BIYU

4.3K 312 1
                                    

Da sallama a bakinta ta shiga gidan, dukda cewar tasan abunda zata iske a gidan amma direct dakin Mama ta nufa. Addua take Allah yasa tun wannan baccin data barta tanayi bata farka ba, dan kuwa tasan in har ta farta dole sai ta nemi shiga bayi, gashi bata nan. May be ta bata jikinta da kazanta. Duk da irin kururuwar da Aunty take mata baisa ta juyo ko kallon arziki ta mata ba, kai tsaye ta daga labulen dakin kawai ta fada ciki.

Kwance taga Mama sai nishi take alamar tana bukatar wani abu, cikin hanzari ta karasa wajenta tana tambayarta ko lafiya? "Mama bandaki kikeso na kaiki? Ko wani waje ki maki ciwo?" Daga kai Mama ta fara yi kafin daga baya ta girgiza kai, inda sabo Zeenah ta saba da yare irin na mahaifiyarta. Take ta cire hijab dinta ta kamo Mama sukayi hanyar makewayi.

Tun kafin tasan ita wacece mahaifiyarta ke fama da cutar shanyewar jiki, tun bata iya kula da ita har ya zamto ita take mata komai. Anty kuwa matar babanta ce, itama tana da yara biyu da Asiya da Firdausi. Duka duka shekara biyu Zeenah ta bawa Asiya, Firdausi kuma ta bata shekara biyar. Amma duk iya awannin da zatayi bata gida haka zatazo ta iske tulin aiki yana nan yana jiranta babu mai taimaka mata. Idan taso tayi ma Anty rashin kuwa kuma Baba hana dawowa zata fada mashi, shi kuma yayi mata dukan tsiya. Tun tana maida martani har ta gaji, dan bala'in tsoron Baba takeyi.

Saida ta taimakawa mahaifiyar har suka shigo daki kafin ta kalli Mama tace, "Mama an kawo maki abincin rana?" A hankali Mama ta girgiza kai, dukda cewar Zeenah ita take dafa abincin gidan amma bata isa ta dibarwa mahaifiyar ta ko ita kanta ba face ta jira Anty ta raba ta bawa kowa.

Dakin Anty ta shiga da sallama, sallah ta iske tanayi saida ta jira ta sallame kafin ta dago ta kalleta, "Lafiya dai sarakan rashin kunya? Ko wani tijarar aka zo yi mani?" Aunty ta tambaya tana kare mata harara.

"Na tambayi Mama tace ba'a kawo mata abincin rana ba, shine nazo na karba. Tunda rashin imani yayi muku yawa, ace yanzu mutum yana kwance ko hannu bai iya juyawa amma baza'a iya samun wanda zai kai mashi abinci ba." Kalle kalle ta farayi cikin dakin, dan kuwa tasan tabbas Anty bata taba ajiye abinci cikin madafa.

"Ke Zeenah wallahi tallahi ki kiyayeni, dan ubanki ita uwar taki taki zuwa ta karba da kanta wato sai ta jiraki dan tsabar munafunci ko? Ke kuwa sarkin yan rashin kunya kizo kiyi fitsara a dauki abinci a baki dan ana jin tsoronki. To abinci dai danaga har yamma tayi bata fito ta dauka ba nagaji da ajiyar shi, gashi can su Asiya suna ci tunda bakiga damar dawowa da wuri ki girka na dare ba."

Ai ko kafin Anty ta gama magana Zeenah ta rafka uwar salati tana fadin, "Kam bala'in can, amma wallahi Anty kinma iya rainin wayau. Wane kalar Mama bata lafiya ko magana batayi ne baki gane ba. Kefa in kinso zalincin ki babu abunda baki iyayi. To na rantse da Allah in su Asiya sun isa suci abincin nan saidai in daskare nan wurin." Ko kallon inda Anty take batayi ba ta karasa wajen su Asiya ta fizge kwanon abincin, dama tsoronta sukeyi dukansu dan ba karamin bugu take masu ba, ta gwanmace idan Baba ya dawo shi ya rama masu.

A harzuge Anty ta taso tana fadin, "Zeenah idan kinasan ki kwana lafiya yau cikin gidan nan wallahi ki ajiye abincin nan. Uban wani yace ki tsaya yawan gantalin ki har mangariba baki dawo gida ba?" Wani wawan tsaki Zeenah taja ta fita daga dakin gaba daya, san har ita Anty bawai daga mata tayi ba, sunsha yin dambe ta bata kashin tsiya saidai idan Baba ya dawo ya rama mata. Dan duk duniya babu wanda ya isa ya mata ta kyaleshi bayan Baba. Shima kuma tsoro ne kawai.

Dakin Mama ta koma kafin ta fara bata abincin a baki, tana kallon yadda Mama ke girgiza kai, alamar bataso taje tayi fada dasu ba dan tasan tabbas babu abunda zai hana Baba dukan Zeenah yau. "To Mama kina jin yadda mukayi dasu fah, rainin wayau ne kawai irin na Anty. Yanzu in banda iskanci ko su Asiya bai ci ace sunyi aikin gidan nan da girki ba kafin na dawo? Dan ubansu kattin banza saidai suna kwance a dafa a basu? Ai wallahi duk sai nayi maganin su." Mama murmushi kawai tayi, wanda hakan yana nufin da Zeenah tayi hakuri. Tunda ta taso bata taba jin muryar mahaifiyarta ba, tun abun yana damunta har yazo ya dai a damunta.

Saida Mama ta koshi da abincin kafin Zeenah ta cinye sauran. Waje ta fita ta fara wanke wanke kafin tayi sharar tsakar gidan. Girki ta dora kafin ta wuce ta wanke bayi. Tana cikin tukin tuwon taji sallamar Baba, wani irin duka gaban ta yayi amma dukda haka bata nuna tsoro ba ta cigaba da yin aikinta. Tana jiyo kukan Anty lokacin da take fada mashi abunda tayi, ai ko ida saurare baiyi ba ya karaso cikin kitchen din.

Bafade ne a masarautar katsina, wanda a halin yanzu yana cikin fadawan dake zama cikin fadar sarki. Da dorinar shi ta dogarai da ita yake dukanta, ko kuka batayi ba har yayi ya gama yanata zage zage. Tashi tayi ta koma ta cigaba da girkinta, dan kuwa tama kanta alkawari duk bala'in dukan da Baba zai mata ta daina mashi kuka, dan ta lura idan tayi kukan shine cikar burin Anty.

Dayake yau yan bala'in takeji ita da Mama ta fara dibar wa tuwon kafin ta leka dakin Anty tace mata an kammala. Tanajinta tana masifa wai ta dibar masu da yawa amma ko kulata batayi ba. Dama tayi sallar maghrib, isha'i tayi kafin tayiwa Mama taimama itama tayi sallarta cikin zuciya sannan ta bata tuwon taci itama taci. Suna zaune Zeenah tanata bata labarin yadda musabakar su zata kasance, ita kuwa Mama babu abunda takeyi saidai murmushi.

A haka suka jiyo sallamar Zainab, daidai lokacin da Zeena ke bata labarin fadan da tayi bakin gidan sarki, kwalalo ido Mama tayi ita kuwa Zeenah ta fashe da dariya. "Allah Mama saima kin ganni ina masifa, nan kuma a zuciyata tsoro ne fal, dan wallahi nayi tunanin wani zaije ya kira Baba inji dukan tsiya a wajen. Dan Sarkin fa, Bilal dinnan da akace ya dawo shi fah!"

A hankali Zainab ta shiga rike da Alquranin ta, gaida Mama tayi ita kuma ta mayar mata da murmushi. Nan suka zaune suna haskawa da wutar fitilar kwai Zeenah tana tata haddara ita kuma Zainab dama ta kasa tisa tata karba kawai Zeenah tayi itama ta karbi tata. Yar fira sukayi kadan kafin Zeenah ta rakata bakin kofa sukayi sallama. Ranar juma'a kaf dinta haddasa sukayi, dan kuwa ranar asabar karfe takwas za'a fara musabakar.

Koda ranar asabar tayi Zeenah tunda tayi sallar asuba bata koma ba, aikin gida tayi, tayi abincin safe ta dibar masu dan tama kanta alkawari an gama yi masu wannan iskancin a cikin gida. Direct dakin Mama ta wuce saida ta tabbatar Mama ta koshi kafin taci. Mama ta fara taimaka mawa tayi wanka ta shiryata sannan itama tayi. Uniform dinta ta dauko ta saka ta kalli Mama sai murmushi take alamar Mamar tanajin dadin yanda Zeenah ke tafiyar da rayuwar ta.

"To Mama zan biyawa Zainab sai mu wuce. Dan Allah Mama ki kula da kanki kinji?" Daga mata kai tayi alamar to kafin Zeenah ta kara wani murmushin. "Nasan a cikin ranki kince Allah ya man albarka kuma ya bani saa ko Mama?" Nan ma Mamar ta kara daga kai tana murmushi. "To Ameen Mamata, sai mun dawo." Daga haka ta fita gidan zuciyarta fall cike da farin ciki.

Koda taje gidan su Zainab saida ta jira ta gama shiryawa kafin suka wuce. Saulawa ce unguwar su, wadda bacin masarautar katsina dake zagaye da za'a iya cewa a hade suke, san kuwa titi ne kawai tsakanin su. Tafiya suke suna hirar yadda musabakar zata kasance.

Dan dukan kafadar Zainab Zeenah tayi, "Ke naji Malam Awwal yace har sarki wai sun gayyata, kar azo ace ana neman Zeenah Kabir Muhammad a zaneni." Tare suka kwashe da dariya.

"Haba Zeenah sundai gayyata ne kawai, amma saidai ya aiko wani ya wakilce shi ai, badai shi yazo ba." A haka suna fira cikin jin dadi suka karasa makarantar.

Yadda Zainab ta fada kuwa haka akayi, lokacin da ake gabatarwa sukaji an fadi sunan wanda Sarki ya aiko a madadinshi, amma sam hankalin Zeenah bama ya wajen. Karatu sunyi shi masha Allahu, Zeenah kuwa ta samu kyauta har illa masha Allah. Sai wajen azahar kafin taron ya watse, cike da hanzari ta barwa Zainab da yan gidansu da sukazo daga baya kyaututtukan ta tayi hanyar fita makaranta, ba kasafai ta cika san barin Mama a gida tayi awanni bata koma ba, dama tunda suka gama secondary school sai abun yazo mata da sauki.

A gaggauce gudu gudu sauri sauri tana tafiya can taji tayi karo da mutum, gashi kanta ya bugu sosai, gashi duk duniya bata hada Mama da kowa ba, dan har Baba wani lokacin gaya mashi magana take saboda Mama. "Dallah malam kai wane irin mutum ne? Dan mugun abu sai kuyita tafiya ko kallon hanya bakuyi sai mutum yayi magana ace yayi rashin kunya ko?" Cike da masifa ta dago nan take idanunta suka sauke cikin na Bilal, wani wawan tsaki taja tayi gefe zata wuceshi amma dogarin dake bayanshi yayi hanzari rikota ya maidota baya.

A JINI NA TAKEWhere stories live. Discover now