MAKAUNIYA CE

By Jiddasmapi

17.9K 991 101

Ta mak'ance ta dalilinshi Amma baisan dahakan ba, ya wulak'anta ta, anci mutuncinta a gidansu.. More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
page 35
page 36
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
Completed✔

Page 4

474 24 0
By Jiddasmapi

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

(An heart touching story)

*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwa ne ga yayata Maryam S Mapi_

  *WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_

    *Page* 4

"Latif ne yafita dagudu kiran likita,
Atare suka shigo cikin ɗakin da Bilal yake kwance  babu alaman motsi atare dashi"

Kiran sauran Ma'aikatan sukayi,
Aka taru aka ɗauke Bilal awajen.

"Anje an birnesu Bilal be sake ganin fuskarsu ba,  yana kwance luff baya hayyacinshi"

"Tin daga wannan rana Bilal yadaina dariya,  yadaina kula mutane idan zaku shekara awaje tare bakayi mishi magana ba,  tofa shi ko kallo baka isheshi ba!

Jinya yake a asibitin bayason cin abinci ya rame yayi haske sosai,  idan anayi mishi magana sai Eh Aa yake iya faɗa.

Baban Latif da Latif ne suke jinyarshi,
Yau kwanansu Uku kenan a asibiti,  doctor ne yashigo yace musu ba wani matsala zasu iya tafiya,
Godiya Baban Latif yayi suka fara tattare kayansu,
Alhaji Umar ne da mamanshi Hajiya Salamatu suka shigo ɗakin,
Cewa sukayi saide Bilal yakoma gidan Alhaji Umar dazama,  da farko Bilyaki yadda saida Baban Latif yasa baki kafin ya yadda.

Bilal yakoma gidan Alhaji Umar dazama,
Amma yana cikin takura,  Afrah ta takurawa rayuwarshi,  gashi Alhaji Umar yanason sashi yin Auren Dole.

Hajiya Salamatu kuwa (mahaifiyar Alhaji Umar)   banda harara da tsaki ba abinda yake shiga tsakaninsu dashi.

"Alhaji Umar yanada yara Uku,  Hafiz, Sabir, sai Autarsu Afrah takwarar hajiya Salamatu,
Hafiz yatsani Bilal,  hasalima bayason ko ganin Bilal ne yayi, 
Tinda Bilal yagane haka saiya fita a harkarshi, 
Yaran haji Umar an sangartasu,  sam sam basusan darajar mutum ba!
Sabir ne kaɗai yafito me hankali,  shine wanda mamanshi tarasu Daddyn Bilal sukaje gaisheshi,
Bilal jiyaje azuciyarshi yayi Babban rashi,  tinda yarasa iyayenshi da kanwarshi"

_cigaban labari_

"Tissue yaciro a aljuhun rigarshi ya goge hawayenshi,
Jiyayi an dafa kafaɗarshi, be ɗago ba sabida yasan Daddyne ko Latif zasu iya zuwa inda yake kai tsaye"

Kayi hakuri Bilal nasan yanda kakejin zafi azuciyarka,  hakika rashin iyaye bakaramin rashi bane,   amma ahalin yanzu ba kuka yakamata kayi ba Addu'a yakamata kayi musu,  kaji?
Cewar Latif

Bilal ne yace "bazan iya ba, wallahi Latif bazan iya ba, iyayena suna matukar sona!  Ina dana sanin rashin binsu gidan rasuwannan danayi.  kuma wallahi ko mata sun kare aduniya bazan taɓa Auren Afrah ba,
Na rantse akan na Auri Afrah gara na nemi 'yar kauye wanda batasan komaiba in Aura,  yarinyan Da idanunta abuɗe yake,  tasan komai na jikin namiji,  bata tsoron jikin maza,  ace in Aureta Kai inaa"

Latif ne yafara lallaɓanshi harya samu Bilal yadaina surutun.
Yace "yanzu dai katashi kashirya akwai meeting dazamuyi yau ana jiranmu a office kuma idan anyi wannan zaman Zai taimaka mana wajen bunƙasa wannan Companyn"

Bilal ne yace "meyasa baka sanar dani dawuri ba?"

Nima bada wuri suka sanar dani ba,  cewar Latif.

Dasauri Bilal yatashi yashiga cikin gida domin shiryawa,
Toilet yanufa sabida yayi wanka.

_Minal_
Ita kuma yau ganin wani faɗa ta tsaya yi a anguwansu har tayi lattin siyan wake,
Sai bayan an gama faɗan kafin ta tafi gida,   sauri take taga ta iso gida.

Tana shiga gida Umma tafara yi mata faɗa "haba Minal aina kikahe siyan waken?  Tin karfe 9 na aikeki sai karfe 11 zaki dawo?  Yanzu kiga kinyi letti har yaushe zaki wanke wake akai markaɗe har ayi alale?"

Minal shiru tayi dan batasan me zatace ba, 
Kuma tasan tayi laifi.

Ba magana nake miki ba?

Minal tace "Umma dama su Ummi ne suke faɗa shine nake rabasu ina musu wa'azi"
Dagajin maganar ansan karya take faɗa.

Minal sau nawa zan faɗa miki ki daina sa kanki a RIKICIN UNGUWA (sunan littafin kanwata,  Walida S Mapi)

Minal shiru tayi tafara wanke waken
Dasauri take aikin sabida ta tafka letti gashi Umma taki tayata,
Surutu takeyi azuciyarta "yazu garin kallon RIKICIN UNGUWA sai in dawo inyi abu letti,  kai gaskiya bazan kara tsayawa kallon faɗa ba,
Tana aiki tana surutu Umma najinta Amma tayi mata shiru.

Dakyar tagama alalen ta girka manja awuta kafin tashirya,
Cikin wani kwano me marfi tasa manjar,
Ɗaukan alalen tayi tace "Umma natafi"

Sai kin dawo cewar Umma.

Bilal wanka yayi da sauri yafito yashafa mai da turare,  ya taje gashin kanshi yashafa mai,
Wani Farin shadda ɗinkin Omo yaɗauko yasa da farin hula farin agogo da farin takalmi.
Keyn motarshi yaɗauka tafita aɗakin da sauri.

Wata farin mota kirar marsandi naga  yashiga,  horn yayiwa megadi aka buɗe mishi get yafita dasauri.

Gudu yake yana Allah Allah ya iso Companyn domin baya taɓa mantawa da maganar Daddynshi akan yakula da dukiyarshi, hakan yasa Bilal baya wasa da harkan Business,
12 cif ya iso Companyn, 
Shiga ciki yayi da motarshi,
Daidai lokacin daya fito yana kulle motar, shine lokacin da Minal tazo wucewa,  juyawan dazeyi kawai yaci karo da mutum.

Ita kuma Minal tsoro da fargaba yasa tayi saurin sakin kwanon manjar hannunta.

"Kwal kakeji kwano yafaɗi kasa manja yazube jikin Bilal"

Tsaya tayi jikinta yana rawa,  manya manyan idanuwanta duk awaje tsabar firgita, ga alalenta ma yazube.

"Mutane kuma sun tsaya sai kallonsu suke kamar sun samu Daɗin kowa lols"

Tin daga sama har kasa Bilal yake kallon kayan jikinshi duk yaɓaci da manja,  bfarin motarshi ma duk manja sun ɗila ajiki.

"Bilal tinani yafara me zaiyiwa yarinyan nan?"

Tafiya yafarayi yana isota,  ita kuwa sai baya baya takeyi a razane.

Latif ne yafito daga office yaga yanda jikin Bilal yaɓaci da manja ga Minal tsaye a ruɗe yace "yau ake yinta"

Isowa wajen dasuke yayi yace
"Ranka shidaɗe An tanadar maka da wajen zama me ɗauke da farin kuhera you are wellcome"
Yakwashe da dariya yabar wajen,
Abun yasa mutane dariya kowa sai kyalkyalawa yake kamar ba gobe,
Takaici, baƙin ciki,  haushi, su suka taru sukayiwa Bilal yawa awannan lokacin.

Minal ce tajuya ta ɗaga skirt nata wanda duk ya ɓaci dazaren da akayita ɗinkawa ta faki idon Bilal ta kwasa da gudu tabar cikin companyn.

Bilal ne yacewa megadi "kai? Karka barta tafita"
Ai Minal tayi gaba sai labari.

Haka Bilal yadaure yashiga motar yabar Companyn rai aɓace,
Ita kuwa Minal gudu tarinka tikawa har gida.

Dagudu tashiga gida tana nishi,
Umma ce ta tashi afirgice tace "Minal 'yata meya sameki?"
Minal tafara kame kame,  daga baya tace Umma cikina ne ya ruɗe.
Toiket tanufa dasauri,  Umma tana kallonta.

Shikuma Bilal kuka ne kawai beyi ba,  jiyayi ya kara tsanar Minal,  yau daza'a bashi bindiga ace ya harbe mutum ɗaya babu shakka Minal ze fara harbewa,  yatsaneta!
Yatsaneta!
Yatsaneta!

Gudu yake akan titi motarshi duk ya lalace da manja.
Ahaka harya iso gida yakira megadi yace awanke mishi motar.

Shiga cikin gida yayi dasauri,  Hajiya Babbace afalo tana kallo,
Bilal yazo wucewa taganshi jiki duk manja ga fararen kaya,  dariya takwashe dashi tana tafa hannu,
Wani kallo Bilal yabita dashi idanunshi duk yayi jaa,
Wucewa yayi cikin ɗakinahi yacire kayan jikinshi yace "na rantse ke zaki wanke kayannan".

_Washe gari_

"Daddy ne yashiga ɗakin Bilal yace "yau bazakaje office ba zan aikeka, 
Bilal yace to,
Daddy yace bani makullin office ɗin?
Bilal ne yatashi yabashi makullin.

Yau Bilal beje office ba Daddy ne yaje amaikonshi,
Zama Daddy yayi akan kujera yace akira mishi Alhaji Nura.

Alhaji Nura shinee kula da companyn idan Bilal baya nan,
Shi baƙi ne yanada jiki,
Bilal ya yadda da Alhj Nura sosai.

Shiga office ɗin Alhj Nura yayi, 
Daddy ne yace mishi "have a sit"

Zama yayi a kujeran dake fuskantar Daddy,
Tashi Daddy yayi yaɗau makulli yakulle office ɗin,
Mamaki ne yakama Alhj Nura.

Daddy ne yayi gyaran murya yace "Am Alhj Nura nasan zakayi mamakin kiranka danayi,  kuma na kulle kofa,
Wata muhimmiyar magana nakeso muyi dakai, 
Wanda banason kowa yaji dagani sai kai"

Alhj Nura yace wani magana me wannan?

Daddy ne yayi gyaran murya yace "Alhj Nura? Shin kanason kazamo me arziki sosai yanda kowa zai sanka aduk faɗin garin Gombe?"

Meze hana?  Cewar Alhj Nura

To wani aiki nakeso muyi amma kasani idan har aiki yayi kyau zan baka kashi talatin nacikin dukiyana,
Idan kuma aiki beyi kyau ba, tofa babu hannuna aciki.

Shiru Alhj Nura yayi yana tunani,  sannan yace "babu komai insha Allah Aiki zeyi kyau"

Daddy ne yatashi yana zagaye office ɗin yace "Alhj Nura aiki akan Bilal nakeson ayimin"

Bilal yanada taurin kai,
Babu yanda banyi ba akan yanunamin dukiyar Mahaifinshi Amma sam yaki,
Hakan be dameni ba nace ya Auri Afrah sabida nasan idan harya Aureta to dukiyar namu ne,
Hakan ma yaki yadda"
Yanzu inason ayi mishi abunda zesa yanunamin dukiyarshi dakanshi basai na tambaya ba.

Alhj Nura yace me za'a mishi?

Daddy ne yace "Makantar dashi za'ayi"

Alhj Nura yace tayaya?

"Ta hanyar watsa mishi ACID inji Daddy"
Mutane Biyu zaka nema,  zan faɗa maka inda yake zama bayan mangariba,  inason awatsa mishi a idonshi kawai shikenan.
Ammafa kasani idan har aka kamasu kada sunana yafito abakinsu.
Domin wanke hannuna zanyi cau incire bakina.

In Allah ya yadda babu wanda ze kamamu cewar Alhj Nura.

Wasu kuɗaɗe Daddy yaciro yabawa Alhj Nura yace "ga wannan karike awajenka nasan zasuyi maka anfani"

Karɓa Alhj Nura yayi jiki narawa yace an gode Alhaji.

Jibi nakeson ayi aikin,  a garden nacikin gidana za'a sameshi bayan mangariba, 
Akula sosai sanman banason kowa yasan muna tare dakai,  karka nunawa mutane kasanni sosai kaji?

To Alhaji,
Akula sosai.

Fita yayi daga office ɗin,  dasauri Minal tamatsa abakin Kofar jikinta duk yana rawa,
Ɓuya tayi abayan wani karfe,
Tsayawa Alhj Nura yayi yana juye juye jin kamar mutum abayanshi.

Jikin Minal ne yafara rawa atake cikinta ya ɗibi ruwa,
Addu'a take Allah yasa Alhj Nura be ganta ba,
Dan idan yaganta tasan kasheta zasuyi.

Juyawa yayi yafita a companyn dasauri,
Daka ganshi kasan bashida gaskiya.

"Minal ganin yatafi yasa tafito abayan karfen dasauri,  har yanzu jikinta be dena rawa ba,
Sauri take afirgice jikinta yana rawa"

Hanyar gida takama tana addu'a tana sauri,
Nida nazo bada hakuri sai kuma inji abunda yafi karfin kunnena?
Nashiga Uku Allah yasa mafarki nake,
Acid a ido kai.

Afirgice tashiga gida,  Umma naganinta tafara tambayanta "'yata meya faru?"

Shiru Minal tayi tana kallon Ua jikinta duk yana rawa,
Hannunta Umma takama suka shiga ɗaki,  Kwanciya Minal tayi akan gado har yanzu jikinta be dena rawa ba.

Umma ce tafara tofa mata Addu'a harta samu tafara bacci.

Hawayene yafara fita a idon Umma tana me tausayawa 'yarta.

_✅ote comment and share_

✍🏻  *Jiddah S Mapi*

Continue Reading

You'll Also Like

3M 193K 89
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...
313K 25.3K 15
MY Creditor Side Story ပါ။ Parallel Universe သဘောမျိုးပြန်ပြီး Creation လုပ်ထားတာမို့ main story နဲ့ မသက်ဆိုင်ပဲ အရင် character ကို ရသအသစ် တစ်မျိုးနဲ...
617K 64.3K 25
في وسط دهليز معتم يولد شخصًا قاتم قوي جبارً بارد يوجد بداخل قلبهُ شرارةًُ مُنيرة هل ستصبح الشرارة نارًا تحرق الجميع أم ستبرد وتنطفئ ماذا لو تلون الأ...
3.1M 254K 96
RANKED #1 CUTE #1 COMEDY-ROMANCE #2 YOUNG ADULT #2 BOLLYWOOD #2 LOVE AT FIRST SIGHT #3 PASSION #7 COMEDY-DRAMA #9 LOVE P.S - Do let me know if you...