"Ba komai Musa na yafe maka", kiran sauran mutanen yayi yace akaishi asibiti, Amma kafin a d'aukeshi rai yayi hali, Bilal zuciyarshi bugawa kawai take, shi yarasa me yayiwa Daddy yake Neman rabashi da rayuwarshi, tunawa yayi da maganar Minal lokacin datace mishi "Bilal na makance ne ta dalilinka" wani irin zafi yaji kirjinshi yayi mishi, da karfi yace "ina kike beauty? Karkiyi min haka please" hawayene yafara fita a idonshi masu d'umi, hawayen tausayin kanshi, juyawa yayi yashiga mota ya kwantar da kanshi jikin sitiyari idonshi yana fitar da hawaye, hannunshi ya d'aura daidai saitin kirjinshi lumshe kyawawan idanunshi yayi me d'auke da bakin eyelashes, lower lips nashi ya tura cikin bakinshi a hankali yafara tsotsa, idanunshi sai fitar da hawaye suke babu kakkautawa, a hankali ya bud'e idonshi karamin yatsarshi ya zuba mishi ido yana kallon zobenta, cikin  muryar kuka yace "waye zai lallab'eni? Waye zai tausayamin idan ke baki tausayamin ba beauty? Karki bari soyayyarki ta kasheni pleasssss" handkerchief ya d'auko ya share hawayenshi yayiwa motar key, a hankali yake tuki sabida zuwa yanzu har jikinshi yafara zafi, kira'a ya kunna acikin motar yana jin zuciyarshi tana yin sanyi, da yayi niyar yaje Asibiti wurin Latif Amma jin jikinshi kamar zazzab'i yasashi ya wuce gida kawai.

***************
Minal kwance take idanunta a lumshe kamar me bacci, tarasa me yake damunta kwana biyu idan ta kwanta shi kad'ai take kallo, tana yawan tuna moment nata dashi, lokacin daya had'a face dakuma lokacin da yake dariya, Murmushine ya kubce mata Wanda batasan ma tayi ba, wani karamin pillow ta janyo ta rungume sosai tana tuna lokacin da yayi mata fyad'e, kamar dawasa sai taji tanason yakarayi mata koda sau d'ayane....da karfi ta bugi bakinta tace.

  "Me kikeyi haka Minal? Bilal fa sonki yake ba, gara ki dage ki nemi ilimi zaifi miki muhimmanci"
Bubbuga Baby tayi wacce ta zage tanata bacci, a firgice ta mike tace "waye"
Minal tsaki taja tace "Baby sau nawa nake fad'a miki idan zaki kwanta kirika Addu'a?"

  "Wallahi sister sai Nazo kwanciya sai na manta shaf, meyasa kika tasheni ina cikin mafarkin munyi Aure da yaya Mujahid mun haifi yara 'yan biyu kyawawa, yaya mujahid yazo kenan zaimin kiss kika tasheni....Minal ce ta mari bakinta tace "bakida kunya ko Baby? Yanzu ni kike fad'awa wannan maganar?"
Baby ce tayi dariya tace "to miye aciki ai ke babbar kawatace, yanzu fad'amin meya faru?"

  "Baby dama wata Alfarma nakeso kimin"
Baby tace "OK fad'i inji"
"Baby makaranta nakeso naje sabida inason in koyi karatu da kuma rubutu"

  "Bakida Matsala kinfi kowa Sanin Daddy yanason mutumin dayake son makaranta"
Minal tace "eh Amma ni gaskiya ina kunyar fad'a mishi"
"OK karki damu zan fad'a mishi Insha Allah dama kinga gobe zamu koma Abuja inji Daddy"
Minal dariya tayi tace "nagode sister".

  "Bilal a daddafe ya koma gida domin jikinshi yayi mishi nauyi sosai, yana shiga gida lokacin Daddy yafito da sauri da Alama akwai wurinda yakeson zuwa, ido hud'u sukayi da Bilal atake jikinshi yafara rawa, ganin irin kallon da Bilal yake mishi, cikin rawar murya yace "Bilal dama ba Kaine kati Accident da motar ba?"

  "Allah baice zan mutu yau ba shiyasa kaga na tsira, drivern dakuke kulle kulle dashi shine ya mutu acikin motar sabida Allah ba Azzalimin bawanshi bane" Bilal yafad'a cikin kunan Rai idunshi yacika da ruwan hawaye kuma yayi jaa ga zazzab'i ga bak'in ciki, Jan jikinshi yayi da kyar ya isa d'aki yana shiga yasawa kofar key yafad'a akan gado, bargo yaja ya lullb'e jikinshi dashi, a halin yanzu jikinshi yafara rawa kamar mazari, wayarshi ya d'auko yakira nombar Latif yace "Latif motarka tana cikin gida makullin ma tana ciki kazo ka d'auka idan ka samu hanya" d'itt ya kashe wayarshi gaba d'aya ya cillata gefe yayi rub da ciki.

  Daddy ya iya rud'ewa ya rud'e, wayarshi ya ciro jikinshi yana rawa yakira Alhaji Nura " Hello Alhaji Nura akwai matsala fa"
'Dayan b'angaren Alhaji Nura yace "Allah yarabamu dashi, Meya faru?"
Alhaji Nura Bilal fa ya gane abinda muke aikatawa Asirinmu fa ya kusa tonuwa"
 
  "Asirinka dai yakusa tonuwa Alhaji Umar, nida kake ganina Banida wata matsala sabida Bilal bazai tab'a sanin inada sa hannu a cutar dashi ba, sabida haka kaika jiyo nikam karka sake kirana awaya domin idan ka kara zan gama tona maka"
"Baka isaba Alhaji Nura tare muka fara kuma tare zamu gama"
"Dakata, Alhaji Ba tare muka fara ba ko ka manta ne in tuna maka?"
Daddy yace "OK Dan Abu yana so yablalce shine zaka barmin ko? To muzuba mugani nida kai shege kafasa"
Alhaji Nura yace "muzuba mana sai me" kitt ya kashe wayarshi.

  Daddy ne yafara juye juye acikin gida yakasa tsaye yakasa zaune, Hajiya Babbace ta leko ta side na parking space sai taga Daddy yana zirga zirga, da sauri ta karasa wurinshi tace "Umaru Lafiya kake kuwa?"
Daddy ne yajuya idanunshi sunyi jaa yace "Mama? Yanzune ya kamata nad'au hukunci me zafi akan dukiyar Dana dad'e ina sa rai, Bilal yagano cewa ina mishi mugunta kuma inason dukiyarshi, Alhaji Nura ya juyamin baya har yana ikirarin cewa muzuba mugani, idan har na sake na kyale Alhaji Nura to hakika zaiyi b'arna sosai ta wajen b'atamin plan Dana dad'e inayi, kinsan me zanyi?"
Hajiya babba tace "ina zan sani"
Wata muguwar dariya Daddy yayi yace.

  "Kashe Bilal zanyi da hannuna sannan in d'aurawa Alhaji Nura hakkin kisan akanshi, daganan sai in kwashe dukiyar inyi yanda naso, Mama nasan bakisan wani Abu ba ko? To yau zan fad'a miki wata sirri, Mahaifin Bilal da Mahaifiyashi da kanwarshi nine nayi sanadiyyar mutuwarsu a lokacin da sukazo gaisuwan rasuwar maman Sabir, nine na kwance birkin motarsu ta yanda idan sukayi tafiya me nisa dole zasuyi Accident, kinsan dad'in danaji lokacin dana ga gawarsu kwance akasa?"

"Amma Umaru Ka samu tab'in hankali ko? Domin na tabbata kanka ba d'aya ba kake wannan maganar, dolene anjima muje Asibiti a dubaka"
Dariyar rainin hankali Daddy yayi yace "idan kin yadda kaina ba d'aya ba to hakan yake, kirike wannan maganar domin koda wani tsautsayi ya gibta aka gano nine nayi kisan to duk Wanda yaji kaina ba d'aya ba dolene ya kyaleni koda ko Alkali ne"
Yana fad'an haka ya juya yabar wurin yana dariya.

  "Da sauri Latif ya danna stop akan wayarshi dayake d'aukan videon Daddy, jikinshi har rawa yake tsabar tsorata, da sauri ya karasa wurin motarshi.
Daddy ne yayi dariya yace

"sannu da d'aukan video Latif, yaro bakasan zafin wutaba sai ranar daka taka"
Yana fad'an haka yaciro wayarshi yakira wata nomba, yace "Ku tsaya akofar gidana akwai wata bakar motar dazata fita yanzu, inaso kubishi har inda zaije idan yafito Ku nuna mishi bindiga yabaku wayarshi inaso Ku fasa wayar kuyi kaca kaca da ita kada kutab'ashi wayar kawai zaku fasa"
Yana kashe wayar ya kwashe da dry.

  Latif dad'i yaji daya samu yad'au videon "Allah yakawo karshenka Alhaji Umar"
Yana zuwa kofar gida yaga wasu gardawa tsaye da bindiga a hannu, da sauri ya koma mota yana kokarin gudu, suma da gudu suka karasa wurinshi d'ayanne ya nunawa Latif bindiga yace "bringam your phone"
Latif yace "me zakuyi da wayata?"
"Ok tambayarmu ma kake? Zaka kawo ko saina tarwatsa maka kai da wannan piston d'in?"

  "Latif ganin mutanen ba imani ne dasuba yasashi Ciro wayarshi yamika musu, yanaji yana gani suka had'a wayar da kasa, saida wayar yayi kaca kaca ba'a ganin komai kafin suka bar wurin, bakin cikine ya lullub'e latif shikenan sun b'ata mishi plan".

   "Minal da Baby had'a kayansu suke domin da karfe 9Am zasu d'au hanya, Minal ce tayi baya baya ta fad'a akan gado tace "wash Allah na gaji Baby bayana har ciwo yake" tafad'a cikin shagwab'arta,
Baby ce yayi dariya yace "Dama ai ke raguwace ba kad'an ba"
Dariya Minal yayi yace "nice raguwar?"

  "Eh mana ke ai mijinki yana tare da wahala ba kad'anba"
Minal ma tayi dariya tace "shifa yanada shagwab'a sosai, kinga ai Nima zai barni nayi nawa"
Baby tace "wato kinada saurayi kike b'oye min ko? To maza kibani labarinshi"

  Minal dariya tayi tace "hmm zandai baki kad'an daga labarinshi, shi dogone fari yanada yawan sumar kai, yanada dogon hanci sannan bakinshi karami ne, idanunshi manya ne yana d'auke da gashin ido dogo dogo, yana yawan yamutsa gashin kanshi Wanda hakan ba karamin kyau yake kara mishi ba, yana d'auke da pink lips, idan yayi dariya kumatunshi lotsawa suke" Pillow ta janyo ta rungume sosai, lumshe kyawawan idonta tayi a hankali ta bud'e bakinta kamar batason yin magana tace "yanason kamshi sosai, yanada sexy eyes, ke idan nace zan baki labarinshi tofa zamu kwana mu tashi ban gama ba, sannan kinsan me?"

  "Aa sai kin fad'a"
Baby duk lissafin danake miki ni kad'ai nake kid'ana kuma ni kad'ai nake rawana, shi baisan ma inayi ba, kinga mubar maganar nan domin b'ata lokacine, shikuma lokaci abune me muhimmanci, sabida Allah ma yayi rantsuwa da Lokaci inda yake cewa acikin suratul Asr (wal asr) Allah yace nayi rantsuwa da lokaci, (innal insana lafi khusur) lalle mutane suna cikin Asara (illallazina Amanu wa amilussalihati watawa saubil hakki watawa saubissabr) saidai wad'anda sukayi Imani sukayi tawassali da gaskiya kuma sukayi tawassali da hakuri".

  Baby tace "lalle Minal kinada ilimin addini inama ace nice ke, sabida iyaye yanzu sunfi baiwa ilimin boko muhimmanci akan ilimin addini, sun manta cewa shine zai Amfanemu a Lahira"

  "Shiyasa nace miki lokaci yanada muhimmanci Baby, yanzu ma lokacin be kure miki ba zaki iya koya idan kikasa kai".

✔ote & comment

  *Wattpad*

_@Jiddah S Mapi_

MAKAUNIYA CE Место, где живут истории. Откройте их для себя