chapter 4

690 25 2
                                    

WACECE YARINYAR
Fateemah abubakar yar asalin garin maiduguri ce . Mamanta ta rasu bayan haihuwarta saboda haka ma sunan mahaifiyarta aka mayar wato fateemah. Bata taso da kaunar uwa ba sai dai ta uba shiyasa komai ubanta ne ke mata.Kuma rashin mamanta Bai sa ya kara aure ba. Maman shi tayi magana, tayi magana harta gaji ta kyale shi.Alhaji Abubakar Muhammad wato mahaifin fateemah babban likitane a garin maiduguri kuma ma babansa wato daddan fateemah babban malamine a garin maiduguri. Haka rayuwa ta ji gaba da tafiya har fateemah ta gama makarantar secondary.Babanta yayi deciding ta tafi London don ta yi forwarding karatun ta daman shima baban nata za a tura shi karo couse na shekara biyar don haka za su tafi tare.Haka kwa akayi suka tafi London tare ta fara karantar medicine a imperial collage.Haka rayuwa taji gaba da tafiya har su ka zo suka hadu da mustapha.Bayan wata biyu da faruwar hakan mustapha da fateemah sun riga sun shaku da juna har ma suna son juna har ma baban fateemah yasani shima abun yayi masa dadi. Mustapha ranan suna waya da hajiyarsa yace " hajiya ina so muyi wata magana dake
"toh ina jinka"
yace" hajiyata wlh akwai wata yarinyar da muka hadu da ita a school din mu amma ita a medical department take......."
yayi shiru Bai karasa maganar ba saboda besan taya zata dauki maganar ba fulani fara tace "toh ina jinka meya faru da ita"
yayi karfin hali yace mamina wlh tun ranar da muka hadu da ita nake muguwar kaunar ta zan iya ce maki wlh ba yanke wlh banga mahalukin da zan ce ina kauna sama ita ba" tayi min abubuwa da dama ita da mahaifin ta, wlh hajiya sun tai makamin ,sun min iya abun da iyayena zasuyi min.
Fulani fara tayi shiru for some seconds tana nazarin maganar da dan nata yake yi kamar tasan haka zai fada mata tun da taji Yana inda-inda. Mustapha ya katseta tare dace mata "mamina yanaji kin yi shiru "
fulani fara tanisa tace"toh yazan yi dakai amman kasan mai martaba bazai taba yarda ka auri mata ba daga cikin royal family ba" kamar yasan haka zata ce yace cikin muyar kuka "ni fa mami wlh ita nake so in ba ita ba wlh zan yi rasa raina gaba daya
"fulani fara tana ji yafara zan cen zai iya mutuwa tayi saurin katse shi tareda cewa "toh zan san yarda za ayi" haka tai ta rarrashin sa saboda tun sanda mustapha ya tashi Bai taba cewa Yana son wata ba har ya gama schooling. Shiyasa daya fada mata to ta son ba karamin abu ba ne tunda har ya budi baki ya fada mata shi yasa ta dinka rarrashin sa har sai da hankalinsa ya kwanta. fulani fara tana mutuwar kaunarsa saboda shi kadai ta haifa Kuma tana kaunar duk abinda yake kauna Kuma haka zalika tana kin duk abinda yace bayaso.haka dai suka yi sallama shima yaji dadi yarda hajiyarsa ta fada masa. Haka rayuwa taji gaba da gudana har shekara ta zagayu su mustapha sun yi jarabawa Kuma Allah ya taimake shi bai fito da carry over ba sai mada second class upper yafito haka fatyn sa da second class upper ta fito daya ke ita a medical department take shi Kuma a engineering department yake sun ji dadi sosai da samun nasaran da sukayi. Haka aka tafi summer holiday ya Kira hajiyarsa yana ce mata result dinsu ya fito da second class upper ya fito Kuma baida carry over.fulani fara taji dadi sosai haka su kayi sallama tare dasa masa albarka tare da a bin kaunarsa wato fatynsa yaji dadi sosai yarda hajiyarsa take kaunar fateemah.Ranan Yana kwance a resting chair din dake parlour dinsa Yana ways da abar kaunarsa wato fateemah suna Shan madarar soyayya sun fi awa daya suna magana sai yaga wani incoming call Yana shigowa tanata ringing Bai dauka ba Kuma Bai duba Wanda yake calling ba saboda Yana tunanin Muhammad ne wani friend dinsa dasuka hadu a london jininsu ya hadu sosai saboda department dinsu daya Kuma shima Dan garin yola ne dake jihar adamawa. Sun saba sosai saboda haka yaza ta shine shi yasa yaki dubawa ana ta calling har se da akayi masa three miss call ana hudun ne ya duba kawai sai ya ga sunan hajiya aykuwa yace da fateemah Yana zuwa hajiya ke kiran. Ya bata assurance din idan suka gama wayar zayi calling din ta back. yana gana fadin haka ya katse wayar Yana Shirin kirinta yaga call din ta Yana shigowa nan take ya amsa da sauri tare da gaishe ta. Ta amsa jiki a sanyaye.
mustapha yace "mamina hope kalau don naji muryar ki wani iri"
tace masa "bade qalau ba"
yayi saurin tambayarta me yafaru tace " hmmm mai martaba ne bashi da lafiya sosai"
yayi saurin cewar "meyasa me shi" tace "wlh wai hawan jini ne da ciwon sugar"
yace "toh Allah ya ba shi lafiya Kuma insha Allah a cikin wannan satin zan taho"
tace "to Allah ya kawo ka lafiya." Haka sukayi sallama jiki a sanyaye.aikwa tuni ya fara shirya-shiryan dawowa zuwa kasa Nigeria.yana cikin hakan ya Kira Muhammad suka gaisa sai yake cewa "Muhammad kaga yanzun nan hajiyata ta kirani Wai mai martaba bashi da lafiya Wai har an kwantar da shi a royal hospital" Muhammad yace Dan Allah?? toh Allah yasawake. Yaushe za ka tafi ne in yaso sai mutafi tare don nima ina son zuwa don nayi missing mommana"
mustapha yace "ameen ina Jin gobe zan tafi cause naji hajiyata na ce wa an kwantar dashi ka ga kuwa dole in yi sauri in tafi. Kuma apart from dat kasan tun da nazo banje Nigeria ba ko sau daya so I want to use dis opportunity to meet my family Kuma inga idan GIDAN SARUTA is now stable. Babu masu mugunta ko masu bakin tsaka.
"A haka suka yi sallama da cewar Muhammad zai zo da daddare ya kawo masa visar Kuma a nan zai kwana in yaso gobe sai su bi jirgin safe. Suna gama wayar ya Kira fatyn sa don ya fada mata zancen tafiyar. Ringing daya sai kwa ta daga tana cewa"bae yanzu nake Shirin kira"
yace "fatyna ya gida kin ga dazu mamina takira ni tana cemin Wai mai martaba bashi da lafiya so gobe ni da Muhammad za mubi jirgin safe zuwa kasa Nigeria"
tace "toh Allah ya kara sauki daman Ina son muyi wata magana da Kai"
sai yace toh Ina Jinki"
tace "daman abbana ne yace in fada maka wai ka fito in ba haka zai aura min wani cousin dina"
babban tashin hankali ne yazo mai saboda mai martaba ya ce masa Wai dole sai yar royal family zai aura ga shi kuma abban fatynsa yace ya fito in ba haka ba zai aura mata cousin dinta.
A sanyaye yace mata "toh bara Ina komawa nasan yarda za ayi saboda mai martaba bashi da lafiya"
haka sukayi sallama tare dace mata ajima kadan zai kirata. haka ya kwanta lamo a kan kujera Yana tunane-tunane.door bell din da yaji yadawo da shi daga duniyar tunani haka ya tashi a sukwane yaje ya bude kofar. Muhammad ne tare da travelling bag a hannunsa kallo daya Muhammad yayi masa yagane abokin nasa Yana cikin damuwa haka suka shiga ciku suka zube a parlour din gidan. Muhammad ne ya kalla shi cikin nutsowa yace "mustapha wai meke damun kane na ganka baka cikin nutsuwa"
mustapha ne yayi nannauyan ajiyar zuciya yace Muhammad kasan gobe za mu tafi Nigeria ko?" Muhammad yace eh mana" mustapha ya ce abban fateemah ne yace in fito" sai yayi shiru Baiyi magana ba"sai muhammad ya ce "to ba a dadin ka bane"
katse shi yayi tare da cewa Muhammad baza ka gane ba mastalar mu daya mai martaba yace bazan aure maccen daba royal blood bace".Muhammad yace toh Amman kar ka damu nasan hajiyar ka baza ta bar maganar ba. Washegari da misalin karfe 8 jirgin su yarima mustapha ya daga zuwa Nigeria. Tunanin shi daya wato meze je ya tarar a GIDAN SARUTA da Kuma yaza ayi aurenshi da fatyn sa. Readers ku biyoni kuji meze faru a gida Nigeria.
VOTE 😊
COMMENT 😊
SHARE
I love you guys. Ina godiya🤗

GIDAN SARAUTA 👑Where stories live. Discover now