chapter 3

699 38 1
                                    

       MUSTAPHA A KASAR LONDON
Mustapha ya isa kasar London cikin kwanciyar  hankali amman a duk lokacin da ya tina da abinda yayi over hearing a sashin fulani sura sai hankalinsa ya tashi sosai.Haka ya fara zo wa imperial collage daman komai a online ake processing so yana isa wa shegari  ya fara zuwa Kuma kullum yana cikin addu'a,yin nafila da karatun al-qulur'ani mai girma  kuma kullum sai ya kunna al-qulur'ani  mai girma yake kwana don neman tsari daga ubangiji.A bangaren fulani sura kuwa boka tsindugu yace so kawo dubu dari da hamsin Dan ya kammala musu aikin.Aikwa ba shiri fulani sura ta aika da kudin don burin ta yayi saurin cika.Boka tsindugu yana zaune a wani katotun dutse can cikin wani daji dake agadas a jihar niger ya kwarara wani ihu sai da dajin yayi kururuwa sannan sai ga wani bakin munmunan aljani ya baiyana ya durkusa a gabansa yace gani ya shugabana wa za a hallaka ko waza a cutar sai yace masa "yarima mustapha Dan sarkin ahmadu na II na garin adamawa Wanda a yanzu yake kasar London nake son  kaje  ka shiga jikinsa ka hanasa karatun kwata-kwata  harse an kore shi. Aljanin nan ya amsa da "angama ya shugabana".Bayan sati daya fulani sura ta kira boka  tsidugu tace"boka wai ya naji shiru har yanzu shiru bai dawo ba"boka yace "hajiya wlh  ya dage da addu'a da babban aljani na ma ya kusanci shi rabinsa  ya kone ga shi can  yana jinya amman kar ki damu ki kawo mana kayansa ko kafi addu'a yake da karfin sihirinmu sai mun jinyata shi".fulani sura tace "ba matsala a cikin wannan sati zan sa a turo maka da rigarsa".Sai ta kashe wayar ta bushe da wata mahaukaciyar dariya tana fadin"sai ni fulani sura sai kwa ka gane kurinka harde ka shiga tarkona"Bayan sati daya da faruwar hakan mustapha yata shi daga barci  Amman duk jikinsa badadi haka dai ya shirya yatafi makaranta saboda yau yana da test Kuma baya so yayi missing dinta.Yana shiga cikin theater din da za su yi test din yaji jiri yafara kwashe shi amman a haka a daddafe ya sami guri ya zauna.A haka dai har suka fara test din yana tsakiya da rubutu kwai yaji kansa ya Sara kamar an buga masa guduma a take a gurin  ya ji shi ya fadi kasa sumamme. Haka wasu students suka dauke shi sai clinic din dake school din.bashi ya farka ba sai wajen karfe uku.Haka jiki a sanyaye ya tashi ya tafi bayan doctor din dake clinic din ya bashi wasu drugs yace masa ya Sha saboda stress ne ke damun sa.Yana isa gida ya kwanta a kan cushion din da ke parlour dinsa a take a gurin barci mai nauyi a dauke sa.Washegari ma haka ya tashi duk jiki badadi haka yatafi school din. Yau kam jikin yayi banban da na  jiya dan yau ji yake kamar ana hura wuta a kanshi. Yana shiga department dinsu yafar jin jiri haka dai a daddafe yakarasa abinda zai yi ya koma gida. Kullum hakan ke faruwa dashi Amman bai  kira gida yafada musu ba.Yau ma haka yata shi jikinsa duk ba dadi ya lura in dai zeyi karatu ko ze shiga makaranta sai jikin shi ya fada masa tsabar azaba da yake Sha. Haka ya shiga school din don ba yaso  yana missing lectures.Har ya gama attending  lectures dinsa zai tafi gida  yaji jiri na neman kayar da shi haka dai da kyar yake tafiya yana layi kamar zai fadi.Yana isa gurin motarsa a parking plot din makarantar kawai sai yaji wani irin Sara a kan shi nan take yayi kasa ya fadi sumamme. Ai kuwa sai wata budurwa wacce shekarunta bai wuce ashirin da biyu ba tana tare da babanta suma gida za su koma don ita ma ta gama lectures din ta suka kawo masa taimakon gaggawa.suka sa shi a motarsu suka tafi da shi gida. Akan hanyan su za su tafi gida sai yarinyar ta ce"Abba wlh daman na lura da wanna bawan Allah kamar bash shi da lafiya saboda ko ranar da muke da test haka ya sume haka ma yau muna lectures idon shi ya juye,  kullum Kuma zaka ganshi yana tafiya ya na layi kamar zai fadi kasa".Abban na ta ya ce "toh Bari mu kai shi asibiti muji me zasuce. Haka bayin Allah nan suka Kai mustapha asibiti. Da aka gama checking dinshi sai likita ke fadawa musu su iya binciken su sun duba sunga bashi da wata matsala. Amman abun mamakin shine har yanzu a sume yake Kuma jikin shi kamar garwashi tsabar zafi. A haka suka dauke shi sukayi gida Abba kam ya Dan tsorata Kuma yashiga duniuar tunani. Chan ya nisa yace kina gani mu maidashi makaranta hukumar makaranta ta sani ko mu kaishi gida. Tace "Abba ay kaishi gidan zefi Amman it's a bit dangerous kar wani abun ya sa meshi a ce mune,ko dayake ay Allah Yana tare da masu tausayi". Abba ne yace"toh bara mu koma gida sai in ga taimakon da zan iya bashi".Suna isa gida ya Kira maigadi ya tai ma ka mishi su ka shigar da shi cikin daki suka kwantar da shi a kan gado. Yacce yake jijjiga ne yasa su suka rude gaba daya. Chan Abba yace "qila he is possess by some spirits" yarinyar ce tace "Abba toh kayi sauri ka Kira Dadda ya baka adduoin da za ka masa" ta fada tare da dialing din number din Dadda din.
Dadda babban malami ne a Maiduguri. Kuma baban Abba ne wato kakan yarinyar da har ynxu ba a bayyana sunan ta ba.
Haka yarinyar ta bawa Abbanta waya sukayi magana da Dadda Kuma aka labarta mishi komai. After Abba yayi ending call din ne ya dauko wata jakarsa ta alqurani da Kuma Allo da su tawada ya fara bashi taimakon gaggawa daman shi Dan malam ne kuma babban malam ne a garin maiduguri.haka dai ya ta yiwa mustapha hayaki Wanda zai sa aljanun  jikinsa su fita Dan dama Dadda ya fada mishi yaran an mishi turen mugayen aljanu. Sai da yayi sati daya sannan yata shi. Lokacin da ya tashi bai san a inda yake ba yaza ta  mafarki yake don sai da ya bude idonsa ya rufe sannan yakara budewa sai yaga ba mafarki yake ba. A daidai lokacin ne yarinyar ta shigo dakin dan kawo turaren da ake masa, qara ta saki tsabar murna ta qwalawa Abbanta kira tana cewa "Abba ya tashi Abba wlh yatashi!!!"aikwa shima ya taho da sauri ya shiga dakin aikwa sai yaga dagaske ne ya tashin. Nan yayi wa Allah godiya da yasa bawan Allahn ya tashi. Abba ne yace" bawan Allah za ka iya fada mana sunnan ka". Da kyar ya bude baki yace sunana mustapha"
sannan mustapha yace "dan Allah za ku iya fadan ta ya na zo nan".
Abba ne ya fada masa duk meya faru yanda suka dauko shi kawo yanzu. Juya wa yayi yace"er gidan Abba hada masa tea ya sha dan satin sa daya a kwance batare da ya ci ko ya sha ba" 
ta ce "to  abbana".
Sai a lokacin mustapha ya lura da ita a gurin,nan ya shiga tunani da a ina yasan fuskar nan a haka dai yayi ta tunanin Amman  ya kasa tuno wa bude kofar da tayi ne ya katse shi daga duniyar tunanin da ya fada. Yarinyar ce tace"Abba ga tea din na hada masa"
Abban ne yace "Toh matso kusa sai in bashi"
matso wa tayi sannan ta miqa cup din tea shikuma Abba ya temaka mishiya jingina da pillow ya karba tea din a hannun ta ya fara sha a hankali har ya shanye. Yana shanyewa wani sabon barci mai nauyi yadau ke shi. Da ganan babban yarinyar ya ce mata"er Abba tunda ya shanye kuma haryayi barci  zo mutafi mu ba shi wuri ya huta kuma da alama aljanun sun sake shi  yanzu". Sai ta ce "abbana ta garin yaya aljanun suja shigesa"yace " ina Jin ture aka yi masa" shiru tayi can ta nisa tace "to Allah ya sawake"
Bata san  meyasa ba tun ranar da ta ga ya sume suna cikin test ta ke jin tausayin shi  Kuma take Jin wani abu game da shi.Sai washegari mustapha ya farka da ga nannauyan barcin da ya dauke shi ya fito daga daki sai kwa su ka hadu da babban yarinyar sai ya gaishe shi  aikwa ya amsa cikin fara'a yace " har ka fito yanzo na ke so inzo in ta she ka don kazo muyi having breakfast tare". Shirun da yaga mustapha yayi ne yasa yace "kasake jiki damu ka ji" gyada kanshi yayi alamar ya gamsu da abun da aka ce mishi. Sun isa dinning area din a lokacin ta fito daka kitchen dauke da flask din tea a hannunta aikwa suka gaisa sannan suka fara cin abinci  harsu ka gama cin abincin ba wanda yayi magana.Shi dai sai satar kallan yarinyar da yaji babanta nace mata er Abba.
Hello readers waye zeyi guessing yarinyar da ta ceto mustapha daga halaka
VOTE 😊
COMMENT 😊
SHARE 😊

GIDAN SARAUTA 👑Where stories live. Discover now