MEE'AD

Bởi Hauwancyy44

4.2K 105 33

Love story💕 heart touching 🤔😍 follow me an read more...😊😊😊 Taku har kullum Hauwa Ibraheem Misau pls fa... Xem Thêm

chapter 1
Chapter 2
chapter 3
chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 35

Chapter 34

77 5 0
Bởi Hauwancyy44


💫💫💫💫
          _*MEE'AD*_
                   💫💫💫💫
            
               

    

           ***CONTINUE***

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

Follow me on wattpad
👇👇👇
@hauwancyy44

 

        JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .
 

√√√√√ MEE'AD fan's kuyi hakuri da rashin post akan time, sbd wasu dalilai. √√√√√√

         
     
**** Pls don't forget to vote, share & comments 👌 love u fan's 💯%. 

🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️
Ina kuke masu son DATA ? ku taho da hazanri ku saya dan kuma nazo muku da Data a sassaukan rahusa idan kuna bukata

    📶 *MTN*📶

*500MB* 👉🏽 *#150*
*1GB*      👉🏽 *#300*
*2GB*       👉🏽 *#600*
*3GB*        👉🏽 *#900*
*4GB*       👉🏻*#1200*

Mai bukata ya tura ta wannan account number
👇🏻👇🏻👇🏻

3142669195 Hauwa Ibrahim First Bank .

Idan ka tura saika tuntubeni ta wannan number
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
09039285813.

Ga masu buƙata akwai Glo da Airtel da kuma 9mobile.

Masu bukatan data maza kuzo ga dama tazo muku har gida.

🎃🎃🎃

Thank you for contacting Hauwa Misau! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE.
    
I am selling MTN data with cheap price.

MTN DATA PACKAGE 
500mb ~ *#150*
1GB ~ *#300*
2GB ~ *#600*
3GB ~ *#900*
4GB ~ *#1200*             

Dial *146*4# Check data balance VALIDITY 1 MONTH.   

Airtel, 9mobile, Glo also available.

You Can Pay Through Bank Transfer Or Cash
3142669195
Hauwa Ibrahim First Bank.

Call or chat for more information ; 09039285813.

63 ~ 64

Washe gari ana idar da sallan asubahi Amal ta dira a part d'in Ummanta inda ta tarar da ita zaune bisa sallaya tana Jan carbi.

Zama tayi bisa gefenta cikin ido take fad'in Umma sauri ki idar wallahi akwai maganar data hanani rintsawa jiya da dare kuma wallahi inaso mu tattauna dake akan zancen.

Cike da hanzari Umma ta shafa addu'ar da takeyi takai dubanta zuwa wajen d'iyar tata tace lafiya Amal miya fito dake a dai - dai wannan lokacin ? Anya kuma baki had'u da 'kananun aljanu jiya dadare ba.

Gyara zama Amal d'in tayi wallahi Umma jiya kasa bacci nayi sbd maganar auren Majeeed da waccar yarinya kinsan Allah kwata - kwata baniso ko a labari naji ya aureta tin jiya nake neman mafita Amma na rsa ta Ina zan fara.

"Shiru Umma tayi kiyi hakuri yar nan Nima abin ya bani mamaki sosai kuma abin ya ta'ba mini rai matu'ka amma inaso ki kwantar da hankalinki kibarmin zancen a hanuna kawai, nasan bakiyi sallah ba tashi kije kiyi sallah zansan abinda zanyi kawai kuma zan kira Aunty ki muyi waya.

Da'kyar ta lallabata ta nufi part d'inta danyin sallah asubahi.

Da gari ya waye dukkansu suka hallara kan darning danyin breakfast.

Bayan sun kammala break fast dinne Majeed yake shaida musu jirginsu karfe hudu zai tashi zuwa Yola, kowa yayi masa fatan alkairi da fatan sauka lafiya, nan sukaci gabada fira cike da farin ciki.

Mee'ad kwance take bisa gado ta kurama pillow dake gefenta ido murmushine akan fuskarta yayinda zuciyarta ke tinasar da ita tsananin soyayyar da take yima dan uwanta kuma Wanda yake Shirin zama ango a agareta wata Majeeed.

Kwance Majeed ya tarar da ita da sallama ya shiga dakin fuskarsa dauke  da murmushi ya karasa bakin gado ya zauna yayi gyaran murya, cikin firgici ta dago dakai sukayi ido hudu a hanzarce ta sunkuyar dakai, tashi tayi ta zauna ta fara wasa da yatsun hanunta, Murmushin ya karayi daga bisani yace yan mata na ya kk ? Ko kinsan anjima zan tafi Yola ? Kuma bazan dawo da wuri ba sbd ina dawowa shirye ~shiryen Auren mu za'a fara, Sunkuyar dakai tayi fuskarta dauke da murmushi, Majeeed yaci gaba da cewa dama nazo naji yaushe zakije Yola sbd muyi shirye ~ shiryen mu acan ? Uhmmm Yaya ai Kaine ya Kamata ka bani time d'in zuwa Yola tinda kana sama dani, Yayi murmushi jin dad'i ok no problem next week kawai zanyi miki Visa ki sameni a can ko Yar 'Kanwata ? Shiru tayi tana murmushi uhmm Yaya baza' a bar tafiyar zuwa upper week ba kuma ? Touh mi zakiyi idan kika zauna a nan din ma ? Kawai next week zaki isoni kinji ? Yana gama fad'in haka ya gimtse fuska ya nufi kofar fita sbd yasan halin Mee'ad da kafiya, binsa tayi da kallo fuskarta dauke da murmushi tace uhmm Yaya kenan shugaban rigima zansha fama wajen rarrashi kam Allah ka bani ikon yi masa biyaya da kuma rarrashin sa Ameeeen, komawa tayi ta kwanta zuciyarta cike da Farin cikin zata Auri wanda zuciyarta take muradi ta rin'ka furta kalmar  Alhamdulillah.

"Amal ta nufi bed room d'in Umma tana kwala mata kira Umma! Umma!! Umma!!! Kina ta inane haka ? Nazo Miki da sabon labari shiru bata ganta a bed room d'in ba cike da murna ta nufi kitchen tana Mai kwala mata kira.

Uhmm gani tanan waike mi yake damun kine kam ? Kinbi kin karad'e mana gida da ihu ? Da gudu ta karasa kitchen d'in ta rungume Umma cike da zumud'i, Umma yanzu muka gama waya da Areeef yake sanar dani yau Mommyn sa zatazo gidan nan domin su gana da Daddy akan maganar Auren mu, A'ah Masha Allah abu yayi kyau Allah ya kawota lafiya kice yau munada babbar bakuwa ? Muna maraba da babbar ba'kuwa kuma sirika a garemu maza jeki kiyo kiran Mommyn ku tazo taji abun arziki Masha Allah.

Falon Mommy ta nufa ta sanar da ita sannan ta nufi part d'in Hajiya Hindu ta sameta tana sallah walaha sai da ta tsaya ta idar kafin ta fad'a mata yadda sukayi da Areeef d'in Hajiya Hindu tayi hamdala da addu'ah Allah yasa hakan ya zama musu alkairi, Ameeeen tace kafin ta nufi kofar fita.

"Dakin Mee'ad ta nufa ta tarar da ita kwance d'aka mata duka tayi cike da zumud'i tace albishirinki dear!

"Goro fari tass tass ",

"Bani goron albishir kafin na fada miki ".

"Touh mi kikeso na baki a matsayin goron albishir ?

"Kiyimin alkawarin za muyi event a bikini mu,

"Ok nayi al'kawari",

Touh yau Mommyn Areeef zatazo tayi maganar Auren mu, ihuuu Mee'ad tayi wooooooh Masha Allah kice zamusha biki nayi farin ciki sosai kuma Ina alfahari da hakan Allah ya sanya alkairi kiji Rabin raina ? Allah yasa ayi a sa'a in alfahari dake y'ar uwa. Murmushi tayi sannan ta 'kura mata ido jiki a sanyaye tace Ameeeen Insha Allahu tare zamuyi komai kiji Besty ? Naji Allah ya bamu ikon yin komai bisa tsari tace Ameeeen, Nan sukaci gaba da firarsu suna daria.

Masha Allah, yinin ranar dai gidansu Amal sun yini da farin ciki sai girke ~ girke akeyi cikin 'karamin lokaci aka kammala komai a ciki harda gyaran gida da tsaftace ko ina sannan aka sanya turaren wuta mai kamshin gaske.

Misalin 'karfe 3;30 Mee'ad suka nufi filin jirgi dan raka Majeeeed suna tafe suna fira mai dad'i yayin da Amal ke zaune a kujerar dake kusa da driver tana faman chat zuciyarta cike da 'kunci da kuma nadaman biyosu da tayi, Majeeed yayi gyaran murya Ihmmmm! Amal naji kinyi shiru Allah dai yasa ba Angon bane ya ta'ba mana ke ? A hasale tad'an juyo tace Angona da yake lalla'bani yafi 'karfin ya 'bata mini rai sakamakon irin matu'kar son da yake mini, murmushi yayi Ihmmmm touh Mee'ad kinji yadda ake soyayya ko ? Bayan aure zan turaki gidansu Amal domin ki koyi course guda akan soyayya.

Amal ta gallah masa harara shiyasa ako da wani irin lokaci Auren wayayyen mutum take da Amfani, duk dama Auren wayayyiyar mace na Mai rabone........

INA ALFAHARI DAKU MASOYANA.

pls

Follow

Share

Vote

Comment

Fisabilillah 🙏🙏🙏.

Đọc tiếp

Bạn Cũng Sẽ Thích

6.2M 201K 31
After she tragically loses her mother, Cassie turns to street fighting-but she soon learns that the biggest fights happen outside the ring. ...