2- Shaheeda

20 0 3
                                    

Shekaru goma sha biyu da suka wuce

Da takalmanta rungume a ƙirjinta ta shigo gidan, saɗaf-saɗaf take tafiya tana waige-waige, alamun dai bata da gaskiya. Ta ci sa'a kuwa ba wanda ya gan ta har ta shige dakin baccinta.

"Allah ya so ni Mommy ba ta gan ni ba, na san da sai ta dake ni... Na shigesu ni Salamatu wayyo Allah na."  Tana cikin farin ciki mamanta ba ta ganta ba idonta ya kai kan report sheet dinta, kwata-kwata ta manta lokacin da ta ari pen din Sa'ada ƙawar ta ta gyara position ɗinta bata mayar jaka ba, ta ashirn ta zo cikin su ashirin da uku, ba ta shiryawa gori da masifar Mommy ba shi ya sa ta karɓi pen ta soke zero ɗin ya koma ta biyu ta zo. A tunaninta kenan.  Report sheet ɗin ta jiƙe sharkaf da ruwa, sai dai ana iya ganin wurin position din.

Da ta tuno yadda Mommyn tata ta kwallafa rai a kan result ɗinta sai kawai ta zauna akan gadonta pink da aka shimfide da pink bedsheet ta fashe da kuka, "Ban shiryawa faɗan Mommy ba" ta yi ta maimaitawa har bacci ya ɗauketa.

****

Falon Mommy a wannan ranar

"Wallahi Ajiya ben gen si ba, na je na samu principal an duba duka koyina ben gen si ba, kai Ajiya wannan yaro bata ji." Murɗaɗɗen mutumin ya faɗa yana miƙawa Mommy key ɗin mota, da alamun driver ne.

"Barr ka ga abinda nake faɗa maka ko?ban san da wane irin yare zan yi wa Shaheeda magana ta ji ba, haba! A ce ba a isa a faɗawa yaro ya ji ba? Ita kenan na haifa amma ciwon kan da take haddasa min sai ka ce mai ƴaƴa ashirin?za ta zo ta same ni ne."

"Look Sadee, kar ki sake ki taɓa min yarinya, ki barta ƙwaƙwalwarta ce ta ke buɗewa, kin fi kowa takura mata akan rashin kokari, ki barta she's just exploring the world. Za a gan ta ne."

Shiru kawai ta yi masa don in da sabo, ta saba. Baya taɓa ganin laifin tilon 'yar tasu, ko akan shi aka fara haihuwa oho. don ma ita ta tsaya akan yarinyar, tana shakkarta da abin nata sai ya fi haka.

Tun hankalin Barr na kwance har ya fara tashi ba labarin Shaheeda, ya kira gidajen 'yan uwa da abokai duk babu labari. Form teacher ɗinsu na makaranta kuwa har an danƙa shi hannun hukuma, a cewar Barr sakacinshi ne da ya barta ta bar makarantar ba a tabbatar an zo ɗaukarta ba, principal ɗin ma don yana ganin girmanta ne, tare suka yi jami'a da ita.

Ana wannan zaman jiran ne, Hajja Talatu, mai aikin gidan ta shigo falon da sallama, sannan ta ce:

"Hajiya akwai sauran aiki ne ko zan iya shigewa ciki in huta?"

"Hajja ina ganin babu wani aiki kuma, kin yanka min alayyahun da Adewale ya siyo?"

"Eh Hajiya, na ma wanke, da har zan tambaya ko an siyo kabewa sai kuma na tuna Hajiya Shaheeda bata ci, sai kuma..."

"Ajja kana da masala fah, an tambiyeki ka yanka Allehu, ka she eh sai ki yi siru ai. Sai ka yi karin biyani kuma?"

"Ka ga Adewale na kasa da kai ne balle ka dauka? Sai shishshigin tsiya, da hausarka da bata isheka ba sai aukin ba ni na iya." Masifaffiyar dattijuwar ta bashi amsa a zafafe.

"Good for nothing" Adewalen ya mayar da martani yana harararta.

"Kai ka isa in gudu saboda kai, in ka ga na bar gidan nan to mutuwa ce ta raba, kai za ka gudu Onica ba  dai ni ba. Ehe!"

"Ka ce kar na yi Ausa, na yi turanci ba ka gane ba, I Said good for nothing, ka ji na she ka gudu ne?"

" Ka ga ni bani da lokacinka, yauwa Hajiya na ce Shaheeda ba za ta yi zazzaɓi ba kuwa? Na ga ta shige dakinta sharkaf da na yi tunanin in ce  ta cire kayanta sai kuma na ce kar ta hayayyaƙo min." Talatu ta faɗa tana sosa kai, ita duk inda zance yake sai ta zaƙulo shi.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 24, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DUNIYAWhere stories live. Discover now