Sauyi

38 8 11
                                    

Cikin hanzari Rahma ta fara baya baya ganin Hafsat na zuwa wajenta. Ko numfashi ta kasa yi sai dai girgiza kai da take ta yi. Da gudu Hafsat ta rungumeta ta fashe da kuka.

Kasa motsi Jannah tayi tana ganin ikon Allah. Idonta ta hau murzawa ko gizo yake mata amma ina, Aunty Hafsat ce ta rungumi Rahma. "My poor child! Are you okay?" Rahma da ko motsi ta kasa, kamar wanda ta daskare, g'yada kai kawai tayi.

Hamdala Hafsat tayi sannan ta rike hannun Rahma tare da janyo Jannah cikin gida. Cike da mamaki Jannah ta biyo ta. A kan daya daga cikin kujerun dake palorn ta zaunar da Rahma.

"Ke Asiya je ki kawo musu abin sha mana". Fuska a kumbure Asiya ta tashi. Saurin girgiza kai Jannah tayi dan kwata kwata baya making sense. "It's okay Aunt Hafsat we are alright, Big sis needs to rest".

Murmushi Hafsat tayi had'e da marin goshinta. " My bad! Gaskiyar ki Jannah you guys need to rest". Baki a wangale Jannah take kallon Aunty Hafsat, sai yanzu ta tabbatar da akwai matsala. Wai Hafsat da bata son turanci kwata kwata ita ce yau take musu magana da shi?

Ta ya za'a ce matar dake nuna musu tsana karara ita ce take tarairayarsu yanzu? It's either ta haukace ko kuma she's up to something. Matar da ko murmushi bata musun ne --" muryar Hafsat ne ya katse mata tunaninta

" Firdausi kuje ku huta kunji? Zan aiko da Aisha da abincinku". Nodding Jannah tayi sannan ta kama hannun Rahma. Bata damu ta dauki er karamar jakar da suka zo da ita ba illa school bag dinta dan Hafsat tace daya daga cikin en aikin zasu zo dashi.

Shigarsu daki ke da wuya Jannah ta cire hijabi da niqab dinta tayi discarding dinsu a laundry basket. Ita ma Rahma haka tayi. Zama tayi a kan gado had'e da rufe ido. Ba karamin tsorata tayi ba da hanlin Aunty Hafsat.

Abin ya bala'in tsorata ta. Matar da last week tana gani aka kusa kasheta kuma wai yau itace take rungumarta?. Allah ya sa tayi realizing mistake dinta. Rahma ta cigaba da addu'a.

"What was that Big sis? Why has she gone nice all of a sudden? I'm sure that vile woman has something up her sleeves babu yanda za'a ce haka kawai ta fara son mu.  Na tabbata wani muguntan ta take--" bude ido Rahma tayi had'e da katse Jannah.

" Astaghfirullah! Little Sis. Zato zunubi watakil  ta gane kuskurenta Maybe she's just trying to make things better." Hararar Rahma Jannah tayi had'e da murkuda baki. Ta ya za'a ce ta yarda da wancan matar? Ta manta it ce sanadin four days da tayi a asibiti.

"Making things better? Stop being delusional big sis. Matar da ko iyayenmu bata so shine zata so mu? She must be up to something. Marar can muguwace bata da mutunci --" sake katse Jannah Rahma ta you had'e da girgiza kai. Dan ta gaji da tunani gashi har kanta ya fara ciwo. "Let's talk about it another time"

Sighing Jannah tayi sannan ta mike ta zari towel da nufin shiga wanka. Taje dai dai bakin toilet kenan aka yi knocking kofar. Er karamar tsaki Jannah taja sannan ta bude kofan ganin Aisha na tsaye a bakin kofa.

"Aunty Hafsat ce tace in tambayeku me zaku ci" gira Jannah ta daga tana karewa Aisha kallo. Kyakkyawa ce na gani da fad'a. Ma Sha Allah. Tana da maidaidaicin tsayi, bakar fata, da dara daran fararen idanuwa da karamar hanci. Red lips da silky eyebrows dinta ba karamin kyau suka Kara mata ba.

Aisha ba ta da kiba kuma da siririyar ba ce. Gashinta ya tsaya ne a dai dai kafadarta. Ga kuma nutsuwa da kirki. Duk da cewa ta girmesu Jannah dan ko a babu ta kai 20 ko 21 bai hana ta basu respect ba.  Sake kallon tabon sallar dake goshinta ta yi. Sannan ta kada Kai.

"We are alright. Zamu sauko dinner" sallama Aisha ta musu sannan ta wuce inda zata. Ko da su ka je dinner, nan ma se wani tarairayarsu Hafsa take tayi.

•••

Azkar Rahma take yi bayan sallahn asuba. Jannah kuwa kasan cewar bata sallah, jinginuwa tayi jikin gado tana tilawar Alqur'ani. Dayan hannunta na dafe da marar ta dake bala'in ciwo.

ILLAR MARAICINơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ