Tashi tayi tana yarfe hannun,.da suka yi ja. "Mugu ban tab'a ganin shi ba. Ahala yana cikin sabida daukar da aka yi ne, banza dashi da fuskar shi kamar Imran Abbas." Tabi hanyar da harara, (🤔🤓 toh meye laifin hanyar kuma)
  
         Dakyar ta mike tare da barin gurin, ita godiyar ta daya da bai damu da abinda ya kawo ta ba. Tana shiga office d'insu ta sami Tasleem tana kuka.
"Baby Queen! Waye ya tab'a min ke?"
Cikin shashekar kuka ta d'ago kanta tare da kallon Noorh, tace mata.
"Amma kema ai kuka kika yi?"
Murza idanunta tayi, sannan ta ce mata.
"Wannan ba matsalar ki bace domin abu ne ya faɗa min a idanu!"
"Ai ba zaki gaya min kome ba? Sannan ni kina son na gaya miki kome?" Inji Tasleem,
"Toh Kiyi hakuri! Wallahi abu ne ya faɗa min a idanu, waye ya saki kuka?"

"Ni da baby Naz!"
"Kayyasa! Da wuri haka, toh kiyi hakuri amma tabbas bai kyauta miki ba. Sai ki dauke mishi wuta kawai."
     "Wai ai nasan idan ya huce zai kirani." Ta fadawa Noorh haka, takaice ne ya kama Noorh. Ta ja kujeranta tana kallon ta. Sabida banzan haukar son da takewa Nazzir, haka suka gama aikin su. Ana tashi suke fito zasu shiga motar su, sai me? Taya a fashe.
Rike baki Tasleem tayi kamar zata yi kuka.
"Yanzun wani mugu ne yayi mana wannan aikin?"

    Ta faɗa tana kallon yadda aka fasa tayar, wani dan sanda ne ya fito daga motar da yake kusa ita, yace.
"CEO Mahir Hamoud Boualem! Shi ya fasa kuma ya kira mu, alama ki saboda yunkurin kisan kai."
Dafe bakinta tayi tare da kallon Noorh.
"Motar da kuka buge bayan shi, ta kamfani ne, kuma ya dauko me kamfanin ne, sai gashi kun buge shi bayan haka kuma kuka kuma buge mishi motar wanda yaja driven shi sai da ya fasa hancin shi, dan haka zamu wuce da ita Office din mu."

     "Akan uban me waye MAHIR?" Inji Noorh, tana isowa gurin. Dai dai dan sanda yana tasa keyarta.
   
    Nan dan sandan yayi mata bayani, ai kuwa tayi tsalle ta dire bata san da zancen ba sai ta ga CEO, ko kuma tayi musu hauka. Mutane dayawa dakatar da ita suka yi. Amma bata ji ba. Fitowar shi tare da Nazzir, tace.
"Ina yake Shi Mahir Hamoud Boualem din."
Nuna mata shi Dan sandan yayi lokacin yana gyaran botirin rigar shi, yana magana fuskar shi a sake.
       "Kaiiii! MAHIR Hamoud Boualem CEO, kazo nan" ta faɗa da karfinta kamar wacce aka karawa karfin hali.

   Bai kulata ba, yayi tafiyar shi. Amma dake yau din tana jin wani irin masifa ce da tsiwa, da sauri ta sha kanshi tare da rike k'ugun ta.

    "Kai waye da zaka saka a kama mu? Eyye kasan darajar dan adam kuwa?  Eyye ka wani dauko farin fuskarka, kasa an kama min yar uwata."

    Kura mata ido yayi yadda take masifa kamar zata kwad'a mishi mari.
"Ke Noorh!"
D'aga hannu yayi tare da musu alama da yatsun biyu, dole Nazzir yayi shiru takaici na kuma kama shi,yarinyar ta lalata mishi kome,
 
Duk wannan shirmen da take bai sanya shi mata magana ba, sai ma ratsa gefenta da yayi tare da wucce ta, zuwa motar shi, aka bude mishi kallon inda dan sandan yake yayi sannan ya mishi alamu ya kyaleta. Ita kan bai kuma bin ta kanta ba. Ya shiga motar shi.  Abu daya ya zauna a kan shi. Ƙwayar idanunta, da kuma yadda ta hana shi cire nikkab din ta.

     Ciwon kai ne ya saukar mishi. Har ya isa Hamoud Boualem Estate.
     Cike da karfin gwiwa yake gyara hannun rigarta, irin yau da bai sake an sake Baby Queen ba, da ta mishi shegen duka. Amma kuma taji haushi rashin tankawar shi, da shegen girman kai a gurin kaman dutsen abuja.
        "Noorh! Dama shine CEO?"
"Oho ina na sani? Bafa shi bane, kuma idan da shine, wallahi korata zayi kawai sun fada ne, dan kar na kwatar miki hakkin ki."

       Isowar Badar ya kalle su, tare da tambayar su, me ya faru da motar Noorh ta gaya mishi. Ita kuma Tasleem ta labarta mishi kanun labaran.

     "Toh wallahi gobe kiyi zaman ki a gidan kawai domin zai kafta miki rashin kirki." Da wannan hirar suka isa gida, tun daga kamfanin bata kuma magana ba, har suka shigo anan taga motar Nazzir.
     Badar yana ajiye su, ya fito daga motar shi, ya tawo gaban ta.
"Meye amfani yarinyar da kuka yi?" Kallon shi Tasleem tayi sama da kasa, taga babu ta inda ya kama Mr Mahir, tsaki taja tare da riko hannun Noorh, duk yadda yaso Noorh ta tsaya Tasleem taki karshe ta tsaya ta mishi tijara, tare da cewa.
"Toh anyi walkiya, kuma mun san kome, dan haka kar mu kuma ganin mutum a gidan nan"

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now