy ta sauko tana kallonsu cike da tausayawa.

“Aleeya kin zo?”

Sai ta gyada mata kai domin kuka ya ci karfinta ba zata iya magana ba.

“Be kamata ki karawa yar'uwarki nauyin zuciya ba, karfafa mata kuiwa ya kamata kiyi ba ki saka ta kuka ba, ya kamata dukanku ku dauki komai a matsayin kaddara, ba kusan abunda Allah ya tsara zai faru nan gaba ba”

Ta gyada kai a karo na biyu tana share hawayenta ta kalli Zinneera cike da tausayawa.

“Umma ma ta damu fiye da ke”

“Bana son jin komai Aleeya bana son komai na tsani kowa ina son kebewa ni kadai a wani gurin da zan manta da komai na dan wani lokacin”

Zinneera ta fada cikin muryar kuka.

“Amman Zinneera...”

“Aleeya please... Kowaye ba zai so jin komai a yanzu ba, kin san wacece Zinneera ki dan daga mata kafa please”

Sadam ya saka baki daga can jikin dinning da yake tsaye. Kai ta gyada masa ta sake kallon yar'uwata.

“Bari na tafi gida Umma bata san na zo nan ba, bari na tafi gida”

Ta mike tsaye sai Zinneera ta riko hannunta suka fito tare. A harabar gidan Aleeya ta kalleta ta ce

“Ina son yar'uwata, ban taba jin son ki kamar yau ba”

Zinneera bata ce komai ba, sai hawaye take. Suna daf da kaiwa gate Sadam ya faka motarsa gabansu ya budewa Aleeya gidan gaba.

“Shigo na saukeki”

Ba musu Aleeya ta shiga, Zinneera ta tsaya a gurin tana kallonsu har suka fice, sannan ta juyo ta nufo gurin da ake faka motocin gidan ta zauna kasa jikin wata motar rumgume da hannayenta. Tunanin ne ya zame mata biyu, ta ina Sadiq zai iya samu miliyan ashiri cikin shekara daya? Idan be samo ba me zasu masa? Idan kuma ta fada masa hankalinsa zai tashi, idan kuma ta bar abun a rufe ta ya zai san abunda ya faru? Tana jin lokacin da Suraiya ta faka motar amman bata dago ba har ta rufe motar ta shiga ciki. Tayi minti talatin a ciki kamin ta fito fuskarta cike da tausayi ta rika zagayen motocin har ta hango wacce Zinneera take zaune taje ta lallabata ta taso da ita ta shiga da ita ciki.

Driving yake kana kallon yadda Aleeya ta kawar da fuskarta tana share hawaye.

“Tsakanin ke da Zinneera ban san wane yafi wani jin zafin lamarin nan, bana son ganin kukanku dukanku ku biyu, babu abunda kukan zai canja musu da zaki daina hawayen nan da kin taimaka min”

Ya fada da hakikan gaskiyarsa, domin kukanta yasa shi jin babu dadi. Juyowa tai ta kalleshi da jajayen idanuwanta, a kalla yau akwai wanda ya damu da zubar hawayenta, sai ta ji wata natsuwa da annshuwa sun ziyarci zuciyarta.

“Rashin uwa akwai zafi, yau ina jin zinneera kamar ta rasa Umma ne, dukanmu ba mu taba sanin wannan ba sai yau, taya dare daya zamu ji wannan? Da ma nice zan iya juyewa amman Zinneera?”

“Zata iya dauka, matukar zaki iya jurewa ki karfafa mata gwuiwa, ni kuma zan goya miki baya har ki tabbatarwa kanki ke din jaruma ce”

Ya fada yana murmushi, be san yadda akai maganar tai tsalle ta fito ba, amman ya san a yau na fada mata wani abu mai muhimmanci daya kamata ya fara ginawa kansa da ita rayuwarsa da ita.

“Na gode Sadam”

Ya fada tana bude motar ta fita.

“Ki kula da kanki”

Ya fada mata lokacin da idanuwanta suka gauraya cikin nasa. Kai ta gyada masa ta rufe motar zuciyarta cike da kaunarsa. Yana sauke Aleeya ya nufi gurin Daddy, be baro can ba sai daf da sallah isha'i, gida ya dawo yai wanka ya canja wasu tufafin, a gida yai sallah isha'i sannan ya saka computer a gaba yana duba wasu abubuwan. Guraren goma da rabi ma dare Daddy ya kira wai ya zo yaga wani abu kamin ya tura masu kula da tafiyar aikin kamfanin da za a bude jibi. A dole ya rufe computer ya hada takardun ya tafi da su. A can din ma sai da suka yi awa daya a falo suna duba wasu abubuwan tare da Daddy sannan ya taso ya nufo part din Mommy, ya san by this time ba kowa a falon domin Mommy tana can bedroom din Daddy tana bachi, Suraiya da Siyama kuma sun yi bachi., amman ga mamakinsa sai ya samu kofar a bude, da mamaki ya tura ya shiga a nan ma ya tarar wutar falon a kunne, hanyar stairs ya kalla. Zinneera ce a zaune a gurin sanye da abayar dazun tana kallonsa kamar yadda yake kallonta. Kayan dake hannunsa ya aje a saman doguwar kujera ya nufi kitchen, tea ya hada cup biyu ya fito rike da su ya nufo inda take zaune, ita kam kallonsa kawai take har ya zauna saiti da ita ya mika mata dayan kofin.

“Kin kasa bachi ko?”

Hannu ta ta karbi kofin bata ce masa komai ba. Sai ya dan kalleta kadan ya dauke kansa yana murmushi.

“Haka na kasa bachi jiya”

Kallonsa tai.

“Saboda me?”

‘Saboda na kasa banbance tsakanin ke da kanwarki’

Ya fada a zuciyarsa, a fili kuma sai ya ce.

“Nima ban sani ba kawai dai na kasa bachin ne”

“Yau kuma miyasa ba kai yi bachin ba?”

Ta bukata tana kallon agogon gmt dake falon wanda ya nuna karfe goma sha biyu saura kwata na dare.

“Aiki muke yi akan kamfanin da za a bude jibi, daddy ma yana can be yi bachin ba”

Ya fada yana mikewa tsaye ya nufi gurin daya aje takardun, ya janyo wani karamin tebur dake tsakankanin kujeru ya dora laptop din sama yana bude takardun.

“Tun da ba za ki yi bachi da wuri ba zo na nuna miki aikin da na ke”

Kamar ba zata taso ba, sai kuma ta taso ta sauko ta karaso inda yake zaune sai ta zauna a karamar kujerar dake kusa da shi. Cikin hotuna ya shiga yana nuna mata yadda tsarin kamfanin yake.natsuwa tai sosai tana kallon hotuna kamar da gaske hankalinta yana gurin.

“Sadam yanzu idan kana bin mutum kudi sai mutumen yai ta tsaba maka alkawari har ka fusata kace idan be  aka kudinka nan da wata daya zaka masa komai me zaka masa?”

Kai tsaye ta jefo masa tambayar har sai da ya kalleta

“Zan iya masa komai ma, ciki har da daureshi ko kuma na saka a wulakanta shi, tun da ya saba min alkawarin yana sabawa, ba zan yarda na daga masa kafa ba”

“Ko da ya roka?”

“To me zaisa na daga masa kafa bayan ya saba sa6a alkawari? Amman miyasa kika tambaya?”

“Ina ayyana kaina ne a rayuwar da nake ciki a yanzu”

“Zinneera ki sassautawa kanki dan Allah, ba komai ya kamata ki yi tunani ba a yanzu hutawa ya kamata ki yi, daga baya sai ki yi tunanin ki, karki takurawa kanki da yawa”

Ta gyada masa kai,  zuciyarta nata raya ma irin abunda zai samu Sadiq, gabanta sai faduwa yake. Sadam be sake ce mata komai ba, ya maida hankalinsa a gurin aikin da yake a computer ita kuma ta tashi zuciyarta cike da tunani ta nufi upstairs.

SADIQ POV.

Ya kasa natsuwa yana gida amman zuciyarsa da hankalinsa suna gurin Zinneera ya saka samun sukuni saboda kawai ya san Zinneera a yau gidansu Sadam zata kwana, ta saba kwana a can kamin yanzu amman kwananta a yau yana sashi jin dabam, domin wacan kwanan da take ai Sadam baya ma garin yanzu kuma yana nan kuma har ya fada masa cewar yana sonta.
Zuciyarsa nata raya masa cewar Sadam zai karya da fuskar Zinneera a gobe, after that Allah kadai yasan iya dadin kalamin da zai fito daga bakinsa ya furta mata, a take ya soma jin kirjinsa na tafasa ji yai ba zai iya jurewa ba, sai yai hanzarin mikewa tsaye ya cire vest din jikinsa ya saka wata blue rigar ya dauki makullin motarsa tare da agogon hannun wanda ke nuna masa shabiyu da rabi, ya san ko zuwa yai ba zai ga Zinneera ba a yanzu ba, amman hankalinsa zaifi kwanciya yai gadinta ko ba komai zai riga Sadam karyawa da kyakkyawar fuskarta da safe. Ba tare da tsoro ko fargabar komai ba ya fito daga gidan ya shiga motarsa ya dauki hanyar loage road. Be dadi a hanya ba ya iso kofar gidan kasancewar dare ya soma rabawa babu ababen hawa garin ma yayi tsif kamar ba kowa. Kusa da gate din gidan ya faka motarsa ta yadda yana iya hango cikin gidan duk kuwa da kasancewar an kashe wutar da zata haske dakunan har na waje ya hango wuta a windows din.

Kwantar da kujearar yai ya jingina yana kallon windows din da be san wacece Zinneera take ciki ba. Murmushi yai yana mamakin yadda ya zama kamar wani wawa akanta, wai yana kishin kar wani ya karya da fuskarta.

“I love you so much Baby”

Ya fada yana jin kamar ace tana kusa da shi, yanzu kam hankalinsa ya kwanta domin ya san yana kusa da sahibarsa, a gurin ya kwana har asuba, sannan yaja motar baya ya fita a masallacin unguwar yai sallah ya sake dawowa cikin motar yana jiran gari yai haske. He just can't wai safiya tai haske sosai around 6:30am ya buga gate din gidan, tun yana bugawar hankali har ya fara bugawa da karfi wanda hakan yasa mai gadin fito dan duba mai buga gate din.

“Malam lafiya?”

“Lafiya kalau, ina son ganin Zinneera ne shiga ciki kace wani yana sallama da ita”

“Tau”

Mai gadin ya juya ya koma ciki, after like seven minutes aka bude gate Sadiq yayi tsammanin Zinneera zai gani ko kuma mai gadin ya dawo ya bashi amsar sakonsa sai yaga Sadam.

“Sadiq kai ne?”

“Ba ni bane kai ne”

Ya fada cike da zafin rai.

“Haba Sadiq miyasa kake abu kamar wani yaro karami?”

“Bana son rigima Sadam Zinneera kawai na zo gani”

“Bachi take a yanzu, jiya bata samu bachi ba, so ba zan iya tashinta yanzu ba gaskiya”

Tsayawa yai kallon Sadam irin da gaske Sadam yake fada masa bata samu bachi ba? So tare suka raya daren kenan? Wata kila suna fira ko tana kuka yana bata hakuri tunda ya san halin Zinneera ba koshi take da kuka ba, no wai wai ba zai tashe ta yanzu ba, so ya same ta a bagas da har shi zai tasheta daga bachi ta kwana a gidansu, so abu ne mai sauki duk Sadam ya fada masa wannan? Wani tunanin be zowa Sadiq ba har sai da Sadam ya shige ciki ya rufo kofar gate din, sannan ya soma tambayar kansa wai Sadam a nan ya kwana ko kuma a'a ai yasan abokinsa ba a gidan yake kwana ba amman tun da Zinneera ta zo dole ya kwana gidan.

Wani irin tafarfasa zuciyar Sadiq take, wani gagarumin yaki duniya na uku ne yake haduwa a zuciyar Sadiq ba, da mugun karfi ya daki motarsa sannan ya bude motar ya shiga ya fisgeta kamar ance masa wani na binsa a baya.

Zinneera tasha bachi sosai yau da safe, domin bata samu yin na dare ba ta kwana tana ta nemawa Sadiq mafita, ta kasa rabe tsakanin fadawa Sadiq an aiko masa da sakon ko kuma ta kyale shi. Sai goma da wani abu ta farka sai tai kwancenta saman gadon abunda ya faru jiya ya dawo mata sabo. Mommy ce ta turo kofar dakin ta shigo da sallama, daker Zinneera ta daga kai ta kalleta sakamakon wani azababben ciwon kai data farka da shi.

“Mommy ina kwana”

Ta fada muryarta a shake.

“Lafiya kalau, tashi ki wanke bakinki ga abincin can yana jiranki”

“Okay”

Sannan ta unkura ta tashi ta shiga bandakin ta wanke bakinta da fuskarta ta fito ta dauki hula da saka a kanta ta nufo downstairs.

“Okay Daddy amman bari tai breakfast sai na kawo ta domin yanzu ta farka, Allah ya bata lafiya”

Kar kalaman da Sadam yake a waya suka sauka a kunnenta, sai tai saurin saukowa ta tsaya gabansa kasancewar ya ba stairs din baya ne, yana yanke wayar ta aika masa da tambaya.

“Waye ba Lafiya Sadam?”

Sai ya kasa ce mata komai sai kallonta yake, natsuwar dake cikin idonsa yake kokarin ya zaunar a nata idanuwan amman ta ko ta bashi hadin kai.

“Waye? Abbah, Umma ko Sadiq Sadiq ...”

Ta juya tana maimaita sunan.

“Umma”

Ya furta sai ta juyo hankali tashe tai tsalle ta dira tana kuka.

“Na shiga uku dan Allah ka kaini yanzu dan Allah”

“Okay okay je ki dauko Hijabinki”

Ya fada mata yana kokarin ganin ta sassauta kukan da take, da gudu ta koma dakin ta dauko hijabin Suraiya ta saka a baibaita ta fito dakin sai ta soma ganin duhu tana jin falon na ta juya mata kamin ta sauko sai kafafuwanta suka zame ya fadi kasa...

“Zinneera...”

Ta karfi Sadam ya kira sunanta ya nufi inda take da sauri, kiran sunanta da yai ne yasa Mommy tai yi saurin fitowa daga kitchen a razane. Taba ta Sadam ya fara yi yaji ko tana da rai sai ta dago kai ta kalleshi ba dan tana ganinsa ba sai dan zuciyarta na raya mata mutum ne a gurin.

“Bana ganin komai, kai ni gurin Umma dan Allah”

“Okay”

Ya fada sannan ya tasheta tsaye ya dauketa zuwa cikin mota, yana sakata cikin motar numfashinta na tsayawa cak.

_______________________

Zabin rai zai rika zuwa muku sau daya ko sau biyu a sati, sakamakon sabon littafin dana fara OUM NAMRA wanda yake na kudi, mai son siya ya min magana ta wannan number 08036126660

Continue Reading

You'll Also Like

Ice Cold By m

General Fiction

2.8M 99.5K 54
COMPLETED [boyxboy] Wren Ridley is always two steps ahead of everyone, or so he thinks. His life seems out of his control when he starts having feeli...
73K 7.5K 55
A life of a strict father who is a soldier raising his 2 kids along with his duties.
84.8K 6K 67
a love story, this is a love triangle between 4 lover's.
323K 25.3K 70
'Mijin yar'uwata nake so, farin cikin da yake baiwa matarsa nake son samu fiye da hakan, so nake na rabashi da matar sa da ya'yan sa ya zamto ba kowa...