K'arfe bakwai suka nufi dinning hannun Kuwaysah rik'e da na Safwah, kowa yazo banda Suwayd ahankali du suka soma cin abinci amma banda Safwah da kanta ya matsanta mata, ture abincin ta tayi ta kifa kanta a table hannun ta dafe da kanta.
       Ajiye spoon d'inta Mammy tayi ta mik'e tsam ta nufi Safwah, ahankali ta d'agota Safwah'ahn tayi saurin rungume ta ta janyo hannunta ta d'aura akan ta, cike da azaban ciwon kai da zazzab'i tace " Mammy dan Allah ki taimaka min kaina zai cire ".
Hannayen Safwah'n ta shiga bi da kallo cike da mamaki, ta riga tasan ansan tambayan ta dan haka rai a matuk'ar b'ace ta kalli Lubna tace " jeki k'iramin yayan ku ".
      " Tohm " ta ansa a nitse ta mik'e ta fice.
Da sallaman ta tashiga amma ko arzik'in amsa mata bata samu ba, cike da haushin sa ta durk'usa ahankali tace " Ya Suwayd ina kwana? " amma yadda kuka san da dutse take magana, rai a b'ace tace " Kazo Mammy na k'iran ka " daga haka ta mik'e tay ficewan ta.
       Bata dad'e da shiga ba ya shigo ya gaida iyayen nasu suka answer cikin sakin fuska illa Mammy dake binsa da kallon takaici.
" Meya faru tsakanin ka da Baby? " Mammy ta jefo masa tambayan ba wasa tattare da ita.
Shiru yayi ya sunkuyar da kai batare da yace komai ba, " dakai fa nake, mai tayi maka kayi mata wannan dukan kaman ta aikata zina? " shiru yayi again.
     Zame Safwah tayi daga jikin ta ahankali ta kwantar mata da kanta kan table sannan ta tako inda yake, tassss kakeji ta wanke shi da wani irin firgitaccen mari, bai gama dawowa daga mamakin abinda ke faruwa dashi ba ta sake tsinke sa da mari.
    Murya na rawa idanun sa sunyi jajir yayin da jijiyoyin kansa duk suka mimmik'e yace " Mam... Mammy ni.. nine fa Suwayd, ni kika mar... Mara yau da hannuki? "
D'aga hannu tayi da niyyan sauke masa wani Ummy tayi saurin rik'e hannun nata rai a matuk'ar b'ace dan ko kad'an hukuncin ta  Mammy bai mata dad'i ba
" Na mare ka, nace na mare ka ko zaka rama? Dama ai girman ka yakai shiyasa kakeji kaman ka haifi mutane, idan ramawa zakayi sai a mik'o maka charger nima ka dake ni tunda ba kanka farau ba bakuma kanka za'a k'are ba, Ummy dan Allah ki sake ni na mare shi naga matakin da zai d'auka ". 
       " Enough Mammy!! Yanzu fisabilillahi hakan da kikayi ya dace? Ki duba fa kiga agaban k'annen sa kika hukun tashi wanda sam hakan bai cancanta ba, du ma da kika d'au laifi kika  d'aura masa kinsan me tayi masa ne? Shikenan bazai hukun ta k'anwar sa ba intayi badai_dai ba ? "
     " Dan Allah ya isa haka Ummy aikin san bak'in halin sa, wallahi na tabbata batayi masa komai ba tsabar bala'i da masifa ne irin nasa da indai baiyi ba bayajin dad'i ".
Saboda tsabar tashin hankali Safwah neman rashin lafiyan ta tayi ta rasa, yau saboda itane Mammy ta d'aura hannun ta akan Ya Suwayd abinda bata tab'ayi ba, har cikin ranta taji zafin hakan saboda tasan shikenan k'ara tsanan ta zaiyi dan this is the first time Mammy ta tab'a daura hannu akan sa.
" Kinji dad'i kin had'a shi da mahaifiyar sa saiki zuba ruwa a k'asa kisha " ta tsinkayi muryan Ummy rai a b'ace.
     Rik'e hannun Suwayd tayi suka fice daga part d'in zuwa nata, suna zama ya fad'a jikin ta yana kuka mai ban tausayi, rasa ta ina zata soma rarrashin sa tayi dan haka ta barshi yayi mai isan sa sannan ta rarrashe shi inda ta samu Dakyar yayi shiru.
Su Ummy na fita ta fashe da wani irin matsanancin kuka, da sauri ta mik'e ta fice ta nufi motan su ta cigaba da kukan ta harsu Kadsah suka zo suka tarar da ita, rok'on duniya sun mata tayi shiru tak'i har suka isa school.
      Exam ta ranan kuwa kawai rubutawa tayi dan tasan ko a saraka barata samu koda five marks bane, Imran sai tambayan ta damuwan ta yake amma tak'i fad'a masa.
Har aka tashi suka koma gida kuka take gashi zuwa lokacin jikin ta yayi tsanani, kwanciya kawai tayi saboda ciwo.
     In tak'aice muku sati biyu suka d'auka suna Exam har suka gama har lokacin kuma bata dawo saiti ba dan ko kula ta Ummy batayi, haka shima sam Mammy ta fita daga harkan sa ba kalan hak'urin da bai bata ba amma tak'i sauraron sa.

Yau ya kama Sunday, Ummy na zaune Safwah ta shigo duk ta fita daga hayyacin ta, tausayi ta bawa Ummy'n sosai inda ta kasa share ta a lokacin, hak'uri ta bawa Ummy'n sosai ta nuna mata komai ya wuce, a ranar har hira sukayi sosai gwanin sha'awa.
Ranar shima ya samu Mammy ta yafe masa.
      K'arfe hud'u Granny ta aiki Safwah bayan layin su, tana dawo wa ta jiyo waya muryar 'yar budurwa tana mata magana, tsayawa tayi tana k'are mata kallo sannan tace " Lafiya dai ko? "
" Lafiya dan Allah Suwayd zaki kirawo min " tayi maganan tana murmusawa.
" Kece Zee? " kawai ta tsinci kanta da tambaya.
" Eh nice " tayi maganan tana fad'ad'a fara'an ta.
   Nan take duk wani annurin fuskan Safwah ya b'ace saboda kishi a masifance tace " andai ji kunya wallahi mace har mace amma ki kwaso k'afa wai kinzo gidan su saurayi, saurayin ma da ba sonki yake ba to wallahi ko zaki mutu yau in baki ganshi ba sai dai ki mutu dan bazan kira shi ba Mtsweee aikin banza kawai ".
     Juyawa tayi zata shiga idanun ta sukayi mummunan gani, ko lura da Ya Sayyid dake bayan Ya Suwayd batayi ba saboda rud'u.
" Lallai Safwah yanzu rashin kunyar taki harta kai ki kalli matar da zan aura ki fad'a mata magana? Bata hak'uri kafin ranki yayi mummunar b'aci ".

Sunkuyar da kai tayi zuciyar ta na tafasa saboda tsananin kishi hawaye kam kamar an bud'e lalataccen tap, ya zama dole ta bayyana masa sirrin zuciyan ta she can't hide it anymore, barata jure ganin Zee ta kwace mata shi ba.
       Saida tayi gathering courage ta d'ago tana kallon cikin idanun sa yadda zaifi yarda da abinda zai fito daga bakin ta tace " Ya Suwayd ina son k....... "

_Den den guys do you think zata fad'a masa? Wat will be his reaction? Me Zee zatayi akai? Sayyid fa? Mai zai faru dashi?_
     *One word for this episode!!*

Follow
Vote and
Comment on Wattpad
@Shuwerh Beelkeey22

MAKAHON SO ~Blinded Love~

*'Yar Gatan Mhiss_B_Hal Ce* 💞

MAKAHON SO _Blinded Love_حيث تعيش القصص. اكتشف الآن