ZABIN RAI

By KhadeejaCandy

116K 15.9K 3.1K

Choice of Life, or Destiny? The link between the soul and the heart. True love, a heart breaking stor... More

ZR-01
ZR-02
ZR - 04
ZR-05
ZR-06
ZR-07
ZR-08
ZR-09
ZR-10
Don't lose hope...
She saw a gun...!
He Wiped Away Her Tears.
There Are Two Different Things.
How i wish
Life Is So Confusing
HAJIYA KARIMA
Life is short
Biological Mother
SMS
Phone Call
Hospital
Jealousy
Some Words
Thirty Million
Mysteries
ZR 27
Don't Rush Things
New face
Cancellation
The Weeding and Accident
At Hospital
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 End

ZR - 03

3.5K 402 43
By KhadeejaCandy

"Wait wait wasa na ke miki papaya ne a ciki"

Ta bata fuska ta turo baki.

"Amman shine ka bani tsoro"

Ya mika hannu ya janyo ta ta fado kirjinsa.

"Sorry Babyna ba zan sake ba"

"Wani zai iya ganinmu fa"

Ta fada tana kokarin zame jikinta.

"Ba wanda zai ganmu"

Ya kara rumgumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya.

"Ina son ki sosai Zinneera"

"Ina son ki Aleeya ina son ki Habiba ina son ki Ramatu, mace nawa ka fadawa haka"

Ya saketa yana dariya.

"Kin fara ko?"

"Ee ai gaskiya ce haka kuke kuje gurin wannan ku ce suna son ta kuje gurin wannan ku ce kuna son ta, ko ranar nan ma da ka kirani ai Aleeya ka ce min"

Ya sake yin dariya, sai ita tai dariya.

"Kaga ni ko? Dariya tana maka kyau shiyasa yan matan nan suke lake maka"

"Ni kam kinga na san a makarantar da kika fara yanzu, da Unguwar nan, na san akwai maza da yawa masu sonki, amman hakan be taba damu na ba, saboda na san ni kadai ne a zuciyarki, da zan hadu da mata dari kullum su ce suna so na, ba zai taba damuna ba, domin ni ke kadaice a gabana"

"Kai ma ai kasan wasa nake yi ko? But seriously am jealous, Sadiq kana da kyau sosai mata da yawa zasu yi crushing kanka, ni ba zan juri ganinka da wata mace ba, ko yar'uwarka ce"

"Eyyye Babyna an fara wayo har da su kishi haka"

Sai ta rufe fuskarta, sai kuma ta bude idon.

"Au da can bani da wayo?"

"Aa da baki da shi da ai ba zaki rika fada da Nabeel kullum ba"

Ya karasa yana mata gwalo, ta bata fuska har da rumgume hannayenta.

"Sorry"

Ya fada yana kama kunnesa alamar yana bata hakuri.

"Yi hakuri wasa nake miki, kawai na yi marmarin wannan fushin na ki ne, kin san ni komai na ki burgeni ya ke, fushinki dariyarki duk kyau suke miki, wani lokaci idan ina gida ko office na kan dauki wayata nai ta kallon hotunanki, ina jin nishadin haka, wani lokacin na kan tuna wani abu daya faru wanda ya kan saki dariya ko fushi sai na rika aina yanayinki, hakan yana kara min kaunarki. Har mahaifiyata ta sani, idan nai dariya sai ta ce Zinneera ko"

Ya karasa yana murmushi.

"Na san nafi ko wace mace a duniyar nan dacen masoyi, hakika ban yi kuken Zabin rai a matsayinka na wanda zan aura ba, wani lokacin na kan yi unkurin auna irin son da nake maka, amman sai na rasa silekin da zai dauki nauyin son balle har na iya irin kwatankwacin son da na ke maka, Umma tana yawan ce mun na yi dacen samun abokin rayuwa irinka, Abbana yana yabon kyakkawan halinka, sai dai ni kuma ina jin kamar akwai wata rana da son ka zai min illa, zai rufe idon na kasa gani a lokacin da ganin yake da muhimmanci, ya maida ni kurma a lokacin da jin ke da muhimmanci"

"Ko da mafarki, wani abu be taba tsikarata na ji akwai wata rana da zan yi zullumi ko dardar da son ki ba"

"ba zullumi na ke da dardar ba, har abada Zabin raina shine zabi bani da haufi akan zabarka a matsayin abokin rayuwa na san bazan yi nadama, a duk lokacin da nake tsara irin rayuwar zamantakewar auren da za mu yi sai na ji wani abu ya tsaya min, ban san ko minene ba, ban san mi wannan abun yake nufi ba"

Ya kai hannu ya rika hannunta.

"Kishi ne?"

Ta daga kai ta kalleshi idonta cike da kwalla.

"Ba ni da tabbacin ko minene"

"Ko ma minene ya tafi can ya bar min matata da ita kadai zan rayu"

Hango hasken motar da tai ne yasa tai saurin janye hannunta daga rikon da yai mata taja baya.

"Ina ganin Abbah ne fa"

Sai yai saurin gyara tsayuwarsa. Kusa da 406 dinsa Abbah ta faka golf 3 dinsa ta jigila ya fito rike da bakar leda, yana kawowa kusa da su Sadiq ya risina har kasa ya gaisheshi, ita kuma ta karbi ledar ta shiga da ita. A baki kofar dakin ta tsaya tai gyaran murya irin yadda Abbah yake idan ya dawo gida sannan ta kwaikwayi muryarsa tai sallama.

"Assalamu alaikum"

"Allah ya shiryaki"

Cewar Umma tana girgiza kai. Sai tai dariya ta aje mata ledar ta juya, tana fitowa Abbah na kawowa bakin tsakar gida, sun sun tai da kai sannan ta fice. Hasketa Sadiq yai da motarsa hakan yasa tai saurin komawa sai ya danna mata horn yai ma motar key ya wuce yana daga mata hannu. Cikin daki ta dawo ta zauna kusa da Abbah tana kallon ledar da Umma ke kokarin budewa.

"Abbah mi ka siyo min?"

"Yar lele lemu da abaya ne"

Ya dan bata fuska

"Kai Abbah na fada maka yau agashe nake so fa"

"To yau Katsina muka je, bamu dawo da wuri ba, wannan ma tasha na siyo kar na shigo gidan haka nan"

"To mun gode Allah kara arziki"

Ta fada tana murmushi, tare da kai hannu ta dauka sai Umma ta buge mata hannun.

"Ba na ce ki rika jira ana baki abu ba"

"Ka gani ko Abbah sai ta rika min abu kamar ba Babana ya siyo ba"

"Kyaleta ai sabuwar Uwa zan kawo miki"

Umma tasa dariya.

"A kawo uku mu zama hudu ai dai ni ce uwargida ba komai"

Gaba dayansu dariya suka yi. Sannan Umma ta tashi dan hada masa ruwan wanka.

Washe gari ma tun da asuba ya bar gidan saboda aikinsa na direbansa ci da yake. Zinneera kam bata tashi ba sai kusan bakwai ta tashi a gaggaucw ta shirya dan suna da lacca 8am. Wani farin lace ta saka da Hijab ta fito rike da jaka da littafai a hannunta.

Nabeel na zaune kusa da makwarara yana wanki baki, sai yasa mata dariya.

"Sannu yar makaranta a rayata jaka a rike takardu a hannu"

"Yes kara a san yanzu Jami'a na ke, na wuce ajin yara"

Ya sake kyalkyalewa da dariya.

"Dan baka sababa, ana ganinki za a ce wannan daga gani yar kauye ce, yar kauyen ma ta can ciki kauye ji wani dress na ki, blue Hijab farin lace chaiii"

Sai ta soma bata rai, sai ta kalli kanta ta kalli Umma.

"Umma kin gani ko?"

"Ke kike kula shi ai, zo ki sha koko ki wuce"

"Eyy tab koko Wallahi State University nan duk yayan manya ne, babu mai shan koko a cikinsu, gaskiya ni ba zan sha ba"

"To zo ga dumame"

Ta buga kafa a kasa.

"Haba Umma dai, ni ba zan sha ba"

"To sai me?"

Nabeel ya tambaya.

"Abani dari biyu naje makaranta na karya"

"Idan kina son dari biyu zo nan ki gaisheni, ki risina har kasa zan baki dari biyar ma"

"Dan Allah da gaske?"

Taje ta risina gabansa kamar yadda ya bukata.

"Yaya Nabeel ina kwana? Ya gida? Ya gari ya gagarin gari? Ya office din? Su Umma da Abbah sun tashi lafiya? Ya komai da komai?"

Sai kawai yasa mata dariya.

"Walallaliya tashi ki ban guri"

Ta tashi tana murguda masa baki.

"Ban yafe gaisuwar ba, kuma Wallahi sai Allah ya saka min"

Ta nufi kofar fita daga gidan gaba daya.

"Tafiya zaki yi baki karya ba"

"Ee ni ba zan ci dumame ba ina yar jami'a haba dai Umma"

Ta fice tana ta gunguni. haka ta bi titi fuskarta babu annuri. Ta gabanta ya bi ya wuce yana sanye da vest da guntun wando kansa sanye da facing cap, gudu yake kadan kadan irin na exercise.

"Kai Mutum"

Ta daka masa tsawa. Sai ya juyo ganin ita ce yasa yayo baya daidai ita ya tsaya.

"Baka ganin yadda ka wuce ni kamar zaka bugeni"

"Amman dai ban buge ki ba"

"Eyyye wato har wani gilashin rashin mutumci ka kasa ko? To bari ka ji na fada maka ni a unguwar nan kaf na fi uban kowa tsiwa da rashin kunya, dan naga alamar kamar kai bako ne, ka yi hankali da ni, kuma wannan ba dabi'ar kwarai ba ce ka fito daga kai sai vest sai short wai kana Exercise, ji jikinka duk waje ko kunya baka ji ba? Mtssssss ka ma bata min lokaci ni jami'a zan je"

Ta sa kai ta wuce tana taron Mai Napep ta barshi nan tsaye yana kallon kansa. He see nothing wrong with his dress, a safiya ce kuma ya saba haka sai dai idan nan ne za masa sa'ido. Sai kuma yai murmushi tuna yadda take drama da yan gidansu ashe har a waje za ta iya yin haka.

Har cikin State University ya kai ta ciro kudinshi ta bashi, sannan ta fiddo wayarta ta dake ringing, tai picking.

"Hi Darling"

"Hello Baby"

"Please tell me something tell me something tell me something please"

"I love you"

"Oh gosh.."

Ta zauna bakin wani aji dake kusa da ita.

"I love you too, fatar ka tashi lafiya"

"Lafiya kalau, ya su Umma? Nabeel be taba min ke ba yau?"

"Ya taba, ai kasan kullum sai yayi, na ma bar masa gidan ina jami'a"

Dariya yai sai kuma yai saurin gintse dariyar.

"Babyna da an taba ki kice jami'a ku ne yan 100l"

Fushi tai sai ta kashe wayar, ya raina mata da wayo. Misalin hudu da ta kama hanyar gida, babu ko taro a jakarta dan kudin napep ne ta ci abinci da su a cafeteria, sai dai hakan be hanata tsada mai napep ba ta fada masa inda zai kaita, suna tafe tana nasa fira har suka iso. Bata yarda ya kawo ta har kofar gida ba, ta ce ya sauketa sai ta fita tana fadin.

"Mai Napep ni fa ba zan biya ba, ka yi fira da ni kuma ni matar aurece dan haka ka yi firar kudinka"

Mai Napep din ya yi dariya ya dauka wasa take sai da yaga ta fara tafiya da gaske sannan ya kwala mata kira.

"Ke Malama zo ki bani kudina ko nai miki rashin mutunci Wallahi"

Ta juyo ta dawo.

"Ni zaka ma rashin mutunci? To tsaya"

Ya sa hannu cikin jakarta ta dauko wayarta ta kira Nabeel yana picking ta ce.

"Abban Siyama zo gani nan gurin Dahiru mai nama, dan Napep din da ya kawo ni ya min maganar iska ci, yanzu kuma wai zai taba ni"

"What are you crazy?"

Nabeel ya fada daga can cikin wayar, ita kuma ta kashe wayar tana rawar kafa ta rike kumkuru.

"Ka jira mijina ya zo, zai shuka maka rashin mutumcin"

"Amman ke baki da tarbiya Allah hada ki da warinki"

Ya shiga Napep dinsa ya wuce yana baza mata kura. Sai da daina ganin kurarsa sannan tai dariya ta kama hanyar gida tana kallon yadda hadari ya hadu sama. Ko kamin ta isa har an fara yayyafi da gudu ta shiga gida ko sallamar arziki ba tai ba.

"Allah ya shiryaki ya baki Natsuwa Zinneera"

Cewar Umma ganin yadda ta shigo wani firgi firgi da ita ta jefar da jakar hannunta ta fito da gudu ta nufi bandaki saboda fitsarin da ya cika mata mara. Kamin ta fito daga bandakin han gwace da ruwa kama da bakin kwarya, cikin ruwan ta tsaya tana rawar indiya tana wanka da ruwa sai shafo kanta take da gashin be wuce na fakin ba, tana jujjuyawa kamar wata karamar yarinya.

Duk abunda take yana tsaye jikin windows yana kallonta yana murmushi shi dai tana sashi nishadi for no reason kiriniyarta tana burgeshi, abunda take ko kanenta basa yinsa. Wata uwar tsara aka yi sai gata ta nufi daki da gudu, sai kuma ta dawo da gudun saboda Umma ta korota karta jika mata daki, jikin kofar taje ta tsaya ta durkusa tana ba Umma hakuri tana marairaice fuska kamar zata yi kukan gaske. Wannan karon dariya yai ya jingina da kujerar da yake zaune.


COMMENTS
&
SHARE....

Continue Reading

You'll Also Like

44.7K 1.7K 154
In the town of mystic falls it's always been a quaint town but what some people don't know is that for decades it has been the home of supernatural b...
1.1M 37.7K 61
WATTYS WINNER When her fiancé ends up in a coma and his secret mistress, Halley, shows up, Mary feels like her world is falling apart. What she does...
59.9K 3.9K 52
labari ne a kan marainiya wadda mijinta ya gudu ya barta da ciki, har tsawan shekaru goma sha biyar da en doriya... keep following me.
258K 4.3K 61
This is an unofficial fan-made English translation of We are...คือเรารักกัน (We are... we are in love). Please do not re-translate to any other langu...