UKKU

3.3K 255 1
                                    

Fizge hannunta tayi ta dawo tana kallonshi. Ganin dogarin nan ba karamin tada mata hankali yayi, dan tasan Baba yaji zancen nan ma yagama. Amma dukda haka fuska tayi tana kallonshi. "Ke Zeenah baki da hankali ne wai? Maza ki bashi hakuri kafin na fadawa mahaifin ki."

Dago ido tayi ta kara kallonshi, ya wani daure fuska alamar yana jira a bashi hakuri, cikin ranta wani irin tsaki taja, ita gar ga Allah bata cika san iskancin yaran sarauta ba, in suna maka shiru sai kayi tsanmanin su suka haifi kansu ba haihuwar su akayi ba. Girgiza kai ta fara yi, "Malam Audu nifa gaskia bazan bashi hakuri ba, shifa ya bugeni bani ba." Abunda ta fada kenan tana girgiza kafa.

Malam Audu abokin Baba ne, ta sani sarai amma haka ta daure, ta gwanmace ta kwashi bugun Baba akan ta bawa wannan me daurarrar fuskar hakuri. "Kayi hakuri ranka ya dade." Abunda Malam Audu ya furtawa Bilal kenan har yana wani runsunawa.

Juyowa yayi wajen Zeenah, "Zeenatu ba magana nake maki ba? Wai kinsan waye wannan kuwa?" A harzuke yake magana.

"Yo ba dan sarki bane, aidai ba sarkin bane. Malam Audu nidai kayi hakuri amma wallahi bazan bashi hakuri. Na baro Mama gida kuma jikinta da zafin zazzabi. Zan tafi." Tana furta haka ko kallon inda suke bata karayi ba tayi hanzarin wucewa. Cike da hanzari ta isa gida, nan ta iske su Anty dasu Asiya zaune tsakar gida suna labari sai hamma suke, nan kowa jira yake ta dawo tayi girki tsabar zuciyarsu ta mutu.

Direct dakin Mama ta shiga, ko tsayawa batayi ba ta saurari maganar da Anty take mata akan ta barsu da yunwa ta tafi yawon gantalin ta. Tana shiga ta iske Mama kwance babu abunda take banda dogon numfashi kamar wacce zata mutu. Tayi maganar amma ko bude ido Mama batayi ba. Cike da hanzari ta rugo waje.

"Anty zo kiga Mama, na shiga uku! Anty wallahi na mata magana bata ansa ni sai numfashi take fitarwa da kyar." Hannun Anty ta riko alamar suje ta gani, amma Anty wani hankada ta tayi.

"To ta mutu din mana, ke dallah karki cika man kunne. Kinje kin gama gantalinki kin dawo kin ishi mutane da maganar banza. Zeenah idan zakije ki dora mana abinci ki tashi." Sakeke Zeenah ta tsaya tana kallonta kafin cikin gudu ta fita daga gidan gaba daya, gidan su Zainab ta nufa, inda ta iske babu kowa gidansu sai Babansu da shima bai dade da dawowa ba.

"Zeenah lafiya kuwa? Ya naga kin shigo a rude kina kuka?" A hanzarce ya taso yana tambayarta.

"Baba Mama ce bata lafiya, dakyar take numfashi karta mutu Baba." Babu abunda yake tada mata hankali kamar rashin lafiyar Mama, kuka take rigis kamar an aiko mata da sakon mutuwa.

"Muje muje a kaita asibiti, daina kukan kinji?" Hular kanshi ya mayar kafin ya tashi ya saka takalmi yana tafe Zeenah na binshi tana kuka. Keke napep ya samo ta dauki Mama da Zeenah gaba daya suka nufi general hospital wanda babu nisa dasu. Kai tsaye wajen da ake bada taimakon gaggawa suka nufa, inda aka karbi Mama da hanzari aka bata gado.

Babu irin godiyar da Zeenah batayi wa Baba ba, iindayaketa shaida mata babu komai bari yaje gidan idan sun dawo sai yasa Zainab ta kawo masu abinci. Nan bakin harabar ta fito babu abunda takeyi banda kuka. Ita batasan abunda sukawa Baba ba, amma idan a gabanshi Mama zatayi suma goma bai taba daukarta ya kaita asibiti. Duk wasu kaya masu mahimmanci nasu Zeenah ta gama siyar dasu saboda ciwon Mama.

Baba kuwa tunda Malam Audu ya fada mashi abunda Zeenah tayi hankalin shi ya tashi. cikin gaggawa ya isa gidan ya iske Anty na girki, yana tambayarta ina Zeenah ta tabe baki, "Yo Malam wannan fitsararar diyar taka ai sai kai. Nan tazo ta kwashi uwarta nasan basu wuce asibiti." Yana gama saurararta ya fice daga gidan bai tsaya ko ina ba sai asibiti. Dama yasan wurin zuwansu, kai tsaye nan ya nufa aikuwa ya iske Zeenah zaune bakin dakali sai kuka take.

Batasan da zuwanshi ba saidai taji saukar bulalar shi akan bayanta. Masifa ya fara yi mata inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Ita kuma ko hakuri ta kasa bashi, dan tasan duk wannan masifa bai wuce Malam Audu yakai kararta. "Kuma ki tashi mu tafi ki bashi hakuri. Zeenatu duk hanyar da kikaga zan shiga cikin matsala ita kike so. Ranar ma an fada man rashin kunyar da kikayi kofar masarauta haka nan na kyaleki."

"Baba Mama fa bata lafiya dawa zan barta?" Bulalar ya kara lafta mata. "Ki barta da ubanki. Nace ki barta da ubanki, Zeenatu." Wajen nurses din ya nufa dan dole suka rubuta takardar sallama yaje ya taho da Mama.

Suna isowa gida daki kawai Zeenah ta shiga da Mama kafin ya jata suka shiga masarautar. Tun tana togewa har taga babu yanda zatayi. Bangaren shi suka isa, nan Baba ya saka masu gadin wajen akan ace mashi ga Babban Bafade yazo wajenshi. Tun Zeenah na tsaye har ta samu waje a kasa ta zaune, ita duk tunanin ta yana wajen Mama, gashi ko abinci bata ci ba ga ciwo.

Sun kusa awa biyu a wajen, amma duk lokacin nan da aka dauka babu abunda Baba yakeyi banda sintiri, hankalinshi duk a tashe yake. Ita kuwa Zeenah bataga abun tashin hankali ba. Can sai gashi ya fito fuskar nan daure kamar an aiko mashi da sakon mutuwa.

Da hanzari Baba ya karasa wajenshi ya russuna ya gaisheshi. "Barka da fitowa ranka ya dade. Na samu labarin rashin hankalin da yarinya tayi shine nazo domin baka hakuri. Ayi mata aikin gafara ranka ya dade, hada yarinta." Shidai yana tsaye ko kallon inda take baiyi ba bare ya kalli wajen da Baban yake, hakan kuwa ba karamin bakanta ran Zeenah yayi ba.

"Zo maza ki bada hakuri Zeenatu." Kamar bazata zo ba haka ta tako tazo. Hararar da Baba ya wurga mata yasa ta durkusa har kasa bawai dan ranta yaso ba.

"Allah ya baka hakuri." Ta fada can ciki, wani irin mari Baba ya sauke mata, a gigice ta furta, "Dan Allah kayi hakuri abunda na maka." Tunda Baba ya mareta yake kallonta can kuma ya dauke kai.

"Malam Kabiru, kana da hali mai kyau, amma tarbiyar gidanka akwai gyara." Yana fadin haka ya barsu nan tsaye ya wuce ya shiga mota, dama gidansu Isma'il zaije wanda yake Barhim estate.

"Allah ya shiryaki Zeenatu. Kina dai jin abunda ya fada a kanki." Hankada keyarta Baba yayi daga nan har suka isa gida.

Haka rayuwa ta cigaba da yina Zeenah. Yanzu ko islamiyyar da take zuwa tana samun sauki ma an basu hutu tunda an yaye su, sai wanda yakeso zai koma domin cigaba da littatafan addini. Gashi Baba yace shi bada kudinshi zata koma wata islamiya ba, tunda baiga amfanin islamiyar da take zuwa ba. Babu abunda ta tara banda fitsara da rashin kunya.

Jikin Mama har yau yaki dadi, dukda ba magana take ba amma Zeenah tana lura da yadda jikinta yake kara rikidewa. Gashi ko suma zata rikayi tana dawowa Baba bazai taba daukar Mama ya kaita asibiti ba. Sati guda kenan, yau bayan ta gama girkin gida tayi wanka. Abinci ta bawa Mama kafin taci itama ta fara sallah. Tun kafin ta idar da sallar taji Mama na kakarin amai. Karshen sallar nan dai saidai Allah ya yafe mata, amma kwata kwata ba cikin hayyacinta tayi ta ba.

Juyowar da zatayi taga Mama na aman jini, wani ihu ta kurma dan kuwa tasan ko tama Mamar magana ba ansa ta zatayi ba, ga jikinta da yayi wani likib. Da gudu ta fita daga gidan gaba daya, yau ba gidansu Zainab ta nufa ba, direct Masarauta ta nufa dan kuwa wannan ciwon yafi karfin kowa, dan ita a tunanin ta ma Mamar mutuwa tayi.

Tana cikin katuwar masarautar taji mota na neman bigeta, wani irin birki motar taja ita kuma nan take ta fadi kasa har kafarta ta gurje. Tana nan durkushe, dan kuwa ba karamin tsorata tayi ba sai taji me tukin motar ya fita. Saitin kanta ya tsaya ya fara masifa, "Dallah Malama ke wace irin mahaukaciya ce zaki shigo masarautar kina gudu kamar wata mai tabin hankali? Yanzu da mun bige ki mun bige banza wallahi dan ko..."

Ai bata bari ya karasa ba ta mike tsaye, idanunta a rufe tsabar yanda masifa ke cin ranta. "Naci uwar rashin hankali wallahi. Inma ba dan iskanci ba da wulakanci ka kusa buge mutum ka fiyo kana man hargagi saman kai? Daka bigeni ka bige banza? Uban banza zaka bige ba banza ba, dan wallahi da sai nama maka asarar da bazaka tana tsanmani ba. Sakarai kawai wadanda basu san darajar dan adam ba." Tana fadin haka ta buga uban tsaki ta bar Isma'il nan tsaye. Bilal yana jinsu daga mota, dan kuwa tunda ta dago ya ganeta, wannan fitsararriyar yarinyar ce.

Tana tafiya tana masifa, ashe shi kuma Isma'il biyota yayi, dan kuwa ranshi yakai kololuwa wajen baci. Tana gab da shiga fada, wanda a nan Baba yake taji an juyo da ita, kafin tasan meke faruwa Isma'il ya gaura nata lafiyayyen mari. "Kam bala'in can kayyasa!" Abunda ta furta kenan itama ta sauke mashi nata yatsun.

Bilal wanda tunda Isma'il ya fara binta shi kuma ya shiga wajen driver ya biyosu dan yaba Isma'il hakuri su wuce inda zasu, shine yaga ta mari Isma'il. Ai kuwa a fuskace ya fito ya faska mata wani marin. "Kai wallahi kun cika yan rainin wayau!" Jikinta har rawa yake yayin da ta daga hannu biyu ta saukesu a duka kumatun Bilal. Dama da haggu.

A JINI NA TAKEHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin