Yanzu duk tunanin Safwah bai wuce yadda zata fad'awa Safwan damuwan ta ba, amma ta rasa hanyan da zata bi ta fad'a masa saboda tsoron Ya Suwayd.

A b'angaren Suwayd kuwa k'arya yama su Abbah wai zaije duban patient Ghana, basu gano komai ba dan haka suka masa izini, kafin ya tafi Saida ya tsorata Safwah sosai wai yasa CCTV camera a ko ina inta ga dama ta fad'a zata ga mai zai biyo baya.

Tad'an samu nutsuwa da tafiyan nasa amma dai still tana d'ar_d'ar.
   Shi kuwa tunda yaje Ghana Iskanci ya dad'u har tsautsayi ya kusa auka masa ya shiga trap d'in wata yarinya, one week yace dasu Abbah zaiyi amma sai gashi da one month a hakan ma badan son ransa ya dawo ba sai dan yadda su Abuh suka dame sa da waya.

Yau Safwah na zaune a falour'n Granny sanye da black three quarter skin tight da dark pink best, kanta ko d'an kwali babu ta baza gashin ta a bayanta tana playing favourite game nata Subway a wayan ta, sai ihu take kaman k'araman yarinya dan tasan monster natan haryau bai dawo ba ga Sayyid ma yaje Abuja bai dawo ba.
Ahankali sukayi sallama suka shigo jin shiru ba'a amsa su ba suke sake nanatawa for the second time but still no respond, sai da sukayi na uku kawai suka k'ara sa shigowa.
Sayyid ya lallab'a ahankali ya rufe mata ido " Ohh Granny please ki bari za'ayi gaming ina " tayi maganan a shagwab'e tana d'an buga k'afa.
   Hannun ta tasa guda d'aya da niyyar cire hannun daya rufe mata ido, " Ya Sayyid!! " tayi ex claiming da k'arfi dan karya ce bata murna da dawowan sa, ajiye wayan tayi a gefe ta mik'e da sauri tayi hugging shi tana fad'a masa how much she misses him, ahankali shima ya zagayo da hannun sa ta bayan ta hugging her back yana fad'a mata shima yadda yayi kewan ta, du anan bata kula da angry Suwayd ba.
   Shikuwa wani jarababben kishi da bak'in ciki ne yasa ya nemi guri ya zauna yaga iya gudun ruwan su.
D'agata Sayyid yayi yana juyi da ita with so much adoration yayin da ita kuma keta dariya kaman Baby.
Da fara'a Granny ta fito tana fad'in " sannun ku da zuwa mutan Ghana da mutan Abuja ",  ajiye Safwah Sayyid yayi cike da kunya ya k'arasa gun Granny yana tsokanan ta wai tabi ta damu kanta bata ga mijin ta ba, to gashi nan yaje ya tawo mata dashi.
Juyowan da Safwah zatayi idon ta ya sark'e dana Suwayd dake binta da wani banzan kallo saboda shigar dake jikin ta.
Mozewa tayi tai kaman bata san mai yake nufi ba.
" Dan uwarki wuce kije kisa hijab " ya buga wata wani shegen tsawa hakan kad'ai ya isa shaida maka yadda yake mahaukacin kishin ta.
Banza tayi masa tana k'unk'uni shikenan ya dawo zai d'aura a inda ya tsaya.
" Don't let me repeat myself " ya nanata da kakkausar murya.
Mik'ewa tayi badan ranta yaso ba ta nufi d'akin su, tana rik'e handle ta jiyo ringing d'in wayan ta and ko ba'a tasan waye dan shi kad'ai ta sanyawa wannan wak'an, cike da zumud'i ta juyo dan harga Allah ta manta da warning d'in Suwayd, tana kai hannu zata d'auka taji saukan gigitaccen marin da saida hab'o ya b'alle mata.
Sound d'in marin ne ya janyo hankalin Granny da Sayyid, har cikin ransa Sayyid ya jiyo marin amma ba yadda ya iya.
Fincikar hannun ta yayi bai tsaya ko ina ba sai d'akin su wane kayan wanki haka ya cillata, sannan ya dube ta a wulak'ance " ke mahaukaciyar inace wai? Sau nawa kike so na fad'a miki ganin ki a haka disgust me? Wallahi, wallahi, wallahi kinji nayi rantsuwa har sau uku duk sanda kika yarda na sake ganin ki haka bazan b'ata lokaci ba gurin cin bura'uban ki shegiya mai idon aljanu kawai mtsweee "  yaja wawan tsaki ya barta yashe a k'asa tana kukan fitar rai.

Sayyid ne ya shigo d'akin cike da damuwa, ahankali ya k'arasa inda take ya d'ago ta yana aiki rarrashi hanky ya ciro a aljihun sa ya soma goge mata jini dake fita ta hancin ta, dakyar ya samu tayi shiru amma yatsun Suwayd na nan tar akan kyakkyawan fuskan ta, hannu yakai gurin cike da tausayi ta soma yarfe hannu dan shagwab'a.
" Sorry princess shiyasa na damu ki bari nayiwa su Daddy maganan auren mu kowa ma ya huta, amma da zaran na soma magana saiki b'ata fuska na fad'a miki Allah zan barki ki cigaba da karatun ki kinji? "
Ita fa Ya Sayyid ya soma takura ta yanzu kullum bashi da magana daya wuce na auren su shin bare gane ita bashi take so yanzu bane!!
Turo baki kawai tayi ta had'e rai ganin haka ya ciro wayan sa ya k'ira mata Safwan yaba ta, tana k'arfa ta sake sabon kuka, ko ba'a fad'a ba yasan sarkin mugunta ne ya tab'a masa ita dan haka ya soma da rarrashi sannan suka shiga hira.

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now