chapter 2

1K 45 0
                                    

    TUNA BAYA
Yarima Mustapha shi kadai ne dan Mai martaba Ahmadu Moddibo ll da Hajiya wacce aka fi sani da fulani fara. Ana ce mata fulani fara saboda tsananin hasken fatar ta irin na yolawa wato mutan Yola. Allah yayiwa fulani fara mutumci da Jin kan na kasa da ita ba kamar sauran matan Mai martaba ba wa en da suka dauki sarauta wata tsiyar. sauran matan Mai martaba sun iya wulaqanci da qasqanta Dan adam. Bayin su suna Shan baqar wahala.
      Allah ya jarabci Mai martaba da rashin yaya dayawa domin dansa daya tal wato mustapha. Wanda dukk al'umar masarutar adamawa sun San anaji dashi. Mustapha ya taso cikin gata gaba da baya domin shine na gaban goshin mai martaba kuma Dan lelan fulani fara. Ya tashi cikin tarbiya mai kyau dan fulani sai da ta tabbatar da ta koya mishi abinda Allah da Annabi yace a koyar. Yana da qwazo,Jin qan bayin gidansu bugu da qari yana da mugun qoqari a both Islamic and Western education. Tun yana qarami matan babanshi suka tsaneshi sosai dan hada baki suke su cutar dashi. Rashin mutumcin su ba a iya mustapha ya tsaya ba dan idan suka sami wuri harda fulani fara sukewa.
Matar mai martaba ta biyu ita ce ake kiranta da fulanin sura. Baqin kishi ne da ita kuma irin matan nan ne da ake Kira da green snake under green grass wato sumi sumi dangin mugunta.kullum baqin cikin fulanin sura be wuce ta wayi gari taga fulani fara a raye ba. Dukk wani abun da zatayi Dan ta kawar da fulani fara tayi Amman Allah baya bata saa. Muguwa ce ta bugawa a jarida. Bata qi ta kashe dukk Wanda taga ze kawo mata matsala a rayuwar ta ba. Mugunta da makirci za a iya cewa a Jinin jikin fulanin sura yake saboda ta tashi taga babarta nayi, ta tashuga taga babarta na ganawa kishiyoyin ta azaba, ta tashi taga babarta ta mai da babanta sakali, ta tashi taga babarta ita ce take shugabanci a gidansu. Saboda haka babarta ta koyar da ita tsantsan makirci da mugunta.fulanin sura cousin din mai martaba ce, babarta ce ta kisa mata ta aureshi dan tazama gimbiyar sarki wato sarauniyar masarutar adamawa. Da farko bata yarda da shawarar ba sai da mamanta ta kwadaita mata son mulki da yacca zata dawo babba a rayuwa dan kowa sai dai ya bita kuma yabi bayanta.Sai matar sarki ta uku wato fulani hafsatu wacce ita ma tana da isa da kasaita sai dai  ita akwai munafunci sosai don wani sa in da fulani sura suke hada baki don cutar da fulani fara. Sai  kuma matar sarki ta hudu  wato fulani hajar wacce akwai mutunci da son jama'a kullum za ka ganta cikin fara'a da walwala shi yasa take shiri da fulani fara.haka rayuwa take tafiya acikin GIDAN SARAUTA har mustapha ya girma.Ranarda mustapha ya shi shekara 18 a duniya ranar ne yafara sannin matsalolin GIDANA SARAUTA Kuma a lokacin ne yayi dai dai da kammala secondary School dinsa. Sabo da qwazon mustapha, mai martaba yakira matansa tare da waziri ya ke sanar dasu niyar shibta Kai mustapha London yayi karatun jami'a. Mustapha yaga tsantsar hassada a waken matan babanshi biyu wato sura da hafsatu. Shi ay a tunanin shi kowa da kowa yana sonshi be san yana da maqiya da yawa ba sai ranar. Dan ita fulanin sura cewa tayi ay idan aka kaishi London watsewa zeje yayi. Ita kwa fulani hafsatu cewa tayi ay zancen sura gaskiya shaye shaye zai je yayi Kuma ya watse dan yaro idan ba a gaban iyayenshi yake ba watse warshi kawai zeyi. Kowa dake gurin yayi mamaki dan kallon idanun sura da hafsatu kawai ya isa ya nuna mka tsantsar baqin ciki da hassada.Ita kwan fulani hajar budar bakin ta sai tace " ai ba a taru dukka an zama daya ba ta ya za ki ce Anna iskanci a kasar London so kuna nufi mustapha zai je yadawo Dan iska...... bata karasa abunda zata fada ba fulani sura ta hayayyakumata  tana fadin "fada da ihu ki kara da kururuwa"ganin abin ya fara kawo rikici tsakinin fulani sura,fulani hafsatu da Kuma fulani hajar sai mai martaba ya tsawatar  musu  daman fulani fara tun sanda mai martaba ya gama bayinin  sa sai taja bakinta tayi shiru tana kallon ikon Allah. Da haka mai martaba ya sallame su sai ya juya sukayi shawara da waziri haka dai aka fara processing din makaranta mustapha.
Sanda mustapha yaje yiwa matan babanshi sallama yasha mamaki. Ya shiga part din sura Dan yi mata sallama abun da yaji tana fada ne ya bala'in girgiza shi ji  yayi tana waya da mahaifiyarta tana fadin"mama wlh bazan yarda a Kai shi  kasar waje ba dan mu  bama  haihuwa shikenan sai a dauki son duniya a daura masa.ki Kira tsidugu na niger ki sa ya tura masa aljanu kawai in ma yaje can ya kasa karatun Dan ni wlh a kan zancen nan zan iya kisa ".Bai ji abunda maman tace ba amman yaji fulani sura tace za ta aiko mata da kudin aikin.Kanshi yayi balain daure wa besan lokacin da hawaye ya zobo masaba jiki a sanyaye haka yaja  kafafuwansa yatafi sashinsa yayi  kwanciyarsa zuciya badadi don har wani zazzabi ne yaso ma kamasa shi a zatan shi fulani sura tana kaunarsa Dan yarda take nuna masa so da kauna a gaban mahaifin shi.haka ya kwana yana tunane-tunane har barci ya sace shi sai da asuba ya tashi ya gabatar da sallah sannan yafara shirya-shiryan tafiya don jirginsu karfe takwas zai tashi.mai martaba yayi masa nasiha da yarike addininsa a duk inda yake sannan mamansa mahaka ta mai nasiha tare da yi masa addu'a.har ya tafi bai je yayi wa fulani sura sallama ita kuma bata damu ba saboda dama can ta  tsaneshi kamar yarda ta tsane mutuwar ta. Daman a gaban mai martabane take nuna tana son shi dan ya dinga bata duk abinda take bukata Kuma bukatar ta ta biya tunda duk abinda ta  tambaya harde harkar kudi ne mai martaba na bata ko nawa ne Kuma hanzu tana  da bokanta tsindugu na niger ai bukatar ta tabiya a gurinta.  Ku biyo kuji ya aka kaya
VOTE 😊
COMMENT 😊
LIKE 😊
SHARE😊          

GIDAN SARAUTA 👑Onde as histórias ganham vida. Descobre agora