_Minal_
Sauri take ta iso gida dan jikinta raɗaɗi yake mata ko ta ina, duba hanunta tayi taga yanda yayi jaa, sai kawai tafashe da kuka, gani take kamar bazata iso gida ba.

Wani me Napep ne yace "ina zuwa hajiya?"

Minal tace "bayan kasuwa"
Yace shiga mutafi.

Minal ce tashiga Napep ɗin suka tafi.
Suna isowa bayan kasuwa daidai kofar gidansu tace "anan zaka saukeni"
Me Napep yana sauketa ta ruga dagudu tabar wajen.

Ke ke ke tsaya kibani kuɗina, ina zakije?
Kafin yakarasa Minal tayi kwana, yanemeta sama da kasa be ganta ba,
Idan nakama ta saita yabawa aya zakinta cewar me Napep.

"Minal kuwa gudu take harta isa gida, tana zuwa ta tsaya abakin kofa tagyara jikinta tsaff kafin tashiga gida,
Tana shiga tasamu Umma tana tsince shinkafa,
Zama tayi agefen Umma takwantar dakanta ajikin Umma,
Cikin shagwaɓa tace "Umma nagaji wallahi"

Umma ce tace "sannu Minal tawa, insha Allah gobe zaki huta, Minal tace "Umma idan nazauna agida ban fita talla ba me kike ganin zamuci?"

Umma ce tayi shiru sabida tasan Minal gaskiya take faɗa,
Tashi kije kicire kayan jikinki sai kiyi wanka,
Minal tace "to Umma amma fa yau nagaji saide kimin wankan"

Umma ce tazaro ido tana kallon Minal tace "yanzu Minal kina katuwa dake zanyi miki wanka?"

Tashi kibani waje,
Minal ce ta tashi tana wani shagwaɓewa, tace Umma to ai har yanzu ni yarinya ce.
Shiru Umma tayi tayi mata sanin halin Minal na shagwaɓa.

_Washe gari_

"Bilal Ne yake lulluɓe cikin bargo, kanshi yana kallon sama, tunani yake.
Tayaya za'ace ya Auri Afrah? Anya wannan ba shiri bane akeson ayi mishi? Ya tabbata da Daddynshi yana raye bazai taɓa yadda ya Auri mara tarbiya ba".

Yana cikin wannan Tinanin yaji an buɗe kofarshi ko knocking ba'ayi ba,
Afrah ce tashigo da gudu tafaɗa jikinshi tana kuka.

Tureta yayi ajikinshi yace "ke bakida hankali ne? Meyake damunki ne? Ko aljanune dake nikam?"

Afrah ce tafashe da kuka tace "yaya Daddy ne yace nahakura dakai"

To sai me dan yace kihakura dani?
Ai gaskiya yafaɗa miki.
Look idan baki tashi kin fita aɗakinnan ba, zanyi maganinki yanzu.

Bilal saide ka kasheni wallahi amma bazan daina cewa ina sanka ba... Mari Bilal yasauke mata afuska yace "get out"

Yaya nika mara? Cewar Afrah.

An mareki ko zaki rama ne?

Yaya tinda na nuna maka "so" baka gani ba, kuma na nuna inasan ka Aureni kaki, duk na hakura.

Amma tinda kaɗau
Hannu kamareni, nibazan iya marinka da hannuna ba, sabida har yanzu ina sanka,
Amma kasani saina mareka da abinda yafi hannu ciwo,
Tana faɗan haka tajuya tafita a ɗakin.

Bilal yace "idan kin fasa ba'a haifeki ba"

Riga yaɗauko acikin kayan wani lemon colour, sawa yayi ko tsayawa yin wanka beyi ba,
Makullin motarshi yaɗauko yafice aɗakin.

Daidai zai fita a falone yaji Hajiya tana kiranshi.

Bilal tsaya.

"Tsayawa yayi yana kallonta harta karaso"

Bilal dama hakuri nakeson baka akan abubuwan dasuke faruwa agidannan, shima Alhajin yace in baka hakuri sabida bayajin daɗin yanda kake zama cikin takaici kullum, dan Allah kayi hakuri.

Bilal shiru yayi yana kallon Hajiya wato mahaifiyar Afrah, yace ba komai hajiya, ai Afrah kanwata ce, komai tayi nasan yarintane.

Hajiya tace to Bilal an gode,
Bilal besake cewa komai ba yajuya yayi tafiyarshi.

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now