CHAPTER 2

2.7K 216 20
                                    

Zaro ido tayi kamar mujiya ganin Wanda tayi wa aika aikar ba kowa bane sai crush dinta kuma malaminta Wanda take matukar kauna saide ta lura kamar ma bai taba lura da ita ba.

Mikewa tayi sum sum ta shige aji abinka da masu waya har an dauka an fara yadawa. Shi kuwa gida ya nufa ya Kira class rep yace yayi shifting lectures din zuwa 3:45pm dama 3:00pm za'ayi yace suje suyi sallah sai a dawo sannan ace ma marakisiyya musbah Aminu taje office dinsa ta jira sa.

Haka ko akayi class rep yace "class, good day to you all! I just spoke to our lecturer and he said the lecture has been shifted to 3:45 I think that must be due to the accident of collision theory we just witnessed.😂😉  Thank you!" Wato

"Yan aji barka da yau! Yanzun nan mukayi magana da malamin mu kuma yace an matsar da lecture din zuwa karfe uku da arba'in da biyar Wanda nake tunanin saboda abinda ya faru ne Wanda muka kalla yanzu.😂😉" Ya fada cike da miskilanci

Kunsan yan jami'a ba'a rasa zogaye nan de suka hau ife ife su. Marakisiyya tazo zata fita wani yasha gabanta ya fadi a kasa tace baby ni bazaki fado jikina bane ? Abokansa suka kyalkyale da dariya. Da ta daga kafanta bata sauke ko ina ba akan .......

Ta take ta mutsittsike yana ihun yana kururuwa ganin zatayi kisa ne yasa Beeba janye ta itako fadi take barni inci..... sa,sh*ge Mara mutunci ana kokuwa da ita sanda mansura tasa hannu tukunna ta bari. Class rep ne yace Ayya kekam marakisiyya sunanki sorry a makarantar nan toh kije office din malam Ahmad level coordinator dinmu yace ki jirasa sannan kuma bayan kun gama mu hadu a office din HOD.

Yana kaiwa nan  yan ajin suka sa ihu ana shewa ana saikayi our one and only class rep. Hatta saurayin da ya tsokaneta aikin class rep din ne Dan haushin clique dinsu suke ji badan komai ba kawai sai Dan sun kare mutuncinsu basu shiga hayaniya.

Gumi ne ya tsattsafo Mata sanda suka nufi office din malam Ahmad tunda take ko kallonta a aji bai taba yi ba. Ko tambaya yayi ta daga hannu baya zabarta kai koda ita daya ta daga hannun ya gwammaci ya fadi amsan da ya zabeta.

Hanky mansura ta ciro tana goge Mata gumi tace haba marakis ya kike Abu kamar ba big girl ? ba ji yadda kike gumi sai kace kin kashe mutum yo ko filin alkiyama albarka. Beeba tace banda filin alkiyaman de. Hawaye ne ya silalo wa marakisiyya tace waiyo Allah ya zanyi beeba? Mansura ku bani shawara kunsan ko magana bana iyayi a inda yake jikina sai yayi rawa ko tunaninsa nayi tsikar jikina tashi yake. Gashi gani nake kamar ya tsaneni. Kuma ni kaunarsa nake wallahi kunsan banida wani Wanda nake crushing akai  irinsa.

Wani numfashi taja Wanda ya bawa su beeba tsoro Dan sun dauka suma ma tayi. Jin  tace "na shiga uku tana dafe kirji ta daura hannu aka idan ya bani carry over fa kinsan phy 304 prerequisite ne😭" yasa hankalinsu kwanciya.

Da fari mansura ta dauka drama ce irin ta marakisiyya amma ganin da gaske take yasa tace kiyi hakuri mana kinsan bazai baki carry over ba kodan mahaifinki saide idan da gaske faduwa kikayi kuma AI kinada kokari sosai ba saide hassada kece fa me highest Gp na 3 a ajin mu shiga ki jirashi mu zamuje mu warware matsalan d'an tashan can a office din HOD.

Godiya tayi musu ta shiga tana addua duk wacce tazo mata yayinda kirjinta ke dukan tara tara. Gashi gaba daya abinda ya faru dazu ya daga Mata hankali saboda Abu kankani ke motsa ta. Zugi maranta ya soma Mata ganin babu sarki sai Allah kawai sai ta fashe da kuka.

Malam Ahmad kuwa yana gama fadawa class rep sakon sa ya kunna motarsa yabar makaranta ya nufi gidansa domin ya canja kaya. Tuki yake ya Dan kanne ido daya yana nazari sosai wannan yarinyar is different from others... baya kyankyamin ta kamar yadda yake kyankyamin sauran Mata. 😳(kyankyami kuma?)

Hasali ma burgesa take yi, bata kula maza batada hayaniya kamar shi. Shima haka yake ko magana bayason yayi idan ba formal ba kamar lecturing ko meeting haka. Toh ai ga irinta nan dalilin da yasa baya ko San shiga harkarta kenan saboda yadda take like ma tunaninsa.  Bawai he is attracted to her ba amma kawai burgesa takeyi ko kuma yace hanasa sukuni take toh yau dole ayita ta kare dole ya titsiyeta.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now