Saukar hawayenta yaji a kirjinsa, sai ya ji su kamar tafasasshen ruwan zafi, ba dan suna da zafi ba sai dan kima da daraja da hawayen nata suke da shi a gurinsa, da sauri ya dago kanta ya kalleta. Idonta sun kumbura ba kukan yau kadai ba har da wanda tasha jiya da dare, yasan wannan hawayen ma baya rasa nasaba da daren jiya, dare mai kima da martaba a gurinsa. Goshinta ya sumbanta sannan ya kai hannu ya rika lallausan hannunta mai kamar kasa yana murzawa a hankali.

“Ban tashe ki dan na katse miki bachi ba, sai dan kusantarda ke ga wanda ya baki ikon yin bachin, asuba tayi tun dazu ya kamata ki sallah tukuna sai ki koma bachin, nasan kina bukatar hutun, a gafarce ni gimbiyata idan kin yi sallah sai ki kwanta”

Dagowa tai ta kalleshi wani irin tsana da kiyayyarsa ce ta cika mata ido ta sauka har cikin zuciyarta, bata jin rashin sonsa ba sai yau, jin tai kamar shine ya cilasta mata aurenta ba ita ta tsara komai ba. Duk farin fatarsa a yau baki kirin take ganinsa saboda ya rabata da abunda zai kara mata martaba a gurin Sadiq, kuma ya yarda cewar ta rike masa alkawari.

Sauka tai saman jikinsa ta kai hannu ta janyo Bedsheet din ta nade jikinta ta soma takawa kamar zata fadi, da sauri yaje ya rika ya kwanto da ita jikinsa.

“Lemmi help you”

Da taimakonsa ta kai kanta bandakin da kansa ya hada mata ruwan wanka.

“Zaki iya ko na taimaka miki?”

Ya tambaya yana kallonta cike da so da kauna.

“Zan iya”

“Okay”

Sai da ya sumbace ta sannan ya fice daga bathroom din. Hakan ya bata damar fashewa da kuka ba tare da sauti ba, tai ta rare kukanta tana tausayin masoyinta da kuma jin nauyin alkawarin data karya.
  Bayan ta gama kukan tai wanka tsarki tare da wankan sabulu sannan tai alwala ta dauki tawul din ta daura ta fito daga bandakin. Wardrobe taje ta bude ta dauko wata atamfa ta saka ta saka Hijab ta gabatar da sallah asuba. Bayan ta gama tai zaman jiran taji ya dawo dakin bata ji ba sai ta tashi ta leka falon nan ma bata ganshi da sauri ta dawo ta dauki wayarta ta saka number Sadiq ta kira ta koma can karshen dakin yadda ko ya shigo ba zai iya jinta ba ko da ya shigo ya tarar tana wayar. Sai da tai ringing har ta katse ta kara kira sannan ya daga kuma yai shiru yana jiran ta fara magana.

“Sadiq ya jikinka?”

Shiru yai yana tunani, ashe da gaske ita ce ta zo.

“Miyasa kika kira ni? Ko baki san kina da aure ba?”

“Na sani kawai na damu da lafiyarka ne”

“Ya akai kika san ban da lafiya”

“Yarinyar data kade ka ta kirani da wayarka ta sanar min a daren da abun ya faru”

“Ke ce kika zo nan da safe duba ni?”

“Ni ce”

“Ya akai kika dauki kiran a gaban Sadam”

“Baya kusa lokacin data kira wayar?”

“Zuwan da kikai nan fa?”

“Maganin bachi na saka masa”

Unkura yai ya tashi zaune.

“Da gaske?”

“Eh”

“Ina kika samu maganin?”

“Na siya ne tun kamin a daura auren”

“Saboda me?”

“Saboda kai, Sadiq kasan saboda kai nai auren nan, komai da nai saboda kai ne, na daukarwa kaina alkawarin zan dawo gareka komai runtsi komai tsanani, zan adana soyayyarmu saboda ni da kai, ban san tsawon lokacin da zan dauka ba, amman tabbas zan dawo gareka, zamu yi irin rayuwar da muke burin samu, zamu biya kudin mu samu farinciki da kwanciyar hankali kamar kowa, kawai ina son kai min alkawarin cewar ba zaka auri wata ba kuma zaka jirani har zuwa lokacin da kaddara ta tsara zamu zama abu daya... Ina sonka Sadiq ina sonka sosai Wallahi saboda kai ne zan dawo gareka Sadiq ko yaushe ne Sadiq....”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now