3-The Ɓagwais

18 1 3
                                    

A sanyaye ta nufi kitchen ɗin bayan ta yi wanka ta canza kayanta, in ta ce alaƙarta da Mommy bata damunta ta yi ƙarya, mutane na mata kallon wadda ta samu kusan komai a duniya, za a kaita makaranta a ɗaukota, tana da sutura, tana da gata, ba a isa a taɓata ba a makaranta, yanzu sai a ɗaure mutum. Sai dai basu sani bane, tana cikin kaɗaici sosai, bata da ɗanuwa ko ƴaruwar da zata bawa labarin makaranta in ta dawo gida;

Daddy yawancin lokuta yana wurin aiki kuma bai cika dawowa da wuri ba, He's a busy man, kai tsaye ba za a ce ɗan siyasa bane, sai dai kasancewar shi babban lauyan Hon. Ɓagwai; ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɓagwai a jihar Kano, yakan shiga al'amuran siyasa sosai da sosai, wani meeting ɗin ma da shi ake yi, shi ne abokin shawarar Hon. Ɓagwai, wannan ne ya jawo mai maƙiya masu yi masa baƙin ciki, tunda a da shi ba kowa bane, wasu a cikin masu yi masa baƙin cikin ma sun haife shi, sanadiyyar principal ɗinsu Shahee wadda ta kasance ƙanwar matar Hon. ya samu wurin zama sosai har ake damawa da shi.

Mommy kuma bata aiki duk da a da ta yi aikin banki, wannan ne ya sa bata wani samu lokacin ƴar tata ba, tun bata wuce wata uku ba ake barinta a hannun Hajja Talatu, da ta so ta ringa kaita gidansu, kasancewar akwai yara sa'anninta a gidan ya sa ake cin zalinta da sunan wasa, wannan ya sa take barinta a hannun Hajja, kuma ba laifi tana kula da ita. Abinda ya yi sanadiyyar barin aikin Mommy bai wuce ganin Shahee ta taso a sangarce ba, babu wata ƙwaɓar kirki da take samu daga Hajja saboda irin kashedin da ta sha a wurin Daddy, ya yi mata alƙawarin ƙarasa rayuwa a gidan yari muddin ya  gani ko ya ji labarin ta kai hannunta jikin ƴarsa da sunan duka, ko kuma ta ɗaga mata murya ta wuce misali. Ga wani irin zagi na ba gaira babu dalili da ta koya, all thanks to Hajja, ko baƙi aka yi suka nemi su yi mata wasa sai ta nemi ta zage su. Akwai wani lokaci da Hon. ya zo dubata lokacin da ciwonta na Pneumonia ya tashi, Shaheed ɗanshi na uku ya kai tissue hancinta zai goge mata saboda ciwon nata ya kan zo mata da mura. Babu tsoron Allah ta kalli idonshi ta ce masa:

"Banja, wawa mai 'aton kai, an ce maka ban iya fyacewa bane?" He was dumbstruck don shi ya ɗauka ma bata iya magana ba.

Hon. ya ɗan yi dariyar yaƙe sannan ya ce mata ta yi haƙuri a fyace mata kar majina ta gangaro bakinta. Shi ma ya samu nashi rabon zagin don ko ce masa ta yi:

"Ina luwanka?Ni bana shon shishshigigi babba da kai amma ka iya gulma wa ya sa da kai?"

Da Mommy ta zauna ta yi tunani sai ta ga ba a ko'ina ta koyi zagi ba sai a wurin Talatu da Adewale, sai ta ga gwara ta ajiye aikinta ta zama full housewife ta kula da tarbiyyar ƴarta. Me amfanin ka nemi duniya ka tara kuɗi ƴaƴanka su taso babu tarbiyya? Da ta faɗawa Daddy bai ƙi bata haɗin kai ba, shi dama ba son aikin yake ba.

Babbar matsalar shi ne lokacin da Mommy ta ɗaura ɗamarar inganta tarbiyyar ƴar tata, ba ta tsaya ta karanci matsalarta ba, balle ta san hanyar da za ta bi. Yaron da ya taso babu ƙwaɓa har ya saba ba lallai ne dare ɗaya ka ce zaka zare masa ido ka dake shi ya gyaru kuma ya gyarun ba. Wasu duka na gyara su, wasu kuma barazana ce, wasu yaran kuma nasiha kaɗai za a musu su shiryu da dai sauransu.

"Mommy kar ki sa kabewa, kin san dai bana ci."

"To Mama Salamatu, sai kuma me?"

"You messed up you idiot!" Shaheed an ta faɗa a ranta tana ɗan dungure kanta, ita da ta zo acting as a good girl ya zata fara da bada order?

"I'm sorry Mommy just wanted to start a conversation." Shaheedan ta faɗa tana haɗe hannunwanta alamun sorry.🙏

Mommy bata ƙara tankata ba, saboda ita yanayin yarinyar ma mamaki ya ɗan bata duk yadda aka yi wani abin take so. Ta ɗauko container ɗin da take ajiye Maggi da niyyar yin haɗi a miyar alayyahun da take yi. Ba kasafai take yin Tuwo ba a gidan, yawanci in dai ta yi to za a yi baƙi ne ƴan gargajiya, kamar dai Hon. duk wayewarshi da kuɗinshi babu abincin da ya fi so sai Tuwo, shi ya sa duk inda zai je baƙunta, da Tuwon ake tarbarshi musamman ma in an haɗa shi da miyar alayyahu.

DUNIYAWhere stories live. Discover now