MATATACE

By Meemartjj

175K 9.1K 377

A story about an orphan teen GIRL More

Chapter 01
Chapter 02
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 05
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
chapter 31
Chapter 32
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 26
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40

Chapter 33

3.8K 196 0
By Meemartjj

🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

page 65~66

__________A hankali take sauke ajiyar zuciya, tare da share Hwayenta, sanda mummy ke dialing number haj. biswa da video call, sosai suka natsu lokacin da kiran ya fara shiga.

  hoton hamshakiyar macace ya bayyana, tana zaune bisa wasu tsadaddun dinning chairs, taji gwala gwalai a hannu, wanda ya futo ta cikin hannun zumbulelen hijjabin dake jikinta har kasa, cikin salama mummy ta fara kai gaisuwa da fadin,,

  ina gaisuwa shugabar kungiya, da fatan an tashi lafia?, cikin kasaitaccan murmushi ta amsa,,

  barka dai haj. yagana, inace me jiki dai taji sauki?, ajiyar zuciya mummy ta sauke tana fadin,,

  to sauki da dama, dama dai kan lamarin nan ne da mukai magana, uwar kungiya a duba mana, a'ikifa ya lallace, komai ya sukurkuce, plsa ki duba…………, da sauri ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu da fadin,,

   dakata, ban fahimce kiba, mun riga da mun gama wannan maganar tuni dake, haj. yagana ko kun manta ranar da kuka zo, a gaban idonki yerki ta shiga kungiyar mu akan biyar bukatanta da yarjejeniyar da mukayi akan kar wata mace ta rabi mijinta, an jaddada mata tace ta yarda, baxan manta ba ana gobe daurin auranta, to sai yanxun zata dawo mana da hannun agogo baya, ko dan taga yanxun ta haifeshi ne harya girma, shine tak……,,

   da sauri suhymah ta fisge wayar, da wasu hawaye da suka wanke mata fuska tana fadin,,

   wlhy ban yarda ba, munyi yarjejeniya akan zan samu biyan bukata nah, kun zalunce nie kunce zan samu yanda nake so, a karshe kuma ina zaune saiga mijina da mata harda cikinta, ta tsananta kukanta da fadin,,

   haba haba, wannan zalunci yayi, yawa, wacce irin kungiya ce wannan mara adalci, to nie gaskiya yanxun bana bukatar komai daya wuce d'ana, bani da burin daya wuce inga na haifi yara da yawa, suna kaiwa da dawowa, amma yanxun mafarki na ya zama ba gaskiya ba, Irfan ne kawai wanda ya rage mun inna kalla zanji dadi, plsss na rokeku kubar mun d'ana, baxan iya rayuwa ba Irfan ba, wani dan murmushi tayi kafun tace,,

  baxai yuyuba suhymah, kin riga da kinyi sakaci, kin riga da kin bama kungiya d'anki, yanxun shi kai d'aine ya rage akan hanya, kuma kungiya nada babban buri akan d'anki, sai dai kiyi hakuri……,,

  karya ne, suhymah ta kara katseta da kuka tana fadin,,

  wlhy baxan baku Irfan ba, sai dai kuyi duk abin da za kuyi, ga mari ga tsinka jaka, da wanne zanji, to wlhy Irfan yafi karfin ku, in kuna amai kuna lashewa sai dai kunci kanku, azzalumai marasa mutun……,,

   da sauri mummy ta fisge wayar tana datse kiran, saboda ganin yanda suhymah ke neman juya lamarin ya koma na tashin hankali, jikin mummy ta fada tana sanya wani kuka maicin zuciya da fadin,,

   wayyo Allah na aunty na shiga tara, na bani ban lalace ba, da sauri aunty ta zungureta tana dagowa, da sallama ya shigo rike da hannun Irfan, ta koma da baya tana kuma rushewa da kuka, gaba d'aya sai yaji zuciyarsa ta karaya.

  ya rasa me yasa ta kasa daukan kaddarar daya shigo rayuwansu, tsam mummy ta mike sum sum sum ta fice, kusa da ita ya zauna yana fadin,,

   suhymah wai har yanxun ba zaki daina wannan kukan ba, kinga yanda kika dawo?, harara ta zabga mai cikin kuka tace,,

  kace haka mana, a'i kaima sadeeq harda kai, ban taba tunanin zaka iya tarayya da wata y'e mace ba bayan nie, ban taba tunanin haka daga gareka ba, sadeeq duk irin son da nake maka, ko da baka da laifi, nawa yafi yawa dana dauka yardana na mika maka, ta karisa maganar da matsanancin kuka tana fadawa saman kirjinshi.

   wani tausayin tane ya kara kamashi, ya rungumota a hankali yana shafa bayanta da rarrashi, ta d'ago raunannun idanunta tana zuba mai, cikin muryan kuka take fadin,,

  sadeeq ina sonka, sonka yaja komai, kuma mannata yayi da kirjinshi tare da sumbatar saman kanta yana fadin,,

  nasan haka suhymah, nima ina sonki, plss ki saurara da wannan kukan, inba haka ba zuciya na zai iya fashewa, don Allah ki dauka abin daya same mu a matsayin kaddarar rayuwa, a shirye nake da in saki farin ciki, xan baki dukkan kulawa, kie manta da abin daya faru, plss my suhymah take everything easy kinji, ajiyar zuciya ta sauke a hankali, tana ruko hannun Irfan ya shigo tsakaninsu, tsam suka hadu suka rungumeshi tana fadin,,

  sadeeq plsss kabar mun Irfan in tafi dashi Abuja, ina bukatar d'ana kusa dani, plss kar barni gobe in tafi da kayana, nisawa yayi kafun yace,, 

  d'anki ne, kema kina da iko dashi, na yarje miki ki tafi dashi, kuka ta kuma sanyawa sanda take rungume d'anta a jikinta.

    shagargarin ranar aka sallamesu, Abuja suka tattara su kayi, bayan ta tasa keyar d'anta, duk da kukan da yakeyi zai zauna wajen maami, kin yarda tayi, don wani soyayyan shine ke ratsa jini da jijiyoyin jikinta a yanxun, da wannan suka tafi, haj. falmata na ikirarin ba zata dawo ba, har saiya shirya rabuwa da ummeetah.

 
         
         

***
  Bisa sallayah take zaune, bayan idda sallar walhan da tayi tana rera karatun al-qur'an, tana karshen suran da take karantawa ta jiyo muryanshi, da suke gaisawa da dattijuwan yer a'ikin maami data sanja, tsam ta runtse idanunta kafun ta bude tana cigaba da karatunta.

   sai data kai karshe sannan ta rufe qur'an din, tana maidawa ta ije a ma'ijiyarsa, ta mike daker tana nade dadduman, kasancewan yanxun cikinta na cikin na wata bakwai kenan, da tutturawa ta samu bakin gado tana zama.

  duk sai taji batai murna da zuwan shiba, don satinshi biyu kenan rabon data sashi a ido, duk da yana fada mata a'iyyuka ne sukai mishi yawa, amma wannan karon yayi kamari, daker dai ta iya mikewa ta nufi falon tana wani faman bata rai.

  zaune yake cikin black suit, yana daddanna wayarsa, sai data matso gab dashi sannan ya dago kai yana kallonta, harta samu waje kusa da kujeran da yake ta zauna da mishi sannu da zuwa, ya amsa mata da murmushin yana daurawa da fadin,,

  ranki shi dad'e barka da futowa, wani murmushi ne ya subuce mata, tana fadin,,

  Baffah ina kwana,,

  lfylau matar Baffah, ya fada yana dan rankwafowa da shafar kumatun ta yana fadin,,

  i like this ur kumatu fa, murmushi ta kuma yie, yana cigaba da fadin,,

   yah,  kinje asibitin jiya?, a sanyaye tace,,

  eh naje, ya lafe a kujera yana fadin,,

  hope dai anyi hoton babu wani matsala?, tace,,

  anyi, sunce komai normal, cike da annurin fuska yake fadin,,

  that's good, in sha Allah lafia zaki haihu, cikin sauki, duk muna miki addi'a, kanta ta jinjina kafin tace,,

  to Allah yasa, yace,,

  Ameen, maami bata nan ne?,,

  eh taje angwuwa, hibba kuma taje school exam, amm amm, ta fada sai kuma ta cije, dago ido yayi da fadin,,

  ummhmm, ina jinki da wata matsala ce?, girgixa kanta tayi kafun tace,,

  a'ah, dama gidan aunty munat ne su hibba zasu yau, shine nace ko zan iya binsu,,

  no sweetheart, kiyi hakuri kisha zaman kie, mijinki baiyi accepting ba, kamar zatai kuka take fadin,,

  to amm……, katseta yayi yana kokarin mikewa da fadin,,

  umm, nie kinga tafiya na, dama daga Abuja nake, nace barin na biyo mu gaisa, bcos those days ayyuka sun mun yawa, itama mikewa tayi tana fadin,,

  to sai anjima, da sauri yake fadin,,

  au bako dan rako mrs, ba tace komai ba, suka fara tafiya, a bakin kofa suka tsaya tana mishi dan bye bye, ya kafeta da ido kafun yace,,

  Humaira wai irin rakon da zaki mun kenan?, d'an bata fuska tayi, kafun tayi aune ya tallafo fuskanta da hannu daya yana sakar mata wani light kiss a labba, a tare suka lumshe ido suna budewa kan na juna, ya sakar mata fuska yana dan sosa sumar kanshi da d'an yatsa, tare da wani kankance ido, yana fadin,,

  kishirya ina tunanin dan anjima zamu futa, misalin 8pm kinji, karki manta fa, kafun tayi magana ya fuce yana daga mata hannu, ajiyar zuciya kawai ta sauke tana komawa ciki.


***
  Sanye take cikin wata maternity gown na atamfa, mai zanen furanni blue&white, saita sanya farin hijjabi, yayin data futo da hannayenta ta hannun hijjabin, tana rike da yer handbag dinta, ta saka wasu yen white plat shoe masu kyau, sai turo baki takeyi da kunkunai,,

   shi Baffahn nan dama da gaske yakeyi, zuwa anguwa da wani dare, ko kunyan maami baya jie, koma meya fada mata oho, nikam banma san inda zamu ba, ta cigaba da kunkunanta tana tafiyanta cikin takun natsuwa dajan hankali.

   kyam ya tsaya daga jikin bangon da yake lafe, yana zuba mata ido, harda baki da hanci, yayin da shaitan ke cigaba da ayyana mishi abubbuwa da dama akanta.

   lallai ko da bala'i saiya samu abin da yake so, ko da wannan tsinanan cikin ne, sai dai ta mutu bayan nan, kai bama zai iya barin komai bros dinshi ya fishi akai ba, dole this time ya nuna mishi akwai banbaci.

  firgit yayi sanda yaji muryan hibba na kwala mata kira, a d'an tsorace ta juyo, tana dariya ta iso tana mika mata wani leda, da mamaki tace,,

   na menene wannan?, tace,,

   uncle sadeeq ne yaje in dauko miki kayan kie set daya in biyo ki dashi, zaro ido ummeetah tayi kafun tace,,

  kai wani irin kaya, nie da zamu je mu dawo...……,, tana wani dariyan ta wuce ta koma, tana daga mata hannu da fadin,,

  ke dai matar Baffahn mu sai da safe, a kwana lafia, harda gwalanta, ummeetah na banka mata harara, muheet daya gama sauraran abin daya faru yaja dan tsaki da raya,,

   ba dole ka rika kwasanta kuna futa ba, ka samu ganima, juyawa kawai tayi ta cigaba da takawa zuwa wajen motar, kamar wasa taji tafiya ta bayanta, kafun tayi aune taji ansha gabanta, daf ya rage bai hada jikinshi da nata ba, dai dai sanda ya futo daga cikin mota, jin shirun yayi yawa yana nufowa inda suke.

   muheeeeeet, ya fada a tsawace, da sauri yaja da baya, itama ummeetah da jikinta ke kyarma kusa da mijinta taxo ta lafe, a zuciye ya daga kafa sai isa gaban muheet, Abba ya futo daga site dinshi, cikin takun manya ya iso wajen yana tambayar,,

  lafia?, da sauri muheet ya dafe kuncinshi da fadin,,

   Abba wai daga na ganta nace mata sannu, shine ya kod'a mun mari, a razane suka zaro idanu waje, sadeeq ya bude baki zaiyi magana, Abba ya daga mishi hannu a zafafe, alamar ya dakata, ummeetah da tayi kasa da kanta tana fadin,,

   ina wuni Abba?, a dakile yace,,

   lafia, daga haka ya yafito muheet, yana rungume kafadarsa suka bar wajen, juyowa muheet yayi yana nuna sadeeq da hannu, tare da mushi alamar *zaka gane,* daga haka ya juya abinshi.

  ranshi bace ya koma motar yana kifa kanshi da steery, shifa abin da muheet yayi mishi ba shine damuwan shiba, yanda Abba yaki saukowa, kullum ya lura ma dada hawa yakeyi, itama ummeetah a natse ta bude site din kusa driver ta shiga, sunfi 10minutes a haka kafun yaja motar suka bar gidan.

***
T unda ya fara driving babu wanda yace tak, har suka isa tsararran sabon gidan da yaji fenti da futullu, sai kamshin amare yakeyi(lol).

   gate man daya gane ko wanene, yana yashe baki ya bude mai gate suka kutsa ciki, yana idda packing ya zare seat belt din jikinshi, kafun ya dan nisa yana juyawa bayan seat, wani brown envelope ya zaro yana mika ma ummeetah da fadin,,
  
   ga wannan in zamu futo ki bama munat, a sanyaye tace,,

   Baffah na menene?,,

   gudummuwan kice, ya fada a takaice yana futa motar, itama futowa tayi ta bi bayanshi da kare ma gidan kallo.

  sosai sukai farin ciki da ganin juna, amarya anyi kyau, anyi wal wal, sai tsiya take ummeetah bata zo da wuri ba, ango ma ya futo sun gaisa nan suka zauna suna taba hira,

  nan da nan aka cika su da kayan ciye ciye, sai da suke shirin tashi ummeetah ta mika ma munat envelope din da take fadin,,

  toh na menene kuma wannan?, da murmushi tace,,
 
   gudummuwan mune yaxo a late, munat ta zaro ido, yayin daya jefa ma ummeetah harara, don ba haka sukayi ba, Abdullah daya amsa envelope din yana murmushi da fadin,,

  ahhh sweetheart, bari muga wannan kyautar ta musamman ce daga mr&mrs, cike da d'oki munat tasa tsalle akan kujera, tana rangado musu godiya, Abdullah na tayata.

   kusa da ummeetah taxo ta rungumeta tana kuma godiya, shi kanshi mijinta ya yaba da wannan kyautan, kyautar gida sukutum, yasan kuma a'ikin sadeeq ne, sun dan kara jumawa, kafun suyi sallama su tafi.

   Gidansu dake new extension suka nufa, a farfajiyar gidan ya faka motar sai wani ciccin magani takeyi, bude motar yayi harya sa kafa d'aya waje, ya juyo yana kare mata kallo yanda ta hakimce a mota, abinma sai yaso bashi dariya……...,,

  madam yadai futo mana, bata rai tayi da fadin,,

  Baffah wai me za muyi a nan ne?, karamar dariya yayi kafun yace,,
 
   oh tambaya ma kikeyi, to bari na zagayo sai in baki amsa, da sauri ta diro daga motar, ya kariso inda take yana mika mata tafin hannunshi, a hankali ta saka nata cikin nashi, yai murmushi yana rankwafowa wajen kunninta da rada mata,,

  yawwa babynah muje kiban honey ko, turo baki ta kuma yie, tana runtse hannunta cikin nashi, haka dai suka karisa ciki sai wani bata rai takeyi.


***
Shagargarin ranan kasancewan weekend ne, yasa sai 10am suka kammala shiryawa, duk da ita ummeetah sai faman korafi take suxo su tafi, a mota ma kuma bata rai tayi ganin sun nufi wani wajen again ba gida ba.

A A sadeeq general marchant and building materials trading company, shine abin data karanta sanda yake karisa yin packing motar a farfajiyar wajen, ya kashe motar, lokacin da taga ya maida hankalinshi sosai kan wayanshi.

  tun tashin su da safe yau ta lura yana cikin farin ciki da annashuw,a murmushine ya subuce mishi akan fuska, kamar ance leka,,

   my angel, shine abin data gani a saman text massage din da aka turo, da sauri ta kauda idanunta, yayin da kirjinta ke wani irin bugawa, ya dan jima kan wayar kafin ya saka aljihu yana kallonta da fadin,,

    jibi su Irfan zasu dawo, don an kammala da processing makarantar dazai fara a nan garin, da murnanta tace,,

   oh my Irfan, nayi missing dinshi sosai, yace,,

   koh, tare da suhymah zasu dawo, in sha Allah, rassss, wani faduwar gaban ya sameta, amma saita fuske da murmushi sosai take fadin,,

   ouk, Allah ya dawo dasu lafia, da fara'a ya amsa da,,

  Ameen, ummeetah tace,,

   shi yasa yau naga kana ta fara'a aunty suhymah zata dawo, gaskiya na tayaka murna, galala ya tsaya yana kallonta kafun yayi pointing kanshi da fadin,,

  nie sadeeq kika fahimce ina murna?, ta jinjina kanta da fadin,,

  sosai ma, tunda ta tafi fa ka rage yawan fara'a, yai dan shiru kafun yace,,

  hakane, keko Humaira ina laifi wanda yace yana sonka, a'i yafi wanda yaki ka ko?, a sanyaye tace,,

  eh hakane, a zuciyarta amma tana kuma juya kalaman nashi, ya futa motar yana fadin itama ta futo.

  tare suka jera ciki, yana sake da hannunshi a nata, ummeetah sai kunya takeji, ko ina suka wuce ana faman kwasan gaisuwa, ba a maganar idanun ummeetah a wannan office din da aka kawatashi, sai kalle kalle takeyi ta samu waje bisa wani sofa chair tana zama.

   gaban wani dispenser ya nufa yana dibo mata clean water, cikin wata yer glass cup, kafin ya dawo gabanta ya mika mata, ta amsa da godiya ta sha kusan rabi kafin ta sauke, hannunta yaja har gaban kawataccan office table din, yana zaunar da ita a a'inihin kujeran oga at the top.

  gefenta ya tsaya yaci serious yana jibge mata wasu document, da nuna mata inda yake bukatar sa hannunta, wasu lokacin irin wadannan abubbuwan na bata mamaki, sun dan jima kafun taji kanta ya fara sarawa, ta yamutsa fuska tana dagowa da fadin,,

  Baffah nidai wlhy na gaji, ta karisa maganar a shagwabe tana mika mishi pen din, yer dariya yayi yana komawa saman table din ya jingina da fuskantan ta, kafun yace,,

   hmmmm lallai da sauran ki, tun yanxun, ta dafe kanta da fadin,,

  Allah Bffah kaina har ya fara ciwo, amsar pen din yayi yana fadin,,

  ouk kawo, amma dole zaki kara himma, don nasa a nemo miki gurbin karatun a jami'a, da zaran kin haihu in sha Allah zaki daura karatun kie, cike da murna take fadin,,

  oh my god, thank yhu so much my Bffah, ya dan ja kumatun ta da fadin,,

  Business Aadministration nake son ki karanta, kina son course din?, da blushing tace,,

   sosai ma, duk abin da kake so, nifa shi nake so, zuba mata idanu kawai yayi da wani lallausar murmushi, baiyi aune ba sai jin tafin hannunshi yayi yana tallafo fuskanta, da daura bakinshi kan nata.

   a hankali salon nashi ya fara tafiya da ita, tasa nata hannun tana dafe nashi kuncin, sunyi nisa a haka, basu fargaba sai da wayanshi ya fara ringing da sauri ya zare bakinshi, yana dafe kanta, kafun ya ciro wayan,,

  Abba, ya fada yana mikewa, tare da daidaita natsuwanshi yana kara wayar a kunni da furta kalman sallama, daga can site din shima amsa mishi yayi yana daurawa da fadin,,

   kana ina ne kai da yer mutane?, da dan in ina, yake fadin,,

  amm amm Abba, dakatar dashi yayi da fadin,,

  kaga dakata, ba wani dogon turanci nake bukata ba, na baku nan da good 20minutes ku taho gida, sannan kuyi da jiki, don ana jiranta ne,,

  to Abba, kawai ya iya amsa mishi dashi, daga haka suka sauke wayar yana jujjuya kalaman Abban na karshe, basu wani bata lokaci ba ya rufe komai suka futo, dukkansu zuciyarsu na dukan uku uku.

***
  A rikice ya futo motar sanda ya faka ya hangi driver na idda zube trolley ummeetah cikin booth, yana futowa Abba ya kariso inda yake tare da dafa kafadarshi yana fadin,,

  muje ciki zanyi magana da kai, zai wata maganar yace,,

  umm umm, bansan musu muje kawai, ummeetah dake ta d'ayan gefen ta gaisheshi, ya amsa mata yau babu laifi, yana dorawa da fadin,,

  maza jeki wajen maamin ku, gata can tana jiranki, ba musu ta amsa da,,

  toh, tana wucewa inda taga maami na tsaye, ita da wasu da bata gama tantance ko su suwaye ba, shima Abba yabi suka wuce ciki.

   cikin sanyi ta karisa wajen maami da fadin,,

  maami gani, maami ta rungumota cike da tausayi tana fadin,,

  ummeetah kiyi hakuri kinji, gida zaki bie yen uwan Affahn ki, in sha Allah nan daba da dad'ewa ba sadeeq zai xo ya daukeki, a firgice ummeetah ta dago kai tana duban wadannan nan mazan su biyu, Baffah Audi da salihu, sai yatsine yatsine sukeyi, wani kunci ne ya dabaibaye rayuwanta tana ayyana,,

  me ake nufi, kodai za'a rabani da mijina ne?, bata dame bata wannan amsar, hawaye ke neman kwaranyo mata, amma tuni taji wani dauriya tana dakewa da fadin,,   

  toh maami, in sha Allah nie mai biyayya ce a gareku, sosai taji dadi, kamar zatai kuka, tace,,

  Allah ya miki albarka, ummeetah banda yanda zan yine shi yasa, amma in Allah ya yarda babu abin dazai faru da auranku, kie kula da kanki, duk wani abu da zaki bukata nasa an miki packing dinsu, kiyi hakuri da rayuwa kinji,,

  tom maami, ta fada da muryan kuka, da wanna maami ta rakata har wajen motar, gaba ta shiga yayin da yen uwan Affah suka make a baya, su dai sai dadi sukeji sun damki kudi, wai su kulata da ita, ba sai taga kudin ba.

    ummeetah naji na gani driver yasa kai ya fuce daga gidan, har sannan maami na tsaye cike da tausayinta.


***
shikam gaba daya zufa ta gama jikashi banda,,

  innalilah wa'inna ilaihir raji'un, ba abin da yake nanatawa, kafun ya dago raunannun idanunshi da fadin,,

  Abba don Allah ka taimaka mun, ka tausaya mun, wlhy zasu iya cutar da ita, har mahaifinta ya koma ga Allah, basu taba kaunar shiba, kayi hakuri zan……,,

  dakata Abubakar, kana nufin kace basu son yer dan uwansu ne?, ko kuwa ita yarinyan akwai wadanda suka wuce y'en uwanta, bana son shirme, ina lallaba kane kawai saboda biyayya da tarbiyan dana sanka dashi, ya numfasa kafun ya cigaba da fadin,,

  baxan zuba ido ina kallon ka ba, da yarinyan da ban gama tabbatarwa matar ka bace, ina bukatar yin bincike na wani lokaci, idan harna tabbatar da gaskiya, to tabbas mata ta zama naka, amma for now, zaka dakata da ganinta na wani dan lokaci, bada yamuna ba idan har kaje inda take, ko kasa wani naka yaje inda take, a firgice sadeeq ya dago kai, yace,,

  yesss, hakama maamin ku nace, ban laminta wani nata yaje ba, don haka ka kiyaye, na basu isassun kudi da zasu ciyar da ita su kula da ita, har lokacin dazan kammala bincike na, daga haka ya mike yana barin wajen, cikin tsantsan damuwa yake fadin,,

  Abba don……, hannu ya kuma daga mishi daga juya mai bayan da yayi, yana fadin,,
 
  Abubakar bana son musu, ka kiyaye, zan kuma fada da babbar murya in maka gwari gawri, idab har kaje inda take, ko kuka hadu, to ban yafe ba, ina son ka sani Aure ba wasan yara bane, yana gama fadan haka yasa kai ya shige bedroom dinshi.

  kanshi ya dafe da hannu bibbiyu, dai dai sanda maami ta shigo falon da sallama, da sauri ya dago kanshi, sulalewa yayi daga zaunan da yake saman kujera yana zube gwiwanshi bisa carpet, da fadin,,

   maami don Allah kie taimake mu, wlhy basu kaunar tah, karsu cutar da ita, cike da tausayin dan nata take kallonshi, inama tana da yanda za tayi, to amma ya ta iya, ta numfasa tana fadin,,

  sadeeq kaga, bani da yanda zanyi akan lamarin nan, nima Abban ku ya samun doka, addu'a kawai zaku cigaba dayi, Allah ya kawo komai da sauki, ummeetah kuwa in sha Allah babu abin dazai faru da ita sai alkhairi, ka cigaba dayin addu'a za kaga dai dai, sannan kayi kokarin zama d'a mai biyayya, ka daure kayi mishi wannan biyayyan kaji, na wani dan lokaci ne.

  kanshi ya jinjina ma maami, ta wuce ta bie bayan Abba, yafi karfin 10minutes yana zaune a wajen, kafin ya mike daga baya yabar falon da wani irin tashin hankali, yanda ummeetah zatai rayuwa a wajen nan kawai yakeji.



***
Hankalin ummeetah bai kuma tashi ba sai da taga da gaske ana yanka daji, wani kuka ta fashe dashi, har suka isa tana faman yie.

   tuni Baffah ninta suka futo sukai shigewansu cikin gida, ta jima kafun ta futo daga motar, driver na sauke mata kayanta a nan wajen cike da tausayin ta, yana kammalawa yaja motar ya juya.

  hijjab dinta kawai tasa ta rufe fuskanta tana rero kuka, tare da cogewa a wajen, nan da nan kuwa yara suka taru suna kare mata kallo ita da yen akwatunan ta guda shida, guda biyu nata ne na da, sai kuma set d'aya mai guda hudu, cikin wanda su mummy sukai mata sunan kayan lefen muheet, don ita din akabar mawa.

    sai da tayi ma isarta sannan ta bude idanunta, tunani ma takeyi ta inda zata fara, can kuma ta saki baki tana kare ma wasu ye'yen shanaye kallo, da suke faman guje gujen su hankali kwance, da alama an tafi kiwo ne aka barsu.

  ta numfasa tana kare ma rugar tasu kallo, ba laifi an samu ci gaba, da kara cukuwan gidaje, karan mashin taji ta waiga da sauri, kusa da ita mai mashin din yaci burki, enmmata biyu da sukai goyo da kayan tallansu, suka sauka suna sallamarshi, caraf tace,,

  sa'ade, wacce ke goye da yaro a baya ta zuba ma ummeetah ido da mamakin yanda tasan sunanta, kafun su gama mamaki sunji tana rangado musu yaren harshensu tana musu bayani, tuni karime tasa tsalle da fadin,,

  lah sa'ade kawar kice da innar mu ke fada mana, ta gidan Baffah ali, kinga kofan gidansu ta tsaya, itama sai lokacin wacce aka kira da sa'ade ta gane ummeetah, kawar ummeetah ce sosai jikan gidan liman din rugar tasu, cike da d'oki suke gaisawa da juna, sai bin ummeetah take da ido wacce ke leka babynta dake goye a baya.

  yara suka ixa ma kayan tallansu, ana tsinke mata da surutu, ba abin dake tashi sai yaren fillo, ta fara bata labarin itama tayi aure a can wata ruga dake jahar sokoto, yanxun ma wankan gida ta dawo, sai tayi wata takwas sannan za a kuma yin wani sabon bikin ta koma, yanxun haka tana talla ne ta samu kudin kayan daki.

  galala kawai ummeetah tayi tana jin wanga al-ada, sun jima kafun su karisa ciki, dama tun a waje mutanan gidan suke faman lekenta, tana shiga kuwa suka fara binta da wani kallo wanda ba zata iya fassara kona menene ba.

   Baffahnta Audi ne yasa dutse ya balle kwadon dake jikin tsohon dakin Affanta, yana zuga mata masifa da nan ne dakinta, ta rika mamaki yanda taga sunxo suna rabar da kudin da aka basu suyi mata amfani dashi, mahaifiyarsu sai zage zage takeyi.

  bata bi ta kansu ba, su sa'ade suka taimaka mata suka gyara dakin, babu koma ciki, sai dai yaji suminti, sharewa sukayi ta goge da ruwa, ko dan abin shimfida basu bata ba, sai da sa'ade taje gidansu ta a'iko mata da wata tabarma da yer matashi, abinci ma su suka kawo mata.


***
  Idanun ummeetah bai kwakwalo ba sai da dare yayi, kasa zaune tayi a dakin, wani tsoro ya cikata, kawai saita sanya sabon kuka bil hakki da gaskiya, a hankali ta sulale bisa sumintin dake dakin, sai ta rika tuno Affahnta kamar yanxun daya sha fada mata a cikin dakin nan, cewa,,

  mahakurci wata rana mawadaci ne, hawayenta ta share tana furta kalman,,

  hakane Affah nah, nayi kewar ka mahaifina, daga haka ta mike ta shimfida tabarman, trolleynta ta bude ta zaro wani kakkaurar dadduma ta shifida bisa, sannan ta kara da zannuwanta, ta ninke wasu ta sanya su sama matashin da sa'ade ta kawo mata.

   a hankali ta maida kai ta kwanta tana sakin ajiyar zuciya, ta lumshe idonta sanda take tuna, jiya uwar haka tana kwance cikin jikin mijinta, koma sai yaushe zata kara ganinshi oho, dan tsaki tayi tana kauda tunanin da fara jero addu'an bacci, kafun wani bacci barawo ya saceta.

***
    bangaren shima kaiwa da dawowa kawai yakeyi a tsakar dakin, kafun ya koma yana zama bakin gado, kamar zai kwanta sai kuma ya mike, yana jefa pillow bisa carpet din dake gefen gadon.

  kwanciya yayi bisa carpet din, can kuma zaraf sai ya mike zaune, gani yake kaman bai mata adalci ba inhar ya kwanta saman carpet din, don baisan a inda zata kwana ba ita.

  saman tyles ya koma, yana daura kanshi bisa pillow, zuciyarsa na faman kai komo da tunanin halin da yer jama'a zata kasance, ganin baccin ya gagari idonsa, ya sanya shi mikewa ya dauro alola tare da kabbarta sallah, don shi yake tunanin zai fiye mishi a rayuwa.

  Asubar ranan daker ya mike tsaye, saboda rikewan da bayanshi yayi, gashi sanyin tyles din had'e da damuwan da yake ciki, na neman saukar mishi da wani zazzabi, da wannan ya gabatar da sallah asuba.

  karfe 7am dot a falon Abba yayi mishi, cikin shigar zuwa office, shima Abban yana falon wanda ya futo don ya saurare abin dake tafe dashi, a natse ya dago kai, cikin kwantacciyar murya yake fadin,,

   Abba don Allah, wani alfarma naxo nema a gareka, dukkan hankalinshi nakan sadeeq din yace,,

  ina sauraron ka, Allah yasa befi karfi na ba, da sauri yace,,

  in sha Allah baifi karfin kaba Abba, dama alfarma nake nema, shin ko zan iya ma ummeetah hidima, ko da banje inda take ba, insa a mata, Abba kaga barinta a wajen nan ita daya yana da hadari, shiru ya biyo falon na kusan minti uku, kafun Abba ya nisa da fadin,,

  shikenan hakan yayi, zaka iya mata hidma, sannan na sassauta maka, zaka iya sanya wani daga bangarenka daka amince da ita/shi, suje inda take, amma da sharadi, ban yarda naji ance kun hadu ba, ko kaje inda take, da sauri yake fadin,,

  Abba in sha Allah zaka sameni mai biyayya a gareka, nagode da wannan damar daka bani, Allah ya huci zuciyarka, da murmushi kan fuska yake fadin,,

  tashi kaje, Allah ya muku albarka, mikewa yayi da fadin,,

  Ameen, daga haka yasa kai yabar falon, sashin maami ya nufa, don yana bukatar ta samo mishi wata amintacciyar dattijuwan daza taje ta zauna da ummeetah.

   bai jima sosai a nan ba, ya futo yana wucewa wajen motarshi da dialing numbern dake rubuce da mahfus, yana dagawa suka gaisa ya daura da fadin,,

  yawwa mahfus ka gane, plss ina son wasu ma'aikata daga cikin masu gina estate din nan na Abuja, shiru yayi kafun yace,,

  a'ah, ina bukatarsu da yawa, wani ginin gaggawa nake son suyi mun, kubar koda kadan ne daga cikinsu a nan, yayi dan murmushi sanda yake fadin,,

  aha, good, daga nan ya sauke wayar, yana cigaba da dialing wasu numbern, harya shiga motar da driver yaja suka wuce.


*fatan alkhairi*

share
comment
vote

*Matatace 2019*
Na meemartjj

Continue Reading

You'll Also Like

2.8M 142K 58
Start Date>>>> 1.4.2020 End>>>20.5.2020 แ€€แ€ญแ€ฏแ€šแ€ทแ€บแ€˜แ€€แ€บแ€€ แ€กแ€แ€ปแ€…แ€บแ€แ€ฝแ€ฑแ€•แ€ฑแ€ธแ€แ€ฒแ€ทแ€œแ€Šแ€บแ€ธ แ€•แ€ผแ€”แ€บแ€›แ€แ€ฒแ€ทแ€แ€ฌแ€€ แ€”แ€ฌแ€€แ€ปแ€„แ€บแ€™แ€พแ€ฏแ€แ€ฝแ€ฑแ€แ€ฒแ€ทแ€œแ€ฌแ€ธ แ€™แ€„แ€บแ€ธแ€กแ€™แ€ฏแ€”แ€บแ€ธโ€‹แ€แ€ฝแ€ฑแ€€แ€ญแ€ฏแ€‘แ€•แ€บแ€•แ€ผแ€ฎแ€ธแ€™แ€แ€ถแ€…แ€ฌแ€ธแ€”แ€ญแ€ฏแ€„แ€บแ€แ€ฑแ€ฌแ€ทแ€œแ€ญแ€ฏแ€ท แ€„แ€ซแ€‘...
314K 8K 76
"แ€•แ€ฐแ€แ€„แ€บแ€ธแ€œแ€ฑแ€ธแ€€แ€˜แ€ฌแ€œแ€ฒ" "แ€€แ€ญแ€ฏแ€€แ€ญแ€ฏแ€ทแ€กแ€•แ€ญแ€ฏแ€„แ€บ" "แ€€แ€ญแ€ฏแ€€แ€ญแ€ฏแ€แ€ญแ€ฏแ€ทแ€€แ€›แ€ฑแ€ฌแ€˜แ€ฌแ€œแ€ฒ " "แ€™แ€ฑแ€ฌแ€„แ€บแ€”แ€พแ€™" "แ€Ÿแ€ฌ..."
1.6M 70.4K 37
adult story(18+) แ€žแ€„แ€บแ€ทแ€žแ€แ€„แ€บร—แ€›แ€ฏแ€•แ€บแ€žแ€ฑแ€ธ 9.1.2023...