"Wa alaikum Salam baby har kin dawo?'' Mahaifiyar ta ta tare ta da murmushi ga dukkan alamu daga kitchen take dan gidan gaba daya kamshin Arabian cuisines yake. Ga kuma turaren wuta dake tashi.

"Eh mama daddy fa?" Jannah ta rungumeta. Ta kosa taga mahaifinta daya dawo daga tafiya. Dama shine abokin wasanta. Wanda yafi biye mata suyi ta shirme. Murmushi tayi tana tuna last fitansu shopping, daurta yayi kan wuyarshi dan ta dauko pack na gummy bears dake shelf na sama a mall din.

Hatta turawan wajen sai da sukayi mamakin soyyayar dake tsakakin su. Dan abin mamaki ne aga mutum attajiri irin Ahmad Jalal a shopping mall. The fact that ya daura yarshi me twelve years kan kafada dan ta dauko abu kuma har sai da aka saka a newspaper.

"Babanki yana wanka" a cewar mahaifiyarta dake kokarin karbe jakanta. Cire mata gyalen tayi da kuma jacket dake jikinta. Dan tasan ta gaji. Sai da ta tabbata jeans da shirt ne a jikinta kafin ta kyalleta sannan ta kara karfin heater.

"Omg! Can't believe it I thought he was kidding ashe dagaske yake zai zo. Wait ya kawo min tsaraba?" Jannah ta fara tsalle cike da murna. Rabonta da tasa mahaifinta a ido kwana uku kennan. Yaso yaje da ita Singapore amma mahaifiyarta ta hana gudun missing classes dinta.

"Ban sani bafa" Mahaifiyarta ta boye murmushinta. "Mom stop it, please! Tun last three days yake Singapore and na bashi list dina fa" Allah sarki Jannah har hawaye ta farayi sai kuma ji muryar mahaifinta

"Jannah?"

"Daddy!..." Tayi tsalle ta rungumeshi. Har ckin ranta take murnan dawowanshi. Kin sake shi tayi na tsawon lokaci dan ji take kamar mafarki. A iya saninta idan yaje business trip sai yayi five days ko one week ko kuma abin da yafi haka kafin ya dawo. To amma da yanzu yayi three days kacal, kasa dena murmushi tayi

"Jannah irin tsalle haka?" Babanta ya murmusa yana me kara rungume yar shi. Yasan yarshi gwanan shirme ce. Kuma har ga Allah yayi bala'in kewarta har resheduling meetings dinsa yayi dan ya dawo ya sameta. Hankalinshi ya mugun tashi ranar da ta kirashi take kuka wai kuliyarta ta mutu.

"Dad I've missed you" ta zumbura baki tana so yin kuka. "Me too Angel can't wait to cuddle with you" ya kara murmushi yana me sumbatan goshinta.

"Haba bawan Allah ya zaka fito haka ko bushewa fa jikinka bai yi ba" Sumayya ta fada tana goge mishi kai da towel. Ta rasa waye babba cikin shi da Jannah.

"Come on wifey da jallabiya fa a jikina" ya kashe mata ido ganin Jannah ba ta kallonsu. Yasan sarai me take nufi amma neman fada yasa ya chanza maganar. "Daddy mom is jealous" Jannah ta furta idonta mak'alle kan TV. Kamar ba dasu take yi ba.

"What?" Sumayya ta rufe bakinta da hannu. Tana mamakin dukansu biyu. "Just admit it Sumy you're jealous" Mijinta ya maimaita cikin muryan wasa. "Jealous of my own daughter? You gotta be kidding me Al'ameen". Duk da tasan cewa wasa suke yi bai hana ta jin kunya ba. Kafin suce kobo sai ga pillows suna flying a direction dinsu.

**

"Dad I didn't tell you yau Mr Francisco yana kiran roll yazo kan sunana tsananin sa ido har yasan I was absent yesterday. And guess what? Har da tambayan reason." Firdausi ta fada tana stuffing bakinta da cinnamon rolls. Harara Sumayya take mata ganin yanda take magana da abinci a bakinta.

"Sai kikace?" Daddy ya tambaya showing interest a maganar. Yana ko karin fahimtarta. "Nace mishi I was down with flu" ta fada with pride kamar abin arziki. Tasan da mahaifiyarta ta fada wa yanzu zata murde mata kunne amma dake mahaifinta ne, sai dai ya gyarata cikin magana.

"Jannah ba kyau karya" Sumayya ta nanata babu alamar wasa a tattare da ita.

"I'm sorry mom amma shi ma ya gane ai" ta tura baki. Alhalin murna tayi da ba'a murda mata kunne ba. Ko kuma ance baza ta je shopping Saturday ba.

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now