ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

113K 15.7K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 03
ZR - 04
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

ZR-05

2.7K 325 37
By KhadeejaCandy

Tun da tai kwaliyar take ta faman fifita a fuskarta, wai kar tai gumi duk iskan fankar dake dakin be wadatar da ita ba. Ita dai kar tai gumi kwalliyarta ta goge Abubakar (Sadiq) be zo ya gani ba, ta yi jiran kiran wayarsa har ta gaji be kira ba, Nabeel sai dariya yake mata shi da Aleeya. Ita kuma ta cika kamar ta fashe dan takaici, baro musu dakin tai ta nufo gurin icen guava ta zauna ta soma kiran Abubakar a wayarta ganin har tara na kokarin wuce bata be zo ba. Ringing daya ya dauka.

"Hello Baby"

"Mai sunan Baba miya han ka zuwa yau?"

"Wallahi Baby ba ni da lafiya, Fever ya rufeni yanzu haka kwance nake sanyi na ke ji"

"Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, Subhanallahi ka sha magani?"

"Ee na sha"

"Ko na zo na duba ka?"

"Aa ba sai kin zo ba, ki yi zamanki anjima kadan na san zai sauka"

"Allah ya sauwake"

Ta aje wayar ba dan ta gamsu da sauki ba, a take ta soma jin kamar ita ce bata da lafiyar, hankalinta duk ya bi ya tashi. Ji tai bata da natsuwa indai bata je ta duba lafiyarta ba. Amman kuma bata da kudin mashi kuma ta san dare ne yanzu gata da tsoron dare. Tashi tai ta nufi dakin dakin Umma, agogon dakin ta fara kallo tara da yan mintuna ya nuna mata, daman ta san indai Abbah ya wuce tara to ba zai dawo ba sai sha daya ko sha biyu wani lokacin ma har karshe daya yana kaiwa idan ya dauki passengers na nesa. Jikin kofar ta tsaya tana ma Umma magana kamar wata munafuka.

"Umma wai Abubakar ya ce na siya mishi kwai da kwai (awara) kamin ya zo"

Umma ta jiyo ta kalleta.

"Abubakar din ne ya ce a siya masa awara?"

"Ee"

"Zo bude aljihun gado ki dauko naira dari ki siyo masa"

Cike da jindadi ta karasa gurin da Umma ke ake kudi ta bude ta dauki naira dari kamar yadda ta fada mata sai ta dawo dakinsu ta dauki katon Hijab dinta ta saka, ta zura talkamin roba ta fice da sauri. Bakin titi ta fito ta tari mai Napep wandabke dauke da mutum biyu.

"Alu quarters zaka kai ni"

"Dari biyu"

"Kai Wallahi dari ne, dan Allah ka taimaka ko babakin Titi ne ka aje ni sai na karasa da kafa, dan Girman Allah ka taimaka min"

Girman Allah data hada shi da shi ne yasa ya ce ta shigo, suka kama hanyar daman mace daya a can za a sauketa dayar kuma a Badoo. Idonta ta mayar gurin titi amman hankalinta na can gurin Abubakar zuciyarta nata raya mata irin halin da yake ciki. A kusa da gidansa aka ajeta kasancewar gidansa na kusa da titin ne.

"Na gode"

Sannan ta cire takalminta ta zura da gudu saboda duhun da ke gurin, @360 ta isa bakin kofar gidansa. Ta shiga buga masa da karfi kamar wacce tai sata aka biyo bayanta, sam hankalin be bata ta kira shi a waya a sanar masa tana waje ba. Kamin ya bude mata har ta fara kuka, dan har ga Allah gani take wani zai zo ya mata wani abun ne a nan. Sai da ya bude haskem falonsa ya hasko waje, be gama tantance ita din ce ko bata ita ba har sai da yaga ta shigo da sauri tana haki.

"Baby mi ya kawo nan?"

Ya tambaya bayan ya maida kofar ya rufe. Sai ta soma sosa kai.

"Ba ka ce baka da lafiya ba"

"Amman ai na ce karki zo, ya akayi ma Umma ta barki kika zo?"

"Bata san na zo ba, karya nai mata"

"To kin koma yanzu tun da kin ganni, idan wani ya ga shigowarki a unguwar nan ma ai sai yai mana wani zargi"

"Amman ai ba komai zamu yi ba, mu ba yan iska ba ne"

"Ba kowa ya san da hakan ba, idan aka ga mace da namiji sun kebe sai a yi musu daukar yan iska, ki koma gida yanzu"

Ta taba fuskarsa.

"Ka ji sauki?"

"Eh na ji sauki"

"Ka ci abincin?"

"Ee na ci"

"Ko na dafa maka"

"Haba Baby dan Allah ki wuce gida mana"

Ya nufo kofa ya bude mata.

"Amman tsoro ma ke ji, ka raka ni bakin titi"

"Ina rakaki za a ce an ganni na fito tare da mace na raka titi"

Ta dan bata fuska.

"Amman ni tsoro na ke ji"

Sai ya saki kofar ya dawo inda take tsaye yana mata magana a hankali.

"Yanzu Baby in ban da yautarki karfe tara da rabi na dare za ki baro gidanku ki zo nan haba Baby"

"Na dauka sosai ne"

"Ko sosai ne be kamata ba tun da ba aure muka yi ba, yaushe zaki fara banbance abu mai kyau da marar kyau ne, ya kamata ki rika tunani irin na mutane mana"

"Na ji tsoro sosai ne, har jin nai kamar nice bani da lafiyar ma"

Ta fada hawaye na sauko mata. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali.

"I know you care for me and i care for you too, amman abunda na ke ina kokarin tsiratar mana da mutunci mune ba wai ina kokarim korarki ne dan wani abun ba, yi hakuri ki yafe min, zo muje ciki ki zauna"

"Aa ni zan tafi indai tafiyana zai saka farinciki zan tafi, amman ka kula da kanka kanji? Kuma ka ci abinci ka sha magani"

"I will i promise you this, i love you"

Ta saki hannunsa ta nufi kofar ta bude tana ta waigensa har ta fice. Shi kuma ya nufi gurin kujera ya zauna, a nan wani tunanin ya zo masa, idan wani abun ya sameta fa? Ko wani ya tareta a hanya ga gurin da duhu, da wani abu ya sameta kara a ganshi da ita inyaso ayi masa duk zargin da za a masa. Saurim tashi yai ya bude kofar cikin rashin kuzari irin na marasa lafiya ya fiton waje amman ko kufanta be gani ba. Ciki ya koma ya dauki wayarsa ya kirata zuciyarsa cike da tsoron abunda zai sameta. Tana dauka yaji hayaniyar ababen hawa hakan yasa shi jin natsuwa.

"Kin kai titi"

"Ee na kai gudu nai"

"Akwai mutane a gurin? Kina jin tsoro har yanzu?"

"Aa nan akwai mutane ai da abun hawa"

"Okay take care of yourself, i love you"

"Thank you"

Ta kashe wayar, tana ta tunanin yadda zata koma gida, tun da babu ko sisi a hannunta kuma ta san yanzu dare ne idan tai mai adaidai wawanci yai mata sakarci asirinta ya tonu a gida.

*** *** ***
Ko da ya shiga part din Daddy sai suka dauko wata hirar basu fita ba sai bayan sallah isha'i, Daddyn ya shiga motarsa dan Sadam ya fada nasa cewar daga can gidansa zai wuce. Alu quarters suka nufa gurin Gwaggo Larai, a can suka dade suna gaisawa,tana da fira da Daddy dan Sadam ba wani saninta yai ba, hasalima shi sai yau ya fara ganinta. Guraren goma saura yai mata sallama ita da Daddy ganin firar ta su ba mai karewa ba ce ya kamo hanyar gida.

_What do you do when you cant let go, what do you say when you don't know how you felt and you know nobody knows how you feel_

Like you by Tatiana manaois. Ita ce wakar da yake saurare a cikin motar, dake cike da sanyin ac da kuma kanshin turarensa mai dadin shaka. Unexpected ya hango Zinneera gafen titi tana tafiya kana ganinta kasan tsorace take, har ya wuce ta sai yai parking gafen titi yana kallonta a nearby mirror har ta iso inda motarsa take sai ya zuke gilashin motar.

"Ke zo nan"

Kamar daman can jira kawai take ya kirata, sai ta karawa kafafunta mai, hakan yasa shi saurin fitowa daga motar ya cire facing cap din dake kansa.

"Kidan ba ko zo nan, idan kika je makaranta gobe sai na zaneki sosai"

Jin hakan yasa ta dan tsaya ta juyo dan ganin ko wanene. Mutumen nan ne na makarantarsu kuma na unguwarsu. Dawowa tai inda gurin motar ta tsaya.

"Ke da wa kika zo nan?"

"Ni kadai"

Ta fada tana dan turo baki.

"Ina zaki je yanzu?"

"Gida"

"Shiga mota muje"

He said, kind of commanded her. Daman tana neman wanda zai kaita gida duk da kasancewar bata san halinsa ba. Sai ta bude motar ta shiga front seat ta zauna. Shi kuma yai motar key suka hau titi yana tafiya a hankali kamar baya so su saurin isa gida. Sai da suka yi dan nisa sannan ya kai hannu ya rage volume din wakar dake tashi.

"Ina kika fito"

Ya tambaya ba tare da ya kalleta ba.

"Gurin saurayina"

Hakan yasa shi kallonta da kyau, sai kuma ya dauko facing cap dinsa ya saka a kansa.

"Amman ba komai muka yi ba, ni ba yar iska ba ce shi ma kuma ba dan iska ba ne, kawai na je duba shi ne bashi da lafiya"

Yayi shiru kamar ba zai sake tambayar komai ba.

"Gidanku an san kin zo?"

"Aa ba a sani ba, kuma daman bama da na komawa da kasa zanje"

Dariya yai sai dai ko kadan be kalli inda take ba. He was imagining yadda zata ta kai kanta tun daga Alu quarters har Abdullahi fodio road da kafa.

"Yanzu idan iyayenki suka ji ko kuka ganki kin fito gurin wani me zaki yi?"

"Fada musu za ka yi?"

Ya daga kafadunsa yana dan mire baki.

"Nima ban sani ba, amman shi ya ce ki zo?"

"Aa fada ma yai min, wai na koma kar mutane su gani"

"To me zaki fadawa iyayenki idan sun ganki?"

"Kai me matarka za ta yi idan ta ga ka dauko ni?"

"Ni ai ba ni da mata, idan kuma kina so na shikenan"

"Aa ni ina da miji"

"Wacan ai ba miji ba ne, duk wanda zai kira mace kamarki ta iskoshi ai ba miji ba ne"

"Wallahi shi ba dan iska ba ne, kuma ba shi ya kirani ba, ni na je da kaina, karka sake ce masa dan iska"

Ta fada a tsawace. Sai ya faka motarsa dai dai road din Clapperto road.

"Fitar min daga mota, haka kawai ki min tsawa saboda wani katon banza"

Da taga da gaske yake sai ta koma ba shi hakuri.

"Yi hakuri to"

Sai yai ma motar key ya hau titi.

"Dazun kika ce na wuce ki kamar zan bankeki ko?"

"To baka ga yadda kake guduba ka saka wasu tufafi kana wani tallatar kanka"

Ya lasa lebensa yana wani shegen murmushi.

"Dan iska ne ni kenan?"

"Ni dai ban ce ba"

"To ko dai na miki ne?"

Ya fada yana kallonta tare da daga mata gira, sai ta zaro ido shi kuma ya sake daga mata a karo na biyu.

"Har kofar gidanku zan saukeki"

"Aa fada za a min"

"Sai dai a ayi miki fada, kin san abunda kika yi be kyau kika aikata kuma"

Ya fada daidai lokacin da ya faka motarsa kofar gidan. Sai ta kalleshi.

"Ashe kasan gidanmu?"

Be ce mata komai ba, ya fita ya zagoyo gefenta ya bude motar.

"Fito"

Kamar ba zata fito ba, dan tana tsoro wani ya ganta, sai kuma ta daure ta fito, yana rufe motar yai mata key ta nufi kofar gida. Sai karo tai da Nabeel da ke tsaye yana kallonsu.

"Na shiga uku"

"Gidan Uban wa kika fito? Waye can mutumen?"

"Taimakona yai ya kawoni gida"

"Wuce ciki"

Ya matsa gefe ta ratsa ta wuce cike da tsoro.

"Sai kin fada min gidan ubanda kika je, babu inda ban aika nemanki ba a unguwar aka ce baki nan, sai yanzu zaki dawo karfe goma da ta kwata ina kika ce"

Umma ta tambaya a tsawace irin tsawar nan da ke razanar da yaro.
Sai ta durkusa saman guiyoyinta ta fashe da kuka.

"Abubakar ne ba shi da lafiya shine na je duba shi"

Umma tasa salati.

"Yanzu dan baki da hankali zaki bar unguwa uwa unguwa kije duba namiji dam be da lafiya, Nabeel zo nan sa bulala ka zane min yar iskar yarinyar nan, indai haukace na fiki hauka da wawanci"

Ta karasa tana kwalama Nabeel kira, daman yana tsaye bakin kofa umarni kawai yake jira sai gashi ya shigo tsakar gidan ya doso inda Zinneera take, ita kuma ta saka ihu iya karfinta.

#Team ZR
#Team Sadam
#Team Abubakar
#Team Zinneera.
# Team Candy 😂

Continue Reading

You'll Also Like

727K 14.2K 46
We have seen over protective brothers, there are maybe 6 , 7 or 8 brothers but what if a girl has 18 brothers, with her over protective parents and c...
1.7M 55.4K 75
Alexander, James and Skye were triplets. They were stolen from their family at the age of 4. The family searched for them day and night never giving...
4.6K 411 24
Forced to marry her childhood crush after she just found her true love, how will zahra cope with this. ABEG JUST READ TO FIND OUT. I'm bad at descrip...
3.9K 316 22
Mutane kala uku ne a duniya. Na farko masu rauni Na biyu masu karfi Na uku masu bada umarni A ko ina ma duniya suna raye. Suna kasuwancin su ne akan...