"Me hadin Toronto da rubuta zunubi?" Sumayya ta tambaya ganin yarinyar ta dauko wata magana. Wanda bama hadinshi da abin da take fada mata. Share maganar tayi dan har kanta ya fara ciwo.

"Me kike son ci?" Sumayyah ta tambayeta as they approached the kitchen. Hannayensu a rike kamar wasu kawaye wanda dayawa zasu dauka yaya da kanwa ne dan har yau ba'a yarda Sumayya ce ta haifi Jannah. Ko a ido bata wuce early twenties dinta ba.

"Alfredo pasta will do" Jannah ta murmusa tana lashe baki.

"Shi kadai?" Sumayya ta tambaya cike da kulawa.

"Yes mom I'm not that hungry."

Later in the afternoon

"Tell me Jannah a ina kike son celebrating birthdayn ki a nan Toronto? " Ahmad ya tambayi yarshi yana kama mata kai da ribbon

"Daddy I prefer it here in Toronto dan ko zanje Wani wajen gobe, Sunday I won't have friends to celebrate with" Jannah ta fada tana mai kokarin mika mishi ribbon . Yanzu suka gama fad'a da Sumyya dan taki amince wa Jannah ta yanke gashinta. Daga karshe ma cewa tayi idan har tana son yanke gashin ta bari sai ya kai guiwanta.

"As you wish princess" Ahmad ya murmusa yana tara mata gashin ta dake dai dai elbownta

"Your sister is coming back today." Sumayyah ta sanar da ita lokacin da ta dauko nail cutter dan yanke mata farce. Sam sam hankalinta bai dauki zuwa saloon yin pedicure da manicure ba.

Hasali ma saloon dinne ma bata so, gani take akwai possibilities na dauko chuttuttuka a can shi yasa suke da home saloon dinsu a cikin gidan.

"Dama one day excursion ne? I thought it would last for a week fa" Jannah ta janye kafarta tana ihu har ma da karamar rawarta. Hakan yasa Sumayya zabga mata harara dan kadan ya rage da yanke kafarta

8:30 Pm

"Happy birthday Jannah" Ahmad yayi kissing goshinta hade da mika mata Kananan boxes guda biyu"

"Thank you baba" ta amsa tana murmushi. Sai wani special take jinta ganin yanzu ita ma teenager ce. Har su maganan driving a fara yi dan tana tsananin son mota.

"Sumayyah birthday Jannah" Momma ta bata boxes guda uku as birthday gift dinta sannan taja hannun mijjnta dan ba yaran space dinsu

"Thank you mamma" Jannah ta fada da karfi.

Bayan an gama celebration Ahmad yace yana da announcement. A maimakon souvenirs ko wani abu da su je gida dashi, ya biya musu tare da friends dinta hutun two weeks a Disneyland after school. Mommy kuma ta dau nauyin shopping..

"Thank you my beloved parent you guys made my day wallahi." Jannah ta rungumesu fuskarta shimfide da kyakkyawar murmushi.

"Anything for you Angel" Sumayya ta sumbaci goshinta

"Sorry am late" Rahma dake bakin kofa ta shiga da sauri. Har wani tuntube take yi, dan ba a nitse ta shigo ba, tun daga bakin gate na gidan take gudu.

"Big sis...!!" Jannah tayi attacking nata da hug, da dukkan karfin da Allah Ya bata, hakan yasa suka zube kasa. "I miss you" Jannah ta furta tana kokarin tashi, had'e da mikar da Rahama.

"Sorry for the late wishes" Rahma ta fada yayin da take zama a kasan, dan ji take kane bata da kuzarin da zata tashi, dan dama ta debo gajiya.

"Yeah you'll surely make up for it" Jannah ta riko hannunta ta taimaka mata ta tashi, dan yanda ya zauna nan kasan bata da alamar tashi a wajen.

"How was your trip?" Jannah ta tambaya. Hannunta rike da jakan Rahma da kuma paper bags da ta shigo dasu.

"Shush Jannah ko hutawa fa batayi ba" Cewar Sumayyah ganin Jannah ta kasa yin shiru ko kadan gashi kuma da gani Rahma ta kwaso gajiya dan har yanzu sport wear ne a jikinta

"Anty and Uncle I'm back good evening" ta dan runsuna tana gaida Ahmad dake ta faman murmusawa. "Evening Rahma welcome back" ya amsa yana me sake mata tattausan murmushi.

"How was your little trip?" Sumayya ta tambaya da ta rungumeta. Tayi kewarta sosai dan kwana biyu da bata gidan.

"It was hilarious, wonderful, amazing, awesome and everything else" Rahma ta fada surutu tana murmushi. Dama Allah ya yita da tsananin son adventure

"Kije kiyi wanka you must be tired" Sumayya ta sake fada tana mayar mata da gashinta cikin turban dake kanta dan ko rolling din ma bata yi yau ba, ballentana ta sa niqaab. "Eh Rahma go freshen up sai kici abinci"

"Toh Uncle. Muje Baby sis". Ta riko hannun Jannah sannan suka wuce upstairs.

**********************
"Oh my...! Ya Allah you got me this?" Jannnah ta zare ido tana kallon silver and gold bracelet da akayi carving "Jannah" da Arabic. Kasa dena murmushi tayi tana sake kare wa bracelet din kallo

"Anything for you Jannah" Rahma ta murmusa tana jan kumatun ta, sosai take son Janah har cikin zuciyar ta.

"Sis mu bude gifts nasu Baba da Mamma mana?" Jannah ta shagwabe fuska tana ture hannun Rahma, daga jikin kumatunta.

"Toh Jannah" dariya Rahma tayi sannan suka nufi inda ta ajiye gifts din cike da zumudi suka hau barewa, a gaggauce.

"Keys na me kuma wannan?" Jannah ta bata rai cikin confusion" tana karewa keys din kallo, gashi nan dai single key ne guda daya, unlike sauran keys data saba gani.

"Whoa..! Tickets! Tickets!" Rahma ta ringa ihu. Harma da tsalle, baki Jannah ta bude tana kallonta cike da mamaki, ita kuwa Rahama bata ma san tana yi ba.

"Chill sis you are sixteen for Allah's sake ki dena ihu" Jannah ta toshe kunne tana frowning, ga dukkan alamu Rahama ce karama ba ita ba, watakil mistake aka yi aka ba Rahama girman.

"Ke come, zo ki gani tickets ne fa na South Korea, Switzerland and Saudi Arabia" Rahma ta fada fuskarta dauke da sheepish smile. Da yake ma'abociyar tafiya ce, har ta Fara tunanin inda zai fara zuwa.

"What? I thought Baba fa ya manta" Jannah ta toshe bakinta cike da mamaki. Duk da cewa sun sha zuwa kasashe daban daban Allah ya daura mata son zuwa wadan nan da bata taba zuwa ba illa Saudi.

"Jannah kina tunanin Uncle zai manta? Ni ma last birthday na haka yayi min kawai dai choice namu ya bambanta" Rahma ta ce tana kallon Jannah dake smiling, kamar wata gonar auduga.

Jannah tayi dariya tace "kin tuna zuwan mu Spain har muka bata a kasuwan Barcelona?" Kyalkyalewa da dariya tayi da ta tuna yanda idanunta ya raina fata. Bata taba tsorata irin na ranar ba.

"In zan manta har wani mashayi ya bi mu" Rahma ta sake kwashewa da dariya tana tuna irin gudun da tayi Ranar dan har kafanta na taba kanta ta baya.

"Subhanallah! Aunt is bae wallahi kalli diamond pendant din nan fa shima sunanki ne aka rubuta da a ciki" Shiru Jannah tayi tana nazarin mesa Rahma bata kiran Sumayya da mama.

Bata tana tambayarta ba amma kullum abin na ranta sai dai bata son bata mata rai. Hakan yasa tasa a ranta kowa da yanda yake son kiran iyayenshi, kamar yanda ita ma take kiran su da sunaye daban daban.

"Keys din kuma na me?" Jannah ta saka daga wasu keys din a karo na biyu, sai dai wannan da tambarin Audi a jiki. So take ta ce na mota ne amma tana shakkun hakan.

"Idiot keys na mota mana baki ga key holder na bunny bane? Ko baki ga logon Audi a jiki ba?" Rahma ta tura mata keys din gaban idonta, dan ta sake ganin ta yarda.

"Sure"Jannah ta murmusa ganin burinta na fara jan mota ya kusa zama gaskiya, murmushi tayi tana me yiwa mahaifin ta addu'ar karin arziki.

Rahma tace "Does that mean dayan na gidane? Remember a twelfth birthday na na samu mansion na"

"Eh fa ga papers dinma" suka zaro ido suna karewa papers na gidan kallon

"Alhamdulillah"

"Alhamdulillah"

Shower your love with votes and comments.

Love you all <3

Bookaholicnutella

ILLAR MARAICIUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum