GOMA

4.7K 200 8
                                    

🦋🦋A Jinina Take... Sarauta 🦋🦋

Na Aysha Malumfashi

Babi na 10

Koda Bilal ya fita direct dakinta ya nufa, har ya bude kofa bata sani ba, tana kwance kan gado tana kuka. Yanajin shashekar kukanta a hankali amma dukda haka bai chanza kudirin daya kawo shi ba. Takasa yaje yayi inda take kwance, fizgo hannunta yayi ya mikar da ita tsaye.

Fizge hannunta Zeenah tayi tana kallonshi kafin ta goge hawayenta. "Dallah Malam lafiya zaka shigo man daki hada su fizge kamar wanda nayi wa sata?" da masifa take magana, duk kuwa da idanunta da sukayi jajir tsabar kukan da tasha. Mama take tunani, magana takesan tayi amma ta rasa wanda zatayi shi dashi.

Ya dade yana kallonta ranshu yana kuna, tunani yake wace kalma zai furta mata? Can dai da jyar ya bude baki ya fara magana, "Idan abunda kike bukata kenan magana kawai zakiyi basai kinje kina sakamin magani a abinci ba."  Shi gani yakeyi tasan maganin yana hanawa ko ya kara, amma na karawar yafi damunshi.

Tsaye tayi tana kallonshi, to wane magani kuma? Sai can kwakwalwarta ta tuna. "Kai dallah malam dakata mun, maganin..." sauri  katse ta yayi. Yanayin shi ya nuna zallar bacin rai.

"Har kina da wani abunda zaki fada mun? Da kinsan abunda kike bukata kenan da dadewa aida ba sai kin nemo maganin da zai tilasta ni ba. Yes nasan an aura min ke dan dole dama na sauke maki hakkin ki..." Wani dogon tsaki taja, ita haushi ma ya bata. Sai yanzu ta gane cewar maganin yayi aiki a kanshi dan ita bata taba sanin yana hana haihuwa ba. Da tayi niyyar fada mashi wanda ya bata maganin, amma ganin yadda ya wani hade yana magana shi a dole an saka mashi magani a abinci yasa ta fasa.

"Dakata mun dallah malam. To wai kai tsaya, nan har ka kai namijin da zaa saka ma magani kafin a janyi hankalinshi? Bari kaji fah, wallahi dana so tun ranar dana zo gidan nan bazaka kara yin wani abu ba face da umurni na. Da dai namijin gasken ne, amma a haka ni banga namiji ba wanda har sai na saka magana kafin na shawo kanshi, ashe ma ba macen bace." Harara ta dalla mashi tana nuna shi daga sama har kasa. Kalamanta ba karamin bata ma Bilal rai yayi ba. Wallahi duk duniya babu wanda ya raina mashi wayau sama da yarinyar nan.

Fizgo ta yayi ta fado jikinshi, tana kallo ya matso da ita har tana gab da fuskar shi, "Kai wai miye haka? Zaka sakeni ko sai na tara maka jama'a cikin gidan nan?" Duk da tsoron dake cinta da kuma kokarin kwatar kanta da takeyi bai hana Zeenah magana ba.

"Namijin da baki gani ba shi zan nuna maki." Daga haka ko kafin ta furta wata kalma Bilal ya hade bakinsu waje daya. Shi har ga Allah da mugunta ya fara mata, a hankali ya fara neman hankali a jikinshi yana rasawa. Saida jikinshi ya gama mutuwa yaji Zeenah ta fizge jikinta daga nashi, wata harara ta zabga mashi kafin ta nuna mashi kofa da hannunta.

"Na rantse da Allah karka kuskura ka kara tunanin hada jikina da naka, anje an saka maganin. Naga dai ka mata nan a duniya burjik ko? Jeka auro ukku gobe, kai in baka iya jira goben tayi samo wata yau ka aura yanzu a masallaci. Fitar man daga daki!" Dakyar take magana, dan numfashinta nema yake ya dauke. Tunda take bata tabajin bugawat zuciya irin ta yau ba. Kiris ya rage a samu matsala wallahi.

Bilal ya dade a tsaye kafin ya fara nufar inda take, wannan yarinyar azzaluma ce ta gidan gaba wallahi. Ta saka mashi magana, sannan kuma har tana da bakin da zata mashi rashin mutunci? Tafiya yakeyi wajenta ita kuma tana jin baya baya, kirjinta bugawa yake kamar ganga. Har saida sukazo bakin gadon kafin ta fada ya bi ta kanta.

"Wai kai miye haka? Dallah malam ka fitar mun a daki!" Nunawa yayi baiji abunda take fada ba. A hankali hannunshi ya fara yawo jikin Zeenah, tun tana tutturewa har ya mutar nata da jiki gaba daya. Wasa wasa gani take magana nasan zama gaskia gashi da alama ya gama fita hayyacin shi. Wani karfi ya zo mata tunowa tayi da irin rashin mutuncin data mashi. Kuma ma idan ta kyaleshi ai wallahi yasa lallai da ita.

Tunkude shi ta mike tsaye tana gyara rigarta, "Fita! Na rantse da Allah Bilal ka kara minti biyar cikin dakin nan zan maka rashin mutuncin da baka tunani. Ka fitar man daga daki. Ana ganinka haka haka ashe jarababbe ne kai."

Tana kallonshi yana takowa har inda take, wannan karan yana zuwa wajen ya fizgo yar rigar barcin saidai Zeenah taga rigar ta yage. Gaba daya jikinta ya bayyana. Batasan lokacin da faska mashi mari ba. "Koda wasa ko a mafarki karka kuskura kayi tunanin kara yiman haka. Fice mun daga daki wallahi tun nida kai bamuyi nadama ba." Tana fadin haka ta nufa wajen wardrobe dinta, wata rigar baccin ta dauko kafin ta cire wannan gaba daya ta saka wata.

Gadon ta nufa ta kwanta hada lulluba kafin ta kashe wutar dakin gaba daya. Tanaji ya kusa minti goma cikin dakin kafin ya fita. Hannu tasaka saitin zuciyarta dake harbawa kamar zata tsinke, "Na shiga ukku! Dama haka akeji? Dan wahala kawai ai wallahi ko ta nan sai na rama iskancin da kake mun. Ita kuma waccan tsohuwar banza gobe zanje inji dalili." Karshe dai kasa baccin tayi saida taje tayi wanka ta dawo kafin da kyar bacci ya dauke ta.

Da safe tana bacci taji muryar Isma'il da Bilal wajen shan iska, dayake ta wajen window din dakinta yake. Duk wani abunda akeyi a wajen tanaji.

"Ni bansan bansan ya akayi ba, to ko jinin ka karfi gareshi da za'ace maganin hana haihuwa kai ya koma maka excess production of sperm? Kasan Allah muje wajen Dr. Dara ya dubaka." Wani irin duka gabanta yayi, hana haihuwa?! Amma ai ita Fulani ba haka tace mata ba, oh shiyasa yazo yana mata wani hucin banza cikin daki? Wai shi za'a hanashi haihuwa?

Amma indai hakane Fulani ita ta maida yar iska bama Yariman ba. Saukin abunda taji daya ne, tunda shi bai mashi wannan illar ba, wannan dayar matsalar kuma shi yaji. Wanka ta tashi tayi kafin ta fara aikin gida, kamar yadda ta saba tanayi tana karatun Kur'ani. Amma ta saka ma ranta dole taje wajen Fulani taji dalilin bawa mijinta maganin haka haihuwa.

Tazo fita kitchen sai ta tsaya wajen fridge shi kuma Bilal yana shigowa, ko kallon inda take baiyi ba itama haka. Ruwa zata dauka a cikin fridge shi kuma zai daukar masu yoghurt shida Isma'il. Shi ya bude fridge din ta tsaya tana jiran ya dauka koma me zai dauka ya wuce. Ya dauko kenan ta mika hannunta zata sauka hannunsu ya gogi juna. A tare suka dago suna kallon juna. Bilal shi ya fara bude idanshi dan kuwa shi har cikin ranshi baiso haka ba. Haushinta yakeji amma kuma abunda yake damunshi na neman rinjayar wannan haushin.

Cups ya daukar masu kafin ya fita itama ta dauki ruwanta ta fita daga kitchen din. Koda Bilal ya koma wajen Isma'il shiru yayi, dama tun zamansu wajen Isma'il zai iya irga maganan daya mashi, dan koda ya dawo yaga yanayin shi ya chanza bai damu ba. Shi dama yasan halin kayanshi.

Daga nan bangaren Fulani sukaje, dan jiya gaba daya ma Yarima baije ya gaishe ta ba. Suna isa suka zauna falo suna jira ta fita, wace yarinya budurwa ce ta fara fitowa daga daya daga cikin dakunan. Daga gani bata wuce shekara 18, murmushi mai kyau ne kwance saman fuskarta.

Wajensu ta karaso, "Ina kwanan ku?" Abunda ta furta kenan, ko Isma'il da yake mai magana can kasan rai ya amsa mata balle uwar gayyar da ko kallo bata isheshi ba. Tv ta kunna ta zauna tana kallo tana cin kayan marmari.

Zuwa can Fulanj ta fito ta zauna tana masu murmushi. Gaishe ta sukayi a tare ta amsa kafin ta kalli Bilal, "Yarima jiya ban ganka ba, ince dai ko lafiya?" Yadda take maganar kai kace wallahi tallahi ta damu kuma kaunar Yarima Bilal din take da gaske.

"Lafiya lau Fulani, aiyuka ne suka sha man kai." Kanshi a kasa ya bata amsa.

"Juwairiyya kin gaida su ko? Wannan diyar yaruwa ta ce da take aure a Abuja. Ta gama secobdary school shine aka zo man hutu." Fulanj ce ta karashe zancenta tana kallon su.

Isma'il ne kadau ya furta "Allah sarki." Yana lura da irin kallon da Juwairiyya take bin Bilal dashi, shi dariya ma ta bashi dan tasan sai tafi baiwa shan wahala indai Yarima zatabi.

Sallama suka ma Fulani kafin suka tashi suka fita. Suna fita kamar an tsikari Juwairiyya haka ta juyo ta rungume Fulani, "Fulaniii!" Ta fada da murya mai cike da zallar farin ciki.

Tallabo fuskar ta tayi tana murmushi, "Ya akayi ne diyar Fulani?"

"Wallahi Fulani yariman can nakeso. Ai banda matsala ko, Fulani?" Duk yarin Maimunatu babu wanda suke shiri sosai da Fulani kamar Juwairiyya, dan ita ta yaye ta lokacin da tana yarinya.

"Indai Yarima Bilal Kabir Usman ne, Juwairiyya kin sameshi kin gama. Kedai kiyi abunda nace kawai." Rungume Fulani Juwairiyya tayi, itama Fulani murmushi tayi, dan ga hanya mashi sauki ta zo, wacce zata cimma burinta nan bada jimawa ba.

A JINI NA TAKEWhere stories live. Discover now