Amaikon yashiga mota yatafi sai naga yabi wani hanya daban dake cikin gidan, wani waje me kyau naga yashiga.

Lambu ne me ɗauke da kayan itatuwa daban daban, plastic chair ɗaya nagani daidai wajen wani bishiyan Mango, iskan wurinne yake shiga jikinshi ahankali yafara samun nutsuwa, jingina yayi ajikin chair ɗin, yaɗaura kafarshi ɗaya akan center table ɗaga kanshi yayi yana kallon sama.
Hawayene yafara fita a idonshi zuciyarshi tana mishi raɗaɗi.

Aduk lokacin daya tuna rayuwarshi nabaya, sai yaji yana tausayin kanshi, sai yaji inama daba'a haifeshi ba, runtse idonshi yayi yana tunanin rsyuwarshi nawasu shekaru dasuka wuce.

_wanene Bilal_

BILAL IBRAHIM USMAN shine asalin sunanshi, Yarone ga Alhaji Ibrahim me gold.

Alhaji Ibrahim asalin bafulatani ne ɗan garin Gombe ne, iyayenshi masu kuɗi ne, yagaji saida gold awajen mahaifinshi Alhaji Usman me gold,
Alhaji Usman me gold yanada arziki sosai, mata biyu ne dashi Hajiya rukayya dakuma Hajiya salamatu,
Hajiya Rukayya itace uwar gida, Allah bai baiwa hajiya Rukayya haihuwa da wuriba shikuma Alhaji Usman ganin Irin dukiyar daya tara ace bashida ɗa ko ɗaya? Hakanne yasashi kara Aure, shine ya Auri hajiya Salamatu, bayan Aurensu da shekara Biyu ne hajiya Salamatu tahaifi ɗanta, murna awajen Alhaji Usman baya misaltuwa, tun daga ranan da Hajiya Salamatu tahaihu tin lokacin hajiya Rukayya bata kara samin farin ciki acikon gidanba, wulakanci kala kala take gani agidan.

Bayan wasu shekarune itama hajiya Rukayya Allah yabata ciki, murna Alh Usman yayi sosai tindaga ranan tazama 'yar gata awajen Alh Usman, ranan suna yaro yaci sunan mahaifin Usman wato Ibrahim.

Ibrahim kyakkyawa ne sosai, hakan yasa Alhj Usman idan ze tafi office to Ibrahim yana gefenshi, abun yana kona ran Hajiya Salamatu, hakan yasa taɗauki karan tsana taɗaurawa Ibrahim.

Alokacin da Allah zai ɗauki ran Alhj Usman, tara iyalanshi yayi yace "kunga yanda nake ciki rai ahanun Allah, addu'arku nake nema, kona mutu kada kudaina yimin addu'a".

Kafin yarasu saida tarabawa kowa gadonshi.

Bayan rasuwarshi ne hajiya Salamatu mahaifiyar Umar, tasace takaddan wani company wanda yake mallakin Ibrahim ne,
Hajiya Rukayya tanaji tana gani aka hanata hakkin ɗanta, hakuri tayi taci gaba da zama agidan.

Kwatsam wata rana sai aka wayi gari Hajiya Rukayya ta tashi da tsananin ciwon ciki, kiran Ibrahim tayi, tayi mishi nasiha sosai tare da faɗin "Ibrahim kaga ka mallski hankalinka, inason idan namutu karka zauna agidannan katara dukiyanka kagudu sabida tsaro kaji?"

Ibrahim ne ya giɗa kai yana kukan tausayin mahaifiyarshi, haka har Allah yakarɓi ran Hajiya Rukayya, Ibrahim yayi kuka kamar ranshi yafita, haka aka ɗau gawan aka tafi da ita.

Adaren Ibrahim yatattara komai nashi yabar gidan,
Wani unguwa yakoma yasayi gida ysci gaba dazama aciki, yana kasuwancinshi yanda yaga mahaifinshi yake,
Har wata rana aka wayi gari yazama me kuɗin gaske,
Abokinshi ɗayane wato Alhaji Kabeer "Mahaifin Latif"

Alokacin dayayi kuɗi lokacin yahaɗu da mahaifiyar Bilal wato Khadija, Khadija tanada nutsuwa sosai gata da kyau kamar me, itama fulana ce 'yar asalin garin Gombe,
Anyi Aurensu suna cikin kwanciyar hankali.

Haka har Allah yabasu Haihuwan ɗa namiji, murna awajen Alhaji Ibrahim sai godiya, ranar data haihu saida yabawa mutane kyautar kujeran hajji.

Ranan suna yaro yaci sunan Mahaifin Alhaji Ibrahim wato Usman Amma suna kiranshi "BILAL"

Bilal yarone kyakkyawa wanda yake kama da mahaifinshi kamar an tsaga kara, hakan yasa Alhj Ibrahim ɗaurawa yaron "so" fiye da tunanin me karatu,
Bilal yasamu gata,
Alhj Ibrahim bayason yaji kukan Bilal ko kaɗan, hasalima akan Bilal suna iyayin kwana uku basuyi magana da Hajiya Khadija ba.

Idan tace "Alhj karage son yaronnan sabida ze iya zama maka damuwa idan baya tare dakai"

To ranan zaiyi zuciya, wai tana cewa yadaina son ɗanshi, ita kuma sai tace Allah yabaka hakuri.
Bayan wasu shekaru ne Allah yakara bawa hajiya Khadija ciki, makka Alhj Ibrahim yakaita yace tahaihu acan.
Bsyan tahaihu ne tadawo da 'yarta fara sol me kama da ita,
Bilal aduniya ba abinda yatsana kamar yaji kukan kanwarshi wato "Nabila" idan tana kuka sam baya gane hankalinshi.
Sun shaku da Nabila sosai, zaman jin daɗi da kwanciyar hankali ake agidan.

Kwatasam sai wata rana aka kira Alhj Ibrahim cewar Matar Yayanshi wato Alhj Umar tarasu,
Gani yayi bazai iya fasa zuwa ba, cewahajiya Khadija yayi kishirya muje mugaidasu keda Nabila, shikuma Bilal zan ajeshi awajen aiki.

Hajiya Khadija ce tace "haba Alhj Kadubafa kaga Bilal yanda yagirma, be kamata ace har yanzu kana kaishi office ba"

No hajiya wannan tsakanina da ɗana ne,
Hajiya khadija taja baki tayi shiru.

Ahanyansu nazuwa ne Bilal yake cewa "Daddy nima zanje nizan jamu amotar"

Aa Bilal kabari kawai gobe sai kaje amma yau inason akwai aikana dazaka karɓamin a office,
Bilal yace to Daddy.

Nabila ce tace "yaya yau zaka siyamin icecream irin najiya?"

Dariya Bilal yayi sannan yayi mata kiss agoshi yace "insha Allah my lovly sister"

Dariya tayi ta rungumeshi,
Hajiya Khadija ce take kallonsu haka kawai taji zuciyarta tana bugawa.

Alhaji ko zamubar Nabila ce suwuce office da Bilal?
Alhj yace Aa hajiya barshi yahuta,
Hajiya tace to.

Suna sauke Bilal yayiwa Nabila kiss agoshi, Daddy yace "ni bazakamin ba?"

Dariya Bilal yayi ya sumbaci Daddy agoshi, yajuya yace "Mommy saura ke"

Hajiya tace ban roka ba,
Dariya sukayi duka kafin Bilal yasumbaci Mommy yawuce office,
Juyawa yayi yace Daddy kayi tuki ahankali dan nasan kafara tsufa,
Harara Daddy yayi mishi yace "ja'irin yaro"

Hajiya khadija tace "karka tsufar min da miji"

Dariya yayi yawuce yatafi yana mejin farin ciki aranshi.

Da yamma Bilal suna zaune a office shida Latif abokinshi tin suna yara, yaji karan wayanshi, numban Daddy yagani yaɗaga yace "Daddy na, kun dawo ne?".

Muryar wani yaji yana cewa "Wannan mutanen motar sun mutu tasanadiyar hatsari dasukayi, babu wanda yafito da rai acikinsu,
Yanzu gawansu yana Federal center azo aɗauka, ɗitt aka kashe wayar.

Bilal ya bushe awajen, wayan yafaɗi ahanunshi Amma har yanzu hanunshi akunnenshi,
Latif ne yake tambayarshi meya faru?

Kaini Federal center shine abinda Bilal ya iya faɗa.

Latif ne yaja hanunshi yayi hanyan waje dashi,
Amota yasashi kafin yashiga motar suka fice da mugun gudu.

Duna zuwa Asibitin faderal center, wani doctor ne wanda yasan Bilal yayi musu iso Zuwa wani ɗaki,
Suna shiga ɗakin Bilal ne yafara hango mutane uku kwance an rufesu da farin kyalle.

Saurin karasawa yayi,
Yana zuwa yafara kokarin buɗesu.

Fuskar Daddy yagani wanda duk ya ɓaci da jini an rufe da bandage,
Yabuɗe ɗayan yaga fuskar Mommy ma babu kyaun gani,
Rufewa yayi da Sauri yabuɗe na Nabila,
Saurin rufewa yayi, yasa kanshi akan Nabila hanunshi rike dana Daddy da Mommy, ihu ya kwala yana buga kanshi jikin Nabila.

_✅ote comment and share_

✍🏻 *Jiddah S Mapi*

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now