_Ya jama'atul muslim ya kamata mu farka daga baccin da muke, make peace with everyone, people are dying... Walai this duniya is nothing, you never know we can die at any time, death awaits no one, dagaske they will come a day when you won't take shower yourself but you will be given one, you won't wear clothes yourself but someone else will do it for you, you won't go to masjid on foot but four people will take you there, you won't pray salah buh a salah will be prayed upon you, my sister my brother please wake up Kullu nafsin za'iqatul maut, zaki mutu! Zaka mutu! Zan mutu! When?  Only Almighty Allah knows mu daure muyi amfani da lokacin mu wurin bauta ma ubangiji tun kafin mutuwa ta riske mu, nobody knows tomorrow and Allah say even if your sins reached of to the clouds in the sky, i would forgive you and I shall not mind, try to seek forgiveness from Almajid, It is so scary death come to us when our imaan is low, let's pray that Allah subhanawu wata'ala takes us when he is most pleased with us, may La'ilah ha'illallah muhammadur Rasulillah be our last word on earth Amin_
     _We love our dear ones buh Allah loves them most, kuka, ihu, aljanu bare tab'a dawo mana da wanda muka rasa ba is better for we guys to stop it, if we can't pray to show love towards them let's just keep calm it will be better, Allah ya k'arba rayuwan mu cikin sauk'i, ya bamu hak'uri da juriyan wad'anda muka rasa Amin_

Sosai al_umma suka cika gidan kowa ya bud'i baki alkhairin sa yake fad'a ba sharri ba, mota guda na marayu aka kawo sukai gaisuwa, sosai yaran ke kuka dan yadda suka bala'in sabawa dashi, Aunty Safwah suka nema a nuna musu aka basu hak'uri dan du a bakin Safwan suka santa.
     Haka dai ranan aka kasance cikin jimami, amma tuni an soma bincike akan abun ga Umaima da ake sa ran inta tashi komai zai zo da sauk'i tai loosing memory.
Sai k'arfe goma na dare Kadsah ta tashi, take komai ya dawo mata runtse ido tai tana tuna last moment nasu, hawaye ne masu zafi suka kwarinyo mata ta k'ank'ame hannun Safwah dake baccin wahala, ta dad'e a wannan halin kafin ta tashi taje toilet ta d'auro alwala ta sauke sallolin dake kanta ta koma sujud ta dinga masa addu'a sosai.
      Sanda ta soma jin jiri ta d'ago ta jingina da gado ta lumshe idanun ta tana hango kyakkyawan fuskan sa da kullum ke cike da annuri, tana wannan halin Safwah ta soma wani irin jijjiga cike da tashin hankali ta soma jijjiga ta amma ina, ficewa tai da gudu tai part d'in Granny nan taci karo da Suwayd, hannun sa ta soma ja dan sam ma ta kasa magana har suka je d'akin.
A matuk'ar firgice ya d'auke ta ya fice kan ya tada mota ya k'ira Dr Alkasim, suna zuwa akai emergency ward da ita ganin ya kasa aikata komai akai waje dashi, du taimakon daya dace aka mata then aka fito da ita zuwa d'akin hutu.
     A daren Mammy tazo dan ita zata zauna da ita, tsayin kwana uku kenan har kuma lokacin Safwah bata cikin hayyacin ta, ga Kadsah ma an rasa gane kanta kullum bata da aiki sai kuka, gashi ta k'aurace ma cin abincin zuwa lokacin sanda tasha ruwa leda hudu.
A rana na hud'u aka sallamo ta sandai bata umm ba umum sai bin mutum da ido, du wanda yazo mata ta'aziya sai dai ta bisa da ido gashi dayawa anzo mata, dan _Beelkeey Shuwerh fans group_, _Miemiebee_, Mhiss_B_Hal_, _Ina da shi_ ma duk sun zo.
       Tsoro sosai ta soma bawa kowa da tsananin tausayi dan gara Kadsah ita tana yin kuka at least yana rage mata wani abun, Safwah kam babu kukan  sai zugi da d'acin zuciya.
Ammey ko kallon Safwah bata yi saboda tsananin tausayi musamman inta tuna lokacin data rabu da nata d'an uwan abin alfaharin ta though shi ba mutuwa ce ta raba su ba, to Safwah fa shikenan ya tafi ya barta da kewa ita dashi sai a darus salam.
    Haka suka kasance har ranan sarakan bakwai, ranan Kadsah tayi kuka like never before, a wurin zaman ne wani mutum yazo bayan yaci abinci ya k'oshi ya mik'a ma su Abuh hannu aka gaggaisa fuskan shi fal annuri wane ba gidan mutuwa yazo ba, koda ya mik'e zai tafi bud'an bakin sa sai cewa yai ”Allah ya maimaita mana Alhaji wallahi munci mun k'oshi, rabon da naci abinci haka har na manta....” tass kake ji Suwayd da zuciya ta ciyo ya d'auke sa da mari, ya d'aga hannu da niyyar sauke masa wani Daddy yai saurin tare sa.
    Abuh kam du yadda yaso kasa daurewa yai sanda ya zubar da kwalla jin mummunar fatar da wannan bawan Allah'n yayi masa kawai dan ya samu daman cin abinci.

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now