MATATACE

By Meemartjj

174K 9.1K 377

A story about an orphan teen GIRL More

Chapter 01
Chapter 02
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 05
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 26
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40

Chapter 27

4.8K 200 1
By Meemartjj

🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

page 53~54

_____________Kwance tayi abinta kan gado, kirjinta ta kifa bisa pillow sai english novel din dake hannunta tana karantawa, wani baccin ne barawo ke neman tafiya da ita, sai wani lumshe ido takeyi.

  iskan dake hurowa cikin dakin ne, ta window dake facing waje, yake dada san yata cikin yanayin bacci mai cike da ni'ima, kadan kadan kuma take jin karar bude windown, yayin da design white cottons din dake windown suka shiga yawo suna hurowa ciki.

   abin sai ya zame mata kaman a mafarki, kamshin turarenshi ne ya sanyata bude idanunta tarr, tare da dagowa a hankali tana juyawa site din da windown yake, sosai ta zaro ido tana dan murmushi, shima murmushin yakeyi tare da kashe mata ido daya.

   zaune yake bisa windown daya hauro ta ciki, ya juya ma waje baya, hannunsa daya rike da wani milk din leda, yayin da dayan yake mata alamar taxo gareshi, mikewa tayi cikin natsuwa shikam saiya zuba mata ido, tana dan gyara pink straight skirt din dake jikinta, sai wata bakin rigar sanyin data sanya a sama mai zip ta gaba, saboda sanyin da ake tsalawa.

   yen labbanta sai faman spakling sukeyi, gashinta a fake yake cikin wani bakin hulan sanyi, saita futo da sauran ta kasan hulan, tayi kyau cass da ita, ga hasken da fatarta ya kara ya amsheta, kusa da dan shi ta matso tana fadin,,

  Baffah sannu da zuwa, yama kasa magana sai cewa da yayi,,

  come on give me a hug, kaman jira take ta fada jikinshi, tana sakalo hannayenta duka biyun ta wuyanshi, tare da hardesu cross, fuskanshi take dan kallo dake kasan nata, sai lokacin tasan da kuma jin kunya, tana boye fuskanta a gefen wuyanshi, hakan ya taimaka wajen kara hada jikinsu waje daya, murmushi sosai yakeyi, yasa dayan hannun yana runguman bayanta, a hankali kuma ta dago, dai dai sanda yake fadin,,

  baby yhu too much happy, idanun kasa kasa tana wani kalan murmushi tace,,

  saboda ina tare da Baffah nah, sosai kalaman suka ratsa can kuryan zuciyarsa, ya kuma tallafo fuskanta da fadin,,

   da gaske kike, kai ta daga alaman eh, idanunta rufe wai ita nan kunya, har lokacin da murmushinta mai bayyanar da dimple dinta, kallonta kawai ya tsaya yie, jin shirun yayi yawa ne ya sanyata dan bude idanunta, kakkaurar white sweater din dake jikinshi take kallo da kuma white p~cap din daya sanya bisa kanshi.

   hannayenta ta sanya ta bayanshi tana jawo hulan dake hade da sweatern, ta daura mishi bisa p~cap din, sai kuma ta jawo tafukan hannunsa da suke a kankakare, saboda snow din dake sauka.

   drower ta wuce tana dauko wasu kauraran handgloves tazo ta sanya mishi, da fadin,,

  Baffah plss ka daina futa ba gloves, kasan snow yayi yawa, bana son kayi mura fa, shidai komai takeyi binta kawai yake da kallon burgewa, itakam duk wannan abin taki yarda su hada ido, can kuma saita dan wayance da kallon ledan daya shigo dashi tana fadin,,

  lah ka siyo mun popcorn dinne?, ajiyar zuciya ya sauke yana dago ledan da fadin,,

  ba dole ba uwar gidan Baffanta sadeeq, zoki zauna in baki a baki, murmushi tayi tana kokarin barin wajen ya jawo hannunta da fadin,,

   ina zaki, dan war tayi tana fadin,,

  zan dauko abin zama ne, hannunta ya jawo sosai yana daurata bisa kafafunshi da fadin,,

   come on, a'i baki da wani abin zaman daya wuce wannan, duk sai taji kunya ya kamata, kafun kuma ta gyare, a baki yake bata popcorn din ana cie ana yer dariya.

   can kuma ta amsa kayanta ta shiga cie, kallonta kawai yakeyi, dabi'unta da dama sun sanja, ciki harda yawan cin abincin da takeyi yanxun, leda biyu ta cinye tana cin na ukun sai kuma ta ije, ya kalleta sosai da fadin,,

  ya dai, harkin gama cin popcorn din?, fuska ta dan taba tana fadin,,

   a'ah, ban koshi ba, amma yanxun ina cie da yawa, sai inji zuciya na ya fara tashi, duk kuma sai inji bana son cie kwata kwata, na rasa me yasa yawancin abin da nake son cie, yanxun na daina sonsu, sosai ta karisa maganar kamar zatai kuka, shidai kallonta kawai yake da murmushi, wani farin ciki na zaga dukkan wani sashi na jikinsa, yana ji a jikinsa akwai wani alkhairi a tare da ita, hannunta ya ruko cikin nashi yana wasa da yen yatsunta kafun yace,,

  sorry kinji, in sha Allahu hakan alkhairi ne a gare mu, wani kallon rashin fahimta take mishi, yace,,

   yes kie yarda da magana na plss, yer ajiyan zuciya ta sauke tana dada lafewa a jikinshi, kanta ya manna a sama kafadarsa yana shafa gashinta dake cikin hula a hankali, a kunni yake rada mata,,

  baby plss zansha melon, ba tare data dago kaiba take fadin,,

   tom muje kitchen sai in hada maka,,

   a'ah, ya fada da daurawa da fadin,,

  nie naki nake so, ya karisa maganar da daura yen yatsunsa biyu bisa wuyanta, yana mata wani irin waiwayi dasu, sai lokacin ta fahimce inda ya dosa, ba shiri ta fara kokarin mikewa da fadin,,

   girki fa zanyi, time yana kurewa, ya mike shima yana kallon agogo da fadin,,

  karki damu zan taya kie, a'i da sauran time, ganin da gaske yake yasa ta fara yarfa hannaye, murya cike da shagawaba take fadin,,

  nidai plss ka rufa mun asiri, aunty suhymah na jiran ka nefa, tsayawa yayi kawai yana zuba mata idanu, ganin yanda take abu kamar wata yer baby, wani murmushi yayi yana nufa kofa, duk tunaninta futa zaiyi, sai taga yasa ma kofan key a hankali.

  sweatern jikinshi ya fara cirewa, tare da cire p~cap din dake saman kanshi, ya zare takalman dake kafanshi yana karisawa inda take tsaye har lokacin tana zuba shagwabanta,,
 
  Baffah plsss……, bata karisa ba taji ya rungumeta tsam, cak ya dauketa ya dora saman gadon, sannan yani bayanta, daganan basu fahimtar duniya da suke, tuni ta mika kai bori ya hau, rayuwa sukai mai cike da annashuwa tare da inganci.

   tare yace sai sunyi wanka, ummeetah harda kukanta, bai saurareta ba ya sungumeta, duk yanda taso zillewa, sai da suka kare wanka nan tare, yace kuma daga ranar haka zasu cigaba dayi.

  tsaf suka kammala shiryawa, sai wani cinno baki takeyi daga tsayen da take gaban mirror tana karisa shiryawa, hannayensa taji saman cikinta, yayi mata zobe dasu, tare da rankwafo da kanshi ta saman kafadarta, kasa kawai tayi da idanuta, cikin kunni yake rada mata,,

    karki damu, ba zata fahimce komai ba, ya karisa maganar da wani lumshe ido, kafun ya bude yana daurawa da fadin,,
 
  ashe haka wanka tare da matayake da dadi, gaskiya an barni a baya, ko ya kika ce, kanta ta dan dago caraf suka hada ido, ya kashe mata ido daya, da sauri ta kauda nata, hannunsa ya zare daga jikinsa yana amsar dankunnin da take kokarin sanyawa, tare da karisa sanya mata.

  thanks, ta fada tana kokarin barin wajen da fadin,,

  bari na duba maka in aunty suhymah bata falon, sai ka futa, murmushi yayi yana fadin,,

   god job dear, a hankali ta bude kofan, can ta hangeta tana sambada barcinta bisa kujera, ta juyo tana hada tafukan hannunta waje daya, tare da mishi alamar tana bacci, takowo yayi ya dauki sweater dinshi yana maidawa, tace,,

   ka manta hulan,,

  ohh, ya fada so silent yana dan zare ido waje, kafun ya sanya yana karisawa inda take tsaye, tsayawa yayi yana pointing lips dinta, sannan ya nuna nashi, kallo daya tayi mishi kafun ta manna mishi kiss din bisa kunci, tare da marairaice fuska alamar yaje mana, murmushi ya sakar mata, kafun yasa kai ya fice, ta sauke ajiyar zuciya tana rufe kofan tare da fara clearing dakin. 
  

   Sai daya futa can waje, ya karisa gidan DR. khamis da yayi packing din motarsa, ya dauko sannan ya dawo, karar motar ne ya tada ita daga bacci, sanda ya shigo tana kokari tashi zaune, da murmushi ya kalleta yana mata magana.

   agogo kawai take kallo dake manne jikin bango, ganin yanda lokaci ya tafi ne ya sanyata dalla mishi wani harara, tare da mikewa ta shige bedroom harda dogon tsakinta, da baki kawai ya bita kallo, sosai yanxun wasu lamuran nata ke bashi mamaki.

   can kuma ta futo ta fara sauke ma ummeetah nata jarabar bata daura musu abinci da wuri ba, wunin ranar haka tayishi rai bace, ita dai shiru ta mata, don yanxun gani take bata da lokacin tama.

   sanda ta cigaba da yanda take so abinta, zuwa yanxun ta fara samu yencin kanta, da tace tana son kaza, bazai taba samun natsuwa ba saiya kawo mata, wani time din har mamaki takeyi yanda yakan biye mata, itakam madam har lokacin ta kasa gane komai.


                           ***
  Yauma a'iki takeyi a kitchen din, yayin da Irfan ya isheta da rigimab zaici kwai, tasan halinshi da son soyayyar kwai, dole ta fashe guda biyar tare da fara soya mishi.
 
    tsaye take bakin sink tana dauraye hannu a fanfo, yayin da numfashinta keyi kamar zai dauke saboda kamshin kwan da bata so, bata ji motsinshi ba sai hannayenshi ta gani bisa nata, cikin tafukan hannunsa ya sanya bayan hannunta, yana dago nata tafukan hannun da suke wani jajjaja saboda haske, sosai yake mamakin irin hasken da fatarta keyi, ga kuma dan kumburin da jikinta yayi, kafun tayi wani magana ya birkito ta gabanshi, ya shiga latsa fuskanta da shima ya ciko sosai.

   jikinta ta zare daga nashi, tana nufa gaban hot plate din data daura suyan kwai, kwashe na ciki tayi, tana kokarin zuba wani, wani irin abune ya taso mata, tayi saurin barin wajen, hannunta ya ruko ta zare kai tsaye ta wuce daki tana toshe baki, hot plate din ya kashe da sauri shima yana bin bayanta.   

   A bathroom ya sameta tana faman kwara amai, duk yabi ya wani rude, sai da tayi mai isarta, sannan ta tsaya, shiya taimaka mata ta tsaftace jikinta sannan suka futo, rike da kanta dake faman jujjuya mata, bakin gado suka zauna yana taba wuyanta da fadin,,

   Humaira dama baki da lafia ne?, kanta ta girgixa alamar a'ah, kafun tace,,

  kawai dai yanxun bana son kamshin suyar kwai, ko yaya naji sai nayi amai, cike da damuwa yake fadin,,

   to me yasa za kiyi?, kinsan bakya so, kaman tayi kuka take fadin,,

   Irfan ne yace yana son cin kwai, shine nake soya mishi, lumshe idanu yayi kafun ya bude da sauke wani ajiyar zuciya, hannunta ya ruko da kyau yana fadin,,

  plss muje asibiti indai kinsan akwai abin dake damunki,,

   nifa Baffah lafia na qlau, ta fada sauri, sosai yake kallonta kafun yace,,

  ouk zaki kwanta?, kai ta daga mishi alamar eh, ya taimaka mata sosai ta kwanta, tare da rufeta da blanket, a gefenta ya zauna yana fadin,,

  bari naje na karisa soya mishi, daga yau kuma bana so ki kara yin wani abu dazai saki amai, indai kinsan bakya so to kimun magana, zan miki, hope kin fahimta, marairaice fuska tayi da fadin,,

  Baffah daka barshi, yanxun jirin nan zai lafa mun, sai in…………,,

  shishshshsh, ya fada da daura dan yatsanshi bisa labbanta, dole tayi shiru, kara jan mata blanket yayi, tare da mikewa ya fuce zuwa kitchen, yana karisa suyar kwan.

  

                            ***
    Daren ranar dakinta ya kwana, cikin dare ta mike zata kitchen shan ruwa, farkawa yayi yace ta barshi ya dibo mata, tayi dan shiru har sanda ya kusa bakin kofa, ta dai daure tana fadin,,

   Baffah harda abinci fa, Allah yunwa nake jie, juyowa kawai yayi yana kallonta da murmushi, kafun ya juya ya futa, bisa wani dan tray ya jero komai sannan ya dawo.

   gefenta ya zauna bisa carpet din dake gefen gado, sun tattankwashe kafa, shiya zuba mata yana saka mata spoon, maimakon ta dauki spoon din, saita bude warmer abincin, tana daukan saving spoon tare da kara abincin.

   da suka hada ido sai murmushin yake ta mishi, shikam sai ya zuba mata idanu kawai yana kallonta, abincinta take cie cikin kwanciyar hankali, can dai ta dan dago kai suka hada ido, hadiye na bakinta tayi tana dan kauda ido da fadin,,

   Baffah zan kware fa,,

   sorry, ya fada da murmushi, shi burgeshi kawai takeyi, ya zuba mata ruwa cikin glass cup, tare da mikewa ya koma kan gadon yana kallonta harta kammala cie, sannan ta dawo saman gadon, jawota yayi jikinshi yana shafa bayanta, har saida wani bacci ya tafi da ita.

        

                            ***

   Safiyar ranan da azumi ta tashi, sai da ba takai ko ina ba ta fara jin jiki, zuwa azhar daker take iya wani a'iki mai karfi, hakura tayi kota iya kaiwa, can dai wajen la'asar daker ta iya yin salla, dabin bango ta futo don ta samu ruwan da zata karya azumin, wani irin jiri ke dibanta tana neman fadi.

   dai dai sanda suhymah ta futo daga bedroom dinta zata futa, wani kallon yatsina take mata, itakam jie take indai bata sha ruwan nan ba kaman zata iya rasa ranta, daker take iya fadin,,

   aunty suhymah plss ruwa, kie taimaka mun, sai data wani kankance idanu kafun tace,,

   nie kike a'ika in miki wani abu, da sauri ta girgixa kanta tana fadin,,

    a'ah, kiyi hakuri  banda lafia ne shi yasa, harara ta zabga mata, kafun ta wuce tana fadin,,

   kie mutu don kazan kiee, daga haka tasa kai ta fice, a hankali ummeetah ta sulale bisa tyles din dake wajen, mamakin rashin imani irin na aunty suhymah takeyi, kawai saita sanya kuka, taji gaba daya jikinta na mata wani irin ciwo.

   tana futa da motarta gate post din, shi kuma yana shigowa da nashi, girgixa kai kawai yayi yana mamakin futar da ake ba izininshi, sanda ya kammala paka motar, tun daga wajen entrance door yake jiyo kukanta, da sauri ya karisa ciki, ganinta dirshen a wajen tana kuka sai ya bashi mamaki.

   a gabanta ya duka kan kafafunshi, ganinshi ya sanya ta sauke ajiyar zuciya murya a dishe take fadin,,

  Baffah ruwa zansha plss help, da sauri ya mike, fridge ya nufa tare da dauko mata ruwan gora, sosai ya tallafo bayanta sannan ya taimaka da bata ruwan, tasha da dan yawa, kafun ta janye bakinta tana sakin ajiyar zuciya, da mamaki yake kai hannunshi saman wuyanta da fadin,,

   Humaira kodai zamu hospital ne, in nace baki da lafia, kice lafiyarki qlau, da sauri ta girgixa kai tana fadin,,

  a'ah, lafia na qlau, azumi na dauka shine na kasa kaiwa, a firgice ya dagota daga jikinshi yana fadin,,

  what, kina hauka ne, a condition din da kike ne zaki ce za kiyi azumi, yamutsa fuska tayi kafun tace,,

   Baffah nifa bana ciwon kom……, katseta yayi rai bace da fadin,,

  shout up kinsan……, sai kuma yayi shiru, itama ganin yanda ranshi ya baci ne, ya sanyata shiga taitayinta, kawai saita kara sanya sabon kuka, hannu ya mika mata alamar taxo, ta make kafadarta alamar a'ah,,

   shagwababbiya kawai, ya fada yana jawota cikin jikinshi, tare da manna kanta bisa kirjinsa, a hankali yake shafa kanta, cikin muryar rarrashi yake fadin,,

  Humaira pls muje hospital mana, kinga baki da lafia, kanta ta dan jinjina alamar gamsuwa, yayi dan murmushi yana jan kumatunta da fadin,,

  good my dream girl, tashi muje kie shirya ko, ya karisa maganar yana taimaka mata suka mike, shap shap ya taimaka mata ta shirya, sannan suka wuce hospital din.


    A nan suka hadu da DR. khamis, sai tsokanar mutumin yake, shiya basu gudunmuwa, suka sami ganin wata kwararriya likitar mata, inda aka mata kyakyawan binciken daya kamata. 

   suna tare da DR. khamis a office din doctorn, yayin da ummeetah kecan dakin da aka bata donta huta, daddadan albishir ne ya ziyarci kunninshi daga likitar, inda ta basu sanarwan ciki har tsawon na wata biyu da wasu yen satuttuka a jikin ummeetah, ba'a maganar farin cikin da fuskan oga sadeeq ya nuna.

   duk da yana hasashen hakan a tare da ummeetah, sai yaji kamar yanxun abin ya dirar masa, ganin komai yake kaman a mafarki, wannan yer ummeetah da yake ma kallon yer kwiciciyar yarinya, itace ake maganar tana dauke da cikinshi, lallai komai a rayuwa nufin Allah ne.

   hawayen farin ciki ne dauke cikin idanunsa, mikewa DR. khamis ya yayi, shima ya mike kawai sai suka rungume juna, sosai ya tayashi farin ciki, itama DR. sai faman congrat take mishi, tare kyawawan shawarwari yanda za'a kula da mai cikin, kasancewarta yarinya karama.

   sosai itama doctor ta mata bayanin yanda zata kula da kanta, baki kawai ummeetah ta saki, tun bata fahimce abin da matar ke nufi ba, hardai ta fahimta, nan idanunta sukai kwal kwal da tunanuka iri iri, shidai bakinshi yaki rufuwa, har lokacin da aka kammala musu da komai, aka bata drugs din da suka dace sannan suka nufi gida.

   tun a mota ta lura da tsananin annurin dake fuskanshi, a sanyaye ta dubeshi da fadin,,

   Baffah plss da gaske ne abin da doctor ta fadi?, cike da annurin fuska ya juyo yana yana shafan kuncinta da fadin,,

  of course dear, kin kusa zama maamaa, kasa tayi da kanta yayin da kirjinta ya shiga dukan uku uku, hannu yasa yana dago kanta da murmushinsa yake fadin,,

  come on put on a smile, kiyi farin ciki kinji, kyauta ne babba Allah ya bamu, murmushin yake kawai tayi tana kauda kanta, daga nan ya cigaba da driving dinshi, hankali kwance har suka isa gida.

   

                             ***
  Gaban dresing mirror take tsaye, sanye take da wasu tausasan kayan bacci riga da wandon, gashin kanta take tufkewa, sai kuma ta tsaya a hankali ta daura hannunta saman cikinta, wanda harya fara sauya yanayi, daga lafaffen data sanshi.

   shiru tayi tana sakawa da kwancewa, wai itace da ciki abin sai yana mata kaman a mafarki, da gaske itace zata haifi d'a kamar yanda taga ana haihuwa, karan bude kofan shine ya sanyata dan juyawa, tsaye yayi daga bakin kofan sanye da wata farar jallabiya mai yakkaken hannu, sosai yake nazarinta, kafun ya kariso inda take.

    ta gabanta ya tsaya yana folding hands dinshi, tare da zuba mata idanu, tunda suka dawo ya lura da yanayin mood dinta ya sauya, itakam bata kalleshi ba, sai bada hankali da tayi wajen tufke gashinta, ta gama tana sanya yer turban dinta, hannunshi ya mika mata da fadin,,

   zo muce mu kwanta, mirror stool ta jawo tana zama da kyau tare da fadin,,

    nie bana jin bacci,  kallonta yakeyi kusan 5minutes, kafun ya wuce duk tunanin tama futa zaiyi, sai taga ya harde bisa gadon yana rufe rabin jikinshi da blanket, tare da kishingida bayanshi da kyau da pillow, wayarshi yake dannawa hankali kwance, can kuma saita mike wajen gado ta tsaya, tana faman sanya fuskan kuka, kafun tace,,

   toh Baffah kayi hakuri zanyi baccin, shiru ya mata ba tare daya kalleta ba, itama sai tayi kasa da kanta ganin yanda ya tamke fuska tamau, can ta juyo muryanshi, cikin natsuwa yake fadin,,

   Humaira zoki zauna kie fada mun damuwanki, tunda muka dawo hospital na lura da mood dinki ya sanja, a hankali ta hauro saman gadon sosai, tana tattankwashe kafafu, ya tallafo fuskanta da take faman kasa dashi, gira ya daga mata yana fadin,,

  plss say something, na damu ganinki cikin damuwa, cikinta ta kalla tana dan yarfa hannaye, kafun ta dago da fadin,,

    zara'uuu, ta karisa maganar zata sa kuka, sai daya dan murmusa yanda tayi maganar, ganin kuma da gaske takeyi ya sashi gintse dariyanshi, tuni hawaye suka wanke mata fuska, da sauri yasa hannu yana share mata hawayen, kafun ya jawota jikinshi da fadin,,

   come on kie daina wannan kukan, zoki fada mun me zara'u tayi, tana damunki da yawa ko? kanta ta girgixa alamar a'ah, ya dan numfasa kafun yace,,

  ouk to meye matsalar sanar dani, yatsunta take kallo da yake wasa dasu, cikin muryar kuka kuka take fadin,,

   Baffah nidah tsoron nakeji, yace,

   tsoron me, haihuwar?, kanta ta daga alamar eh, tana daurawa da fadin,,

   inna tah ta sanadiyar haka ta rasu, Affah nah yace ko ganina ba yiba, tsoro nakeji, tsoro nake jie in haihu kaga aunty suhymah bata son kishiya, ba zata taba rike ye'yen……, hannunshi yasa da sauri yana rufe bakinta, kafun ya tallafo fuskanta, sosai suke kallon juna cikin idanu, girgixa mata kanshi yakeyi alamar kar tayi, dai dai sanda kwalla ke ballewa daga idanunta suna zama hawaye, kuncinsa ya sanya yana share mata, kafun ya ruko hannunta da kyau yana fadin,,

  Humaira plss kie daina fadan haka, kar in sake jin kince haka, in sha Allahu lafia zaki haihu, zan baki dukkan wani gudummuwa, zan tayaki da addu'a, sannan da mun koma gida zan sanar da maami komai, suma zasu rika miki add'a, in sha Allah lafia zaki haihu, karkisa wani damuwa kinji dream girl dina, kanta ta girgixa da karfin gwiwa data samu kafun tace,,

   toh, in sha Allah nima zan rika addu'a, bana so nabar ye'yen mutane suyi irin farkon rayuwan da nayi, murmushi yayi da shiririta irin na ummeetah, ya kuma dan dago fuskanta yana fadin,,

  ye'ye har nawa zaki haifa mun jaruma tah?, da kunya ta rufe fuskanta, ya janye hannun nata cike da tsokana yake fadin,,

   fada mun kodai yen twin zaki haifa mun, zaro ido tayi waje, kafun ta girgixa kanta tana fadin,,

   nidai ban sani ba, haihuwar twin zaiyi wuya, dan d'aya dai zaifi sauki, tunda aunty suhymah itama zata haihu, kaga ka samu yen twin din kenan, jikinshi ya jawota sosai, a saman kanta yake sakar mata kiss, sosai yake jin wani abu game da ita,,

    ke ta dabance, ya fada yana shafar kanta cikin natsuwa, wani bacci ke shirin fisganta, dama tasha magungunanta, don haka ya taimaka mata ta gyara kwanciya yana rufeta da blanket, idanunta a lumshe suke, amma tana iya jie a jikinta kallonta yakeyi, idanu ya zuba mata har sai daya ga baccinta yayi nisa, sannan shima ya gyara kwanciya yana tofesu da addu'a.

 

   Da asuba da smiling face dinshi tayi karo, gani kawai yake ta kara kyau da cikin babynshi, itadai mikewa tayi ta wuce bayi bayan sun gaisa, tare sukai sallah a nan dakin.

   kulawa sosai take samu na musamman, lokacin daya dauke mata yawancin a'ikin gida, duk yanda taso ya bari tayi baya bari, duk wani girki daya san zai sanya ta amai, shi keyi yanxun, madam kuma tayi ta fada, kwanaki data futo ta tarda ummeetah na bacci, shi ya futa can backyard yana hada musu breakfast.

   masifa ta rikayi, musamman da yace, don bata son kamshin kwaine shine ya taimaka mata, mita ta rikayi sosai, kan sai kace wata mai ciki, daker dai ya samu ya kashe maganar, itadai ummeetah ta kanta takeyi, donma bata ciwo ko kadan, sai dai salo irin name ciki.

   sosai yakan cie dariya, inya farka tsakar dare ya hangeta tana cin abinci, yanxun kam a'i da warmer abinci take kwana a daki, daya dawo office baya iya yin komai saiya dagata sama, tare da kissing cikin sannan ya direta, har mamakin irin kaunar da yake ma cikin takeyi, motsi kadan saiya ta jero mata tambayoyi.


                        ***

   Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu ta ko wani fanni, a yanxun ummeetah cikinta na gabda shiga na wata hudu kena, duk ta dan kara cika, yen matsalolin da dake fama dasu kuma na dad'a raguwa, yanxun ba abin dake damunta sai yawan cin abincin da takeyi.

  ga kuma tumbin daya fara bayyana tun cikin nada wata uku, zuwa yanxun kam bata iya xama ba hijjabi don ras ya futo, kamar wani cikin wata biyar din, shikanshi yana mamakin girman cikinta, kullum cikin ziyarta asibiti suke, ana ce musu komai qlau.

     

                   £……£……£

    Wani iftila'ine ya fada ma iyalan Alh. Bukar bagudu, mahaifi ga madam suhymah kenan, tsawon shekara daya da rabi kenan daya ije a'iki yana cin daularsa a hankali, sai dai yanxun tsawon wata shida kenan da ake bincikarsa akan batan wasu makudan kudade da su kayi, a lokacin da yake kan a'ikinshi, iya bincika da uzuri am mishi ba'a samo bakin zaren ba.

   don haka gwamnati ta kwace duk wani abu daya mallaka, wani karamin gida daya kacal ya rage mishi, ranar suna jie suna gani aka kulle katon gidan da suke rayuwa a ciki, kayan sawansu kawai da yen sauransu sukai packing, kafun su koma can karamin gidan da zama.

   sai dai hankalinshi ya kasa kwanciya, yayin da karancin imani ya sanyashi yanke jiki ya fadi, asibiti suka nufa dashi hankali tashe, acan ne likitoci sukai iya bakin kokarinsu, inda suka sanar musu ya kamu da mummunar shanyewar barin jiki, sosai hankalinsu ya tashi, banda koke koke ba abin da sukeyi, harda mummyn munat data diro garin a ranar, maami kuma da munat shagargarin ranar suke shirin zuwa.

  

                          ***

   laptop ne gabanshi dake bisa center table, ya maida hankalinshi sosai, a'iki yake sosai yen kwanakin nan, saboda wani dalili, gefe daya ga maltmilk din dake cikin tambulan yana sha hankali kwance.
  
   tafiya take daker saboda kiban data zauna ta narka, ga cikin jikinta da yake cikin wata na takwas yabi ya hade da tebanta, kadan kadan kake iya ganinshi, wani light purple din sleeping dress ne a jikinta mai shegen kyau da tsada, hannun vest ne dashi saiya sauka straight har kasa, ita kanta rigar ta burgeta tun sanda taga an zo mata dashi, daga shopping din dasu ummeetah suka futa last.

   kusa dashi ta zauna, nan da nan ta cinye two seater din da yake zaune akai, kanshi ya dago yana kallonta, kafun yayi dan murmushi da fadin,,

    wai sannu fa, tayi wani dan yatsina tana fadin,,

  kayi mun sannu tunda ka hadani da a'iki, ka taso muje mu kwanta dare yayi, da yer dariya yake fadin,,

  au tasa nie zama ayi yau, far tayi da idanu kafun tace,,

  of course, na gaji da yanda kwana biyu nake farkawa in nemeka in rasa kusa dani, da nakan dauka ko kana bathroom ne, amma zuwa yanxun na lura bai kamata ina sakaci da hakan ba, kafana kafanka, ta karisa maganar cike da neman tsiya, cigaba yayi da danna laptop dinshi yana fadin,,

   nie kuma ba yanxun zan kwanta ba, kinga a'iki nakeyi sai dai in zaki jirani, bata rai tayi da fadin,,

  kai kai kai boo, nifa bacci nakeji, ka tashi kawai m...……, karan bude kofa ne ya katse mata maganar da takeyi, dubansu duk suka kai kofan dakin ummeetah, wacce ta futo dai dai sanda ta juya tana dan rufo kofan, hijjab ne a jikinta baki har kusan gwiwa, amma sai ta dageshi ta baya,

    sanye take cikin wata sleeping dress light pink, ba inda yabar na suhymah kuma, da tsananin mamaki take bin rigan da kallo, kafun tace,,

  what!cikin karaji, da sauri ya dawo daga duniyar kallon da yake ma ummeetah, duk da ta baya ya nuna, bai hana ya bayyana tsananin kyaun da rigar ta mata ba, dan cass a jikinta, itama a dan firgice ta juyo, da sauri kuma ta sanya hannu cikin hijjab tana tutturawa da boye abin da zata boye, itama suhymah a fusace ta mike, da dan yatsa take nuna rigar sai kuma ta nuna na jikinta tana fadin,,

    are yhu mad, kina hauka ne, zan sanya kaya kema kie sanya, har yaushe muka kai wannan matsayin ni dake, gidan uban wa kika samu irin night gown dina, a tsorace ummeetah ta manne jikin bango, bata kaunar tashin hankali, bare yanxun data ninkata kusan uku a jiki, a fusace tayo kanta da fadin,,  

   ohh ina magana kin……, bata karisa taji ya ruko hannuta ta baya, a sittin ta juyo da fadin,,

  sadeeq ka kyaleni in koya ma yarinyan nan hankali, waishin ta inama ta samu irin sleeping dress dina, ko shima kaine ka sai mata?, dan runtse ido yayi da budewa yana fadin,,

   plss suhymah mubar wannan maganar, meye a ciki don kin saka kaya itama ta saka irinshi, naga itama yer adam ce kamar kowa, harara ta zabga mai tana nuna kanta da dan yatsa, kafun tace,,

  nie insa kaya, wancan abin ta sanya, never wlhy, da mamaki sosai yake fadin,,

   toh why not, doguwar tsaki taja kafun tace,,

  da banbaci, ka mance nie yer waye kenan, sannan matar……, koda banga laifinta ba, kaine ka ba dani daka siya mana kaya iri daya kuma na rantse……,

  saita cire, ya karisa mata yana daurawa da fadin,,

   inhar wannan ne karshen maganar ki, to ba zata cire ba, zaro ido tayi da mamaki yace,,

   yes saboda itama mutumce kamar kowa, zatai wani maganar ya ja hannunta sukai bedroom, harda rufi kofan, ita dai ummeetah na binsu da kallo, ajiyar zuciya ta sauke tana karisawa kitchen don tasha ruwan daya tada ita.

 
   A daki kam kallon kallo suka shiga yin ma juna, mamaki sosai abin ke bata kafun tace,,

  wait sadeeq na kasa ganewa ne, wai meke faruwa?, yer a'ikina nefa kake neman cinmun zarafi a kanta, donme ma, a kancin me zan sanya kaya ta saka, who the hell born her father, ta karisa maganar a tuke, tana kokarin komawa falon, da sauri yasha gabanta yana fadin,,

   suhymah look bana son  rigima, kina maganar ummeetah yer a'ikinki ne, to kibar wannan zancan ummeetah ta wuce matsayin yer a'iki, inba ki sani ba……,

   ahh, ta fada tana dafe cikinta, da sauri ya rukota, ta kauda hannunshi tana zabga mishi harara da fadin,,

  ina sauraranka, waskewa yayi yana cigaba da fadin,,

   ummeetah yer abokina ne, aminina kuma, tunda take mana a'iki a gidan nan so nawa kika ga mun taba biyanta, ko sau daya, don haka mu kecin azzikint……,,

  enough sadeeq, idan bamu biyata ba, a'i muna biya mata school fees, ka tashi ka sanyata makaranta mai tsada, kallonka kawai nakeyi, ga kuma suturar da muke siyan mata, a banxa zamu bata, da sauri yace,,

  good, kin gani kimba kanki amsa, a'i suturar ne kuma kike tsiya yanxun a kanshi, plss karki tada mun hankalin baby, kie tada naki, harara ta zabga mishi tare da zama bakin gado, sosai wasu al-amuran nashi yanxun ke bata tsoro, kwafa tayi da ayyana,,

   soon dai ka kusa zuwa hannu, sai ka zama tamkar yaro nah, tswwww sai kuma taja wani tsakin, dai dai sanda wayarta ke faman tsalla ihu, jawowa tayi samar side drower tare da duba mai kiran,,

   zahira, ta ayyana a zuciyarta, kafun ta daga wayar da dan murmushi, duk yana tsaye yana kallonta, seconds biyu sunyi yawa annurin fuskanta ya sauya, tuni ta cillar da wayan tana mikewa zumbur da sa wata uwar kara, ta dafe cikinta tana faman kiran sunan daddy.
  
    da sauri ya rukota yana tambayarta meke faruwa, amma ta kasa bashi amsa, sai kuka data sanya tana fadin,,

   daddy nah sun cuceshi, zaunar da ita yayi, yana jawo wayarshi tare da dialing number mom dinta, ita take sanar dashi halin da ake ciki, sosai ya jajanta musu, kafun ya mika ma suhymah wayar.

   da kuka ta amsa, sun dan jima suna magana da mom din nata, kafun ta sauke wayar tana mikewa, kayan jikinta ta kalla hankali tashe kuma ta soma balle yen bottons din dake gaban rigar, safe ta nufa tana jawo towel tare da cire rigan.

Continue Reading

You'll Also Like

973K 35.2K 42
🚨 ဒီ Fic မှာ Adult Scences တွေပါဝင်တာကြောင့် မကြိုက်တဲ့လူများရှောင်ဖို့ ကြိုတင်အသိပေးပါတယ်နော် 🚨 🚨 ဒီ Fic မွာ Adult Scences ေတြပါဝင္တာေၾကာင့္ မႀက...
1.3M 172K 149
BL
664K 75K 126
credit to original author Shui Qian Cheng. This story belongs to Rosy0513 . I am just a translator. This cover photo is not belong to me.
391K 9.9K 51
တစ်နေ့တစ်နေ့ခေါင်းထဲမှာကလဲ့စားချေမှုသာအပြည့်ရှိနေသော ခပ်အေးအေးနေတတ်သော မာဖီးယားနှင့်.... ဘာပဲလုပ်လုပ် တလွဲတွေလုပ်တတ်နေသော ကောင်မလေးတို့ နှစ်‌ယောက်ဟာ...