ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

116K 15.9K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

Life Is So Confusing

2.2K 324 31
By KhadeejaCandy

Tafiya take kalaman Sadiq na kai kawo akwakwalwarta, kokarin banbance ganganci da kuma son zuciyarsa take, da gaske yau tunani take irin na mutane. Daga unguwar lodge road zuwa Abdullahi Fodio Road tafiya ce mai nisa, amman cikin kankannen lokaci ta iso kamar wace tai tafiya cikin iska. Ita kanta ba san ta iso ba sai da ta tsinci kanta a kofar gidan. Wata farar takarda ta fara arba da ita aje a zauren gidan. Bata yi tsammanin ita aka ajewa dan ta karanta ba, kamar yadda zuciyarta ke raya mata ba iska ya dauko ta ya kawo ba, domin takardar fara ce kal babu alamar datti ko tamukewa a tare da ita. 
  Risinawa tai ta dauka, sai ta fara arba da sunanta a saman takardar kamin wani dogon sharhi ya biyo baya, a zuci ta karance kalaman ta haddace su akanta tas, sannan ta doshi cikin gidan tana share hawaye. Bata samu kowa a tsakar gidan ba, hakan kuma ba karamin dadi yai mata ba. Kai tsaye ta wuce dakinsu ta zaune a gurin da take ganin zai isheta tai kukan da babu mai jinta, yau kuka take ba na shagwaba ko fada da wani ba, kuka take na damuwa irin damuwar da bata taba jin yanayinta, bata iya tantance komai a yanzu, da gaske son Sadiq take ko tsanarsa? Ranta yana sosuwa a kowane harafi na labarinsa, ina ma be zayyana mata komai ba.

  Kanta ne ya fara rawa dama na haka yake mata a duk lokacin da take kuka. Kana jin yanayin kukan kasan bana mutane ba ne, ta ba yi ta ci abunta har ta tsude Umma bata ce mata Uffan ba, amman yau sai ga Umma da gudu cikin dakinta ta rikata.

“Zinneera lafiya”

Idonta ne ya fara rikidewa kamin tabar jikin Umma ta soma shureshure abunda bata taba ba.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”

Ita kadaice kalmar dake fito daga bakin Umma, domin ita kanta yau ta san Zinneera ba ita kadai take ba. Tashi tai zuwa kiran mutane, domin Abbah tun fitarsa yai gaba da bacin ransa. Makota ta shiga tana kukan a taimaka mata domin babu kowa a cikin gidan sai ita kadai. Ka kace kwabo gidan ya cika da mutane mata, duk wanda ya san Zinneera a ranar sai da ya tausaya mata domin ta fita hayyacinta wasu abubuwa take da duk wanda ke kallonta ya san ba yin kanta ba ne. A take aka je har Islamiyarsu aka nemo mai makaratu har mutum biyu suka suka yi alwala su ka soma yi mata ruqya. An kusan magariba ana abu daya sannan su soma bada hakuri suna fadin za su tafi.

“Su waye ku?”

Daya daga cikin malaman dake mata karatun ya tambaya. Sai suka yi shiru ba su ce komai ba, a nan ya cigaba da yi mata karatu sai ta fara kugi cikin wata kalar murya, tana fadin.

“Zamu tafi?”

“Miyasa kuka shiga jikinta?”

“Son ta muke, tun tana da wata hudu a duniya”

“Me tai muku kuka shiga jikinta?”

“Batai mana komai ba, a bakin kofa Karima ta ajeta mu kuma muka shafeta, da ta girma sai muka shiga jikinta, duk wani abu da take mu ne mune muke saka ta”

“Ku fita da izinin Allah, ko na kona ku”

“Zamu tafi, amman za mu dawo”

Shine abunda suke ta fada jikinta nata karkarwa, bakinta har kumfa yake fitarwa. Ta samu minti talati tana haka sannan ta soma bachi kamar ta suma. After like five minutes ta farka a firgice tana kallon mutane dake zagaye da ita, Umma kam aikin kuka kawai take.

“Lafiya miya faru?”

Ta tambaya tana kokarin tashi tsaye, iyakar abunda ta sani, kuka take na abunda ya faru tsakaninta da Sadiq  bayan shi bata sake sanin abunda ya biyo baya ba sai ganinta a tsakar gida kowa yana kallonta,ga malaman makarantarsu har biyu rikeda kur'ane. Umma taje ta rikata da sauri.

“Ba komai zo ki yi sallah ki kwanta”

Sannan ta kalli malaman.

“Idan Malam ya dawo za a aiko da abun sadaka, an gode sosai”

“Ba komai, ta dai cigaba da azkar da sallah akan lokaci da karatun kur'ane”

Daya daga cikinsu ya fada. Allah ya bata lafiya shine abunda kowa ke fada, dama can wasu sun dade suna zargin abunda Zinneera take ba yin kanta ba ne, yayinda wasu kuma yanzu ne suka san dalilin kiriniyar nata.
  Har aka yi abunda akai aka shude Abbah be dawo ba, hakan kuma ba karamin tada hankalin Umma yai ba, ta san duk damuwar da zata shiga akan Hajiya Karima Abbah zai fita shigarta. Ga Nabeel ma tun fitar safe har yanzu be dawo ba, ba aikin office yake ba balle tace shine ya kai shi har dare, aikin Sadiq na karantarwa ne a makarantar primary. Ga shi ba waya hannunta balle ta kira ta tambayi lafiyarsa. Ita kadai ta san tashin hankalin da take ciki yau, a tsakankanin ganin Hajiya Karima da kuma fadawa Mijinta Labarinta da na rashin ganin danta bata san wane yafi damunta ba. Har kusan goman dare bata saka komai a bakinta ba kamar yadda bata ci abincin rana ba bayan karin da tai da safe... Sai can guraren sha daya na dare taji an turo kofar gidan an shigo, cike da kuzari ta unkura ta fito tsakar gida, ganin Abbah da Nabeel a tare suna dariya yasa taji dan sanyi a ranta amman hakan be hana ta rufe Nabeel da fada ba.

“Ina kaje tun safe baka dawo ba, ban sha fada maka cewar ka daina dade a waje ba”

“Yi hakuri Umma, Wallahi Abbah ne ya dauke ni muka je Gasau kai wani sako”

“Amman ai sai a kirani a fada min, ko bana da darajar da za'a kirani a fada min dana ya yi tafiya ne?”

Wannan karon Abbah take kallo domin ta fahimci shine mai laifin.

“Ka gani ko daman na ce kina can kika fadan nan na ki, ga danki ban cinye shi ba”

Nabeel yai dariya. Ita kuma ta juya ta koma cikin daki cikin da fusatar da bata san dalilinta ba. Abbah ya rufa mata baya rike da leda a hannu daman ya saba daman baya taba shigowa gida hakan nan ba tare da wani abunba.

“Sannu da zuwa”

Ta fada ba dan ta sauka daga fushin ba.

“Yauwa, ina yara duk sun yi bachi?”

“Eh”

Tashi tai ta dauko masa abincinsa da ruwa ta dire masa a gabansa. Sai da ya ci ya koshi sannan ta koro masa da bayanin abunda ya faru dazu da Zinneera. Shiru Abbah yai yana tuna wani lokaci can baya lokacin daya taba shigowa cikin gidan ya samu Zinneera a bakin kofa kwance sai fisge fisge take tana kuka sosai.

“Karima ta gasa min gida a hannu, ta azabbatar da ni da azabar da tafi ko wacce zafi”

Idonsa ne yake cika da kwalla yayinda da bakinsa yake furta wadannan k alaman.  Umma ta matso kusa da shi tana magana ahankali da yadda babu wanda zai ji.

“Tun da har kaga ta dawo akwai abunda ya dawo da ita, bana son cigaba da aje wannan sirrin mu kadai, ya kamata ace yaran sun san gaskiya kar gaba su cutu”

“Babu wani uzuri da zan karba daga gareta, kamar yadda babu wani uzuri da zan karba daga gareki, bana son wata magana daga yau”

Kawar da fuskarta tai tana sauke ajiyar  zuciya, Abbah mutum ne mai wuyar sha'ani wani lokacin duk yadda take son fahimtar da shi wani ba zai fahimta ba.

Batai mamakin kin daukarta da bachi yai ba duk kuwa da kasancewar tana jin gajiya da ciwon kai mai nauyi. Labarin Sadiq yana taba ko'ina na jini da tsokarta, tausayinsa take, saboda yana bukatar rayuwa ko dan saboda mahaifiyarsa da kuma kanensa, sai dai ita ina nata makomar yake idan har ta tsaya jiran lokacin da zai bada kudin? Ita zata iya jira amman iyayenta fa?zuwa shekara nawa zai biya kudi? Idan kuma ta kasa jira me zai biyo baya? Wata kila jiran ko rashin jira ya haifar masa da wata matsalar.  Akaddara ta jira din, ta ina zai samu har naira miliyan ashiri?

Haka ta raya dare tana yi ma kanta tambayoyin da bata san da ina suke zuwa mata ba, ba laifi a yau kam tana jin ta a mutum mutum mai tunani da damuwa, sai yanzu take jin akwai abunda ta rasa a baya wanda ya hanata cika cikakkiyar mutum, domin a baya bata san damuwa ba, balle har tai tunani sai gashi s yau ta shiga duniyar da bata san da wanzuwarta ba, har tana kokarin neman mafita. Wata kila dan yana Sadiq ne love of her life. Ko kadan bata kawo ma kanta tambayar dalilin taruwar jama'a akanta ba kuma a cikin gidansu, shafin Sadiq ya shafe ko wane shafi yau a rayuwarta.
  Kiran sallah ta taji ne ya hankaltar da ita cewar garin Allah ya waye, ashe dai zata iya wayar gari ba tare da bachi ya shiga idonta ba. Unkura tai ta tashi sai taji kan yayi mata mugun nauyi sai dai tana jin kan kamar babu komai a ciki. Katifar Aleeya ta kalla da Aliyu da Larai sukan bachinsu suke hankali kwance, tana jin lokacin da aka bude da alama Nabeel ne ko Abbah ya fita sallah asuba, daman sai sun dawo suke tashinsu. Labulen dakin ta yaye ta fito jiki ba kwari ta doshi inda buta take ta dauka ta shiga bandaki. Bayan ta fito tai alwala tai sallah asuba sannan ta dauki carbi ta rike. Abbah ya riga dawowa kai tsaye ya nufo dakinsu ya tashi Aleeya da Aliyu da Larai ganin Zinneera saman sallaya ya tabbatar masa da cewar tayi sallah.

  “Abbah ina kwana?”

“Lafiya kalau”

Ya fada yana haskata da fitila kasancewar babu wuta. Maida kanta tai kasa. Har ya juya ya fita sai ga Nabeel ya shigo yana mika mata wayar hannunsa.

“Ga Sadiq yana son magana da ke”

Tsayawa tai kallo wayar kamar ba zata karba, sai kuma ta kai hannu ta karba ta kara a kunne. Nabeel ya juya ya fice.

“Zinneera...”

Daga can cikin wayar yai mata kira, ita kuma ta gagara amsawa.

“Zinneera...”

Har yanzu bace komai ba.

“Kawai ina son na ji muryarki ne, ki ce wani abu mana, na kasa bachi jiya ina ta tunaninki, ina tsoron na rasa ki Zinneera, ina tsoron kar nai miki karya ki cutu, gashi kums gaskiyar ta cutar da ke”

Nan ma bata ce komai ba, hawaye kawai suke mata zuba.

“Ina son ki sosai Zinneera, bana son na rasa ki, na san akwai zafi mutum ya boye maka gaskiya tun daga farko, kuma akwai zafi ka fada soyayya da mutumen da be dace da kai ba”

“Ina sonka Sadiq, komai ka aikata ina sonka”

Shine kawai abunda ta fada ta kashe wayar. Lumshe ido yai ya sauke ajiyar zuciya, ji yai ko ina jikinsa ya saki tsabanin dazun da yake jinsa a rike. Hannunsa yake murzawa yana jin hannun na masa zafi kamar garwashi tana jin haka a duk lokacin da ya tuna ya harbi abokinsa.

“Zan tara kudin zan biya, ko dan nai rayuwa cikin kwanciyar hankali”

Ya fada yana bude idonsa.

“Amman hakkin kisan Isma'il yana kan wa?”

Wasu yawu da karfi kamin ya mike tsaye ya nufi windows dakin.

SADAM POV.

Yana fita gidansa da sauri family House ya koma saboda kiran gaggawa da Daddy yai masa. A tunaninsa maganar kamfani ce, amman a yadda ya tararda da Mommy yasa jin wani iri domin babu walwala a fuskarta ko kadan. Guri ya samu kusa da ita ya zauna a kasa yana kallon Daddy wanda ke kallonsa fuska da murmushi.

“Sadam! Ina son na tambaye ka ne ko kana da wacce kake so ko kake nema?”

Gabansa ya fadi amaimakon ya amsawa Daddy tambayarsa sai ya samu kansa yana yima kansa wata tambayar.

‘Mi yasa ya tambayeni?’

“Aa Daddy babu”

“Alhamdulillah to na maka mata”

“Mata...”

Ya maimaita yana kallon Mommy cikin yanayi na rashin fahimta.

“Eh wata yarinya na nan yar wajen gwaggonka Safiya, sunanta Aleeya”

A dinmauce ya kalli Daddy.

“Aleeya? Amman Daddy miyasa?”

“Saboda na yaba da tarbiyarta, kuma hakan zai kara karfafa zumuncin da ke tsakaninmu, kuma nasan zaka so ta domin yarinyar tana da kyau, ba kuma yanzu za'ayi auren ba, hakan zai baka dama kai yi iya shekarun da kake tunanin za ka iya yin aure dan naga kamar baka shirya a yanzu ba”

Gyara zama yai ba dan ya gaji da zaman ba, sai dan jin abu yana sokarsa tun daga kansa har cikin cikinsa.

“Indai dan kar zumunci ya lalace ne, to Zinneera zaka aura masa ba Aleeya ba, domin ita yake so”

Daddy yai saurin tashi zaune yana kallon Mommy wacce tai maganar.

“Zinneera kuma?”

“Eh Zinneera dan ka yake so, ya fara son ta tun kamin ya san an mata baiko”

Daddy ya daga mata hannu.

“Karki soma, yaushe ya hadu da ita ba zuwan da nai da shi a gidan ba, a gabansa aka fadi cewar tana da wanda zata aura sai kuma yanzu ku biromin da wani zance, idan har baki son dan ki ya auri yar uwata ba sai kin biyo ta wata hanyar da kika san ba zata taba yiyuwa ba”

“Zinneera ce zabin ransa, ita yake so ka aura masa ita kawai ba wai ka cilasta masa auren wata dabam ba”

Cikin sauri Sadam ya tari numfashin mahaifiyarsa.

“Ba Zinneera ba ce Mommy, Aleeya ce, Aleeya ce na ke so ba Zinneera ba...”

Ya fada fuskarsa da murmushi kamar gaske ya matse hannunsa na dama sosai dan karawa kansa kwarin guiwa. Cike da murmushin jindadi Daddy ya kalleshi Mommy kuma tai masa kallon rashin fahimta.

“Aa Fovarite Zinnee....”

“Wata kila baki fahimta ba ne, amman ina son Aleeya, Zinneera ai na san an mata miji”

“To kin gani kina ta wani kumfan baki ashe ma itace yake so, Alhamdulillah abun ya zo da sauki, zan samu mahaifiyarta mu tattaun na ji daga gareta daman ni kadai na yanke shawara a nan, idan su ma sun yi na'am sai kaje ku ga junanku”

“Na gode sosai Daddy Allah ya tabbatar da alheri”

Ya fada cike da far'a. Sannan ya unkura ya tashi har ya fito Mommy bata daina masa kallo mamaki ba bakinta ma ya rufe ruf ta kasa cewa komai.

“Life is so confusing”

Shine abunda ya fada yana driving.

“What we want we don't get, we only get what we are not satisfied with, what we expect never happens and what we hate generally repeats”

Magana yake tayi da kansa yana cika ma bakinsa iska.

“Zan cutu idan har na auri kanwarta bayan kuma ita na ke so, amman ba yadda zan yi maybe hakan ne mafi alheri”

Yaja wani dogon numfashi ya sauke tare yin murmushi.

Continue Reading

You'll Also Like

125K 7K 44
When she wants to go to her dad's house as she was missing them!! Her husband who was searching online how to "stop your wife from going away from yo...
815 116 44
AL'ADARMU No description, Just get your self ready, seat properly and enjoy reading this amazing heart touching story AL'ADARMU
63.9K 7.8K 47
Halinta na girman kai, rashin kunya da wulaqanci su suka sanya ya tsane ta.. baya qaunar ya bude idanuwa ya gan ta a gaban shi... she disgusts him!! ...
3K 220 26
Is a story about a soldier and love which is completely a fictional character.