Nigeria

144 14 3
                                    

"Ki yi hakuri kukan nan ya isa haka Sumayya." Baba ya fad'a yayin da yake zama a gafenta. Hankalinshi gaba d'aya a tashe dan tun da ta fara kuka a Toronto International Airport bata dena ba gashi yanzu har sun iso gida Nigeria.

"Ya zaka ce in dena kuka Al'ameen? Yaya na nagani fa after long fifteen years amma kace inyi shiru? So kake inyi pretending kamar ban ganshi ba?" yanda tayi maganar a fusace yasa Baba jan baya.

Dan bashi k'adai ba hatta su Jannah da suka shigo yanzu sai da sukayi mamaki. K'aro na farko kenan data fara d'aga murya tsawon rayuwarsu gaba d'aya. A lokaci d'aya jikin Baba ya mutu." I didn't mean-"

katse shi tayi tare dacewa "Then what do you mean? Tell me Al'ameen? Kai kana da Ya Majid, Ya Umar harma da Abdul amma ni ka gayamin wa nake dashi? He's my only family for crying out loud. How do you expect me to react?" ta k'arasa tana matsanaicin kuka.

"Kina dani" Baba ya furta a sanyaye. D'agowa Sumayya tayi tana kallonsa "Al'ameen -" "Shhh!" Ya daura hannu kan bakinta. "I'm so sorry" ya fad'a tare da rungumeta shi a rayuea babu abin dake d'aga mishi hankali kamar kukan matarshi ko 'ya' yanshi. "Me too" ta fad'a hawaye na ambaliya a fuskarta.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Anya kana so ka gama da duniya lafiya kuwa Ahmad. Shashasha mallakake. Dubi yanda yarinya karama ta saka a gaba tana surfa maka zagi harma da ihu amma sai hakuri kake bata sai kace wani d'anta. Anya lafiyarka kuwa? Toh wallahi kasani ba a gidana za ayi isakancin nan ba"

Umma da yanzu ta shigo ta fara masifa tana ta faman zabga wa Sumayya harara. "Umma ba-" "yi min shiru Shashasha" sai kuma ta wuce d'akinta tana ta faman huci.

Nan suka wuce d'akunanasu banda Jannah da ta share hawayenta tare da jan doguwar tsaki. "Lafiya baby sis?" Rahma ta karaso inda take cike da damuwa.

K'ada kai Jannah tayi tana me k'arewa mak'ek'en gidan kallon. Gida ne na gani da fad'a da aka k'awata da kayan more rayuwa. Sai dai ita Jannah tun da suka yi landing a Kaduna International Airport tasan akwai aiki ja a gabanta ganin irin ranan da yayi welcoming dinta.

Da misalin takwas na dare, iyalan gidan Jalal suka taru a nacin abinci full house. Daga mazansu da matansu harzuwa ga 'ya' yansu. Al'ameen ya kula tun dazu Sumayya bata cin abinci, wasa kawai take da spoon din.

Cikin kulawa ya dafa kafadarta. Juyawa tayi tare da k'irk'iro mursmushi duk da cewa ana iya ganin sauran hawaye a jajayen idanuwanta da suka sake kumbura.

Murmushi shi ma Al'ameen din yayi ba tare da kula da muguwar hararan da Umma take aika musu ba. Dafe kai Jannah tayi dan wani irin ciwo daya ke mata.

Ga abincin ma ba gane kanshi take yi ba. Daga wanda yayi gishiri sai wanda yayi yaji. Gashi Umma tace sai abincin Nigeria za aci. Sake kallon kwan tayi h'ade da jan guntun tsaki. Tsabagen soyuwa har wani golden golden ya somayi. Pepper soup din kayan cikin kuma yayi mata gishiri dan su baya baya suke ci a gidansu.

"Jannatul Firdaus?" d'agowa tayi tana kallon Uncle Abdul idonta cike da hawaye. "Why aren't you eating" kuka ta soma tare dacewa. "I can't. They're all spicy and yucky i feel like throwing up" ta k'arasa tana kallon tuwon da Umma ta bata sai kuma pepper soup na kayan ciki me yajin bala'i da soyayyen kwai bayan akwai wasu abubuwan.

"It's okay don't cry Angel" Uncle Abdul ya fada tare da debo mata chips da kwai, white rice da kidney sauce, fried spaghetti da strawberry shake. "Thank you" ta karba. A hankali ta faraci tana me godewa Allah duk da tasan sunyi nauyi a ci da dare amma yunwa da take ji bana wasa bane.

"Mtcheeewww. Ba ga irinta ba ace yara bara su iya cin abinci ba sai k'azantansu na chan?" Umma ta hau fad'a "Kiyi hakuri Umma a hankali zasu saba" Ummul Khair ta bada hakuri.

"Jannah baza ki kwana a wajena tare dasu Sulaimi ba?" wani wawan kallo ta watsa wa Hafsat, matar ya Umar tare dacewa "Zan kwana da big sis".

Ita haushinta take ji sanin irin yanda ta tsani mamanta da Rahma amma yanxu dake a gaban mutane suke har wani kashe murya take yi. Ai idan gaskiya za a bi su Sulaimin ma ba sonta suke yi ba.

"Yarinya karama sai bakin hali?" a cewar Umma. "C'mon Umma ai halinki da dauko" "Karya kike shegiya" Umma ta fusata. "What is shegiya again?" Jannah ta juyo tana tambayar Uncle Abdul. Shiru yayi ya rasa me zai ce mata.

"Uwarki ce shegiya" Umma ta sake zabga mata wani zagin. "I don't know what it means but my Mum isn't shegiya and yes Umma why don't you speak English? Please don't tell me you didn't go to school?"

Jannah ta zaro ido tana jiran amsar Umma. Salati Umma ta sake tare da kama baki. "Lalle Jannah watan cin ubanki yayi. Yanzu ni uwar ubanki kike wa haka? Toh idan baki sani bama ki sani. Ni da kike gani a England nayi karatu cikin Cambridge University. Kuma har PHD ne dani"

Juyawa tayi tana kallon Uncle Abdul. Gani tayi ya g'yada kai alamar eh. "Toh why don't you speak English?" "Jannah she's a retired English professor fa" Uncle Abdul ya fad'a mata.

"God why didn't you teach Sulaimi and Asiya? Their English isn't that fluent" Kama baki Sumayya tayi tare da zaro ido. Tabass Jannah zata sa zaman gidan nan ta gagaresu. Kama baki Hafsat tayi ido a waje. Ji take kamar ta shake banza dama tun asali ba sonta take yi ba.

"Jannah apologise " Sumayya ta fad'a cikin bacin rai."" I'm sorry Mother". "Not to me" juyowa tayi ta kalli Umma. "Sorry" Umma ko takan Jannah bata yi ba sai ma komawa kan Sumayya da tayi. "Munfuka sai kace ba ke kika koya mata ba" "Umma my Mother isn't Munfuka. She's a good Muslim for fudge sake"

"Jannah?" ta jiyo muryar babanta "Father I'm sorry". Sai kuma ta sake kallon Umma "Sorry granny" zumbura baki tayi tana kallon Hafsat. "Sorry." "Sorry Sulaimi and Asiya." Gani tayi Umma bata sauka ba har yanzu. A hankali ta zauna gefenta tare da riko hannunta.

"C'mon old woman i said I'm sorry" "ni ki k'yaleni" Umma ta tureta. Rungumota Jannah tayi tanace wa "nak'i" Maida numfashi Umma tayi tana kallon kyakkyawar yarinyar dake kwance a jikinta. Babu k'arya kab jikokinta ta fison Jannah sai dai bakin tan ne bata so.

Kuma duk yanda taso taji haushinta bata iyawa da zaran ta kalli kyakkyawar fuskarta da d'ara d'aran idanuwanta. "Fine naji ki d'agani". "No Umma my head is aching" ta sake gyara kwanciyarta.

Taba kanta Umma tayi taji da zafi. A hankali ta zame gelen da ya rufe dogon gashinta tana cewa "Ai gashin nan ma kadai zai saki ciwon kai. Gani fa ya wuce elbownki" "Na yi ma mommy maganar haircut but she refused" "wani haircut kuma? Ke arniyace? Ai kitso za'a miki" da wuri Jannah ta mike daga jikin Umma tana cewa "bana so baza a min braiding kai na ba"

Yau ta kama asabar kwana uku da zuwansu Jannah kenan. Jannah ce ta matsa wa Rahma wai suje night-walk.

Kasancewar sun saba a can tare da bodyguards dinsu a bayansu wanda baza ma ace bodyguards bane saboda distance da suke bari tsakanin su. "Please Rahmaatii" "no Jannah nan bak'on wajene. We can't just go."

a haka suka karasa parlour Jannah tana faman roko Rahma tana kad'a kai. Uncle Abdul ne ya tambaya Rahma ta gaya mishi. "Toh ai Jannah dare yayi this is not Toronto fa." "Ayya mana Uncle Abdul ni ko ice cream ne ma muje mu siya I'm tired of staying here." "Akwai wani ice cream palour a nan kusa. Baifi three minutes walk ba. Idan kina so sai muje."

"Eh Uncle Abdul thank you amma fa you'll keep your distance. Kamar thirty footsteps ko one minute walk" "Naji" nan ta tattaro su Rahma da Mufida da Zara dasu Asiya.

Sun gama siyan ice cream din sai taga wata tana siyar da wani abu square da bata san menene ba. Gani tayi wani saurayi na zuwa cike da fara'a ta tsayar dashi. Cak ya tsaya yana kallon kyakkyawar halittan dake gabanshi sai kuma yaji tace. "Hi, dan ubanka what's that?" ta nuna abin da matar take sayarwa.

"What??" so yake yayi confirming abin da tace. "Dan ubanka what's that?" ta sake nuni da abun. Allah sarki Jannah ita duk a tunaninta please take cewa saboda Sulami tace mata alternative form na dan Allah ne. "Nikike cewa dan ubana" nodding tayi tana murmushi sai kuma taga ya daga hannu zai dake ta. Da gudu na juya ta nufi Rahma da ke zuwa wajenta.

"What is it little sis?" Nuni tayi mata da mutumin dan ta kasa koda magana Rahma na ganin mutumin yana binsu yasa duka suka hau gudu. A bayan Uncle Abdul suka buya. Hakuri ya bawa mutumin sannan suka dawo gida.

Anan Jannah ta bada labarin abin da ya faru." Toh ke waya koya miki?" Ummul Khair ta tambaya. "Ummu Sulaimi ce ta fada min when i asked her the meaning sai tace min another way of saying please ne".

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now