ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

116K 15.9K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

There Are Two Different Things.

2.1K 364 115
By KhadeejaCandy

A harabar gidan yai parking. Sannan ya kalli Zinneera ya ce

“Sis fita ki shiga Mommy tana ciki”

“Allah yasa ba wani laifi nai mata ba”

Zinneera ta fada tana yar dariya.

“Kin taba mata laifi ne?”

Ya tambaya idonsa akanta kamar zai cinyeta.

“Kamin na shiga university, idan na yi ma Umma laifi tana kira Daddy ta fada masa saboda Abbah yana min fada, shi kuma Daddy sai ya fadama Mommy sai Mommy tasa a dauko ni a kawo ni gidan ta hukunta ni, saboda Daddy ma baya iya min komai”

Sadam yai murmushin da be san ta ina ya zo masa ba, har yanzu kallonta yake ya kasa dauke idonsa akanta.

“Fada min wani irin hukunci take miki?”

“A ranar ni zan share gidan nai mopping ko ina, kuma tace ni zan girka abincin da zan ci da kaina nawa ni kadai, kuma tasan ban iya ba”

“Kamar ya baki iya ba?”

“Idan na girka chabewa yake ko kuma hannayena su lankwshe na kasa yin aikin”

Ya dan yi shiru alamar mamaki yana kallon kofar falon da aka bude.

“Kamar ya hannayenki suke lakwashewa? Umma bata saka ki girki ne?”

“Bata sani cewa take bana yin na masu hankali, imagine komai Umma cewa take na mahaukata nake, kowa haka yake ce min”

Har ya bude baki zai sake wata maganar, sai ya hango Mommy wacce ta fito sanye da doguwar rigar buba da lace mai dan karan tsada. Kallonsu take cike da burgewa, yadda Sadam ya dora hannunsa saman sitari ya karkata ya maida hankalinsa gurin Zinneera, ita kuma tana da faman murmushi mai yanayi da dariya.

“Look at them...”

Ta furta tana musu kallon burgewa. Kamin ta soma ta ko stairs din ta sauko ta nufo inda suke. Ganin hakan yasa Zinneera bude motar ta fito.

“Mommy laifi nai?”

“In ji wa?”

Mommy ya fada tana mika mata duka hannayenta biyu, ta rika na Zinneera sai ta rumgume ta, abunda bata taba mata ba. Fitowa Sadam yai a motar ya tsaya yana kallonsu, murmushi yai haka kawai sai abun ya burgeshi.
  Zinneera ta dago ta kalli Mommy.

“Mommy lafiya dai?”

“Lafiya kalau”

Sai rika hannunta suka nufi cikin falon. For the first time Mommy ta rika ta ta zaunar sannan ta zauna kusa da ita.

“Tausayi kike ba ni, kawon ki ya fada min aure za'a miki”

Ba laifi nan kam ta dan ji kunyar Mommy yar da sadda kai kasa.

“Eh amman Mommy kin ga ai na huta da fadan da muke da Umma”

“Amman Zinneera karatunki fa?”

“Sadiq ya taba fada min tun kamin na shiga makarantar cewar zai barni na cigaba da karatuna ba zai hanani ba, kin ga shi ya siya min form din ma”

Mommy ta kawar da fuska kamin ta sake kallo ba Zinneera.

“Amman kin tabbatar kina son Sadiq din nan ko kuwa ko dai cilasta miki akai? Dan mu dai fada mana kawai akai wai za a miki baiko washe gari aka kawo mana minti da goro wai na baikonki, waya sani ma ko cilasta miki akai?”

“Aa ni nace ina son shi”

“Kin tabbata? Amman an bincika ansan waye shi? Yana da aikin yi ma, ina kika hadu da shi?”

Tsayawa tai kallon Mommy jin tana mata tambayoyin da bata taba mata ba, sai yau.

“A karanta ma hadu da shi? Mommy karki da mu Sadiq yana da kirki sosai, ba shi da wata matsala, sai dai ta mahaifiyarsa da kannensa basa so na”

“Saboda me?”

“Su ma dai kamarUmma cewa suke bana yin abu na masu hankali”

“Kin taba yin wani abun da be dace ba ne a gabansu?”

“Lokacin da ina Junior secondary school, makaranta daya muka yi da kanensa Nana girls, to kullum fada muke saboda bana son yadda suke raina min wayo, shine har wata rana na jima dayar, da muka shiga senior secondary sai aka canja mana principal aka kawo wata yayar Mamanshi, to ita dai sai ta dinga cewa bana da tarbiya, lokacin da yana zuwa gurinta ne muka hadu da shi har nai masa kwatancen gidanmu, kuma na taba fada da mamanshi a kasuwa, naje na wuce itama ta kawo sai mukai karo sai ta fara min fada wai bana kallo gabana,ni kuma na rama, sai ta mareni ni kuma na janye mata mayafi na fisge jakarta na jefar sai da aka raba mu”

Mommy ta rike baki

“Amman ke ba ki san mahaifiyarsa bace ko da gangan kika kai?”

“Aa ban sani ba, saboda lokacin ba amana engaged ba, sai da aka kusa mana baiko ne, ya kai ni gurinta sai ta daure min fuska, a lokacin ta yi ta fitinar wai ba za ayi baikon ba, shi kuma ya ce yana so na, kuma tunda kurkure ne a rashin sani ya kamata ta yafe min amman ta ki, kuma har hakuri na bata fa, wai ita har abada ba, zata taba ganin mutunci na ba”

Kamar da shagwaba haka take maganar tana nuna ita bata ga wani abun ki a abunda tai ba. Mommy ta kama hannayenta ta rike gam tana mata kallon da zata fahimcin kalamanta

“Zinneera, abunda kike yi ba kyau, ko waye ba zai jidadi dan kin yi fada da shi ba kuma ace har ki janye mata mayafi ki fisgi jakarta ki jefar, wannan zafin zuciyar na ki yayi yawa, kuma ba tarbiya ba ce ko baki bata hakuri be kamata ki mata haka ba, akalla ta haife ki, duk ko wanda ya kai matsayin mahaifinka ya cancanta ka girmamashi”

“To ai na bata hakuri”

“Maganin kar ayi kar a fara, da baki mata tun farko ba, da yanzu sai dai ta yaba tarbiyarki ta kara son ki, amman yanzu ina dadi zaman aure uwarshi bata sonki”

“Ai shi yana so na, ina son shi, ina ruwana da wata uwar miji, tun da ba ita zan aura ba, kuma Wallahi duk tai min sai na rama, dan ba tsoronta na ke ba”

“Uwar mijin?”

Mommy ta tambaya tana zaro ido.

“Eh ina ruwana da wata uwarmiji”

Ta fada tana turo baki, daga haka Mommy tai shiru bata sake cewa komai ba sai ta sake hannayenta ta tashi tsaye.

“Me kike so a girka miki?”

“Bana son komai ni gida zan koma”

“Yanzu?”

“Eh akwai abunda zan yi”

“Amman da kin jira Favorite ya dawo sai ya kai ki gida”

“Waye haka?”

“Sadam”

“Aaa ba sai ya dawo ba, ina son na tafi dai”

“Ni da na ke son ki dawo nan da zama”

“Tab ai Abbah ba zai bari ba, ko lokacin dana ke zuwa nan weekend ai fada yake”

Ta fada tana kokarin mikewa tsaye.

“Zan sa kawonki yai masa magana idan kina so”

“Eh ina so, ai ni na fi son nan ma”

“Zan mishi magana, kinji?”

“Okay. Na tafi”

Jikinta har bari yake ta bar gidan saboda hankalinta gaba daya ya koma can wani guri. Da kallo Mamaki Mommy ta bita har ta fice.

Ko da ta fito harabar gidan babu kowa saboda rana ta fara budawa, da kanta ta bude gate din ta fita tana ta sake sake.

‘Kamata yai naje na fadawa yan sadan, ko kuma naje gidansu na fadawa Mamanshi?’

Shine abunda take ta sakawa a zuciyarta, sai a yanzu take ganin ya kamata ta fada.

“Ai su yan sanda dole ya fada musu gaskiya, amman ni zai iya min karya”

Wannan karon a fili tai furucin. Tana rufe baki motarsa ta faka gabanta sai tai saurin yin baya shi kuma ya bude motar ya fito.

“Sadiq me kake yi nan?”

“Na biyo bayanku ne, kawai hankalina be kwanta da Sadam ba ne, na san inda zai kaiki waya sani ko da cutar da ke zai yi? Baby you shouldn't trust him, yaron nan manemin mata ne...”

Sai kuma yai saurin gutsure maganar ya shafa kansa.

“Sadiq bindigar me a dakinka?”

Tayi masa tambayar abunda ya fi damunta. Sai ya matso kusa da ita sosai.

“Zo mu shiga mota zan miki bayani”

“Sai dai ka min anan”

“Wani zai iya jinmu a nan akan titi mike fa”

“To miye in wani yaji? Wani abu kake aikatawa marar kyau ne?”

“Aa, ban taba aikata wani abu marar kyau ba. Ya kamata ki yarda da ni”

“Na yarda da kai, amman bindigar da na gani na ji tsoro”

“Na sani, amman ba zan cutar da ke ba zo nan”

Ya mika mata hannunsa, sai da ta kalli hannun kamin ta mika masa nata. Gaban mota ya bude ya sakata sannan ya zagayo ya shiga mazauninsa ya tashi motar. Bata ce masa komai ba harya tashi motar suka bar unguwar. A titi wurno road ya tsaya da motar ya faka gefen titi gurin itace ya juyo ya kalleta.

“Me kike son ki sani?”

“Miya hada ka da bindiga? Kuma karka boye min ba zan sake yarda da kai ba idan kai min karya”

“Na sani, amman sai kin fara min alkawarin cewar ba zaki fadawa kowa wannan sirrin ba”

Ya hade yawun bakinsa.

“Na yi alkawari”

A take ta fada. Wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya ce

“There are two different things, ban san ba ko zaki yarda, idan na fada miki cewar ni dan fashi ne zaki yarda ki zauna da ni? Idan na fada miki cewar zuwa nai na yi garkuwa da ke za ki yarda ki so ni? Idan na fada miki cewar saboda na kare lafiyarki yasa na ki amincewa da maganar auren da mahaifinkin yake ki zaki yarda?”

Kallonshi kawai take irin kallon nan na rashin fahimta da sanin inda ya dosa...

Bayan tafiyar Hajiya Karima Umma ta shiga cikin daki tai ta rera nata kukan, har Aleeya ta farka ta zo ta same ta a hakan. 

“Umma lafiya kike kuka?”

Firgita tai domin bata ji shigowar Aleeya ba, sai maganar ta taji kamar daga sama. Saurin share hawayenta tai.

“Na komai kin farka?”

Umma ta tambaya ba tare data kalleta ba.

“Eh na duba madubi ma ga bakin ya koma daidai”

“Alhamdulillah”

Sai a yanzu ta kalleta kadan dan bata son Aleeya ta ga yadda idonta suka kai ja akan kuka. Sai tai saurin tasowa ta baro dakin ta fito waje ta dauki ruwa ta wanke fuskarta.

“Umma dan Allah me kike yi ma kuka?”

Umma ta ji kamar bata ji, idonta sai kara cika da kwallah suke. Aleeya ta dawo gabanta ta tsaya kamar tai kuka.

“Umma dan Allah mi kike yi ma kuka?”

“Rayuwata da ta Zinneera nake yi ma kuka, Mabanbantan abubuwa guda biyu da za su faru nan gaba na ke yi ma kuka”

Umma ta fada cikin wani irin kuka dake zuwa mata da karfi.

“Me zai faru nan gaba? Wani abu Zinneera tai?”

“Batai komai ba, nima ban yi komai ba, amman ina jin tsoron faruwar wani abu”

“Minene wai?”

“Ban sani ba Aleeya, amman na san Zinneera bata dauka ba, ni ma kuma ba zan iya jurewa ba, ina ma Allah zai kashe ni kamin zuwan ranar”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Umma wai miye ne haka?”

Ganin hankalin Aleeya ya tashi yasa ta tsagaita hawayenta.

“Ba komai kawai wani mafarki nai marar dadi,kuma ance ba a son fadin mafarkin da ba na kwarai ba, Allah ya tsare kar ya faru, ”

“Amin”

Aleeya ta amsa cike da fargaba, Abbah ya fado mata rai, waya sani ko Umma ta yi mafarkin Abbah ya rasu ne, shiyasa take cewa ita da Zinneera domin sun fi kowa shakuwa da shi... Butar Umma ta dauka ta shiga bandaki, Aleeya kuma ta koma dakinsu zuciyarta cike da zullumi.

Continue Reading

You'll Also Like

5.5K 723 38
Wallahi ko zaka mutu bazan taba auren kaba yaya Abba na tsaneka na tsani duk mai sonka, "ni sa'ad nakeso kuma shi zan aura" ta karasa fada tana fashe...
309K 22.6K 54
α€”α€Ύα€œα€―α€Άα€Έα€žα€¬α€Έα€€α€­α€― α€œα€­α€™α€Ία€Šα€¬α€šα€°α€α€²α€· α€‘α€†α€­α€―α€Έα€œα€±α€Έα€›α€²α€·β€Œα€‘α€€α€Όα€±α€¬α€„α€Ία€Έ....
27.5K 1.4K 29
LABARI NE WANDA YAKE DAUKE DA BOYAYYAR SOYYYAH, BOYYAN HALI MARA KYAU,DA TSANTSAR BIYAYYA.
Ice Cold By m

General Fiction

2.8M 99.4K 54
COMPLETED [boyxboy] Wren Ridley is always two steps ahead of everyone, or so he thinks. His life seems out of his control when he starts having feeli...