"Relax Rahma. I promise I'll come back as soon as possible" Kuka Rahma ta sake sawa tana girgiza kanta.

"He also promised to come beck amma where is he? He broke his promise and left us alone. And Aunty followed him shortly. You're the only one remaining please don't leave".

Rungumeta Ummul Khair tayi tana shafa bayanta.

"Bumblebee" ganin Jannah a bakin toilet yasa Uncle Abdul karasawa inda take. "Come" zaunar da ita yayi gefen Rahma yana mata bayani. "I promise I'll be back" shiru tayi batace komai ba illa ido data zuba mishi.

"Say something Bumblebee". Uncle Abdul ya kura mata ido. Tun ranar da Sumayyah ta rasu bata sake magana ba har rana kamar ta yau. Ko kuka bata yi.

Da kyar Ummul Khair tasa Rahma shan custard. Har kuka sai da tayi kafin Jannah ta sha spoon biyu. Ba karamin tausayi take bata ba. A ce har sati uku da cannula a hannunta. A kowani lokaci sai dai a saka mata drip ko a mata nutritional injection. Dan tana yawan suma akai a kai tsananin yunwa da damuwa da rashin kwanciyar hankali. Kuma ko bacci bata yi.

Kwana goma sha daya da tafiyar Uncle Abdul ya dawo. Alhamdulillah an gano ba kowa bane me barnan illa manager na J stones da accountant na Rahma Textiles. Ba karamin wahala ya sha ba amma Alhamdulillah har bashin da ya bayar  sai da ya tabbatar ya karbo kuma ya maida wanda ake binsa. Haka zalika  Sumayyah.

Sai dai ba a kulle bakery na  Sumayyah me suna Jannah's ba  kuma ba a kulle Rahma desserts da  Sumayyah Catering ba.

Yaune kawana  arba'in da rasuwan Al'amin. Kamar yadda addini ya koyar aka raba gadon sa. Daga ciki an mallakawa Rahma kamfaninsa na kaya Wanda ya bude da  Rahma Textiles wanda tun asali da sunanta ya siya saboda koya mutu yasan ya bar musu wani abbu. Jannah ma an mallaka mata J stones shima company na na jewelries da duwatsu masu daraja irinsu diamond, gold, Ruby da sauransu.

Kara Jannah ta sake sai kuma ta fara kuka ganin dagaske mahaifinta ya rasu. Karo na farko kenan da ta fara kuka ganin dagaske ba zai dawo ba. Kuka me sosa rai ta ke tana Kiran sunan Babanta da mamanta. Numfashi taja sai kuma ta yanki jiki ta suma.

Bayan ta tashi aka cigaba da rabon gadon duk da cewa ta kankame Rahma tana kuka ranta kamar zai fita.

Ba a saka Rahma Textiles da J stones a cikin gadon ba tunda tun asali mallakinsu ne.

Ganin hakane  Ya Umar ya taso yace ai Rahma ba yar cikin Ahmad bane yar riko ce. Rahma dake kuka konkallonshi bata yi ba dan ita kadai tasan abin da take ciki. Kafewa Ya Umar yayi yace bata da gadonsa.

Ganin haka Uncle Abdul ya dauko wasiyyan da Ahmad ya bari kafin ya rasu. A ciki ya rubuta idan aka tashi raba gado a raba da Rahma kamar yanda za'a raba da Jannah.

Ga kuma littattafan gidaje da sunan Sumayyah da Rahma da Jannah. Ga na filaye da motoci da sauran kadarori. Ya Umar kamar yayi hauka ganin irin arzikin da ya sa sunnan yaran tun kafin rasuwansa. Yasan ko ba'a basu komai a cikin gadon ba sun raba hanya da talauci har abada.

Da ga karshe banda Umma ba Wanda ya tashi da komai Illa shares nashi na family business me suna The Jalal Brothers  da sukeyi su hudu wato Abbul Khair da Ya Umar da Ahmad da Uncle Abdul. Shima ya rubuta kuma yayi signing akan cewa idan ya mutu ya yafewa en uwansa rabonsa.

A ciki Abbul Khair da Ya Umar da Uncle Abdul suka samu million 200 da dubu dari bakwai da talatin. Ba karamin haushi Ya Umar yaji ba ganin ko million dari na kanshi be samu ba.

Da misalin la'asar su Jannah suka shigo cikin gidan. Kin barin jikin Rahma tayi ko na minti daya. Ko da suka shiga daki rungumar Rahma tayi tana kuka me taba zuciya.

Tsoronta daya kar abin da Ya Umar ya fada ya zama gaskiya. Ina zata sa kanta idan akace za'a raba ta da Rahma. Rahma ce tayi karfin hali tana lallabata har sai da tayi bacci.

Washe gari su Ummul Khair suka fara shirye shiryen tafiya dan su Mufida da Zahra dake boarding a Abuja sun kusa fara exams kuma ana neman Ummul a wajen aikinta.

A palour suka tarar da Umma da tayi tagumi idonta jajir. Hafsa ce a zaune a gefenta tare da su Sulaimi da Asiya daga gefe kuma Ya Umar ne da Ashir da Abbas.

Gyaran murya Abbul Khair yayi, bayan ya gaida Umma ya fara magana dai dai lokacin da Uncle Abdul ya shigo tare dasu Jannah. 

"Umma dama so muke mu koma Abuja tare da ke da su Rahma."

A razane Hafsa ta kalleshi "wani irin magana kake Ya Majid?" Kallonta yayi cike da isa yace "gani nayi zama anan din bazai musu dadi ba saboda a nan suka rasa iyayensu. Kuma kamar zasu fi jin dadin can"

Ita dai Umma bata ce komai ba. Ya Umar ne yace "haba Ya Majid ya za'ayi ka tafi da Umma da marayun nan Ina laifin kabar daya daga ciki".

Cikin shakakkiyar murya Umma tace "zan bika Majid. Bazan iya zama a nan ba abubuwan da na ma Sumayyah da Ahmad baza su barni ba" kuka tasa tana share hawayenta.

"It's okay Mother you don't have to cry. Ai sun yafe miki".

"Still Majid. Da nasan zasu mutu da wallahi banyi musu haka ba. Na dauka hakan ne zai sa su zauna tare da ni a waje daya. Da na sani da na barsu a Canada abinsu. Jannah ku yafeni. Please forgive me".

Umma ce ta sauko ta yi hugging na Rahma da Jannah tana Basu hakuri. Kuka sosai suka sha. Daga baya Ya Umar ya ce sai dai a tafi da Umma da Rahma a bar Jannah anan tunda ba kowa a gidan Ya Majid. Yaransu suna boarding kuma suma suna zuwa aiki. Rahma zata kula da Umma a can ita kuma Jannah zata zauna anan.

Kuka Jannah tasa. Allah ya kasheta ta zauna anan ita kadai. Ba yanda Uncle Abdul bai yi ba amma Ya Umar ya kife yaki barin Jannah ta tafi sai dai idan anyi hutu su ringa zuwa suna hutu a can. Ganin haka Rahma ta ba Umma hakuri tace zata zauna tare da Jannah.

Jansu daki Ummul Khair tayi. Nasiha sosai tayi musu sannan ta basu kudi me tarin yawa. "Ku rike a wajenku zaku bukaci wani abu. Zan ma Abdul magana akan bank dinku. Zan gani ko za'a bude muku joint account cikin week dinnan". Godiya sosai suka mata kafin ta fice a dakin sai da ta basu addu'o'i na kariya da na yau da kullum.

Suna tsaye a bakin gate motar su
Ummul Khair ya fita. Umma tana kuka ta musu sallama tana mai sake neman yafiyansu.

'za kuci kwal ubanku' Hafsa dake bakin main entrance ta fada tana kallonsu Jannah dake bakin gate. Fuskarta dauke da shu'umin murmushi.

Eid mubarak

50 reads  for another update.

Thank you for reading

~Zahr❤️


ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now