1: Yankan ƙauna

62 5 3
                                    

"Yanzu me kike yi a kitchen Shahee, ni dai a dan ilimina na san duk amaryar da aka kawo gidanta a lullube da mayafi angonta yake samunta a dakinta amma banda ke, wai ke a komai sai kin fita daban ne? "

"To fisabillillahi Ya Sheed ni da gidana ba zan wataya ba? Kai din fa tun ina yarinyata ka san ni, kuruciyar nan a gaban idonka na yi  an min share majina...kai an fa sha fama da mu. " Amarya ta bashi amsa tana kyalkyalewa da dariya da alama memories din da ta tuna masu dadi ne.

"Shahee tawa yanzu dai me kike yi a kitchen daga rakiya na barki a daki na dawo ban ganki ba. " Ya fada da murmushi a saman lebensa.

"Wallahi plate da cups na zo dauka, na san in ka raka su Ya Salim ba lallai ka dawo da wuri ba, ni kuma na fiso in ci kazar da zafi zafinta, ka san ta fi dadi musamman ma in da yaji yaji, Allah ya sa ta wurin Bashari me nama ka siyo. " Ta fada da tsalle tana dariya.

Baki ya sake yana kallonta, duk da ya saba da rashin kunyarta amma ta yau kam ta fi karfinshi.

"Shash kawai, Allah kin fiya kwadayi,ga tsoro, Kura kawai"

"Za ka fara ko? Kullum sai ka ce min shashasha,da kwadayayya, ko gajiya ba ka yi? "
Ta fada tana zumburo bakinta da ya sha jan baki.

"Ke ma ai ba kya gajiya da rashin ji, ga cin tsiya na rasa in da kike kai abincin da kike ci sam ba kya kiba. "

"Ni fa ka san Allah wataran ina sane nake rashin ji kawai don ka min magana"

"Ni ma fa kin san Allah ina sane kullum ki kai rashin ji sai na miki magana saboda kawai ki zumburo bakinki, karaKyau kike musamman yau da kika sa lipstick, kina da kyau Shahee ba zan gaji da gaya miki ba, kuma sai na ga yau kin kara kyau sosai, gayamin me sirrin?

"Kai Ya Sheed har ka kusa bani kunya, maybe don an min kwalliya ne, kuma yanzu zan je in wanke ni bana son kwalliya wallahi. "

"Sai kika yi rashin sa'a mijinki, Ya Sheed dinki na so, kinga dole ki ringa yi min Shahee... "

"Gwara ma ka yi mata kallon karshe don ba za ka kara ganin fuska ta da kwalliya ba. "

Diff aka dauke wuta, abin ya bawa Shaheed mamaki don gaskiya a yadda Abbanshi ya gaya mai unguwar ba a dauke wuta don gudun abinda ya faru yanzu, don ko ana dauke wuta Shaheeda ta rukunkumeshi, ba ta son duhu ko ya yake, wannan baya rasa nasaba da wani abu da faru a rayuwarta,wanda ya yi nasarar sace mata nutsuwarta, kafin ya gama dogon tunaninshi shesshekarta ta katseshi.

"Ya Sheed ka kunna mana Gen don Allah, wallahi zan iya mutuwa ban son duhu. "Ta fada cikin kuka tana sake kankameshi.

"Shhh I'm here , yi shiru kin ji mu je Parlour ki zauna in kunna mana Generator, sai mu je ma ki ci kazar,harda favorite yoghurt dinki na siyo miki mai sanyi. "

" A'a ni dai mu je tare ba zan iya zama ba. "

"To na ji mu je"

Fita suka yi, ita dai sai waige waige take duk da ba abinda take gani don in banda hasken torch light din wayar Shaheed,babu wani source din haske a gidan.

"Wayyo Allah kamar inuwar mutum nake gani a can" Shaheeda ta fada cikin ihu tana kara rukunkume Shaheed.

"Shahee ba fa na san Shashanci, tsoro fa ba hauka bane, kina ji Generator din ma ba mai, bayan sai da na gayama Abba a kawo min dan gudun irin haka, kin zo kuma kina cikawa mutane kunne. " Ya fada cikin daga murya yana tureta.

"Tun ba a je koina ba ka fara gajiya da ni ko? Don ka ga ni marainiya ce, ai dai ba ni na dorawa kai na tsoron duhun ba,kuma ni ba karya nake ba, dazu ma da ka fita rakiya na ga kamar giftawar mutum ta window. " Ta fada tana cika shi ta dan matsa gefa da shi dukda ko gaba daya jikinta karkarwa yake.

DUNIYAWhere stories live. Discover now