ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

113K 15.7K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

HAJIYA KARIMA

1.9K 263 16
By KhadeejaCandy

BAYAN KWANA BIYU.

         Umma tai farinciki sosai lokacin da Daddy yai ma dansa tayin Aleeya, tasan yayi hakan ne ba dan komai ba, sai dan karfafa zumuncinsu. Ko ba komai ta san yarta zata jidadi sosai aure gidan naira kuma inda ake ganin kimarka ake girmamaka. Sai dai hakan be sata ta hanke hukunci ba har sai da tai ma Aleeya maganar kuma ta fadawa Abbah.
  Abbah kusan yafi kowa farinciki domin Abbah na cikin irin mutanen da keson aurar da yarinya da zarar ta fara girma musamman Aleeya dake da jiki sosai lokacuta da dama idan suka fita tare da Zinneera ana daukar cewar ita yayar Zinneera saboda yanayin jikin Zinneera.

Unexpected maganar auren ta zo ma Aleeya.

“Ni ni Umma? Ko dai Zinneera?”

Shine abunda take ta tambaya, lokacin da Umma ta labarta mata cewar Sadam ya ganta kuma ya aiko yana sonta.

“Ke ba mutum ba ce da zai yana son ki?”

“Umma kawai ina mamaki ne, kin san irin yaran masu kudi basu cika son chubby girls ba, musamman idan ace mutum ya zauna kasar waje”

“Ai ba duka aka taru aka zama daya ba, anjima zai zo ku gaisa dan haka sai ki shirya”

Ta yi saurin rufe fuskarta cike da kunya da kuma farinciki da bata taba jin irinsa ba, ba zata ce son Sadam take a take ba, amman ta jindadin wannan albishir din da Umma tai mata.

“Idan kin ganshi kina son shi kun daidaita kanku sai iyaye su shigo ciki, n Ji Abbanki ma yana zancen hade ki da Zinneera”

Tashi tai cikin dariya da kunya ta bar dakin. Umma ta bita da kallo tana murmushi kamin da maida dubanta gurin Zinneera wacce ke zaune a dakin amman har suka ci maganar suk sude bata saka baki ba domin hankalinta baya jikinta kwata kwata.

“Zinneera...”

Sai da Umma tai mata kira hudu a na biyar ta amsa da sauri da alama sai yanzu ne hankalinta ya dawo jikinta.

“Na'am Umma magana kike?”

“Zinneera me ke damunki?”

Ta sanda kanta kasa tana wasa da hannunta idonta cike da kwalla.

“Maganar da Abbah ku yai ne?”

Nan ma shiru tai.

“Zinneera iya hakurin daya kamata ayi Abbah ku yayi akan Sadiq, domin ba kowa ne zai so ana magana ana dagawa ba, wannan shi ne karo na hudu da Sadiq ke ta daga auren ba tare da wani uzuri ba, ban san uzurinsa ba, amman ina tunanin indai har da gaske yake ya kamata ya unkuro ya kawo jiki ko da ayi auren a yanzu ba, san an biya sadakinki ko kuma ma an saka muku rana nan da wani lokaci, Zinneera wannan karon uzurin Mahaifinki zan karba, idan mu ne yau gobe ba mu ba ne, kuma duk uba na gari yana son yaga yarsa ta kama dakin mijinta, musamman mahaifinki da ba karatu yake so mai zurfi ba, amman ya yarda ki cigaba da karatu ya kamata ke ma ki faranta masa rai ta hanyar auren nan”

Ta dago tana kallon Umma hawaye shar a idonta.

“Sadiq ya fada min Abbah yace masa daga wannan ba zai sake daga masa kafa ba, amman Umma baku yi tunanin shi ma Sadiq din yana da wani uzuri na dabam ba? Kuma duka yaushe Sadiq ya fara neman aure da har za'a ce an dade ba yi ba”

“Amman ke Zinneera baki taba tambayar kanki miyasa Sadiq yake ta daga auren ba? Yana da gidan zama har mota yake da ita kuma yana aiki amman kullum sai ya rika cewa be shirya ba, sai yaushe zai shirya ne? Amman ya kamata ace ko sadakinki ne ya biya yadda hankalin mahaifinku zai dan kwanta”

Hannu tasa ta share hawayenta.

“Ina da damar nai masa wannan maganar? Idan nai masa maganar ba zaki ce na yi rashin hankali ba?”

Umma tayi murmushi.

“Ba zance ba Zinneera hakan ma zai nuna min cewar kin yi hankali har kin fara sanin ciwon kanki da yi magana mai muhimmanci akan aurenki”

“Zan yi magana da shi anjima idan ya zo”

“Hakan yayi kyau Allah yai miki albarka, ni kuma zan daɗa magana da mahaifinki, ki kwantar da hankalinki”

Ta gyada kai tana sauke numfashi a hankali. Ido Umma ta kura mata tana mata irin kallon nan na tausayi da kauna dake tsakanin uws da diya, Zinneera ta natsu sosai fiye da tunaninta sai kwana biyun nan ta saka kanta cikin damuwa sosai tun daga ranar da Abbah ya tuntubi Sadiq da zancen auren da yace sai a watan mauludi, gashi watan ya kare har wani ya shigo babu wani labari. A bangare daya kuma tana tunanin halin da ita da Zinneera zadu samu kansu idan har abunda aka shekara ashirin da biyu ana boyewa.

   Misalin takwas Aleeya tai wanka ta kure adaka domin Abbah ya ce takwas da rabi Sadam zai zo su gaisa da Aleeya. Wannan karon Zinneera sai tsokanarta take.

“Aleeya ba ko kunya har da yin kwalliya”

Aleeya ta sakar mata harara.

“Oh ke da kike kwaliya idan Sadiq zai zo da ba'a ce miki komai ba sai ni?”

“Ai ni daman can ya sanni kamin nai kwalliya”

“Ni kuma aka ce miki ba san ni ba? Shi da kansa yace yana sona ai”

Zinneera tasa dariya.

“Lallai Aleeya baki da kunya”

“Ke wallahi yanzu an daina kunya, balle irin Sadam mai kyau”

Wannan karon sosai Zinneera take dariya.

“Shegiya, daman can kin ga abunda ke miki kenan”

“Haba dai Zinneera ai yana da kyau gaskiya”

Shigowar Umma ne yasa Zinneera hade maganar da zatai.

“Tashi kije Sadiq na kiranki”

“Ina kika ganshi?”

“Yaro ya aiko, Aleeya kwaliyar ce ake”

Umma ta karasa tana kallon Aleeya da murmushi, sai Aleeya ta rufe fuskarta Zinneera ta tashi tana dariya ta dauki hijabinta ta saka sannan ta dauki turaren Aleeya ta fesa, da sauri Aleeya ta fisge turarenta.

“Eh lallai sannu sai ki boye naki ki feshe nawa, ai kama baki da nasiha”

Gwalo Zinneera tai mata.

“Na ji dai amaryar Sadam ba kunya ba nasiha”

“Eh din”

Ta murguda mata baki. Da far'ar ta fito daga gida, kamar yadda far'arta ta dada karuwa lokacin da idonta sukai arba da masoyinta, yayi kyau matuka yana sanye cikin wata farar shadda sai kamshin turare yake kamar ango. Kallonta yake da murmushi har ta karaso ta jingina jikin motarsa tana kallonsa.

“You look very calm and quiet, kwanan biyu kin zama yadda na ke sonki”

“Baka tunanin akwai abunda ta kamata ya dame ni ne Sadiq?”

“Kamar na me? Na san dai baki cik tunani ba, irin tunanin wani abun ya dame ki ba, ko dai Umma ce tace kin yi wani abu ba daidai ba?”

Ya fada yana murmushi kamin ya mika mata ledar dake hannunsa.

“Ga yogurt na siyo miki na san kina so”

“Na gode”

Ta fada bayan ta karba.

“Sadiq miyasa kake aikin gwanati bayan kace min aikin banki da kai applying ya fito daga baya”

“Ban samu yi ba, saboda aikin ya fita daga raina daga baya, domin shi aikin bude banki baka da lokacin kanka sai na su, Shiyasa na jira har wannan ya fito ya fara duk kuwa da kasancewar wacan ya fi albashi mai tsoka”

“Amman da aikin kake da yanzu sai su ara maka kudi ka...”

Sai ta kasa karasawa.

“Na biya ko? Nima na yi tunanin yin rance amman sai banki ba zasu bani har miliyan ashiri ba, amman komai da sannu sannu yake zuwa karki damu Zinneera zan samu na biya in sha Allah”

“Amman zuwa yaushe zaka biya?”

Ya kalleta irin kallon nan na mamaki.

“Ban sani ba, mai yiyuwa nan da shekara biyar ko uku ko sama da haka?”

“Kuma kana tunanin iyayena zasu jira har lokacin?”

“Zasu jira mana tunda muna son junanmu, Zinneera you're just 17 going to 18 years fa, a lokacin ba zaki wuce ashirin da uku ba ko da hudu”

“Idan kuma ya bullo maka da wani abun kamin ka biya fa? Wata kila ma zai iya tunanin ba zaka ce iya ba, idan kuma baka samu damar biya ba har lokacin ya zo fa? Sadiq na damu da maganar Abbah ne, yace fa ba zai sake daga maka kafa ba”

“Naji, yanzu ai idan iyayena zasu sake cewa zasu saka lokaci mai tsawo ne, wanda zai wadace mu, ban san miyasa Abbah ya damu yai miki aure da wuri ba, ba wani girma kikai ba Zinneera balle har ace ya damu sosai akan rashin aurenki”

“Ta ina zaka samu kudin ka biya?”

“Ban sani ba, amman dole nai tunanin mafita”

“Idan kuma mafitar bata samu ba fa?”

“Zinneera”

Ya fada yana kallonta da mamaki, sai ta hade yawun bakinta hawayen dake makalle a idonta suka zubo mata. Hannu ya kai ya rika hannunta.

“Babe zamu samu samu mafita, zamu yi aure cikin kwanciyar hankali da natsuwa komai zai wuce kamar ba mu yi ba”

“Amman Sadiq ya kamata ko sadakina ne ka biya ta yadda hankalin mahaifina zai kwanta ya yarda da kai”

“Zinneera ina tsoron kar na biya sadakinki ne wani abun ya same ki, zan iya jure komai ya same ni, amman ke ba zan iya jurewa ba, ba zan iya yafewa kaina ba ina son ki sosai Zinneera, karki saka damuwa a ranki zamu samu mafita”

Haskesu da akai da mota ne yasa yai saurin sakin hannunta.

“Share hawayenki”

Ba musu ta share hawayen. Idon Sadiq na kan motar da aka faka nesa da gidansu Zinneera wacce ke facing dinsu har sai da ya gano mai motar.

“Sadam ne wacan”

Zinneera ta waiga ta kalli gurin da motar take.

“Ina jin shi”

“Gurinki ya zo ko?”

“Aa...”

“Gurinki ya zo, na sani ai”

“Ba gurina ya zo ba, gurin Aleeya ya zo”

“No gurinki ya zo Zinneera, ke yake so ai ya fada min?”

“Sadam din?”

“Yes tun kamin mu hadu nan da shi ya fada min ke yake so”

“No you're wrong”

“No you're wrong gurinki ya zo Zinneera”

“Gurin Aleeya ya zo da ita akai mass maganar aure, shi ya ganta da kansa yace yana son ta”

“Aleeya?”

“Eh, har daddy yayi magana da Abbah ma akan maganar”

“Okay”

Ya fada ba dan ya gamsu ba. Kamar jira ake ya rufe bakinsa sai ga Aleeya ta fito daga gidan ta nufi inda Sadam yake.

SADAM POV.

Bude motar yai ya fito yana kallonta. A first abun dariya ya so ya bashi, sai kuna ya cinci kansa da bacin rai. Be san me zai ce mata ba, so bayan gaisuwa sai shiru ya biyo baya daga ita har shi babu wanda ya sake cewa wani abu. Ita kam dai ta kasa daga kai ta kalleshi shi kuma hankalinsa da idonsa suna kan Zinneera da Sadiq, be san miyasa yaji ransa ya bace sosai da ganin Sadiq tsaye tare da ita ba.

“Abbah yace na zo mu gaisa, bana ma jindadi na zo ne kawai dan kar na saba alkawari”

“Allah sarki me ke damunka?”

“Ciwon kai ne, bari na tafi na samu na kwanta”

Ya bude motar ya dauko manyan ledodi ya mika mata.

“Ga wannan ki shiga da shi gida, ins gaida Umma”

“Zata ji, na gode”

Kai kawai ya gyada mata ya shiga motar ita kuma ta wuce cikin gidan. Sai da ya haskesu da Hasken mota sannan ya yai mata key ya juya ya koma ta inda ya fito.

Sun dade suna fira sai da ya tabbatar duk wani bacin rai da damuwa da ke cikin ranta ya kau sannan ya duba agogo hannunsa.

“Tara da rabi tai fa, ya kamata na tafi kar Abbah ya dawo ya tarar da ni a nan”

“To meye idan ya tarar da kai? Ai yasan kai ne

“Yes nine amman be kamata ace kullum muna fira har lokacin da yake dawowa ba, muje n raka ki gida”

“No kai zaka fara tafiya”

“Na fi son sai na saka ki cikin gida na tabbatar babu abunda ya same ki”

Murmushi tai.

“I love you Sadiq”

“I love you more”

A tare suka jero ya rako Zinneera har kofar gidan sannan ya jingina da kofar yana kallonta.

“Good night?”

“Goodnight, ice cream dina yayi sanyin”

Ta fada tana matsawo da fuskarta murya can kasa kasa kamar mai rada.

“Yes Baby daman bana son ki sha shi da sanyi, ki yi addu'a kamin ki kwanta okay i love you”

Ya fada shima kamar mai rada. Sai da shiga gidan ta turo kofa sannan ya juyo ya nufo gurin motarsa, ya kai hannu ya bude yaji am masa sallama.

“Assalamu Alaikum”

“Wa'alaikussalam”

Ya amsa yana mata kallon rashin sani.

“Nasan baka sanni ba, amman ina son ka taimaka ka bani aron lokacinka ina son magana da kai”

“Wacece ke?”

“Sunana Hajiya Karima”

‘Hajiya Karima’

Ya maimata sunan a ransa.

“Ina son nai wata magana da kai mai muhimmanci”

“Kamar ta me?”

“Ba zan iya yinta a nan ba, amman zan iya baka number wayata sai ka fada min inda zan same ka mu yi maganar ko kuma na fada maka inda zaka same ni”

Magana take ido raurau kamar mai shirin yin kuka. Kallonta ya tsaya yi bata masa kama da masu bukatar taimako ba, kana ganinta kaga babbar Hajiya.

“No ba zan yi ba”

Ya bude motar yana kokarin ta ce

“Dan girman Allah ka taimaka min”

“Ba zan iya ba gaskiya, taimako yana da wahala yanzu, after all miyasa sai ni za ki yi magana da ni?”

“Na hada ka da Allah ka saurareni”

“Ba zan yi”

“Ko da maganar ta shafi Zinneera?”

Da sauri ya kalleta.

“Me kike so?”

“Magana kawai nake son yi da kai”

“Fada min ko minene yanzu”

“B zai yi yanzu ba sai dai gobe idan ka bani dama?”

“A ina zan same ki?”

“A wannan addireshin”

Ta mika masa yar karamar takardar dake hannunta. Hannu ya kai karba.

“Na gode”

Ta Fada sannan ta nufi gurin motarta, sai yanzu Sadiq ya lura da inda ta faka ta. Sai da ta shiga motar ta bar gurin sannan Sadiq ya shiga tashi motar yana kallon takardar mai dauke da sunan unguwa da  number gida da kuma number waya.

“Hajiya Karima...”

Ya fada cike da mamaki.

Continue Reading

You'll Also Like

3.9K 316 22
Mutane kala uku ne a duniya. Na farko masu rauni Na biyu masu karfi Na uku masu bada umarni A ko ina ma duniya suna raye. Suna kasuwancin su ne akan...
28.9K 2.8K 36
her life is ending becouse of her biogical brother,he rapping her the frist tym that he see her in his life
8K 415 10
Authentic Dua's from the Qur'an and sunnah for all occasions to be implement on our daily routine.
32.8K 4.4K 54
"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a...