MEE'AD

By Hauwancyy44

4.2K 105 33

Love storyπŸ’• heart touching πŸ€”πŸ˜ follow me an read more...😊😊😊 Taku har kullum Hauwa Ibraheem Misau pls fa... More

chapter 1
Chapter 2
chapter 3
chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35

Chapter 19

69 1 0
By Hauwancyy44

💫💫💫💫
          _*MEE'AD*_
                   💫💫💫💫
            

                    
           ***CONTINUE***



*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

%% wattpad__@hauwancyy44 %%

 

        JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .
 

√√√√√ MEE'AD fan's kuyi hakuri da rashin post akan time, sbd wasu dalilai. √√√√√√

         
     
**** Pls don't forget to vote, share & comments 👌 love u fan's 💯%.
          
                         

               

                   
  

                      33 ~ 34

Dago kai Amrah tayi zuciyarta faal takaici, kallon Amal take cike da gadara,  fiskarta dauke da lallausan murmushi mai nuna alamar ban haushi, dogon numfashi ta sake jaa kafin tace su Amal an girma kodai kin fada tarkon soyayya ne ? gyara tsayuwa Amal tayi kafin tace kinga zamuyi magana 'anjima yanzu dai muje class kinsan lecturer da zai shiga ba mutunci ne ya isheshiba ko ? Daria Amrah tayi kafin tace ba matsala muje sallama sukaima Yaya Majeed suka nufi class.

Kai tsaye gida ya nufa bayan yayi parking moto ya nufi cikin gida yana yan wake2 sa,"

Bai tarar da kowa a falon ba kai tsaye dakin Mee'ad ya nufa fiskarsa dauke da murmushi ya murda murfin kofar baiyi mamakin samun kofar a bude ba,"

kutsa kai cikin dakin yayi bakinsa dauke da sallama shiru baiji motsin kowa ba,"

Corridor dazai sada shi da cikin dakin yabi, kwance ya hangota bisa gado, ba abinda take sai bacci,

A hankali ya karasa kusa da gadon da take kwance, kare mata kallo yayi daga sama har kasa kasan cewar lallausan bargon data lulluba dashi ya yaye,"

Sanye take cikin wata lallausan doguwar sleeping dress jaa mai hannun shimi, rigar tanada duhu sosai, sai dai tayi mata kyau kamar baturiya.

Idonsa kurr a kanta ko kirfawa bayayi, juyi tayi hade da dan bude ido irin na mai bacci murmushi tayi masa cike da magagin bacci, shima murmushi yayi mata,

A firgice ta tashi ta janyo hijabin dake gefenta tana kokarin sayawa, cewa take

"kai juya waya baka izinin shigowa dakin nan ?

"Juya mata baya yayi Yana daria kafin yace miyasa baki rufe kofar dakinki ba, bayan kinsan gidan bake daya bace ?

Hararar sa tayi kafin tace ni dai
karka kara shogowa dakina ban tare da kayi knocking ba 😏

Fashewa yayi da daria sai da yayi mai isarsa kafin yace kema kinsan bazan taba bin umarnin kiba, kawai ki dauki shawaran dana baki kinji yar kanwata 😜 yana gama fadin haka yayi ficewarsa yana daria.

Bin bayan shi da kallo tayi fuskarta dauke da murmushi take fadin Allah ya shiryamin kai Yayana. Kwanciya ta sake yi ta kuma lullube jikinta.

    

                %%%%%%

Bayan su Amal sun fito daga text kai tsaye capteria suka nufa fira sukeyi sama2 har suka isa.

Sun kammala cin abincinsu a nitse Amrah ta kalli Amal tace Kawalli dazu baki bani labarin abinda ke tsakaninki da Majeed ba,

Murmushi Amal tayi kafin tace kawata kenan, bari kiji labari tin lokacin da Majeed ya dawo kasar nan baki dayan hankalinsa na kaina baya kallon ko wacce mace  a matsayi masoyiya bayanni.

Hmm kema kanki kisanni da son fari, dogo kuma kyakkyawan namiji ko dan shiga gari da shopping da kuma nuna ma kawaye irinki Aminiyata,"

Dariyar mugunta irinta ban haushin nan Amrah tayi zuciyarta cike da kuncin maganar da Amal ta fada mata,

Murmushin yake tayi kafin ta dafa kafadar Amal tace ina tayaki murna da samun masoyin kwarai kamar Majeed,"

Daria Amal din tayi kafin tace godiya sau 1k kawata, Ina yinki sosai.

Kallon takaici Amrah tayi mata zuciyarta cike da sake2, tace kinga tashi mu koma class sbd kar muyi letti irin na dazu.

To kawai Amal tace kafinta tashi ta dubeta fuskarta dauke da murmushi tace kinga yar' uwa akwai wadansu maganganun da nakeso mu tattauna 'amma ba yanzu ba.

Amrah ta ce baki da matsala idan har maganganune saimun hadu kawai yanzu dai muje class, daria Amal din tayi kafin sukaci gaba da tafiya.

Mee'ad kuma na kwance sai da tayi bacci mai isarta kafin ta tashi, wanka tayi da kwalliya ta kuma dauki wayoyinta ta sauka kasa.

"Umma barka da rana, ya hutawa kuma ?  

"Alhmdllh tace"

"Yau baki fita school bane ?

Eh Umma yau ban fita ba, yayi kyau Umma tace sannan ta tashi ta nufi bed dinta.

Mommy ce ta fito daga kitchen hannunta rike da basket da 'alama abincine a cikinsa, a hanzarce Mee'ad ta karbi basket din tace sannu da aiki Hajiyata,

Murmushi Mommy tayi kafin tace yauwa kikai ma Yayanku abincin nan dazu ya kirani yace na 'aika.

To bari nakai masa, murmushi Mommy tayi kafin tace Allah yayi Miki albarka, Ameeen tace.

Da sallama ta shiga part din a falo ta tarar da shi sanye da three quarter wando da shimi.

"Barka da rana Yaya"

"Barkan kidai yar' kanwata"

Karasawa tayi ta ajiye basket din dake hannunta bisa table. A hankali ta nufi kofar fita.

Majeed ya dakatar da ita da cewa Kanwata yaya zaki tafi bazaki tsaya muyi fira ba ?

"Jijjiga kai tayi kafin tace sorry Yaya zanje nayi break ne dan ban wani dade da tashi ba kuma inajin yunwa sosai ta karasa maganar tana mai shafa cikinta.

Tashi yayi fuskarsa dauke da murmushi ya nufi wajen da take tsaye kamo hannunta yayi ya zaunar da ita bisa kujera, ya nufi darning table bude kwanukan abincin yayi ya debo musu a flat guda 1 da cokala 2.

Ajiye flat din yayi akan rool carpet din dake shimfide a falon, a freezer ya dauko musu exotic mai sanyi da cup guda 2.

Zama yayi bisa carpet kafin ya dago kai yace Bismillah yan mata, murmushi tayi kafin tace nikam bazan iyacin abinci dakai ba kunya nakeji 🙈 daria yayi mai isarsa kafin ya dubeta up and down yace su Mee'ad an girma yau kuma ni akejin kunya 🤔 dallah sauko muci abinci idan kuma kinki saina zaneki yanzun nan.

A hankali ta sauko suka fara cin abincin, jalop rice ce mai dadi taji kayan hadi da nama babu 'abinda take sai kamshi.

Cin abincin suke cike da nishadi sai santi da labari yake zuba mata, tin tanajin kunyarsa harta sake sosai dashi.

Wash Yaya na koshi sosai, hararar ta yayi kafin yace dan wannan abincin da kikacin ?

"Shagwabe fiska tayi tace Allah na koshi Yaya"

Nasan baki wani koshi ba debo abincin yayi a cokali yakai bakinta, dakyar ta karba sbd kunyarsa da takeji.

Dago dara2 idanunta tayi ta kura masasu sai murmushi take, shima murmushin yayi kafin yace kanwata naji dadin zuwanki da tayani yin lunch din nan sosai, da'ace nida Amal ne zaune anan da nafi kowa jin dadi, sbd banida wani burin daya wuce naga na mallaketa 'a matsayin matar aurena.

Shiru Mee'ad tayi kafin tadan gyara zama tace nasan ka zuciyarka ta dade tana kaunar Amal, inayi muku fatan alkairi, kuma zanci gaba da rokon Allah ya cika maka burin auren yar' uwata.

Murmushi yayi kafin yace na gode sosai, Amma kinsan wani abu kuwa ? Jijjiga kai kawai tayi, inaso kici gabada zama kawa kuma Aminiya ' a gareni  har iya tsawon rayuwar mu. Domin na gane kinason farin cikina, kinsan komai nawa fiye da tsammanina pls kada ki gujema abotarmu har abada kamo hannunta yayi yanayi mata magiya waita amince da Amintarsu 🤔 tab.

Murmushi Mee'ad din tayi kafin tace nayi maka 'alkawarin hakan amma idan har nayi aure ba lallai hakan yaci gaba da...

Bude kofa sukaji anyi bata dau lokaci ba ta karaso cikin falon cewa take mizan gani Mee'ad anan kika yada zango kenan to tashi ki fita tin kafin ranki ya baci, dama jikina ya bani akwai abinda kk aikatawa ne shiyasa baki dawo da wuri ba daga aika ?.





Mai karatu biyoni kasha lbr 💯





Pls vote, comments and share Fisabilillah 🙏🙏🙏🙏🙏.

Continue Reading

You'll Also Like

6.2M 201K 31
After she tragically loses her mother, Cassie turns to street fighting-but she soon learns that the biggest fights happen outside the ring. ...