Episode 36

1.8K 106 8
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
   . ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

Wattpad @Shuwerh Beelkeey22

        *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*
_The page goes to *Nana Khadija*, *Ummu Islam*, *Ummu Unais*, *Sweetheart Leesha*, *Zainab Chinade*, *Darling Faheeta Ummu hani*, *Rukaiya Muhammad*, *Ayeesha*, and *Amira dalla 2*, really appreciate the love and supports I luff You guys fisabilillah wallahi_

Episode 36
13_1_2019
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Basu dad'e ba suka isa aka wuce da ita emergency ward dan bata taimakon daya dace, dakyar aka samu dawowan numfashin ta akai du abinda ya dace then suka wuce da ita d'akin hutu.
      Zama Arif yai ya rik'o hannun ta ya had'a da nasa yana kallon fuskan ta dake nan looking so pale, ahankali kalamun ta na daren jiya suka soma dawo masa akai _Ya Arif na rok'e ka dan Allah kayi hak'uri, wayyo zaka kashe ni please have mercy on me, i beg of you dan Allah ka kyale ni! Ya Suwayd save me_.... daga haka bai sake jin komai daga gare ta ba, runtse ido yai da k'arfi yana dana sanin abinda ya aika ta.
Dafa san da Suwayd yai yasa ya d'ago, "Ya haka ta faru? Don't you see she is young?" Cewan Suwayd fuska a had'e.
     Sunkuyar da kai kawai Arif yai dan baima san miye ne zaice ba, kallon agogo yai ganin sha biyu da rabi zuciyan sa ya buga da k'arfi "Am going kai *PureLamp* is sick".
Fad'a masa abinda zaiyi inta tashi yai ya wuce da sauri, yana fita Dr Alkasim na kawo kai da sauri yace "Suwayd please we really need your help!"
     "Help?"
"Yeah please let's make it pass bamu da lokaci".
"Am sorry but am not going anywhere! My wife is sick so I have to take care of her".
      "No please dan Allah karka ce haka! That family you are seeing there really need your help and...." Ko rufe baki bai ba wani mutum yazo yana kuka ya k'ank'ame k'afan suwayd din yana neman taimakon sa, jikin sa ne yai mugun sanyi kawai suka wuce dan taimaka wa matar bawan Allah'n data kasa haihuwa za'a mata Cs.
Bashi ya samu kansa ba sai k'arfe uku and masha Allah the Cs went successfully, takura sa Dr Alkasim yai sukayi sallah anan sannan yabar sa ya tafi...
       Safwah k'arfe goma da rabi ta farka da mugun zazzab'i da ciwon kai, jikin ta banda ciwo ba abinda yake saboda yanda yai mata tsami, ga mahaukacin yunwan da take ji wane taci babu dakyar ta daure tana kuka ta janyo wayanta ta soma k'iran sa, sandai the saddest thing is har three missed call bai d'aga ba.
Jifa tayi da wayan ta fashe da kuka mai ban tausayi, sanda tayi mai isanta ta lallab'a ta sake zuwa tai warming kanta  ta dawo ta zura gown mara nauyi ta kwanta jikin ta na kakkarwa.
     Sallama Sayyada tata yi amma shiru ba respond dan haka ta wuce part ta Safwah kai tsaye, nanma sallaman tayi shiru kawai ta wuce bedroom ta safwah'n da take tsammanin tana ciki.
Da sauri ta k'arasa gano ta kwance tana rawan jiki "sweetheart are you alright? What's wrong?" Tai questioning nata a rikice ganin yadda idanun ta suka kumbura kuma still she is crying so hard.
      Ganin tana k'ok'arin mik'ewa ta kasa ta taimaka mata tana mai jin tausayin ta though bata san maye ne ya faru ba, k'aran azaban da Safwah ta sake ne tana yarfe hannu yasa hankalin ta mugun tashi, du kanta ma ya kulle ta rasa abin yi abinda kawai ya iya yazo bakin ta shine "zaki ci abinci?" Gyad'a mata kai kawai tai dan batajin zata iya furta ko wani kalami.
Juyawa tayi da sauri dan sama mata mai zata ci, hango kaman anjera abinci a dinning tai saurin nufan gurin, without any hesitate ta kwasa a babban plate ta koma dak'in, a zaune ta samu Safwah'n ta jingina da fuskan bed sai cije baki take.
     Stool taja ta daura abincin akai then ta soma feeding ta dakan ta, Safwah data mugun tsanan cin abinci mai sanyi batasan when ta bud'e ciki tana ci ba wane wadda ta shekara bata ci ba, da kallon mamaki kawai Sayyada ta rik'a binta ganin ita ba gwanan cin abinci ba yau ta zage sai ci take, tass ta cinye komai ba ragi ta kora ruwa ta kwanta nan bacci ya sake taken over nata.
Zama tayi tana staring ma beautiful face nata ganin zaman won't work ta kwashe kayan taje ta wanke, ta gyara mata ko ina nan take kuwa komai ya d'au haske, turen wuta mai dad'i ta zuba a bona ta kunna sannan ta sake komawa d'akin ganin ko ta farka.
      Ganin still bacci take ta yanke solution d'in yi mata girkin rana, had'ad'd'en jalof rice and papa meat tai sai zob'o.
Tana shirya komai a dinning Safwah ta fito tana k'ok'arin saita tafiyan ta, tsayawa kallon ta Sayyada tayi from head to toe, ita ai sai yanzu ta fuskan ci inda matsalan ta dosa dariya take so tayi amma ta moze, k'arasa jerawan tai ta k'araso kusa da Safwah'n ta bata hak'uri kan abinda ta faru jiya.
    Murmusawa kawai tayi ta nuna mata komai ya wuce then suka shiga hira, jin k'iran sallah yasa suka tashi suka sauke farali suka ci abinci suka cigaba da hiran su, du attention ta Safwah bata kan Sayyada saboda bak'in cikin ina Suwayd ya tafi, kowa zataji a wannan rana mijin sa na zama dashi yai ta lallashin sa amma banda ita, shikenan ya dena son ta dan ya samu abinda yake so, hawaye ne suka zubo mata tai saurin kai hannu tana sharewa kar Sayyada ta gani, amma ina ta makaro dan tuni take kallon ta.
Sunkuyar da kanta tayi k'asa abin na cigaba daci mata rai she just can't help har sanda ta fashe da kuka mai cin rai,ita du tunanin ta ma bata yake yana can yana shaye_shaye,  janyo ta Sayyada tai hugging her so tight tana calming ta, sanda tai mai isanta tai shiru breaking hug d'in Sayyada tai ta rik'o hannunta ta soma magana in sorting tone "haba mana Baby me haka? ki fad'amin akan ki aka fara ne?"
    Girgiza kai tai tana hawaye tace "amma fa Sis tunda ya fita bai dawo ba! Kuma na k'ira sa baya picking".
"Shine dalilin kukan?" Gyad'a mata kai kawai tai.
    Murmusawa tayi ahankali tace "kibar kukan haka nan zai dawo! Ki bari in kika ji dalilin sa na k'in picking call naki da dad'ewa bai dawo ba sai ki yanke hukunci, don't just judge him with what you don't really know!"
"Tohm" ta ansa tana murmushin da bai kai zuci ba.
     Har k'arfe biyar suna tare kafin Sayyada ta mata sallama ta tafi, d'aki kawai ta wuce ta fad'a toilet tai wanka danjin dad'in jikin ta, koda ta fito hoda da lipstick kawai tai applying ta nemi gu ta sake kwanciya, wayan nata data yasar d'azun ta d'auko tana son k'iran sa amma ta kasa.
Suwayd nakan hanyan sa Granny ta masa waya lallai tana son ganin sa, du yadda yaso bata excuse tak'i dole ya juya kan motan tasa, cilla wayan nasa gefe yai batare da ya duba missed calls da aka masa ba, kafin yaje gida anyi la'asar dan haka ya soma shiga masallaci yai sallah.
      Yana fitowa gidan ya shiga kai tsaye, ko part d'in su Mammy baije ba ya wuce wurin Granny, bayan sun gaisa ta masa bayanin dalilin neman san da take kan maganan karatun su Safwah.
Wane zaiyi kuka yace "amma Granny ko a waya ai zamu iya wannan maganan!"
      Make sa a k'eya tai tace "nasani ganin ka nake so nayi shiyasa, dagani ma baka ci abinci ba".
Mik'ewa yai yace "ni na tafi zanci a gida!"
      "Wannan kuma baka isa ba dole ka zauna kaci, zamuyi magana ma kan Safwan da Kadsah I think a had'a su suma kawai hankali na zaifi kwanciya".
"Ya ilahi dan Allah Granny ki kyale ni wallahi a gajiye nake! Maganan Safwan da Kadsah kuma sa'anni ne baki ganin za'a samu matsala?"
     "Bawani matsala nama tsayar da lokaci k'arshen watan nan so kai na soma fad'awa kafin na fad'awa iyayen ku!"
"Allah yasa hakane yafi alkhairi, now am going".
     "Amin, bara fa ka tafi ba sai kayi sallah can't you see an kusa kira".
Jin rai a b'ace tai maganan yasa yaja bakin sa yai shiru, yana ji ta kira su Ummy tasa aka kawo masa abincin, gudun b'acin ranta yasa yaci kadan ya ture, jansa tata yi da hira har aka yi k'iran sallah daga masallaci kuwa ya gudu sai kira yai ya fad'a mata.
    Saida yai sallah'n isha ya shiga gida, gun Zee ya soma shiga ya tarar da ita sam ba'a nitse ba, yana sallama ta sake kyakkyawan ajiyan zuciya ta k'araso ta fad'a jikin sa, hugging ta yai na 'yan seconds kafin ya zame ta suka k'arasa ciki, kan two seater suka zauna ta soma jera masa tambayoyi, murmushi kawai yai yace "an k'ira ni urgent ne sai yanzu na samu kaina am sorry".
"Amma meyasa baka d'aukan wayan ka?"
    "Na manta a mota".
"Oh tohm sannu Baby!" Mik'ewa tai ta kawo masa kunun aya mai sanyi knowing that is his favorite.
    "Awwwn thnak you Very Own!" Shan abin sa ya soma yi yana ta zuba mata santi though hankalin sa nakan *PureLamp* tasa, nan take fad'a masa Daddy'n ta yana neman alfarman ya barta gobe zasu je sudan ziyaran 'yan uwa, kallon ta yai sosai kafin ya d'aure fuska kai tsaye yace "bazaki je ba!"
Maimakon yaga ranta ya b'aci saima murmushi da take abin ta, rik'o hannun ta yai ya had'a da nasa yace "wasa nake miki Sweetheart muje mu shirya miki kayan ki".
      Kallon sa itama tai tace "Allah Baby indai baka so karka damu basai naje ba".
"Not at all Very Own! Am just kidding".
Cike da farin ciki ta k'ira Daddy'n nata ta shaida masa an barta, daki suka wuce ya tayata ta shirya kayan ta then ya kashe ta da good night kisses ya wuce wurin Safwah.
Gaban sa na mugun fad'uwa ya shiga part d'in nata, dakyar ya daure ya shiga cikin bedroom d'in nata, ganin tana sallah ya sake ajiyan zuciya ya wuce toilet.
      Tana idar da sallah ta nad'e sallayanta ta ninke hijab nata ta miyar ta ajiye then ta nemi guri tai kwanciyan ta, bata dad'e da kwanciya ba ya fito d'aure da towel a k'ugun sa sai k'arami yana tsane yalwataccen suman sa, murmusawa yai ganin ta kwance ya k'arasa gadon ya zauna a gefen ta.
K'ok'arin d'ago ta ya soma yi ta fuzge da k'arfi har tana fama ciwon ta, can gefe ta matsa wane wadda ke tare da aljani, mik'ewa yai ya shirya ya haura kan gadon ya janyo ta gaba d'aya ya k'ank'ame, du yadda take fighting kwatan kanta ta kasa dole ta matse sa ajikinta ta cigaba da aikin kuka, sanda tai mai isan ta ya d'ago ya soma rarrashi.
       Zamewa tai daga jikin sa ta mik'e zata fice daga d'akin yai saurin tare ta yai locking k'ofan ya zare key d'in, tsugunawa yai har k'asa gwanin ban tausayi ya rik'o both hannayen ta ya had'a da nasa a nitse ya mata bayanin du abinda ya faru dan ya lura Har kallon zargi take binsa da, tun kan ya k'are ta zame ta fad'a jikin sa, rungumar ta yai sosai ahankali yace "kinci abinci?"
Girgiza masa kai tai meaning no, jin jikin ta da zafi ya janye ta daga jikin sa suka k'arasa gadon, wayan sa ya cire ya k'ira Zee yace ta kawo masa abinci part d'in Safwah.
    In less than five minutes sai gata ta kawo ganin kiran ta cikin Wayan sa ya mik'e ya fita ya karb'o ya dawo, ci suka yi suka k'oshi yaje part d'in sa ya d'auko pain killer da man zafi ya dawo.
Ganin ya soma kwaye dogon rigan dake jikin ta hankalin ta yai mugun tashi, a rikice ta soma ture hannun sa tana rufe santala santalan cinyoyin ta da suka bayyana.
      Kallon ta ya tsaya yi baki sake kafin yace " *Flower* stop it please you are sick, magani ne kawai zan shafa miki".
"O'o ni bana so" tai stating tana turo baki.
    "You want it in a trouble way ko?"
"Nahhhh!"
      "Yauwa 'yar albarka bari na shafa miki ahankali kinji?"
With nod kawai ta basa ansa ya bud'o man zafin ya lakato yaja right leg nata ya shafa, ihu ta sake ta soma ture hannun nasa jin yadda yake murza mata cinyan, hannu d'aya yasa ya rik'e both nata then ya cigaba da murmuza wa, ihu Safwah ta shiga yi tsakanin ta da Allah amma sam yak'i ya kyale ta har sanda ya tabbata ya ratsa k'afan, zuwa lokacin ko ihun ta kasa sai hawaye.
     Hannu yakai ahankali yana share mata hawaye yana rarrashi amma tai banza da shi, ganin haka yaja d'aya k'afan itama, saboda azaba bata san sanda ta soma jera masa Allah ya isa ba har ya gama, tissue yaja ya goge mata hanci da tears d'in da suka kasa tsayawa sannan ya d'auko pain killer da ruwa nanma dakyar ya samu tasha.
Janyo ta jikin sa yai ya rungume yana rarrashi, ita kuwa sai ajiyan zuciya take saukewa haka har bacci ya d'auke ta, gyara mata kwanciya yai ya tofe su da addu'a shima bacci ya d'auke sa.
       Da asuba koda ta tashi ko kallon sa batayi ba, suna idar da sallah ta koma tai kwanciyan ta abinta ko morning azkar bata tsaya sunyi ba, sanda ya gama komai ya jona ta shima baccin ya d'auke sa.
K'arfe goma ya tashi yai wanka yaje ya shirya musu breakfast, Koda ta farka taga baya nan kuka ta shiga yi ahakan yazo ya same ta, a rikice ya soma jera mata tambayoyi.
     K'in kulasa tai ta wuce toilet abinta, bata wani dad'e ba ta fito dan karya gudu, da kansa ya shirya ta duk da sai shan k'amshi take.
Breakfast suka je sukayi ya wanke kwanikan da suka b'ata ya gyara mata falour'n nata though ba wani dirty yai ba then yaja hannun ta suka wuce part d'in sa, kwantar da ita yai ya d'aukan mata diary nasa ya koma part d'in ta, gyara mata bedroom d'in yai yaje suka gaisa da Zee ya koma.
     Kwantawa yai ya jawo ta jikin sa teasingly yace " *Amirul Qalb mai wannan zaka...." Jifa tai da diary d'in ta toshe masa baki cike da kunya.
Wane zata yi kuka tace "Haba mana *Habibi* You know this is not fair!"
         Murmusawa yai ya sake cewa "Ka tashi ka fita bana son ganin ka! Kuma wallahi sai Allah ya saka min mugu kawai!...”
    Turo baki tai ta soma k'ok'arin tashi dan sai daga baya ta soma tuna kallan rashin hankalin data dinga yi, matse ta yai yadda bazata iya kwacewa ba yace " *PureLamp* na raguwa!"
"Allah ni ba raguwa bace".
      Dariya yai yace "to bari naga ko ba raguwan bace" jin yanda ya soma shinshinata ta soma bashi hak'uri a rikice.
K'in jinta yai ya tura hannun sa cikin rigan ta jin haka ta fashe masa da kuka, da sauri ya nutsar da kansa ya soma rarrashin ta.
      Haka ranan suka kasance tare sai hiran soyayya yake mata har k'arfe hud'u yai, abincin da Sayyada ta kawo musu suka ci then ya shirya ya tafi kai Zee airport cause flight na k'arfe biyar zasu bi.
Kaman baza su rabu har suka shiga jirgi, sanda yaga tafiyan su ya dawo ya gida.....
     
    _U might see some errors I no g*t time to edit srry for making you guys wait much love my peoples_

Follow
Vote and
Comment on Wattpad
@Shuwerh Beelkeey22

MAKAHON SO ~Blinded Love~

*'Yar Gatan Miss_B_Hal Ce*💞

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now