chapter 030: 💞 The decision 2 💞

743 80 2
                                    

💝Ni Nuwaylah💝💝
☆☆na☆☆
👑👑Bilqeessah Alpher 👑👑
📚📚Marubuciyar 📚📚
🖤🖤🖤BAKAR ZARGI🖤🖤🖤

✍Alpher's pen*
Bismillahir Rahmanirr Raheem

The next day mummy na hada kayan daddy because washegari zai koma duty post nashi, daddy yace
"Sweet, zo ki zauna akwai wata maganar da nakeson muyi"
Mummy ta zauna kusa dashi, ya kamo hannunta ya rike yace
"Akan maganar yaran nane, bayan dogon nazari na sami mafita, wanda nayi istihara akansa kuma na tabbata itace the only solution to be just to both parties, so na yanke hukuncin haddasu aure."
Mummy ta mass kallon bata gane ba tace
"Wani yaran?"
"Abdullah da ita wannan yarinyar Nuwaylah"
Mummy tayi saurin zare hannunta daga nashi
"It's a joke right? Because that won't be possible!"
Daddy ya kalleta cike da mamaki yace
"Why?"
"Yarinyar da bamu san asalin taba bamu gasgata abinda tace ba zamu dauka muba dan cikin mu da nufin aure?"
"I thought da kanki kikayi confirm abinda ta gaya miki, why yanzu kice ba gasgata abin ba"
"Ni dai ban yadda da wannan hadin naka ba, me kakeson duniya suce? Why not we should just settle her kawai?"
"Settle her? With what? Money? Amma kin ban mamaki, kinajin tsoron abinda duniya zasuce akan danki amma baki damu da halin da maraniyar Allahn nan zata shiga ba. I thought you're a human rights activist or the rule does not apply to your son."
Mummy batace komai ba for like 1min sannan tace
"I know that nothing can justify what he has done but marrying her is out of the picture. Please reconsider to avoid making mistakes".
"That's my final decision!"
"Then it's a rash decision. Did you at all consider your son? Nayi imanin cewa baka ji nasa ra'ayin ba. You can't force him to marry someone he doesn't love, sai dai kawai in kanason ruguza masa rayuwa."
Daddy yayi murmushin takaice yace
"Ko ya so ko yaki sai ya aureta, ko ki amince ko ki ki"
Yana gama fadin haka ya fita. Mummy ta ciza lebanta, tasan da kyar yayi averting din maganarsa. Gashi babu wanda zata iya tinkari da maganar a familyn ya magance mata shi kasancewar kowa na tsoron shi.
She wondered why he decided to turn deaf ears to what people might say, yanzu wani irin aure yakeson ayi?
Bazai taba yiwu ayi aure da cikiba definitely sai ta haihu, inko hakane ta yaya zasuyi presenting babyn a matsayin jikarsu.
Shima yasan duniya bazasuyi shiru ba and it's not possible suce silent wedding akayi, they are public figures not just ordinary people.
She kept pondering about it har sai da yamma da ya dawo, tayi presenting fears nata but duk inta ta shiga sai ya nemo mafita, daga karshe sai kawai ta fashe da kuka tana rokansa still hakuri ya bata, he just want to be fair to the poor girl.
Dole ta hakura tace Allah Yasa shine mafi alkhairi, daddy ya jawota jikinsa yace
"Ameen now you're talking like my sweet Sallama"
Murmushi tayi da ya bayyana dimples nata ta kara shigar cikin jikinsa ta ɗora kanta kan kirjinshi.

Thank you all for being patient with me 🙏🙏🙏

Ni Nuwaylah A Hausa Love StoryWhere stories live. Discover now