ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

114K 15.7K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

ZR-07

2.6K 340 25
By KhadeejaCandy

“Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un”

Shine abunda Umma ta fada ganin irin kwancin bulolin da ke bayan Nabeel.

“Miya same ka Nabeel?”

Umma ta tambaya idonta na cika da hawaye zuciyarta kuma cike da al'ajabi. Daga kwance da yake rub da ciki ya soma magana a wahalce.

“Wallahi Umma dukana akai jiya da dare har garin Allah ya waye”

“Waya dake ka?”

“Wallahi Umma ban sani ba, amman jiya ban yi bachi ba, dukana akaita yi har safe, kamin a dake ni din ma sai da akai ta kaini sama ana sakoni ina faduwa, ina ta ihu amman babu mai jina, daga baya kuma na gan ni cikin daji mai duhu ga kura da zaki sai sun zo kamar za su cinye ni sai na gan ni a dakin nan, sai kuma na kara ganina can sai kuma na gan ni a nan, babu kalar ihun da ban yi ba amman babu mai jina, daga baya kuma nai ta jin kamar an dannemin kirji na kasa tashi sai dagani ake sama ana jefowo da na fado kife shine akai ta dukana a baya har safe, Wallahi Umma jikina ko'ina ciwo yake ko motsi bana iya yi”

Ya fada hawaye na fito ta gefen idonsa. Umma ta zauna kusa da shi tana kallon bayansa.

“Kai ka cire rigar daman? Wannan abu ko gamo kai”

“Ni ina zan sani, ko Sallah asuba zan yi ba”

Ya amsa a wahale. Aleeya kallon tausayi take masa, a dayan bangaren kuma tana dariyar yadda yake raki rabon da ta ga hawaye a idonsa har ta manta, ta san halin yayan nata mugune na karshe indai aka ce dukansu zai yi ba ya musu da sauki, musamman idan aka ce Zinneera zai doka, amman yau gashi shi ma ya sha dukan ya ji yadda suke ji, wani karin abun dariya ma babba da shi amman an masa wannan dukan har da su hawaye lallai ta san ba karamin duka ya sha ba.

“Sannu Ya Nabeel, gaskiya ka ji jiki”

Umma ta rafka uban ta gumi tana fadin.

“Ina ganin gamo kai?”

“Ni na fi tunanin ko dan na da....”

Sallamar da akai ne ya hanashi karasa maganar. Daga cikin dakin Umma ta amsa Aleeya kuma ta fita tana amsawa.
  Wasu yan mata ne su uku dayar na sanye da abaya, sauran biyu kuma na sanye da gown din atamfa.

“Abubakar ne ya kawo mu, zamu gaisa da Zinneera ne, mu kanensa ne”

Dayar ta fada wacce ke sanye da bakin gilashi.

“Okay, amman Zinneera bata nan ta tafi makaranta sai dai idan ta dawo”

Umma ce ta fito tana musu lale martabun.

“Sannunku da zuwa, ku shigo daki mana”

Sai duk suka gaisheta. Wacce tai magana dazun ta sake cewa.

“Aa mun gode, Abubakar yana waje yana jiranmu, sai dai in mun dawo”

A tare suka juyo suka fito daga cikin gidan, sai suka samu Abubakar tsaye jikin motar yana jiran fitowarsu.

“Wai bata nan ta tafi makaranta”

“Kai amman Babyna tayi saurin zuwa gashi na kira wayarta kashe, muje na kai ku makarantar sai ku gaisa a can”

Ya bude motar ya shiga, sai suma suka shiga yai mata key, yana driving suna fira har suka isa State University. Department dinsu ya nufa ko da yaje ya samu ta shiga lacca hakan yasa ya dawo ya fada musu ta shiga class.

“Kun san yadda za ayi? Ku bari sai anjima na san lokacin ma ta koma gida sai muje can ku ganta”

“No Yaya ni zan bar garin nan 12, sai dai mu dawo ko zuwa goma ko sha daya, dan gaskiya ina son na ga matar nan ta mu, labarinta kawai muke sha ya kamata dai yau mu ganta face to face tunda mun zo garin”

“Okay no problem”

Ya fada yana daga kafadunsa. Cikin motar ya koma ya maida su gida, shi kuma ya koma gidansa da ke Alu quarters ya shirya ya wuce office. Misalin goma da rabi suka sake kiranshi sai yaje ya dauko su ya nufo scul din da su.
  Department din ya sake nufa ganin dalibai a waje yasa jindadin sai rabon ido yake ko zai ga babynsa, but unfortunately sai hangota yai ana rikonta kanta ba dankwali Hijab dinta a kunkuru tana tsalle sai ta riko wani. Da sauri ya karasa gurin sisters din suna biye da shi.

“Lafiya miya faru?”

Shine abunda ya tambaya sai daya daga cikin matan da ke rikonta ta fada masa abunda yake faruwa. Hannu ya mika ya rikota yana girgiza ta.

“Zinneera Zinneera”

Sam bata jin abunda yake fada, kuka kawai take kamar wata karamar yarinya.

“Marina yai marina yai wayyo Allah”

Shine kawai abunda take fadi. Sai ya saketa ya juya gurin mutumen cikin bacin rai.

“Amman kai wawa ne Wallahi ina ruwanka da abunda ke tsakaninta da yaron ko dukansa tai ina ruwanka da zaka saka hannu ka mari mace dan kana katon banza”

“An mareta zo ka rama mata idan ka isa, ku kuke daure mata gindi tana yi ma mutane iskanci kala kala ko? To Wallahi sai na ci ubanta cikin makarantar nan matukar bata canja hali ba”

Ana rufe masa baki yana fadar hakan, wani kallo Abubakar yai masa, ba zai biye shi ba dan a akwai kurciya a yanayinsa amman har ga Allah ya ji zafin marin da yai ma babynsa, malaman ne suka shiga fadan akai ta ma yaron fada daga baya kuma aka dawo gurin Zinneera, Abubakar ala ala kawai yake kar ta zagi wani daga cikin malam.

“Ba ya ci sai ya ci ubana ba? To ya zo ya ci ubana zan rakashi na bashi mai da yaji”

Ta fada tana kwance Hijab din dake kugunta ta saka. Sai Sadiq (Abubakar) ya kama hannunta ya jata zuwa gurin motarsa, wannan friend din tana tana biye da su a baya rike da jakar Zinneera, sai da suka kusa isa sai kawai ta bankare tai baya kamar zata fadi sai da ya riko.

“Yanzu fa ya sha marin banza, ya mareni a banza”

Ta fada cikin wata irin murya tana numfashi kamar wacce za a cirewa rai. Zaunar da ita yai a gurin ya rika fuskarta.

“Za a rama miki trust me”

“Wa zai rama min?”

“Za a rama miki ki yarda da ni kawai, yi hakuri ki daina kuka gaban mutane kar a mana dariya kinji Babyna”

Kai ta gyada masa ta share hawayenta. Sannan ta tashi tsaye ya bude mata front seat ta zauna ya karbi jakarta dake hannun yarinya ya saka mata a ciki, sisters dinsa suka shiga baya shi kuma ya shiga mazaunin direaba yaja motar.

“Yaya wannan ita ce matar da zaka aura?”

Daya daga cikinsu ta tambaya tana tsire baki, Sai Zinneera ta juyo ta kallesu daman ta gansu tun dazu amman hankalinta be bata ta tambaye shi su waye ba ko ta tsaya ta tantacesu ba sai yanzu.

“Eh ko wata zaki canja masa?”

“Gaskiya dai baki dace da shi ba”

“Ai sai ki nemo masa wacce ta dace da shi, kuma Wallahi ko kina so ko baki so sai na aureshi sai dai ki mutu”

“Wallahi ba zaki aureshi ba, dan Yayanmu ba zai auri marar tarbiya ba”

“Kam uban nan, ni ce ba ni da tarbiya? Wallahi bari mu fita cikin motar nan sai na miki shegen duka”

“A haka za ki min dukan ai ko da jijjiga kurna ta fi magarya, marar hankali kowa”

Sadiq ya taka burki da karfi ya faka motarsa gefen titi, ya juyo ya kalleta.

“A gan idona zaki kira Zabin raina, marar hankali marar tarbiya? Fitar min a mota”

Ya fada a tsawace, ba ita kadai ba su duka suka bude motar suka fita, ba tare da damuwa ba yai ma motar keys ya hau titi tare da rikon hannun Zinneera.

“Babyna dan Allah ki rika natsuwa irin abubuwan nan da kike ki daina bana so”

“Yanzu ba gabanka ta kirani mahaukaciya ba”

“Da baki yi abunda kika kai ba, ai ba zata kira ki mahaukaciyar ba, ba zan lamunci kowa ya fada miki magana marar dadi ko ya ci zarafinki ba, amman dan Allah ki daina halayen nan please”

Ta fisge hannunta.

“Fine kai ma kana ganin bana da hankali ko? Sauke ni bana son ka kaini gida”

Sai ya kalleta cikin damuwa.

“Daga magana? I'm sorry”

“Ni dai ka sauke ni kawai”

Be sauketa ba, be kuma sake ce mata komai ba sai da ya isa cikin unguwar sannan ya sauketa kofar gidansu. A kufule ta bude motar ta fita, shi dai da kalli ta bita har ta shige gida sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tashi motar.
 
Da tsingilta ta shiga gidan tana sallama can cikin makoshinta. Daga Umma da ke wanke wanke har Nabeel da ke wance karkashin itaciyar mangoro be dago ya kalleta ba. Dakinsu ta wuce ta aje jakarta sai kuma ya fito ta nufo inda Umma take ta risina zata karbi wanke wanke.

“Kawo na wanke”

“Tashi tashi kar raina ya bace”

Da sauri ta tashi tsaye dan ta san halin Umma idan ranta ya bace duk abunda ke gabanta zata iya dukanta da shi.

“Umma yi hakuri dan Allah, ba zan sake zuwa gidansa ba, jiyan ma saboda na duba lafiyarsa ne dan Allah ki yi hakuri”

Sai a lokacin Umma ta dago ta kalleta.

“Da karki yi da ki yi duk uwarsu daya Ubansu daya a gurina, ni dai na yi budurcina lafiya na kare babu wanda ya taba kuka da ni, idan ma kika je kika kwaso abun kunya ke ta shafa ba ni ba, tun da na haife ki Zinneera ban huta ba tun kina karaka kullum cikin kawo min kararki ake, yanzu kuma da kika girma kina son hawan jininki ya kasheni, duk yarinyar da ta kai kamarki ta san ciwon kanta tana da hankali ta san ciwon kanta amman ban da ke, kullum haukarki kara yawa take, Wallahi ke kan kinji haushi rayuwa...”

Ta bata fuska sosai, ita a rayuwarta bata ganin abunda take as rashin hankali ko rashin natsuwa, ita dai a daidai take ganin take.

“Wuce gidan Maman Ramatu ki karbo min kudin adashena”

Umma ta fada mata tana hararta. Ita kuma ta cira kafarta ta nufi kofar fita ranta na sosuwa da bakaken kalaman da Umma tai mata.

***     ***     ***

Dariya yai yasa yatsansa yana zagaye bakin mug din dake cike da tea.

“Allah Mommy I'm jealous, jiya fa kamin na cire layin kira uku yai mata raina ya ba ce sosai”

“Favorite ana kishin mace ba tare da ta sani ba? Baka tsoron tai maka fada idan ta ga ka cire mata sim?”

“Ai fadan nake son tai min ni tsiwarta tana burgeni sosai”

“Yanzu ka yarda na fika gaskiya ko? Ta tabbata son ta kake”

Mikewa yai tsaye yana dariya ya nufo downstairs, a nan ya samu kansa a harabar gidan, domin falon da dakin da komai na gidan a sama suke.

“Na yarda ina kishinta”

“Ka yarda son ta kake, duk mace da kake jin dadin ganinta take burgeka to son ta kake, kuma idan baka sonta mi zai kawo kishin?”

“Shikenan sonta na ke”

Daga can cikin wayar Momy tai dariya.

“Wannan kam, anjima ka zo Daddynku ya ce zai kuje gurin wata gwaggonku”

Ya nufi gate yana fadin.

“Oh Daddyn wai su dangin nan basa karewa ne, tun na dawo kusan kullum sai munje wani gurin”

“Ai gwaggwanin ne naka da yawa, kuma kai baka sansu ba shiyasa yake son kana zuwa kasan halin babanka da son danginsa”

“Okay zan zo... Oh my God Mommy gata nan tana zuwa”

“To a gaishe min ita, kamin mu aiko gidansu”

Dariya yai ya kashe wayar yana jan gate din. Murmushi yake yana kallon kafafuwanta kamar mai kirga takun da take, kanta na kasa hannayenta cikin Hijab idan ka hango kamar mai cikakkiyar natsuwa.
   Sai da ta iso kusa da shi sannan ta daga kai ta kalleshi.

“Ina sim dina da ka cire?”

Ya rumgume hannayensa, yana cigaba da kallonta cike da burgewa.

“Ni ban daukar miki sim ba”

Har ta zaro ido zata masa masifa sai kuma ta danne zuciyarta, tana ta kokarin ganin ta zama yarinyar kirki kamar yadda Umma ta ke so.

“Dan Allah ka bani abuna, ku kuke min abu amman idan na yi fada a rika cewa ba ni da hankali”

“Waya ke cewa ba ki da hankali?”

Ya tambaya yana kallon lips dinta, yana lasa lebensa.

“Kowa haka nan yake cewa wa bani da hankali bana ni da mutunci”

“Duk wanda yake ce miki hakan nan, be san kimarki ba ne, amman abunda kike babu rashin hankali ciki ni burgeni ma kike?”

“Da gaske?”

“Amman har Sadiq cewa yake na rika yim abu na masu hankali”

“Waye Sadiq”

“Wanda zan aura”

“Wannan dan iskan da kika je gani? Shine ya kira ki dakinsa ko?”

“A a, ba shi ya kirani ba fa, ni naje dan kaina gashi nan ma sai da aka saka Ya Nabeel ya dakeni, kuma yau wani ya mareni a makaranta”

“Me kika masa?”

Ya tambaya da serious face. A take ta zayyana masa abunda ya faru har ya kai ga ya mareta, da kuma dukan da Nabeel yai mata, ya ji haushi sosai a take ya fusata har jin yai kamar ace a gabansa ne.

“Fada min waye ubanshi a garin nan da zai saka hannunsa ya mareki?”

“Ban san waye shi ba”

“Ki bincika cikin makarantar ku sunansa sunan mahaifinsa da kuma unguwarsu”

“Me zaka masa?”

“Na rama miki mana, ko baki so”

“Ina so?”

Ta fada da far'ah, tana waigen bayanta.

“Bari dai inje inda aka aike na na dawo”

“Fada min sunanki”

Ya tambaya yana kallon kirjinta.

“Zinneera”

“Ni kuma Sadam Sadam Adamu Kazaure”

“Sunan wani kawonmu mu Alhaji Adamu”

Yayi murmushi.

“Na nan gidana ne idan kin dawo ki yi knocked sai na fito”

Ta daga kai tana kallon katon gidan.

“Laaa kai ke da gidan nan, amman ana cewa babu mutane a ciki, ashe ma kusa da mu kake kana da mata hala?”

“Aa sai dai in na aureki”

Mtsssssss taja wani dogon tsaki.

“Kai ni fa nina da miji ko dan ja ganni haka ka dauka bani da miji ne?”

Dariya yayi ya bi bayanta da kallo, har sai da ta karya kwana sannan ta juyo ya dawo cikin gidan.

“Za'a rama miki yarinya babu wanda ya isa ya tabaki yanzu kam”

Stairs din ya taka ya shiga falonsa, hannu ya mikawa yarinyar da ke zaune saman kujera, sai ta taso ta nufo inda yake tana wani irin karairaya, kamin ta kawo kusa da shu ya hade yawun bakinsa sau hudu, sannan ya saka hannunsa ya rika kunkurunta yasa babban yatsansa yana wasa da gefen fuskarta, sai kuma ya saka mata yatsan a baki kamin ya cire ya hade bakinsu....

Continue Reading

You'll Also Like

728K 14.2K 46
We have seen over protective brothers, there are maybe 6 , 7 or 8 brothers but what if a girl has 18 brothers, with her over protective parents and c...
231K 6.9K 64
What happens when Chan adds random numbers to a group chat? A lot of crazy stuff, apparently. Now please, sit back, relax, and prepare to be bombard...
1.1M 36.8K 62
WATTYS WINNER When her fiancรฉ ends up in a coma and his secret mistress, Halley, shows up, Mary feels like her world is falling apart. What she does...