chapter 6

583 37 11
                                    

Dakin ya dau shiru sai waziri ne yayi karfin halin cewa "kayi shiru za musan yanda za ayi"
haka dai sukai ta bashi baki har yayi shiru.Bayan sati Daya likita ya sallame su tare da kara jaddada musu kar su sake barin shi cikin damuwa.
Suna isowa su batare da wani bacin lokaci ba aka wangale musu katon gate din masarautar, bayi mazan su da matansu suka fara ajiye abunda suke yi suka fara zubewa a kasa don nuna girmamawarsu ga fulani fara da yarima, sai a lokacin ne yarima ya kula da canje-canje da dama sabida ko kayan da ke jikin bayin ya canza. matan riga da skirt ne sai earing kala daya da Kuma wata anklet kuda daya a kafarsu ta dama,sukuma mazan riga da wando ne a jikin su shima lemon green in colour wanda za a iya ce masa da uniform.koda yake sanda ya dawo daga London bai lura da canje-canjen ba don tsabagen tashin hankalin daya dawo da shi.suna isa parking plot din dake cikin gidan sarautar tuni fadawan da ke aiki a wanjen suka karaso da sauri tare da budewa fulani fara da yarima kofar motar tare da gaishe su dayi musu sannu da zuwa.bayin da fadawan da suke gurin tuni suka fara basu hanya tare da zubewa a kasa suna kwasar gaisuwa. fulani fara ce kawai take daga musu kai shi kuwa yarima ko a jikinsa wucewa kawai yake yi sai a lokacin yarima yace da fulani " ni na wuce sashina sai na zo din anjima"ta ce dashi "toh sai ka zo." yayi tafiyarsa tare da sauran kuyangin da fadawa dake binsa a baya. Fulani fara tana isa sashin ta kuyangin ta suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa gefanta na dama takalla tare da cewa jakadiyarta taje ta kira mata waziri bata jira abinda zata fada ba tayi wucewar ta daman tun da isowar ta aka wangale mata kofar da zata sadar da ita zuwa falonta.parlour ne na gani na fada babbane ya sha royal chairs white and golden.komai na parlourn white da golden ne. ba kowa a ciki sai karan sautin ac dake tashi. direct bedroom dinta ta nufa.bayan mintuna kamar talatin sai ga jakadiyarta ta karaso tai knocking sai ta bata izinin shigowa ta shigo tare da durkusawa tana fadin "fulani wazirin ya karaso. " batare da ta kalli gefanta ba sai tace kin ce mai ya shigo?" ta amsa da a'a hajiyata ."
"so sai ki ce masa ya shigo." Bayan kamar 2 minutes ta fito ta sami Daya daga cikin chairs din dake parlourn ta zauna suka gaisa tare da wazirin. Daman ta aika a kira mata shi akan zancen yariman.waziri zaune a parlourn fulani fara bayan sun gama gaisawa sai fulani fara tace "waziri daman abunda yasa na aika a ka kiraka shine a akan zancen yarima daman nakira kane don a san yarda za ayi sabida Mai martaba yace bazai taba hada jininsa da na wajeba wato ba royal blood ba Kuma gashi yarima yace in ba wannan yarinyar ba zai iya rasa ransa ." Waziri ya numfasa yace "sanda naje gida nayi tunanin kawai in zai koma why not in bishi muje a daura auran amma batare da sanin Mai martaba ba in yaso daga baya sai a daura mai auran da neice din fulani sura." Fulani fara ta shiga cikin duniyar tunani da ga bayane ta nunfasa ta ce "toh ba matsalar koma Mai martaba yasani daga baya baze ce ya sake taba sai dai yayi hakuri." Waziri yace "toh inzai koma in yaso sai in bishin". Haka sukayi sallama suna jajanta zance kuma sukayi wa juna alkwari da cewar babu wanda zai ji zancen.
Bayan two weeks da sallamar yarima daga hospital yaje sashin mai martaba suka gama gaisawa Mai martaba yace da yarima "mustapha tun dawowar ka kaje ka gaisar da sauran iyayen na ka?" yarima dagowa yayi ya kallesa sannan  yace" a'a banje bah."
Mai martaba yace " toh yanzu daga nan ka je ka gaishe su daya bayan daya." ya amsa da "toh inshallahu. " Sukayi sallama ya ta shi duk jiki a sanyaye ya fita. Sashin fulani sura ya fara zuwa ya na zuwa kuyangin dake wurin suka bude masa kofar da zata sadar da shi zuwa parlourn ta.yana shiga dai dai corridor din parlourn yayi over hearing fulani sura da fa'iza suna magana ko dayake  yaji an ce wai fa'iza ta zo. Ji yayi fulani sura tana cewa"daman na fadawa mai martaba cewar dole sai yarima ya aure ki, daman kinga Mai martaba mutuwa zai yi kinga yarima ne zai karba karagar mulkin kuma kina haihuwa sai mu kashe yariman shikenan masarautar adamawa zata dawo a tafin hannun mu sai yarda mukayi da ita." saigaba dayansu suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya har dasu tafawa.
Jikinsa a sanyaye har rawa jikin nasa yake tsabagin firgitar da yayi da sauri ya fita.yana tafe yana tunane-tunane daman haka fulani sura take ,ashe daman muguwace duk makircin ta da yake tunani ashe ta wuce nan ,bayan attempt din kashe shi da tayi a baya bata hakura ba gashi  Mai martaba yasa baki akan dole sai ya auri faiza yanzu shi ya zayi da rayuwarsa.haka dai ya dinga tunani har ya karsa sashinsa.bedroom dinsa ya shige direct ya kwanta akan katoton gadonsa yan kallon ceiling din dakin idosa a lumshe Yana tunani ko ya fadawa mai martaba da fulani fara don a san yarda za ayi  da fulani sura sai Kuma yayi tunanin  condition din Mai martaba kuma fulani fara in ya fada mata yasan tsabagin shock din abinda zata ji zai iya samata hawan jini,karar ringing din wayarsa yaji wadda ta farfado dashi daga duniyar tunani daya shiga zarota yayi da pocket din wandonsa yayi ya amsa tare da sawa a kunne   yace "hello fatyna ykk." a dayan bangaren aka amsa da lpy qalau." Sukai shiru sannan yace faty" next week zamuzo  maiduguri ni da uncle din don a yi maganar auranmu." wata nannauyar ajiyar zuciyar ta sauke  sannan ta daura da ce war " toh Allah ya kawo ku lpy kuma zan fadawa Abba saboda yau ma sai da ya tinatar min dace dadda yayi mai maganar aurena saboda wai be kamata a kara ajje ni ba wai lokaci tafiya yake gashi wai har na gana karatuna." yace toh inshallahu next week zamuzo ni fa uncle dinna." suka yi sallama tare da cewar inshallahu zai zo.a take wajen ya yanke shawarar zai je ya fadawa fulani fara cewr  tasa yarima ya bishi zuwa maiduguri don ayi zancen auran su shi da fatynsa kuma zancen su fulani sura kawai ya kalesu Allah na nan tare da shi, inshallah  Allah zai kare sa daga duk sharrin fulani sura da fa'iza.
Bayan sati  daya da wanna tunani da yarima yayi ranar  Monday shi da wazi suka shirya domin zuwa maiduguri.sun dau hanyar zuwa maiduguri wajen karfe 12 na rana basu suka isa ba sai wajen karfe 3 suna isa garin maiduguri sai yarima ya ciro wayansa ya Kira faty tana ringing daya aka dauka suka gaisa sai tace mai " kun karasune?" daman tunda safe ya kira ta yace mata yau za suzo shi da ubcle dinshi wato waziri.yace a yanzu ma mun shigo garin maiduguri kwatanta mana gidan na ku."sai tace "in kun shigo cikin gari ku tambaya ina ne  adullahi Muhammad link in kun karaso sai ku kirani." yace "ok ba matsala." sun gane kwatancen sabida haka  sun shiga Abdullahi Muhammad link ya kira ta tare dace mata yanzu suna Abdullahi muhammad link din tace dashi "ku tambaya ina ne gidan alhaji Abdullahi muhammad." ya amsa da" toh shikenan sai mun karaso." Suka tambaya aka nuna musu gidan.gidane na alfarma sama da gasa gidan tun daga waje za kasan gidane wanda ya tsaru.suna isowa suka gaisa da maigadin gidan.maigadin gidan wane dattijo da shi yace dasu "kokune bakin da za ayi yau ne." suka amsa da" a mune." da sauri ya bude musu babban gate din gidan,sukayi parking a parking plot din gidan sanna duka fito daga motar tasu sai ga maigadin yakaraso yace dasu" muje in muku jagora zuwa parlourn gidan." suka bishi gar zuwa kofar parlourn gidan ya kaisu suka Mai godiya tare dazaro kudi suka bashi yayi tayi musu godiya sannan yayi gaba abinsu.kwankwasa kofar da aka yi musu nuni da kofar parlourn gidan, daga ciki ne aka ce musu su shigo suka bude kofar suka shiga da sallama parlourn babbane ya sha wasu leather chairs milk in colour gashi banda sanyin AC dake tashi ba abunda yake tashi sai wani sanyayyan kamshin turaren wuta mai dadin kamshi.aka amsa tare da ce musu su shigo su zauna.suka zauna sannan suka kara gaisawa, baban fateeman ne sai wasu uncle's dinta guda biyu zaune akan gujerun parlourn.suka gabatar da kansu da cewar sunzo neman auren fateemah ne.akayi maganar auren aka tsayar da rana nan da wata Daya musu zuwa inshallah a nan suka bayar da 1M  kudin nagani ina so.  anyi musu tarba me kyau sabida an kawu musu abinci kala-kala tare da abin sha kala-kala aka jere musu shi a gabasu.bayan suyi sallar magariba sannan sukayi  musu sallama za su tafi.baban fateemah ne yace "baza ku bari sa gobe  bah." waziri ne yace" aa ai daga adamawa zuwa nan ba nisa." baban fateeman ne yace "toh ay shikenan."sukayi sallama tare da fatan alkhairi.sun dau hanyan adamawa wajen karfe 7 basu suka sauka va sai wajen karfe 9 suna isa fada yarima ya wuce sashinsa tare da yi wa waziri godiya da sallama.shi kuma waziri sashin fulani fara ya nufa Dan ya sanarda ita abunda ya faru tsakanin su da baban fateeman.yana isa sashin fulani fara yasa ayi masa iso. Jakxadiyar ta ce ta shiga ta sanar da ita zuwan wazirin.tafito tacewa waziri "wai tace wai ka karaso." ya shiga parlourn tare da yi mata sallama amsa tare da mai  iznin da ya shigo ya zauna   suka gaisa sannan waziri ya daura da cawar " yanzunnan muka dawo daga maiduguri shine nace bara inzo in sannar dake yarda muku yi da iyayen yarinyar." ya kwashe duk yarda sukayi a maiduguri ya fadamata. nannauyan ajiyar zuciya ta saukar tare da fadin toh Allah ya tabbatar mana da mafificin alheri.waziri yayi nata sallama sannan yatafi.
    Bayan wata daya,a sati na farko aka kai lefe gidansu fateemah.lefe ne nagani nafada base on the kanuri's culture.akwatine guda 24wato dozen biyu da kayan sa rana akwati 6.wato akwati  30 ne in total.sanna auren za ayi shi nan da sati biyu masu zuwa
          Ansha biki amarya da ango sun sha kyau abin ba a magana duk event Din a maiduguri akayi su babi wanda akayi a adamawa sabida kar ayi Mai martaba yazo yaji.A dangin yarima daga dangin fulani fara sai waziri da matarsa ne kawai sukaje duk abin nan da akeyi Mai martaba bai sani ba lokacin ma da za su tafi fulani fara da waziri karya suka yi wa mai martaba dacewar gurin wani malamin gargajiya za su tafi akan lalurar yarima ko za a dace sabida acewarsu yarima bai ji sauki ba har yanxu zuciyar shi na mai ciwo tunda ba a dace da na asibiti ba a dace dana gargajiya.mai martaba ya yarda da shawarar su ya basu izinin tafiya tare da basu kudade masu yawa wai na maganin yariman.anyi biki sabida har sati daya aka shafe anayi ranar jumu'a ne aka daura auren  bayan salla akan sadaki 1M.bayan sati daya ne yan biki suka watse sabida ango da amarya za su wuce London don a chan zasu zauna.tare da amaryar suka dawo adamawa amman basu shiga da ita cikin fada ba. akwai wani guess house din yarima a bayan gidan sarauta anan suka ajje ta shi da Muhammad sabida tare ma suka je bikin da muhammad.sun ajje ta tare da ce mata yau Muhammad zai je yayi mata visa gobe za su wuce London.suka yi sallama tare da ce mata goba za su dawo. Da yarima suka koma fada  sai shi da fulani fara suna isa aka bude busu kofar da za ta sada su izuwa ga parlourn Mai martaba suna isa suka ganshi a gishingide suka gaisha shi ya amsa cikin sakin fuska sannan fulani fara ta daura da fadin "daman zuwa mukayi don mu sanar maka dacewar yarima zai koma london gobe inshallahu." yace da ita Mai zeje yi acen bayan ya riga ya gama karatun sa  ay naza ta ya dawo ba zai Kuma ba kenan gashi inw son a gagauta aurensa shi da fa'iza." gumine yake kecowa yarima duk da sanyin AC dake tashi  a turakar sarkin.fulani ce dace "dashi wai ay takardun sa zai karbo."da kyar de suka shawo kan Mai martaba ya yarda ya koma London amman da sharadin cewar sai ya auri faiza.fulani fara ce tace ay" base dole ya na nan za a daura auren ba tunda gamu iyayensa ay shikenan in yaso in yakara dawo wa sai su tare." Mai martaba ya gamsu da abinda fulani fara tace sabida haka yace ya tafi goben koma Allah yakiyayi hanyan.sai a lokacin yarima yayi magana dacewar" ameeen na gode Allah ya bar girma."sannan ya sauke wata boyayyiyar ajiyar zuciya.ya ta shi yayi mai sallama shi da fulani fara sanan yawuce abinsa. guess house dinsa ya nufa direct.yana isa ya danna doorbell din gidan saboda gidan sak tsarin gidan turawa akayi wa gidan daga cikine aka bude masa kofa suna hada ido da junan su suka sakar wa junan su murmushi cikin si fa kaunar juna sannan suka rungume junan su.suka kara parlourn gidan suka zauna yarimane yace da ita ta shirya gobe zasu bi jirgin karfe 9 na safe zuwa London.tace "toh ba matsala." suna tare har wajen magariba sannan sukayi sallama tare da ce mata gobe zai zo wajen karfe 8 inya so sai so tafi daga nan.
       Washegari kamar yarda sukayi karfe 8 Yana gidan itama har ta shiyar cikin shigarta Mai kyau. atamfa ce a jikinta  kirar super Holland red and white ta Sha dikin borno style da ita sannan ta yafa dan siririn gale a kanta bayan ta sha daurin nan na zamani wato ture kaga tsiya.fari white takalmine a tsiririyar dogowar kafarta takalmin mara tsayina za a ayi cemasa da slippers dannan ta dauki Jakarta itama fari a kafadarta.tana zaune a daya  daga cikin cushion din dake parlourn gefanta trawly din kayan tane data ke needing.ringing din doorbell ta jiyo ta tashi take ta bude Mai kofar shima yana sanye cikin shadda kirar gezner white in colour baisa hula ba amman sai da gashin kansa ya sha gara sai sheki yake ga wannan  sassanyan kamshi tyraren nan nasa data san shi da shi tun farkin haduwarsu.bashi hanya tati ya wuce ya zauna akan daya daga cikin  cushion din dake parlourn itama din a gefansa ta sami guri ta zauna tare da gashe shi.ya amsa cikin murmushi sannan yace hadon cofee insha inya so sai mutafi.bayan ya gama shan coffee din ne yace su ta si su tafi Muhammad Yana jiransu a waje.ya karbi trawly din hannunta yace "mutafi koh." ta daga masa kai allamar eh.busu Dade da zuwa airport din ba jigin su ya ta shi .har da Muhammad suka tafi.suna isa kasar London direct gidan da zasu zauna suka nufa gidane flat amman ya tsaru suna shiga suka zube a parlourn gidan tsabagin gajiya.daman tun kafin ya dawo yana da takardar aikinsa a hannun.
       Bayan shekara daya da zuwansu London fateemah ta haihu da na miji aka samai abubakar  bayan shekara uku da haihuwar abubakar  takara haihuwa ya' macce aka samata sunnan maman fateeemah data rasu wato Aysha.yaran sun taso ciki da so da kuana daga iyayensu.
        Hello readers kunji yanda akayi auren yarima da Fatima har suka haifi yaransu biyu. Ku biyoni kuji yanda suke dawowa Nigeria da irin hargitsin da suka jefa fulanin sura da faiza.
Shin yarima na auren faiza??
Mai martaba na yafe musu??
Wani tashin hankali fateema ke shiga a GIDAN SARAUTA
Answers din dai sai kun biyoni kun cigaba da karatu kuji meke faruwa.
VOTE😊
COMMENT😊
SHARE😊
Thank you I love y'all ❤️

Je hebt het einde van de gepubliceerde delen bereikt.

⏰ Laatst bijgewerkt: Dec 24, 2020 ⏰

Voeg dit verhaal toe aan je bibliotheek om op de hoogte gebracht te worden van nieuwe delen!

GIDAN SARAUTA 👑Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu