MATATACE

By Meemartjj

175K 9.1K 377

A story about an orphan teen GIRL More

Chapter 01
Chapter 02
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 05
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 26
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 40

Chapter 39

4.1K 200 3
By Meemartjj

🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

🇳🇬®
*_ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION📚✍️._*
[❄Dance above the surface of the world,let your thoughts lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty ummeetah, and my fa'ixation._

   *_wanga pages kyauta ne ga dukkan masoyan littafim matatace, a duk inda suke ina musi fatan alkhairi._*

wadanga writers kuna raina

_my janaf_
_Hafnan_
_sis Nerja'art_
_lashminzy_
_miss xerks_
_mhizzphydo_

  *_kai da sauran suma baki daya, musamman writters na kungiyar aboriginal writers, ina muku addu'a Allah ya taimake ku, ya kara basira, fikra da fasaha, much fatan alkhairi, yours meemartjj._*

page 77~78

__________Gaba daya wajen sai da kowa ya juyo da kallonshi kan Suhymah dake zaune zufa na faman kyato mata, dai dai sanda Irfan ya tsaya cak da scissors din dake hannunshi kan dogon pink ribbon din da aka daura tsakanin classrooms din.

  Ummeetah dake bayanshi tayi saurin janye hannun nashi daga jikin al-makashin, wanda yayi sanadiyar faduwan scissors din bisa ribbon din.

  wal, wani hasken shocking ya haska tare da bada sauti bisa igiyan, har zuwa jikin wani electric connection da akayi, a firgice duk wanda ke wajen ya fiddo ido, ummeetah ta kuma jan Irfan baya tana kankameshi a jikinta cike da firgici.

  Suhymah dake zaunen can tana kallon komai ta sauke wani ajiyar zuciya, yayin da aka shiga kallon kallon abin mamaki, da mamaki Abba ya kalleshi yana fadin,,

  "Sadeeq meke faruwa ne?" da sauri yabar wajen shida wasu mutanenshi yana fadin,,

  "Abba bari na duba", dai dai sanda su mummy suka kariso wajen harda suhyma, haj. falmata ta fisgeshi daga jikin ummeetah tana tattabashi, kafun ta dago kai a matukar firgice take kallon Ummeetah da fadin,,

  "me kika mishi ne, nace me kika shirya ma jika nane, duk abubbuwan da kika gama kwace mata bai ishe kiba, sai kin hada da kashe mata yaro kwaya daya tall, me kika nufi dashi neeeeeee?" a firgice Ummeetah ta fiddo idanu tana girgixa kanta da hawaye, tama kasa magana, Abba zai magana aunty mashkura ta riga da fadin,,

  "ban fahimta ba hajiya, ta yaya zaki rika mata wadannan tambayoyin, me Ummeetah ta sani?", haj. falmata dake rungume da Irfan a rude take da abin daya faru take fadin,,

  "dom me baxan tambayeta ba, na farko tace sai dashi zata yanka ribbon din nan, na biyu an tasashi a gaba, gaba daya wannan maci amanar yarinyan ta gama wargaxa mata farin cikin gidanta", kowa ya gama tukewa da mamaki, cike da daurewan kai aunty mashkura ke nuna Suhymah dake tsaye gefe tana risgar kuka da fadin,,

  "a'ah, waishin donme ba zaki tuhume yarinyan kiba, ita da tace karya yanka ribbon din?", zatai magana Abba yace,,

  "kunga ku dakata don Allah, komai zai warware, abi komai a sannu", buden bakin haj. falmata sai cewa tayi,,

  "babu abin da za abi a sannu Alh. Ameenu", sai kuma ta sanya kukanta da gaskenta tana matsar kwalla da gefen gyalle, tare da nuna Ummeetah da hannu take fadin,, 

  "wlhy ke wannan diya Allah baxai barki ba, kin aure mata miji sannan kin mallakeshi, yanxun kuma bansan me kike nufi da danta kwaya daya tal daya rage mata a duniya ba", sai lokaci Suhymah ta dago kanta da fadin,,

  "a'ah mummy kar kice haka", a tsawace take fadin,,

  "toh in bance haka ba mezan ce, itace sillar faruwan komai, kina zaune da mijin kie lafiya, bansan me taxo dashi ba, harta da dukiyar ya mallaka mata gabda daya, komai ya lalace, Allah ya isa tsakininki da kishiy……..."

  da sauri tasa hannu tana toshe bakin mum din nasu, tare da girgixa mata kanta, da hawayen daya wanke fuskanta take fadin,,

  "Mum kie gane Ummeetah bata da laifi ko kadan, ba itace sillar faruwan komai ba", ta nuna mum din sannan ta nuna kanta wajen fadin,,

  "mum mune sillar faruwan komai, mu da muka dauki kishiya makiyiya, muka dauki karan tsana muka daura ma abokiyar zama, abin da yake halastacce, son zuciya da son kanmu yasa mun kasa fahimtar idan har ka samu ta azziki, to mum baka da yer uwan data wuceta kusa da kai", ta numfasa tana sakin kafadar mum din data dafa da rushewa da wani sabon kuka, ta nuna Ummeetah da dan yatsanta tana fadin,,

  "kishiyar dana tsana a rayuwa nah, harna kauce hanya a kanta, mum could yhu believe itace wacce ta taimaki rayuwa nah, ta agaxa mun a lokacin da nake tsananin bukatar agaji, bacin ita mum, ba abin dake ciki na bane kawai abin da zaku rasa, maybe daga cikin har gawa na zaku zo ku dauka a wajen, na cutar da ita iya cutarwa wands bai kamata ace ta taimaka mun ba, mum duk ta mance wannan ta taimaka mun da hannunta na shiga mota sannan ta kaini asibiti, wanda hakan ne Allah ya nufa numfashina na gaba harna rayu", kawai saita zube bisa gwiwowinta tana sanya wani kuka mai rikita zuciya, hannunta ta daga cikin tsananin tashin hankali take yarfawa da fadin,,

  "wayyoo nie Suhymah naga ta kaina, yau mahaifin da nake takama dashi, gashi can cikin nakasa, dukiyar da nake gadara dashi yau babu shi, mijin da nake tunkaho dashi, ashe ma daular ba nashi bane duka", ta karisa maganar cikin gunjin kuka, mutane da yawa jikinsu yayi sanyi, harda mum dinta da itama take ruskar kuka, ashe Ummeetah ce takai diyarta asibiti a wancan ranar, Ummeetah ma dai kuka takeyi idanunta nakan Irfan daya taka daya biyu, sai kuma ya tsaya, Allah sarki be kalli kowa ba a wajen sai mahaifiyarshi yana fadin,,

  "mummy ina jin bacci bacci in ina tafiya", kafun kace kwabo ta rarumoshi jikinta tana rungumewa da kuma sanya sabon kuka, yana wani numfarfashi kamar dole yake share mata hawaye da fadin,,
  "mummy plss kie daina crying, nima ina girma zan gina miki katon makaranta irin na aunty ummee, a'i kina so ko...?" ya karisa maganar a wahalce, da sauri ta shiga girgixa kanta tana fadin,,

  "eh ina so, don Allah Irfan karka tafi ka barni, ka yafe ma mumyn ka kaji, ina sonka wlhy yaro nah", ta karisa maganar cikin sanyin muryan kuka, a firgice kuma take fadin,,

  "Ir……" ta kasa karisa maganar da kyau, saboda hannunshi da yayi luww zuwa kasa, kuma rikicewa tayi tana girgixa shi da kiran sunanshi, kowa a wajen ya rude, Ummeetah ma karisowa tayi ta duka tana kiran sunanshi, tuni hawayen dake idanunta suka kafe, bata san sanda ta fisgoshi jikinta ba ta fara tofa mai duk addu'an da yaxo bakinta.

  ganin ya dan bude idanunshi dake war sai farin na cikin kawai kake iya hangowa, ya sanyata mikewa tsaye rike dashi a hannu, dai dai sanda sadeeq ya dawo wajen da securities din wajen, don su duba taya akayi wannan badakalan shocking din ya afku, a rude yake fadin,,

  "meya sameshi?", ya karisa maganar yana amsarshi a rikice, cikin tsawa ya kuma tambayarsu ita da Suhymah da suka tsaya mishi cirko cirko a gaba,,

  "nace meye ya faru dashi kuma?", duk sai kuma suka shiga kallon kallo ita da Ummeetah, Abba daya matso kusa dashi ya dafa kafadarshi da fadin,,

  "kaga baku da lokacin wannan bayanin, ina tunanin ku wuce dashi asibiti kawai", Suhymah tayi saurin fadin,,

  "a'ah, Abba babu maganin ciwon Irfan a asibiti", cikin mamaki yake fadin,,

  "kamar yaya? " bisa gwiwowinta ta kuma durkusawa dayin kneel down tana fadin,,

  "zan fada muku, zan fadi gaskiya", sosai Sadeeq ya zuba mata idanu, ta rika nuna bakinta da yen yatsu tana yarfa su, alamar tana cike da tsoron abin da zata fada, kafun ta bude baki daker tana fadin,,

  "Sadeeq nie ce, nice Suhymah na bada d'anmu ga kungiya, nice na shiga kungiyan asiri da hannuna na basu first born d'in dazan haifa, duk saboda bana son wata mace ta rabe ka bayan nie, yanxun lokaci yayi da zasu amshe abinsu, don Allah ka taimaka mun", cikin sanyi da karayan zuciya yake girgixa kanshi da fadin,,

  "a'ah ba nasu bane, rayuwanshi na hannun Allah, basu isa su cutar dashi ba da yardan Allah, but suhymah plss kie sanar mun mafarki nakeyi ba da gaske bane, ta yaya za ace my angel zata a'ikata irin wannan danyar zunubin", wani kukan ne ya kuma barke mata tana fadin,,

  "Sadeeq wlhy dagaske nakeyi, a gaban mummy na shiga kungiyan ana gobe daurin auran mu, surayya kawata ita tamun hanya, kuma sunce ma yau za suyie a'iki akanshi, an hada wannan shocking dinne jikin ribbon din, wanda da nake tunanin nie zan yanka, sai in bama Irfan shi ya yanka, don kawai a jingina mutuwar shi da hakan, daga baya kuma sai asan yanda za asa ma Ummeetah laifin", a razane mutane da dama suka fiddo ido a wajen, jie kawai tayi mum dinta ta dafo kafadarta, ta juya sukai 4eyes tana fadin,,

  "Suhymah da gaske kike har lamarinki yakai ga shiga kungiya", sai kuma ta dago tana kallon mummy da cigaba da fadin,,

  haba haj. yagana, ya zaki mun haka kungiyan asiri, wani irin lalacew……..., bata karisa ba tayi kasa luwww tana dafe kirji da hannu bibbiyu, a rude sukai kanta suna kiran sunan,,

   "Mum plss kie tashi", don suma tayi gau a wajen, harda su zahira da suka matso wajen suna  faman rera kuka, hankulan jama'a da dama ya tashi, yayin da wasu suka jiku da kallo da sauraran da abin mamaki.

   bai tsaya wata wata ba, bisa cewar Abba da yayi, su wuce da Irfan din islamic clinic din DR. zainul Abideen kawai, tunda kwararren likita ne a wannan fannin, ko ya samu wani kulawan ta wannan bangaren, bai musa ba suka wuce shida babban likitan, wanda shi kanshi yake cike da tausayin d'an yaron.

  suma su suhymah tattagan mahaifiyarsu sukayi zuwa asibiti, haka taro ya watse, yayin da jama'a suka dauki darasi da dama akan abin daya faru, wasu kuma suna kara jin kaunar Ummeetah da jinjina mata, musamman da Suhymah ta bada labarin nan.

   ***
  Kai tsaye suka wuce dashi clinic din, suna isa suka fara mishi duk abin daya dace, sun jima a kanshi, cikin ikon Allah numfashin shi ya dawo dai dai, sai kuma ya fara mimmika yana firgice firgice, da fadin,,

  "daddy zasu tafi dani, sunce mummy ce ta bani su, gasu nan sun zagaye nie, daddy plss help", kuka yakeyi da wadannan surutan, sai da shima ya koka ma dan nashi, wannan dalilin ne ya sanya sukai mishi allurar bacci ya samu ya natsa, nurses ne har hudu aka bama tsaron case dinshi, don clinic ne mai tsadan gaske.

   ***
  Itama haj. falmata suna zuwa wani general hospital suka fara bata taimakon gaggawa, sai da tayi good 5hours kafun ta farfado, Suhymah na zaune jugum bisa wata white plastic chair, yayin da kanninta ke rakube bisa wasu design chair dake daga gefe, ko wacce taci kukanta ta koshi.

   mummy ma na manne jikin bango rataye da yer jakarta a hammata, haj falmata data fara dawowa dai dai, ta miko hannu tana fadin,,

  "wash wash, ku bani Irfan, don Allah jika nah guda daya tal karya mutu, ko harya…….." da sauri suhymah ta ruko hannun nata daga zaunen da take, tana sanya sabon kuka da fadin,,

  "Mum plss kiyi hakuri, Irfan bai mutu ba, bana so wani abu kema ya sameki", duk ita da uwan suka sanya kuka, su zahira ma suka matso kusa da mahaifiyarsu suna matsar kwalla, ta mutsutstsuke idanunta da kyau tana dan numfasawa da kokarin dagowa, da sauri suka taimaka mata ta zauna, ta dan dube site din da mummy ta matso tana mata sannu tare da basarwa, cikin dan shashsheka take fadin,,

  "haj. yagana kin cuceni, kinci amana tah, ban taba tunanin zaki iya yarje ma Suhymah ta a'ikata irin wannan mammunar laifin ba, kungiyan asiri habaaaa abin yayi yawa", mummy dake daga gefe ta share hawayenta itama da fadin,,

  "amma yayah duk don ta samu farin ciki nayi, banyi don in cutar da it...…"

  "sai dome!", haj. falmata ta fada cikin tsawa, tana juyowa site din da mummyn take da cigaba da fadin,,

  "kiyi don farin ciki, to gashi ya koma bakin ciki, yau wa gari ya waya, ko da baki da laifi, nice dana sakar miki yarinyan, gashi nan kin kaita kin baro, ke kie shiga kungiyan mana, ko kuma kikai maimuna ta shiga inda dadi", cikin zafi itama mummy ta goge hawayenta tas tana fadin,,

  "kai yayah ya isa haka, ya zaki dauki laifin gaba daya kie daura mun, ce nayi kece wacce na taso na gani akan dabi'ar bin gidanjan malamai, kuma ke kika daurani akan wannan tubar, tun ina karamata iyayan mu suka mutu, ke kika goyani, na kuma taso kika daurani akan akidar tsanar kishiya da mai mata, wannan dalilin ne ya hanani yin aure da wuri, ganin duk masu zuwa wajena masu mata ne, sai daga baya da naga ina neman yin kwantai na rufa ma kaina asiri na hakura na aure Alh. Aminu, tunda na riga dana lura auran mai mata na cikin kaddarar rayuwana, zuwa wannan lokacin kuwa na kware da zuwa gidajan malamai, ko dan a'ikena da kika sha yie, to yanxun kuma meye laifina don na tafiyar da yerki akan dabi'ar da kika koyar dani", wani kuka haj. falmata ta sanya da fadin,,

  "amma na rantse ban taba shiga kungiya ba, kuma baxan taba a'ikata hakan ba, amma kefa kina kallo gudan jini na ta shiga, kika kuma kasa hanata, haba haj. yagana wace irin rayuwa ne", mummy dake cigaba da zubda hawaye tace,,

  "yanxun nie ake daura ma laifin bakomai kiyi hakuri…….." bata karisa ba haj. falmata ta nuna mata kofa da fadin,,

  "kinga futa, maxa kie bace mun a nan", zatai magana wasu nurses suka shigo suna fadin su rage muryansu, tare da tausasa haj.falmata wanda akace jininta ya hau amma take faman zazzaga masifa, hakanan mummy taja kafa ta futa zuciyarta na kuna.
 
   ba tasan me yasa yer uwan nata za taga laifin taba, bayan ita din goyan tane, itama can nata bangaren kuka ta kuma rushewa dashi, tana mai tsananin takaicin rayuwa data rike kanwarta da yerta a bisa wannan dabi'a.

  mummy kam reception ta nufa da ninyar barin asibitin, sai dai tana sawo kafa cikin reception din taci karo da wasu yen samari su biyu dake tsaye gefe suna magana rada rada, jin sun kira sunan muheet ne ya sanyata ja ta tsaya waje daya, daya daga ciki yana fadin,,

  "baksow wai kai ya aka yine ka barshi harya kai tsawon wadannan kwanakin a dakin ka?", dayan dake shafa gantalallan sumar kanshi yayi dan tsaki yana fadin,,

  "hmmm kadai bari, nifa na rasa inda su kaje suka dawo shida mamzet, sunsha duka jikinsu ina fada maka gayu duk tabbai, duk yanda naso mamzet ya fada mun meya faru, shegen kie yayie, ya sababa shidai ya gudu, amma wannan dan taurin kan saiya bukaci kayan a'iki, ya rika banka ma kanshi kwayoyi, kai muheet shege ne", ya fadi maganar da dan karfinshi, kafun kuma ya tausasa murya yana cigaba da fadin,,

  "kai gayu ina fada maka ranar farko daya sha sai da yayi almost 2days yana bacci, yana farfadowa ya kara narka ma kanshi, shie nefa tunda ya fara bacci sai jiya ya farfado, amma fa ko dan yatsanshi bai iya dagawa, ganin har yau bai motsa bane sai surutu bakan gado yakeyi, yasa kajie nace ka taimakamun mu kaishi asibiti, nie tsoron da nake jin mishi, kar yaxo brain dinshi ya tabu saboda shaye shayen daya ringa yie", dayan yace,,

  "kai nie kuma ba wannan ba, tsoro nah daya ace mu mukai mishi wani abu, kaga baksow nifa zan gudu, kaima ina maka wannan tunanin kawai mu sabe", shiru ya danyi kafun yace,,

  "hakane, nie kaji bani da kudin dazan cigaba da dauwainiya dashi ma, insun gaji sa kira family dinshi", daga haka suka sakai suna kokarin barin wajen, da sauri mummy tasa ihu tana fadin,,

  "d'anah ne, don Allah ku kaini in ganshi", sai lokacin ma baksow ya lura da ita, don yasan mahaifiyar muheet din nesa ba kusa ba, ba musu sukai mata jagora hade da nurses din da suka juyo ihunta, duk suka rankaya tare, suna zuwa kofar dakin suka nuna mata ta shige suka samu suka sulale, ta shiga nurses din na biye da ita da faman jera mata tambayar,,

  "shine wannan?" a'i mummy bata san sanda ta saka kuka ba, tana yarda jaka gefe da zube gwiwowinta bisa kasa gadon, ganin hannu muheet duka biyun a daddaure, sai faman zuba surutu yakeyi ba kai ba kafa, cike da tausayin dan nata take fadin,,

  "na shiga uku, na bani nie yagana ban lallace ba, Alh. Aminu kaga abin da kaja mun ko, sai da nace ka bincikar mun halin da dana yake ciki, amma kayi burus da maganar, nie gashi ye'maca ce ba abin dazan iya, fisabilillahi jubi yanda d'ana ya dawo", ta karisa maganar cikin matsinacin kuka, sudai nurses sai suka koma a'ikin rarrashi da ban hakuri.

  ***
  Sanda maami itama taji labarin abin daya faru wajen taron, har hawaye sai da tayi don tsaban takaicin wannan lamari, tana kuma kara gode ma Allah, da tayi hikimar tashi tsaye da addu'a sosai akan danta.

  Ummeetah kam itama tasha kuka har kanta na ciwo, daker aka Samu taci wani abu sannan tasha magani, gaba daya tunaninta nakan Irfan da babanshi, Sosai yaron ya bata tausayi, duk da su aunty batula da suka je, sunce jikin nashi da sauki.

  Zaune take gefen gado tana shayar da zahra nono, yayin da yen uwant keta harhada kayansu don gobe zasu koma, itama sun kammla shirya Mata Nata Kayan saboda tare zasu wuce, aunty Amrah sai tsiya take musu wai taga alamar duk sun kosa su gudun musu da ita ne.
 
  Aunty batula data shigo dakin ta zuba ma Ummeetah idanu dake shifidar da zahra, fuskanta dauke da damuwa, itama ta zauna cikinsu da fadin,,

  "Ummeetah yadai ko jikin ne?", murmushi tayi cike da basarwa tana fadin,,

  "A'a aunty batulah bakomai", munat data dan fahimce wani abu tayi saurin fadin,,

  "zaki uncle sadeeq ne KO"?, zaro ido Ummeetah tayi cike da kunya, janan ma ta sako nata da fadin,,

  "Allah sarki matar baffantah, tana tunanin mijin tane", tuni tasa hannu ta rufe fuska, aunty mashkura data dauki zahra tana kokarin sauya mata kaya zuwa marasa nauyi na bacci, ta jefa musu harara da fadin,,

  "Kunji kunya kuna manyun yayi". Aunty batula na dariya tace,,

  Wlhy fa, kinji tashi ma kije kie kai mishi abinci yana sashin baki, daga nan ma kudan zanta", dariya aka sanya, yayin da Ummeetah ta manne jikin gado cike da kunya, aunty Amrah itama cewa tayi ta tashi su hibba su rakata, ita dai ta kasa tashi, sai da aunty mashkura ta mike taja hannunta tana fadi,,

  "oya tashi kie gani, amma karki dade kinji", kanta ummeetah ta gyada alamar gamsuwa, ta yafo mata wani babbar gyale bisa doguwar rigan dake jikinta, kafun ta futa ita dasu hibbat, sai tsokanarta su munat keyi, aunty mashkura na rama mata.

  suna zuwa bakin kofan site din su hibbat suka sabe, da kallo kawai ta bisu suna mata dariya, kafin ta numfasa rike da wani dan karamin basket ta shiga ciki.

  fayau babu kowa a falon shiru, don haka ta nufi bedroom din dake facing dinta kai tsaye, sai da tayi dan jim rike da handle din kofan da yake a sakaye, tana juyo tattausar muryanshi dake fadin,,

  "faruk kuna hauka ne, donme last week kunce biyar sun mutu, yau kuma kuce har 7, haba wani irin shashanci ne wannan", duk da maganar fada yakeyi, amma cikin taushin murya, yayi dan shiru kafun yayi dan karamin tsaki yana daurawa da fadin,,

  "taya zaku rika barinsu suna kwanciya, kunsan da sun kwanta wasu ne zasu bie ta kansu, ko tausayin hakkin rai ba kwayi, toh kunga bana son sakarci wannan kayan ba nawa bane, shin baku ganin irin tafiyar dasu muslim sukeyi ne, da wuya suje su dawo suce mun ko dabba daya ya mutu, next time idan hakan ta kara faruwa, to ku tabbatar zan yanka ma kowa tara kuma saiya biya", daga haka yayi dan shiru.

   hawayen dake idanunta suka karisa silalowa, duk wadannan abubbuwan yana yine saboda ita da rayuwar wasu, gaba daya sai taji wani sabon wani abu ya lullube dukkan jikinta, ta numfasa sanda ta juyo yana cigaba da fadin,,

  "yanxun kace yau raguna 130 kuka dawo dasu ko?" sai yayi dan shiru, kafun yace,,

  "ouk good, plss ku kara sanya himma, kasuwa biyu kawai ya rage mana, daga next monday, sai wacce zata zo gabda salla, plss ina son wadannan manyan a samu su shige duka, koda zaku rage 2to3k ne daga kudin su........."

  bude kofan da Ummeetah tayi ne ya sanya shi dagowa a slow motion yana zuba mata idanu, juyawa tayi ta dan rufo kofan, kafun ta cigaba da takowo inda yake zaune, bisa wata yer tattausar kujera dake gefen gado, ya kishingida bayanshi da jikin kujeran, kafarsa daya nakan daya, yayin da yake mammatsa yen yatsun kafar dake bisa dayan da hannunshi.

  cigaba yayi da amsa wayarshi, alamar baya son ya katse magana, daker ya iya kakalo mata murmushi, don shi yasan irin kuncin da zuciyarsa ke ciki a yau dinnan, yana kallonta ta dire basket din a kasa, dai dai sanda ya sauke dayan kafar dake bisa jikinshi, yana dan mimmike yen yatsunshi duka.

  pillow ta jawo bisa gadon, ta sauke bisa carpet din dake gefen gado, duk ta gefen ido yake binta da kallo, ta zauna bisa pillow din cikin natsuwa tana tankwashe kafafu tare da jawo kafarshi daya ta soma mammatsa mishi, a dan razane ya dago yana dan janye wayar daga kunni, sukai 4eyes ta kauda nata, amma shi saiya kasa.

  ya wani lumshe ido yana budewa, sanda take cigaba da mishi massaging kafar har zuwa yen yatsunshi, ajiyar zuciya ya sauke tare da cigaba da wayarshi hankali kwance, ya dan jima yana wayar yawanci duk akan business dinsu ne, kafun ya yanke wayar.

  idanu kawai ya zuba mata sanda take masta mishi dayar kafan kamar karta daina, hannunta ya ruko a hankali yana dawowa saman carpet din shima ya zauna da fadin,,

  "nagode matar mutunci nah, sannan shugaban mata nah har a gidan aljanna in sha Allah", murmushi ne ya subuce mata, tana mai jin dadin sunan sosai, cikin sanyin murya take fadin,,

  "yaya jikin Irfan?", shiru ya danyi da damuwa sosai a fuskanshi, kafun ya sauke wani ajiyar zuciya da murmushin yake, yake fadin,,

  "toh da sauki, amma bema san wanda ke kanshi ba, Humaira har yanxun ganin abin nake kamar a mafarki, sai dai kawai mu bishi da addu'a", kamar zatai kuka, don tuni har idanuwanta sun tara hawaye take fadin,,

   "in sha Allah babu abin dazai sameshi, yanda kullum kake kokarin wajen tallafa ma rayuwan yeyen wasu, haka Allah zai tallafi rayuwan naka, in sha Allah zamu cigaba da mishi addu'a, Irfan yafi karfin su da yardar Allah", sosai yaji dadin kalamanta, koba komai sun sanyaya mishi zuciya, a hankali ya jawota jikinshi yana shafa bayanta da rarrashi, saboda kukan dake neman kwace mata,,

  "plss karki wannan kukan", ya fada da dan damuwa, kafun ya daura da fadin,,

  "likitan daya dubashi ya sanar mun jininshi nada karfi, sannan duk da kasancewarshi yaro yana da rukon ibada, don haka baxa su iya mishi ba", ya numfasa kafun ya cigaba da fadin,,

  "yanxun matsala daya ne firgitan da yakeyi, shima saboda jininshi da suka fara samu ne, shi yasa yake irin wadannan abubbuwan, wanda maybe kuma ya iya shafar kwakwalwanshi, ammma ina tunanin in sha Allah nan da 3days zan futa dashi kasan, baxan iya juren ganin Irfan a haka ba", muryanshi yayi zafi alamar tsantsan baci rai yake cigaba da fadin,,

  "har yanxun na rasa dalilin dazai sa suhymah ta a'ikata irin wannan mummunar laifin, duk irin so da tattalin dana nuna mata saita hadani da irin wannan kazantar, ban taba tunanin son kanta harya kai haka ba, ya zama tilas in nuna mata irin kuskuren da tayi a rayuwa", a sanyaye ta dago kanta tana zuba mishi ido kafun tace,,

  "hakane, ta a'ikata babban laifi, amma don Allah Baffah kayi mata haku……." wani kallo daya bata ne, ya sanya ta hadiye raguwan maganar ba tare data shirya ba,,

  "tashi mun a jiki" ya fada maganar cikin zallar bacin rai, a sanyaye ta janye jikinta, yana cigaba da fadin,,

  "zan iya samun wani abin inci, don yunwa nake jie?", da sauri ta jawo basket din data shigo dashi tana fara saving dinshi abincin, ta kammala zuba mishi white rice din tare da sanya miya, cokali ta sanya tana dibowa da kawowa wajen bakinshi, amma saiya amsa yana wani hada rai da fadin,,

  "no thanks", shiru kawai tayi tana kallonsa kamar tai kuka, ganin yanda yayi cukun cukun da rai, ta ruko hannunshi tana mishi magiya da fadin,,

  "Baffah plss don Allah ka kawo mana in baka", banxa ya mata sai kuma ya saki spoon din cikin plate din, serious yake kallonta da fadin,,

  "Humaira yau rana ce me muhimmaci a wajena, ranar dana dade ina jiran zuwanta, ranar farin ciki a gareni, amma suhymah ta lalata komai da wannan bakin cikin data dasa mun, kamar matata ce za ace tana wani kungiyan asiri", ya girgixa kanshi da fadin,,

  "unbelievable, sannan ke kina maganar wani hakuri ko?", da wani irin huci ya karisa maganar, narai narai tayi da idanuwa, daga bada hakuri sai ya zama rigima, ta dan runtse idonta tana budewa, kafun ta kama kunninta daya tana kyalle mishi idanuwa da fadin,,

  "ouk am sorry if i say anything wrong", tasa hannu tana dibo abincin tare da kaiwa bakinshi tana fadin,,

  "don Allah kaci abinci, kace fa yunwa kake jie", bai tanka mata ba sai zuba mata idanu da yayi yana bin gashin kanta daya futo ta dan gaba gaba baki sumul da kallo, ta dan langwabar da kanta cike da shagawaba take fadin,,

   "haba mijina na alkhairi, plsss ka amsa mana, kaji Abban Irfan......"

  "sai kuma wa?", ya fada yana tsareta da idanuwa, sai data dan taba fuska kamar mai kuka tace,,

  "zahra'u", yanda tayi maganar ne ya sanya dan murmushi ya subuce mishi yana fadin,,

  "wai nikam shin daxun wajen taron nan da nasha bunch of kisses, me kike fada, sai naji kamar kin fada wani abu, dan maimai……" bai karisa maganar ba saboda abincin data zube mishi cikin baki, sai daya hadiye lomar sannan yace,,

  "kai Humyhra zaki mun dure ne?", a kagare tace,,

  "aunty mashkura tace kar in dade, kuma kaga dare nayi", bai kara tankawa ba harta kammala bashi abincin, bisa gefen gado ya koma ya zauna yana binta da kallo, lokacin da take karisa tattara kayan abincin a natse,,

  kai komai nata ma na daban ne a rayuwa, ya ayyana hakan sanda wayarshi dake ije gefe yasa kara, wani dogon tsaki yayi sanda yaga mai kiran nashi, kai tsaye ya rufe wayar baki daya yana jifa da ita cikin kunan rai, da sauri ummeetah ta dago kai suna hada ido, tayi sauri saukar da nata, sosai ya koma ya zauna bisa gadon yana kishingida bayanshi da pillow, yayin da hannayeshi ke rungume bisa kirji, duk sai taji babu dadin yanda ya bata rai, juyawa tayi dai dai sanda yake fadin,,

  "zo nan Humaira", ya fadi maganar cikin taushin murya, dole tazo a hankali tana dofanewa kusa dashi, ya dan yunkuro yana ruko tafin hannunta da fadin,,

  "meye faru kuma naga kin wani bata rai ne?", a sanyaye tace,,

  "bakomai, kawai dai bana son ina ganinka cikin bacin rai ne?", idanu kawai ya zuba mata sanda ya tallafo kuncinta da tafin hannunshi daya, sai bakinshi kawai taji saman nata, da sauri ta runtse idanuwanta tana kuma kankameshi saboda lulawan da suka fara yie wani duniya.

  kai mutumin nan wlhy solonshi na daban ne, gudun karsu zurma da yawa ne, ya sanyata dagowa daker tana janye jikinta daga nashi,,

  "Baffah plss dare yayeee", da wani kankance ido ya dago yana kallonta, sai kuma yayi baya yana rungumota a kirjinshi,,

  "baby nah zanyi kewar kie, plss in kunje can kie kula mun da kanki da my sweet zahra kinji", yayi kissing saman kanta da fadin,,

  "i luv yhu soo much baby"

  "i luv yhu too my lollipop", ta fada cikin rawar murya, dagota yayi yana mai da mata rigarta dai dai, sannan suka mike.

  tare suka jera har zuwa bakin kofan site din maami, itafa dole sai dai ya barta a nan, shi kuma yace har daki zai rakata, kamar tasa ihu, daker ta samu ya barta a nan, sai da yaga ta shige sannan ya juya.
 
 

  ***
  Shagargarin ranar su ummeetah suka wuce ita da yen uwanta zuwa Adamawa, duk da sai da suka biya ta asibitin da Irfan yake taga jikinshi, har yanxun dai yana kan alluran da suka mishi, tasha kukanta harta gaji tare da jera mishi addu'a, da wannan suka dauki hanya, su munat ma kowa ta koma gidan mijinta.

  hankulansu bai kuma tashi ba, sai da suka jie halin da muheet ke ciki, don zuwa yanxun har an yanke shawaran wucewa dashi secartry, don samun cikakken kulawa, Allah sarki sadeeq shine wanda ya rattafa hannu akan komai, har aka wuce dashi can.

  Abba kuwa yayi nadaman auran mummy yafi a kirga, dama tun ranar daya jiyo tana waya da wani malami, kan a juya musu kan sadeeq sai yanda suka yie da dukiyarshi, yaji wani mugun tsanarta, wanda shine dalilin da yace sadeeq din ya bude sunan makarantar kowa ya gani, sai kuma ga wannan ya biyo baya, 80% mummy ce wacce ta taimaka wajen rugujewan tarbiyan yaron, dole ne kuma yanxun tasan matsayinta a gidanshi.

  ***
A wannan ranar ne sadeeq yayi reporting case din kungiyan su suhymah, wacce aka tasa keyarta har gidan da suka ije don meeting, an kuwa samu sa'an sun hadu baki daya suna gudanar da taro akan yaron dake nemar fin karfinsu, wanda hakan shi zai iya kawo rugujewan wannan kungiya.

  sanda sadeeq yaga irin muhallin nasu duk wasu abubbuwa tsifface tsifface, da jajayen doguwar rigar dake jikinsu, ga wasu tambulan a gaban ko wannesu dake dauke da wani red tik liquid, wanda baxai iya tantance jini ne ko menene ba oho, tabbas kuwa wannan ya kara bashi tabbacin abin nasu da gaske suke.

  ranar dai dubunsu ta cika, kunya iya kunya sunsha, ba kamar shugaban kungiyan wacce mijinta ya kasance babban malami, harda hawayen bakin ciki sai da yayi, yana mai tsantsar mamaki, itama kam ta muzanta iya muzantuwa, aka tarka tasu baki daya zuwa mota, mazajen da suma su kaji sunan matansu suka rika tir da halayensu.

   tijara iya tijara police ke musu, tare da daddaka musu tsawa sanda zasu dura su a cikin mota, harda surayya dake faman ciccika, suhymah dai dake baya baya sai kuka takeyi, muryanta harya dishe.

  yana daga cikin motar daya jawo da kanshi, ya jingina bayanshi da kujera tare da daga kanshi sama don tsaban takaici, ya numfasa yana dagowa sanda yake dad'a jujjuya wata yer brown envelope a hannunshi, ajiyar zuciya ya sauke kafun ya bude handbag dinta dake ije gefe daya, ya sanya mata ciki sannan ya maida jakar ya rufe.

  hankalinshi ya mayar wajen police din dake waje, ta cikin window motar, wani police ne ya kallenta bayan sun kare sanya su a ciki ita zata shiga last, a yatsine yake fadin,,

  "madam pls jeki, ke an riga da an gama warware case dinki da mijinki", a raxane ta kalleshi tana kallon inda motar sadeeq yake a pake, shi kuwa sai yai saurin kauda kanshi, cikin sanyin jiki taxo ta shiga motar tana rufe kofan, murya a dakushe take fadin,,

  "sadeeq nagode daka taimaka mun, wlhy tsoro nake baxan iya zaman prison ba", fuska babu walwala yayi ma motar key yana fara driving da fadin,,

  "karki damu, ba wannan hukuncin bane wanda ya dace dake", cikin sanyin jiki ta kalleshi sosai, shima juyowa yayi yana facing dinta da fadin,,

  "ina son kie fahimce wani abu, ba a shuka alkhairi da sharri", ya karisa maganar yana maida hankalinshi ga titi, cikin dan shashshekan kuka take fadin,,

  "sadeeq me kake nufi, duk fa akan sonka nayi komai", a zafafe yake fadin,,

  "duk don kina sonah saiki kauce hanya, sai ki biye ma son zuciyanki, suhymah tell me something, ina ce ranar da kika fara cemun kina sonah, ba a kwana ba sai dana maida miki da martani, kinsan saboda menene?", kanta ta girgixa da sauri tana nokewa jikin mota, ganin yadda yake masifa, sai daya tausasa murya kafun yace,,

  "saboda ina matukar girmama wanda yace yana sonah, atleast mai sonka yafi makiyinka wanda kullum shi burinshi yaga bayanka ne, amma ba don wani abu ba, naji kunyar matsayin kie na ye'mace harki furta mun kalman so, sannan in kasa amsa miki a ranar, sai ina ganin kamar bai dace ba, na daure hakanan na maida miki da martani, gradually kuma sai naji kin fara kwanta mun a rai, saboda son da kike nuna min, duk wannan bai isaba sai kin hada da tabaibayeni da igiyoyin sharri"

  ya karisa maganar yana dukan steery, idanunsa sunyi jaxur, tuni hanjin cikinta suka kada, komai da ya fada gaskiya ne, bata iya magana ba, sai kuka data sanya, harya faka motar a haraban asibitin da aka admiting mahaifiyarsu, ta share hawayenta tare da daukan jakarta, cikin sanyin murya take fadin,,

  "sadeeq i luv yhu, i luv yhu soo soo much, har abada kuma baxan daina sonka ba, rashin ka zai zama babban tabo a rayuwa nah, zan iya jure komai amma……"

  "enough", ya fada cikin daurewan fuska, kafun ya daura da fadin,,

  "madam plss ina da abubbuwan yie a gaba nah, zaki iya adana kalamanki in mun hadu next", a sanyaye ta kuma gyada mishi kanta daga haka ta fice daga motar, tana daga mishi hannu da fadin,,

  "bye sweetheart", daga mata kai kawai yayi idanunsa a lumshe, sai daya tabbatar ta rufe motar ta juya sannan ya bude idonsa, ya jima yana kallonta harta shige ciki, kafun yaja motar ya bar wajen.

  itakam cike da murna ta karisa shiga asibitin, bata taba tunanin zai bi ta sauki irin haka ba, ashe sadeeq yana sonta har haka.

*~(hmmmm, alkhairi yaafeee inxa kai shukawa).~*

  _2days bani da caji a waya nah, kuyi hakuri shi yasa kuka jini shiru._


*fatan alkhairi*

share
comment
vote

*Matatace 2019*
Na meemartjj

Continue Reading

You'll Also Like

215K 24.5K 33
ရိုးရိုးအချစ်ဇာတ်လမ်းလေးတစ်ပုဒ်ပါပဲ
97.5K 12.4K 77
English title - The Green Tea's Crushing Victories in the '70s [ လက်ဖက်စိမ်းမလေး၏ ၇၀ပြည့်နှစ်များဆီက အောင်ပွဲများ ] translation novel
1.6M 66.6K 78
ငါလား.... စိတ်ချ...... နိဗ္ဗာန်ရောက်ရင်လည်း မင်းကိုပဲ ချစ်နေအုံးမှာ.......... သုနေတင်ထွဋ် ကမ္ဘာပျက်သလို လေပြင်းမိုးသံတွေထ...